Showing 27001 words to 30000 words out of 87292 words

Chapter 10 - Duk Kyan Takalmi Complete Hausa Novel

Eeshat   

16 Jul 2026

293

fara zama
kurma har a ambaci aisha farida inji ba daidai
ba. Babu abinda zance miki tunda boye boye
kike yi min tun yanzu. Sai dai kiyi hankali da
mutane, ki kuskuri bin shawarar batattun
kawaye, ki rike mairaici da talaucinki. Ta juya
ta fice ta rufo mana kofa. Na sulale na kwanta
na dora hannu aka ina juye juye, sai dai ban
fasa karanto innalillahi wainna ilaihir rajiun ba.
Yadda naga rana haka naga dare, barci ya
gagareni. Fargaba da tunanin haduwata dasu
uwani ta gallebe ni. Haka na kwana ban rintsa
ba saboda tashin hankali, don haka da asuba
kiran sallar farko na mike na shiga bandaki
nayi wanka, duk da sanyin ruwan ban damu da
saina dumama ba, na fito nayi sallar asuba na
kakaba kayan makaranta. Na dauki jakata na
dauko biro da takarda na rubutawa abida
wasika na ajiye takardar a bude akan
tabarmata yadda zata gani daga shigowarta.
Na fita daga dakin ina sanda tamkar barauniya
nayi sauri na fice, da yake kofar gidan a bude
take maza masu zuwa masallaci sun bude. Na
rufe fuskata saboda kada inci karo da mazan
gidanmu, duk da banji motsin fitowar yayana
ba, daga dukkan alamu kafar ta matsa masa
da ciwo tunda bai fito sallar asuba ba, dan
baya fashi in dai lafiyarsa kalau. Sai nayi ta
tafiya da kafata sabida rashin babura
kasancewar gari bai waye ba duku duku ne. Na
dade ina takawa da kafata sannan Allah Ya
jeho min mai babur na hau, mun dade da fara
tafiya ba tare da nasan inda zance ya kaini ba.
Ya sake tambayata malama ina zan kai ki? Da
farko nace masa asibitin aminu kano, har
munyi nisa na canza shawara nace ya kaini
jakara, umguwarsu ummi wato gidan iyayenta.
Muka isa kofar gidan na sauka daga kan acaba
sannan na biya shi kudinsa. Abinka da cikin
gari 'yan gargajiya basu san baccin safe ba
kowa ya tashi ya shiga safgoginsa. Mai kosai
ta ta fara suya, masu waina suna danawa.
Haka masu koko da masu shayi da biredi sun
fara tafasawa. Duk inda ka waiga yara ne
dauke da 'yan kwanuka a kansu an aiko su
sayan abin karin kumalllo. Na shiga cikin
gidansu ummi cike da fargabar abinda zanje in
tarar, ummin na iske a tsakar gida ita kadai ta
saka buta a gaba da alama alwalla za tayi,
tunani da damuwa sun hana ta sukuni. Ta
buga tagumi kamar mai tunani yayin da
idanuwanta sukayi luhu luhu. Tayi matukar
firgita data daga ido ta dubeni , ta cika da
mamakin ganina a daidai wannan lokacin. Ta
fada cikin firgici aisha umar lafiya? Sai na fara
zubar da hawaye shar shar shar daga
idanuwana. Ta mike tsaye da sauri taja
hannuna zuwa dakin da take kwana, a cike
yake da yara daga dukkan alamu kannenta ne,
yara 'yan kuci kuci da masu dan wayo.
Kowannensu barci yake da munshari yayi da
zarnin fitsarinsu da warin daudar jikinsu suka
daki hancina. Kamar inyi amai, na dai daure na
zauna akan wata dakwalkwalalliy ar katifa da
ummin take kwana don naga 'yarta a shimfide
a gefe. Anan tace in zauna bari taje tayi alwala
tayi salla sai tazo mu zauna. Kallonta kawai
nakeyi tamkar gunki na kasa magana, na dubi
yaran da suke linkaya a cikin fitsari babu
abinda ya dame su. Naji dama nice su nake
linkaya a cikin fitsarin nan da irin wannan
rayuwa da na jefe kaina. Ba jimawa ummi ta
shigo sanye da hijabi da alama ta idar da
sallah ko addua batayi ba sabida rashin
mutuswar dake tattare da ita. A firgice ta shigo
tana sauri kamar zata ci da kai, ta goya 'yarta
duk da himilin fitsarin da ta ci a napkin, zarni
kwar. Tace in taso mu tafi gidan malam. Na
mike da sauri muka fice ba tare da ta leka
dakin mahaifiyarta tayi mata sallama ba. Tafiya
muke fankam fankam tamkar fatake, muna tafe
muna tayar da kura kamar shanu, mu dukanmu
hankalinmu a tashe. Na juya na dube ta nace
ummi malamin nan kuwa yana da gaskiya?
Nifa har yanzu banga komai ba. Ummi ta tabe
baki tace uhmm ke dai bari. Ai shiyasa nake so
muje mu ritsa shi kafin ya gudu, macucin
banza. Kinsan mijina ya sake ni kuwa? Korar
kare yayi min fa. Na zabura na dafe kirji nace
au daman kinsan macuci ne kika kaini wurinsa.
Tace ke dai muje muji abinda zai ce mana. Na
fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun.
Allah ba Ya dorawa bawanSa abinda ba zai iya
ba sai dai bawa ya dorawa kansa. Ina zan
sami himilin kudin da na ranta in biya masu
shi, ummi yaya zanyi? Ummi ta dubeni a
fusace tace to ni kinsan irin zaryar da ake yi
min a gidanmu saboda bashi? Ke dai kawai
Allah ya rufa mana asiri. Na fusata nace babu
wanda ya taba saka ni a tozarci da tashin
hankali a rayuwata irinki. Ta harare ni tace dan
Allah aisha ki rufe min baki, gara kema baki
aure shi ba balle ya sake ki, nifa har da goyo,
na zama bazawarar karfi da yaji. Haka dai
muka tafi muna ta fada a hanya kamar zamu
cinye kanmu a cikin bus. Tana jin haushina ni
har nafi jin haushinta fiye da malamin ma.
Muka iske shi a zaure yana ganawa da wasu
guda biyu da alama hamshakan masu kudi ne,
daga ganin motar da suka zo da ita da kuma
kayan da yake jikinsu. Malam yana ganinmu
sai ya bata rai, bai amsa gaisuwarmu bai sai
bakinsa ne suka amsa. Muka wuce jikinmu a
sanyaye zuwa cikin gidan, da kyar daya daga
cikin matansa ta bamu tabarma muka zauna
sai wani irin kallon banza suke yi mana dan
suna suyar dakwalen kajin da aka karba daga
wajen mutane na sadaka amma suke juyewa a
cikinsu babu wata sadaka. Shi da iyalansa sun
zama tika tika saboda da cin kaji da raguna da
suke karba da sunan za'a rabawa almajirai. Na
zunguri ummi na nuna mata kajin da ido, ta
gyada kai ta fada a hankali tace eh kudinmu
ne, ai yau sai na masa rashin mutunci. Can
malam ya shigo ko kallonmu baiyi ba ya wuce
dakinsa, yayin da matarsa daya ta dinga
wucewa da abinci kala kala tana kai masa,
kamar shayi, kaji soyayyu, wainar kwai da
biredi. Mu dai muna zaune muna kallon ikon
Allah. Su kayi kasonsu a faranti yara da manya
suka dauka kowa yana ci babu ko sala daya da
suka bamu. Malam yaci ya gyatse, yazo ya
wuce ya shige wanka. Ya fito ya shiga daki ya
fesa kwalliya da farar shadda mai kyau sannan
yazo ya wuce ciki daki in da yake ganawa da
baki. Sannan ya aiko matarsa yace ta kiramu.
Muka shiga muka iske shi a tsaye a tsakiyar
dakin, muka sake gaishe shi ya amsa a
gaggauce. Yace daman yau mu kayi daku zaku
dawo? Haushi ya kama mu, sai ummi ta kalle
ni, nima na kalle ta sai ta murguda baki tace
yau ne laraba ko? Kuma yau kace mu dawo. Ya
kalli agogo yace kuma ce muku nayi kuyi
sammako? Ummi ta fada a fusace, kamawa
tayi ka ganmu yanzu kasan ba lafiya ba. Ni dai
ina zaune a lungu nayi kuri ina kallon irin
wannan damfara kiri kiri, a lokacin da zai karbi
kudinmy yana fara'a yanzun da muka zo karbar
aiki rai ya baci. Ummi tana durkushe tana
kokarin sakko da goyonta. Sai yace ba sai kin
sauke goyonki ba yanzu zan sallame ku akwai
inda zanje don sauri nake yi. Ummi tace ko
yanzu zaka sallame mu ai na sakko da 'yata
tasha nono ko? Tunda ta farka tana kuka. Yace
meye ma yake tafe daku? Ummi ta waigo ta
sake dubana tace kinji ya manta ma. Saina
sankare a zaune na tabbatar mun fada hannun
mayaudati kamar yadda kawayena khadija da
maryam suka fada. Ummi ta sake cewa malam
gaskiya komai ya kwabe tsakanina da mijina,
har ya sake ni. Ga kawata ma taji shiru bai zo
ba. Yace kuje zan bincika naga abinda yake
faruwa, amma aiki dai na gama. Ummi tace
wanne bncike kuma, kai da ka mance abinda
muka fada maka. Ya zazzare mata ido yace ke
ba'ayi mana tsiwa ana kibi a hankali. Ummi ma
ta zare masa ido tace tsiwwa ko zance
gaskiya? Ni dai ba zan gidan nan ba sai an san
abin da za'ayi, kudin da muka biya a banza
kenan, bashi muka ciyo muka kawo maka.
Aisha farida kiyi magana kyayi shiru. Na fada a
sanyaye mai zance ummi? Ya jawo wata jakar
leda a fusace sai ga daurin rubutu kashi kashi,
ya miko min daya ya mikawa ummi daya, ya
sake kwance wata ledar ya miko min laya daya,
ya mika mata daya. Duk iri daya ce. Yace kuje
kusha rubutun nan a tsaye, sannan ku kasance
layan nan a jikinku sai kuyi kokari ku hadu da
mazan da kuke so, ku tambayesu duk abinda
kuke so daga gare su zasu yi muku. Ummi ta
karba ta tabe baki tace mu fa ba wani abu
muke nema a wajen mazan ba illa soyayyarsu.
Yace to ai haka nake nufi ko soyayya ko kudi
duk zasu baku. Na zuba abubuwan daya bani a
cikin jakata na mike tsaye nace da ummi taso
mu tafi. Ta mike a fusace tace zamu tafi
malam, sai dai gaskiya idan bamu ga canji ba
zamu dawo, asan abinyi dan bangane irin
wannan aikin ba. Muka fice yayin da ya bimu
da harara, muka fito tsakar gida dukkanin mu
rai a bace. Matansa sunyi carko carko suna
kallonmu domin suna jiyo duk abubuwan da
ummi take fada. Ta harare su tace Allah Ya isa
kudinmu da ake damfarar mu ana cin kaji, ko
wacce shegiya tayi bul- bul da abincin haram.
Ni dai nayi wuf na fice kada a biyo mu da duka,
har zaure suka rako ummi suna zaginta tana
zaginsu. Naja hannunta muka tafi, a hanya ta
fashe da kuka don takaici, ni kukan ma na kasa
yi sabida tsananin tashin hankali. Tace dani
aisha kinga macutan malamai ko? Wallahi ni
ban taba kula da cutar da wannan dattijon yake
min ba sai yau. Duba kiga yadda komai ya
dagule mana. Nayi ajiyar zuciya nace yanzu
ummi meye abinyi? Tace kije wajensa ki gwada
ki gani bayan kin sha rubutun kin daura layar.
Nima yanzu gidan yassar zanje in gani ko zai
kula ni, idan abinda ya bani bai yi aiki ba
wallahi sai na dawo na tarawa malamin nan
mutane. Nace kina ganin wannan rubutun da
layar daya bamu ta gaskiya ce? Ta wa da naki
fa iri daya ne, babu wani suna daya tambaya
balle ace kowa daban, rubutun ma daga gani
ba namu bane saboda baiyi niyyar bamu komai
ba sai da yaji kince babu inda zakije idan baiyi
wani abu ba sannan ya bamu. Tace ke dai
muje mu gwada mu gani. Mukayi sallama na
hau acaba zuwa asibitin malam ummi kuwa ta
hau bus zuwa unguwar zango gidan yassar. Ina
sauka na bude jakata na zaro kullin runutu na
tashi tsaye kamar yadda ya umurce ni na
shanye, yayin da na ciro layar nan na damke a
hannuna na nufi ofishin sahibina. Ina mai
karanto adduoi don neman dacewa. Zuciyata
cike da fargaba. Na tura kofar ofishin a
sanyaye gami da yin sallama, zazzakar
muryarsa ce ta amsa sannan na tura kai na
shiga. Kallo daya yayi min ya dukar da kansa
kasa bai sake dagowa ba yaci gaba da rubuce
rubucensa. Na gaishe shi ya amsa a shelake
yayin da fuskarsa babu annuri. Na dade a tsaye
bai ce dani komai ba kuma yaki dagowa ma ya
kalle ni. Nayi ajiyar zuciya na tambaye shi a
tsorace dr lukman ya zo kuwa? Da yazo da
baki ganshi ba. Amsar da ya bani kenan. Nace
likita ina da tambaya game da kurajen fuska.
Sai yace dani ke fita ki bani wuri, nan ba
ofishin dr lukman bane, ya koma ofishinsa a
room 8 an gama masa gyaran, kada ki sake
shigowa nan nemansa. Nayi sadan sadan na
fice, na dade a tsaye a bakin kofar daga waje
ina takaici tamkar in rusa ihu. Sai wata zuciyar
ta raya min ko in saka layar a bki in tauna zata
fi aiki. Sai na zura ta a baki ina taunawa na
sake tura kofar na zura kaina ciki. A tsaye a
tsakiyar ofishin na iske shi yana duba wani
littafi a jikin durowar littattafan dake kusa da
bakin kofar. Nace dan Allah likita zan iya bar
ma sako ka bawa dr lukman? Naje ofishinsa
baya nan..... Ban rufe bakina ba naji ya banko
kofar ya rufe booom saura kada ya bame da
fuskata, ba dan na daka tsalle nayi baya ba,
daya illata ni. Tunda na kalli kofar waje
bansake waiwayr ofishinsa ba, na saka a raina
ni dashi har abada koda kuwa zan mutu banyi
aure ba a duniya dan wannan wulakancin ya
isa. Naji na tsane shi na tsani kaina. Na tsani
ummi da ta saka ni a hanyar halaka kuma na
tsani malamin daya cuce ni ya tagayyara ni. Na
toho da layar daga bakina na farke ta saiga
takadda a ciki babu abinda yake ciki sai zanen
wani hatimi mai gida gida an rubuta alifun,
ba'un, ta'un kawai aciki. Na fusata na yayyaga
kuci kuci na watsar yayin da kuka ya turnuke
ni. DUK KYAN TAKALMI 14 Kawata ummi
wacce na taba baki labari tana son wani
malamin mu a sakandirw abdulyasar shi kuma
baya son ta amma daga baya ya fara sonta har
ya aure ta, ita na tuntuba don ta bani shawara.
Sai tace dani malamai ne suka yi mata aiki,
dole akayi masa yazo ya aure ba a hayyacinsa
ba. Don haka sai ta jani wajen malaminta ya ce
in kawo masa naira dubu ashirn da biyar zaiyi
min asirin da dr shureim zai zo har inda nake
da kansa, ya aure ni. Dogon salati abida ta
dauka ta dafe kirji tace farida boka? Me ya
kaiki bin bokaye akan wannan 'yar karamar
matsalar? Sai na daga ido da sauri na dube ta,
ina mamakin yadda ta ambaci matsalata 'yar
karamar matsala. Nace a raina lallai abida bata
san yadda dr shureim take ba da yadda
halayensa suke ba shiyasa take ambaton haka.
Abida ta dora hannu aka tace innalillahi wa
inna ilaihir rajiun. Aisha farida kinyi kuskure.
Wai shin ina wayon nan naki? Ina dubarunki?
Ina iya zama da jama'ar da kika koya daga
wajen magabatanki? Ai wannan matsalar taki
karama ce. Ke kika zamar da ita babba gashi
kin cuci rayuwarki duniya da lahira. A duniya
kin jawowa kanki bashin da zai kaiki zuwa ga
kotu a daure ki, kin dauko hanyar rugurguza
karatunki. Sannan kin taba lahirarki domin
ibadae ki ta ragu saboda damuwa da kika jefa
kanki, kinje wajen boka mai duba wanda Allah
Ya haramta, duk wanda yaje wajen mai duba,
mai zuba wuri ko mai bugun kasa kuma ya
gasgata abin da ya duba ya fada masa tabbas
bashi da sallah har kwana arbain , Allah ba zai
karba ba. Idan kika mutu a tsakanin wadannan
ranakun me zaki cewa Ubangijinki? Kin zama
makaryaciya domin karairayi iri iri kike
shirgawa wanda ada ba halinki bane kuma
kinsa makomar makaryaci wuta ce. Baki kyauta
min ba farida da baki fada min matsalarki ba
har sai da komai ya cabe. Na girgiza kai nace
na hakura da dr shureim yadda iyayena suka
bar duniya na san na rabu dasu har abada
haka na rabu da shi daman bai san abinda
nake yi ba. Wallahi anty abida ba da ganfan na
dorawa kaina sonsa ba haka na tsinci kaina,
nima ba da son raina ba. Abida tace haba haba
kamar yaya zaki hakura dashi bayan wadannan
bala'I da kika fada a dalilin sonsa ai ba zai tafi
a banza ba. Nayi miki alkwarai da izinin Allah
(SWT) sai kin sami soyayyar dr shureim cikin
ruwan sanyi. Na kasa kunne ina sauraron
maganar abida tamkar tatsuniya. Na dauke ta
a matsayin mai iya zance don hankalina ya
kwanta kawai. Duk da nasan babu abin da ya
gagari Allah, amma abin da kamar wuya wai
gurguwa da auren nesa. Abida ta luta da
tunanin da nake yi a zuciyata ta ga alamar ban
yarda da abubuwan da ta fada min ba. Tace
aisha farida kin manta da yadda akayi na auri
yayanki hussaini? Kin manta ra'ayinsa na son
girma ba zai auri kanwarsa ba a lokacin da
iyayenmu suka yi sha'awar hadamu aure yake
kokarin bijirewa? Kin manta yadda muka fara
zama dashi a gidan nan, ni dake muna
tsoronsa ko muryarsa muakji jikinmu sai ya
dau rawa muna guje guje? Yaya kika ga
zamana dashi a yanzu? Bari in fada miki
abinda baki sani ba farida, yayanki hussaini a
tafin hannuna yake yanzu idan naso in daga shi
sama, idan naki sai in kifa shi kasa ya fado.
Yaya hussaini a halin yanzu baya iya bacci
idan ina fushi dashi sai ya bani hakuri na
hakura sannan hankalinsa yake kwanciya.
Hussaini baya boye min komau na game da
samunsa, baya boye min duk halin da yake ciki
na game da abokan sa zuwa danginsa balle
'yan matan waje domub mazan zamaninan
ba'a rasa su da 'yan matan zamani, ko basu ce
suna sonsu ba su 'yan matan zasu kawo
kansu. Ki tambaye ni ya akayi haka ta faru? Ta
ina na samo kansa? Farida wallahi ban taba
zuwa wajen wani boka ko malami ba nace ina
neman a mallake min hussaini. Mutane suna
mamakina yadda nake tankwasa hussaini yake
yin abinda nake so, har wasu kawayena da
'yanuwana suke tsokana ta wai ina hada su da
malamina wanda ya tankwara min hussaini.
Idan na fada musu ban taba zuwa wajen wani
malami ba a rayuwata sai suki yadda. Aisha
farida bana addua har karshen rayuwata in
taka kafata wajen wani malami ko boka don
yayi min adduar mallaka. Ina daga hannayena
sama in roki Allah Ya mallaka min mijina, mu
zauna lafiya, yasoni kamar yadda nake sonsa.
Na girgiza kai nace na fada cikin kuka anty
abida na hakura da dr shureim saboda bai san
halin da nake ciki ba, mutumin da baya kallon
fuskata baya amsa min gaisuwata, ta yaya zai
soni? Kawayena guda biyu har mota gare su
kyawawa ne, ko khadija bata fini kyau ba.
Maryam ta fini kyau suma dole suka gaji da
wulakancinsa suka hakura dashi. Na rasa
yadda zanyi in daina sonsa duk da adduoin da
nake kwana ina yi don Allah Ya yaye min sonsa
amma sai karuwa yake yi na fada tsaka mai
wuya, hatta da karatuna ya tabarbare saboda
sau biyu supervisor dina yana zuwa yana duba
ni daga makarantar mu bana nan. Don haka na
san in banyi da gaske ba dole sai na maimata
attachment dinnan wata shekarar. Ko a littafi
ban taba karanta labarin wacce ta fada irin
wannan matsananciyar soyayyar da na fada ba,
makauniya kuma gurbatacciyar soyayya don
bai san dani ba balle ya san abinda nake yi ba.
Sai na rushe da kuka. Abida tayi murmushi ta
dafa kafada ta sai ta girgiza ni tace haba
farida, ke macece fa, dama akwai wani da
namiji da zai baki tsoro duk haduwarsa? Ina so
ki yadda da kanki, ki dauka duk in da wata
mace ta je zaki iya zuwa, ki dauka duk abinda
tayi zaki iya yi. Ki manta da farar fatar
baturiyar da yake aure, ke bakar fata sai ki fita
a wajensa. Sai naji abida ta fara bani haushi da
wadannan maganganun nata masu kama da
almara. Na rasa yadda zanyi in fahintar da ita
waye dr shureim. Na tambaye ta cike da
damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har
nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na
fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga
dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni
yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin
manta kissar matan nan da akayi mana a
makarantar islamiya? Kin manta matar nan da
take wajen malami ta nemi da ya bata abinda
zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu,
an samu sabanin malamai, sabanin malamai
kuwa rahama ce duk dai abu daya suke
nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa
malamin cewar maganin mallaka take so ya
bata, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login