Showing 51001 words to 54000 words out of 87292 words
na hakura. Na kagu inji
halin da kake ciki, kai da janan. Muazzam
ya lumshe ido yace alhamduliilahi kanwata,
naga falalar addua da hakuri, kuma na rike
mutuncina yadda kika ce. Naje mata da
siyayya iri iri na kaimata, ko kallona takiyi.
Sai na sami waje na zauna nace mata janan
ina so ki saurari bayanina kiji dalilin zuwana
wajenki yanzu. Ada na soki ba kya sona, a
yanzu naso ki bakya sona, don haka na
hakura ba a dole a soyayya. Allah Ya sauya
min da wacce take sona har ma an saka
mana ranar aure. Kiyi hakuri da takura miki
dana yi a da. Ina so a yanzu ki saki jikinki
dani, ki dauke ni a matsayin yayanki, kuma
lauyanki bayan nan babu wata alaka
tsakanina dake. Ina gama fada naga
alamaun jikinta yayi sanyi. Kullum naje sai
inga tana yawan kallona tana kuma bude
baki tayi min magana, duk tambayar da
nayi mata. har na hada baki da wata matar
yayan, sai tayi ta kirana a waya a dai dai
lokacin da nake tare da jana, sai na dinga
amsawa kamar da budurwata nake
magana. Sai inga fuskarta kamar bata jin
dadi. Aisha farida ta cika da mamaki tace
duk a kurkukun ake wannan? Barr muazzam
yace eh ai ana bari na in shiga sai a
kirawota a hado ta da maikaciyar kurkukuk
daya,ta kawo ta inyi mata tambayoyi
saboda neman hujjojin da zan bayar da
kuma nemo shaidu a kotu. Aisha farida tace
lallai ni abin da na lura janan tanan sonka,
tsabar jan aji take yi maka don ta tabbatar
kana sonta, kuma baka fushi duk
wulakancin da zatayi maka. Muazzam yace
haka ne wallahi, sai yanzu na yadda da
haka. Ai nuna mata nake bata gabana kwata
kwata yanzu. Baraka ma ta samu sauyi na
fada mata duk yadda zatayi, kuma ta
aiwatar tana addua kuma tana hakuri,
sannan kuma tana jan ajinta tana yi masa
girki, ta tsaftace gida, ammma ta fita
harkarsa bata bari ma su hadu a gidan,
kwana biyu ko uku tana gidan bata bari ya
ganta. Sai gashi yana fada min wai baraka
ta sauya halinta yanzu ta daina damuwa
dashi, in bashi ya leka dakinta ba, ita ba ta
fitowa. Sai na kalle shi na watsar nace au
har dakinta kake takawa ita da kake korarta
da idan ta shiga dakinka? Sai yace ai dole in
leka inga halin datake ciki, kar inje ta shiga
daki ta kashe kanta ko ta hadiyi zuciya ta
mutu. Nace masa ashe kasan kana kuntata
mata har zata iya hadiyar zuciya ta mutu
ko? To kaji tsorn Allah. Sai yayi shiru bai ce
komai ba. Itama barakar take cemin wallahi
ya fara sauyawa, yanzu da kansa yake
dawowa gida yaci abinci, dga lokacin cin
abinci yayi, da kuwa har kifarwa yake yi a
gabanta idan ta matsa masa yaci. Aisha
farida tayi dariya tace alhamdulillahi, Allah
Ya kara yi mana jagoranci. Barr muazzam ya
dube ta yace ni naga duk kin rame, lafiya
kuwa? Ko dai shuraim din ne ya taba min
ke? Aisha farida ta girgiza kai tace babu
ruwansa bawan Allah, wlhi antina ce abida
bata da lafiya sosai, gabobinta gaba daya
tun daga kafa har wuyanta duk inda
mahadar kashi take ta kumbura suntum,
tana yi mata ciwo, da kyar take tafiya.
Shien muke ta sunturi asibitin kashi na dala
(autopeadic). Anyi xray da gwaje gwaje
sunce basu ga komai ba, ciwo kima sai
karuwa yake. Yanzu da kyar take iya
takawa komai sai anyi mata. Shiyasa kaga
duk na susuce. Subhanallah, Allah Ya bata
lafiya. Inji barr muazzam.
Aisha farida tace amin ai munyi sati biyu da
barin asibiti, rabona da dr shuraim kenan
amma akwai cigaba sosai. Ta zayyanowa
barr muazzam labarin abubuwan da suka
faru tsakaninta da dr shuraim da kuma
mataki na hudu da abida ta karanto mata.
Barr muazzam ya dubi aisha farida cike da
rashin fahimta yace to ni kamar ni ta yaya
zan yi mata biyayya? Kuma kamar baraka
wacce tayi biyayyar a baya bata ci riba ba,
sai da ta share shi ta fara samun saukin
wulakancin? Aisha farida tace ai a ganina
duk daya ne mu ukun. Yanzu kamar baraka
taci gaba dayi masa haka har lokacin da zai
karkato sosai, yana son zaman nata sai ta
dawo tayi masa biyayya sosai, tayi duk abin
da yake so, ta bar abinda baya so, ta nan
zai fara mantawa da nafisa. Ko kuma zai
fara kokonto ko ya rike matarsa ne, ya rabu
da waccan don na tabbata ba zatayi masa
biyayyar da baraka take yi masa ba. Saboda
wadannan dalilan nawa na farko kace babba
ce har ta dade da gama jam'ia. Na biyu
tasan yana sonta don haka zatayi ta jansa a
kasa kasan halin mata. Barr muazzam ya
gyada kai yace lallai kanwata na yadda da
tunaninki, kamar kina zaune a wajen duk
yadda kika fada haka ne. Aisha farida tayi
dariya tace kai kuma a bangarenka kaci
gaba da nuna mata ka sami wata bata
gabanka yanzu. Kada ka bari alakarku ta
rabe, ku cigaba da yawan haduwa ko bayan
ta dawo gidan a matsayin abokinta zaka ga
ta dawo. Kada ka fada mata da wasa kake
da wuri, kayi ta kyautata mata, kanayi mata
duk lallashi da tarairaya. Kayi ta yin duk
abin da kasan tana so, ka kiyaye wanda ba
taso tabbas zataji kai kafi dacewa da
rayuwarta, ko bata zo tace tana sonka ba,
zata nuna alamu. Barr ya gyada kai yayi
murmushi yace gaskiya ne wannan kinyi
hikima, Allah Ya sa mu dace. Bani lambarki
don muci gaba da tattaunawa a waya. Ya
zaro wayarsa daga aljihun, aisha farida tana
karanto masa lambar yana rubutawa har
suka cika. Sannan ya kira lambar ta shiga,
amma wayar tana gida. Aisha farida tace
idan na shiga ciki zanyi saving. Barr
muazzam ya zaro kudi daga aljihu, naira
dubu biyu ne 'yan dubu dubu guda biyu, ya
mika mata nan fa ake tataburzar, don aisha
farida ta tubure ba zata karba ba, shi
kumwa yace sai ta karba. Ko zubarwa zatayi
sai dai ta zubar. Sai da ta ga ya dage sosai
har ransa zai baci sannan ta durkusa ta
karba, tayi masa godiya suka yi sallama ya
tafi, tashiga gida cike da farin ciki kamar
kuwa yasan suna cikin tashin hankalin
rashin kudi, asibiti duk ya cinye musu
kudin. Cefane ma sai harhade harhade ake
yi, a dafa a ci ba dadi don kar a mutu.
Ciwon abida kamar da wasa, abu ya fara
tsananta hankalin kowa ya fara tashi, don
har hussaini yayi waya ya sanarwa da
iyayenta da 'yanuwansu na shagamu.
Babban likitoci yanzu take gani a asibitin
kashi, don ciwon ya wuce kananan likitoci.
Magani take dirka amma fa a banza, ko
alamun canji bata ji a jikinta. Daga nan sai
suka rabu da zuwa asibitin kashin ma, suka
dawo gida aka fara na hausa, wannan yace
sanyin kashi ne, waccan tace mayu ne.
Kowanne magani hussaini yaji sai ya karbo
ya kawo, burinsa matarsa ta sami lafiya.
Abinka da mai ilimi aisha farida bata son
wannan gwafje gwafejen magungunan
gargajiyar ko hussaini ya kawo ya bata, sai
ta boye bata bari tasha. Gara ma na
shafawa a gabobi tana shafa mata kamar na
sanyin kashi da aka karbo musu a wajen
sarkin ruwa na wudil. Maganin sanyi kashi
ne da man shanu ake kwabawa a shafa a
gababin. Sai man tafarnuwa dashi ma akace
ta dinga shafa mata a gabobi shima tana
shafa mata kullum da daddare kafin su
kwanta.
DUK KYAN TAKALMI 2* 11
Babu abinda abida ke iya yi, sai anyi mata
tana kwance kawai. Amma tana magana
radau kuma idan an bata abinci tana ci
sosai. Sai tsananin sanyin da take ji, sai tayi
ta makerketa duk da bargunan da aka lufga
mata, kuma a lokacin zafi ne. Ba asiha
farida da hussaini da 'ya'yan abida ba kadai,
duk wani mahalukin da yake da dison imani
a cuciyarsa hankalinsa sai ya tashi idan yaga
ciwon nan kuma ya tausaya mata. 'Yan
dubiya basa karewa layi layi mata suna
shiga, wasu na fitowa. Sai yanzu 'yan gida
da 'yan unguwa suke zayyano kyawawan
halayen abida. Idan akace yau asabar da
lahadi ce lokacin yaya hussaini yana gida
baije aiki ba, to mazan unguwa da abokan
aikinsa sai suyi ta tururuwar zuwa dubiya.
Kuma yawanci basa zuwa hannunsu haka ,
suna riko kayan dubiya kamar ayaba da
lemo, ko kayan shayi, wasu kuma sai su ba
da dan kudi suce a sayi magani. Aisha
farida ta labe tayi kuka har ta gaji, addua
take Allah Ya tashi kafadun abida uwarta,
ubanta, yayarta kuma kawarta, sannan
aminiyarta mai bata shawara. Aisha farida
ta tari yaya hussaini a bakin kofar dakinsa
ya shirya ya fito zaije aiki. Bayan ta gaishe
shi ta shawarce shi tana son ta kai abida
asibitin malam aminu kano a duba to ko
Allah zai sa a dace.
Hussaini yayi shiru can yace kina ganin aje
asibitin nan alhali na tabbatar ba ciwon
asibiti bane, tunda ga kasusuwan sun
kumvura suna ciwo, amma likitocin kashi
sunce basu ga komai ba. Aisha farida tace
ina ga ai ba bangarensy bane, wata kila
ciwon ba a jikin kashi yake ba, gara in kai ta
tunda can akwai likitoci manya manya zasu
gano ciown. Hussaini yace kinga abin da
yasa nace bana asibiti bane, idan tana bacci
sai tayi ta zabura har sai na rirrike ta cikin
dare. Aisha farida tace haka ne yaya, ai
asibitin ma suna da maganin razana da
zabura. Ya lalubo kudi ya bata yace suje,
Allah Ya sa adace. Aisha farida ta harhada
'yan kudaaden da take adanwa na masu
dubiya, misbahi ma dubu daya ya bata,
haka wani yayansu da yazo daga shagamu
shima dubu daya ya bata, taje ta hado
cefanen dambu ta shirya wa rabin ranta dr
shuraim. Bayan ta yi wanka ta fesa kwalliya
da wata doguwar rigarta bakai mai dankwali
(abaya). Sai ta shirya abida aka kirawo
musu mai adaidaita sahu yazo har kofar
gida. Sai da matan gidan suka taimaka mata
aka rirriko abida aka saka ta ciki domin duk
gabar da aka rike mata ciwo takeyi mata.
Sai ta dau kuka kamar wacce ake balla mata
kashinta don azaba. Aisha farida rike da
kwandon abincinta ta shiga adaidaita sahi
suka tafi. Ta dubi abida ta zubo da hawaye
don tausayi tace wannan dambun ne nayi
wa su dr shuraim in kai musu ko in kyale
su? Abida tayi murmushin karfin hali ta cije
baki saboda tsananin ciwo ta gyada kai tace
ki kai masa.
Mai adaidaita sahu ya kai su har bakin
GOPD kafin su sauka, sai aisha farida ta
shiga ciki da sauri tayi magana da maikatan
suka bata kujerar tura marar lafiya. Lebura
daya ta dauko kujerar ta biyo ta da ita. Nan
ma sai da aka agazawa aisha farida sannan
aka dora abida akan kujerar saboda tsabar
ragargazar da kashinta ke yi har kara zaka ji
yana yi bas! Bas! Idan ta motsa. Aka turata
aka shiga dasu wajen bude file kasancewar
duk ta sanu ba ta bi dandazon layi ba aka
bude musu, nan da nan aka mika musu file
din dakin likita. Nan ne fa za asha jira
sabida likitoci basu karaso ba, don haka
dole a sha jira akan bencina. Aisha farida ta
dubi abida wacce har yanzu take kan wheel
chair tace inje ofishin dr lukman in dawo,
zaki iya zama ke kadai? Abida tayi
murmushi tace kije a tsanake ki gama
abinda kike yi, kada ki damu don kin barni,
ni kadai zan zauna a cikin kabarina. Ni kadai
zan zauna babu mai tayani zama, saini sai
halina. Sai aisha farida ta runtse ido yayin
da kuka ya kcece mata, ta kasa magana
saboda jama'ar dake kallonsu. Cikin sanyin
jiki ta dauki kwandon abincin ta tagi.
Hawaye yake ya tsaya har ta kusa isa
ofishin dr lukman don haka ta sami lungu ta
labe tayi kuka har ya isheta, ta goge
hawayen ta fito. Amma kuwa kallo daya
zakayi mata kasan kuka ta sha, don
idanuwan sunyi luhu luhu.
A sanyaye take tafiya cikin nutsuwa ta
kwankwasa kofar ofishin dr lukman ta
shiga. Bata iske shi ba, sai wasu daliban
likitocu guda biyu ta samu suna zazzaune
suna jiransa. Bayan sun gaisa sai ta tura
kwandon abincin a lungun da saba ajiyewa,
sannan ta tambaye su inda ya tafi. Suka
tabbatar mata yace su jira shi yanzu zai
dawo, ba zai dade ba. Sai ta sami kujera ta
zauna tana zama sai taji an bude kofa,
yayin da gaba daya hankalinsu ya tafi wajen
kofa. Dr lukman ne a gaba, dr shuraim ba
biye dashi. Kowannensu da laptop dinsa a
rataye a kafadarsa. Idanuwan dr shuraim
akan aisha farida ya fara dira, yayin da ya
jima yana kallonta sannan ya dauke idonsa.
Ita kuma murmushi kawai takeyi tana mai
sunkuyar da kai tana jin kunya. Dr lukman
ya dube ta yayi dariya yace 'yar shagamu
daga ina kika diro? Na dauka ai da aka gama
karatu sai kika hada 'yan komatsanki kika
koma shagamu. Tayi dariya tace ina nan
yyayana, kai ka share ni ai ba ka nemana
gashi kuwa na taso takanas na zo in gaishe
ku. Dr lukman yayi dariya yace kin kyauta
'yar shagamu, ni daman nasan kinfi ni kirki,
to bari inje in sallami daliban dana zaunar
tun dazu suna jirana. Ya juya ya dube su
yace to ku taso muje lab din in nuna muku.
Suka bi shi a baya suka fice, sai ita sai gogan
nata dr shuraim kadai aka bari a ofishin.
Yana zaune akan kujera ya bude laptop
dinsa yana dube dube. Ta dubi
zankadediyar fuskarsa sai taji zuciyarta ta
hau dukan uku uku saboda tsananin kyawun
dataga ya kara yi. Ta fara tambayar kanta
da kanta “anya kuwa mutumin nan bai fi
karfina ba? Anya kuwa zan kai labari a
tafiyar nan? Anya kuwa hakata zata cimma
ruwa”? Sai bayanan abida ya fado mata
cewar babu abinda ya gagari Ubangiji,
samun dr shuraim ba wani abin wahala
bane idan har ta rike matakan nan guda
biyar. Ta silmiyo daga kan kujera ta gaishe
shi cikin wata kintsatsiyar murya bata mike
daga durkuson ba har sai da ya amsa mata,
sannan ta koma ta zauna. Tayi shiru kanta a
sunkuye a kasa, sai dai su biyu suna hada
ido in dai ta dago zata kalle shi, sai taga
shima ya dago ido ya dube ta.
Sunyi mintuna biyar cur babu wanda ya
sake magana a cikinsu. Sai taji muryarsa
kamar a mafarki ya ambaci sunanta. Yace
aisha farida, 'yar shagamu, 'yar acaba.
Wanne ne sunanki a cikin su. Sai ta dago ta
dube shi tayi masa lallausan murmushi ta
sunkuyar da kai ta sosa goshi alamar kunya.
Tace sunana aisha farida umar shagamu.
Yayi wani dan siririn murmushi yace kin
amsa sunayen uku daya kika cire, mai yasa?
Ta girgiza kai tace ai na daina hawan acaba
yanzu. Yayi murmushi yaci gaba da
daddanna laptop dinsa. Yace kinsan sunan
wa kike dashi? Sunan mamana ne aisha,
haka farida sunan kanwata ce wacce take
bina. Ya akayi kike amfani da sunaye biyu?
Aisha farida tayi murmushi tace mai suna
aisha ai farida ce duk daya ne. Yace okay
kenan ummata da farida sunansu daya ni
ban ma taba ji ba. Aisha farida tayi
murmushi tace haka ne, ai ba kowa ne ya
sani ba. Ya dube ta da wutisyar ido yace
baki da lafiya ne? Ta dago ido da sauri ta
dube shi cike da mamaki ta girgiza kai tace
lafiyata kalau. Ya girgiza kai yace shikenan,
naga kinyi kama da marar lafiya ne, ko kuka
kikayi ne? Wannan tambayar tasa ta sake
bata matukar mamaki, sai taji kamar a
mafarki. Tayi shiru har zuwa dan lokaci
sannan tace eh. Ya dago ido da sauri ya
dube ta sai ya cika da mamaki yayin da ya
maimaita amsar da ta bashi eh??! Yaci gaba
da duban laptop dinsa ya ma rasa tambayar
da zaiyi mata. Ta sharbe hawaye tace
yayata ce bata da lafiya sosai, har bata iya
tafiya ita na kawo asibiti. Yayi shiru na wani
dan lokaci sannan ya nisa ya ce me yake
damunta? Aisha farida ta zubo da hawaye
mai dumbin yawa tace an kasa gano ciwon.
Dr shuraim ya girgiza kai yace a'a bakuje
inda za'a gano muku ciwon ba dai, har
akwai ciwon da ba a ganewa, ko wanda
bashi da magani? Aisha farida ta matse
hawaye da hannunta ta dagi da jajayen
idanuwanta ta dube shi, ta girgiza kai. Tace
asibitin kashi na dala muka yi ta zuwa suna
bata magani, amma bata jin sauki. Sai ma
gaba yake. Shine yau na kawo tana, tana
GOPD a layi, likitocin ne basu karaso ba. Ya
tambaya cike da kulawa yaya take jin
ciwon? Aisha farida ta kwatanta masa duk
yadda ciwon ya fara har izuwa yanzu. Sai
yayi shiru can yace ciwon yayarki
rheumathoi athritis ne ko systemic lypus
erythramatosis. Aisha farida ta kalle shi
cike da rashin fahimta tace na'am? Ya
girgiza kai yace kada ki damu likitocin da
zasu duba ta yanzu zasu hada da likitan da
ya dace. Allah Ya bata lafiya. Aisha farida
tace amin nagode. Sai ta mike a nutse ta
duka tace zan tafi saboda kada likitocin
suzo a kira mu bata iya tafiya, nice zan
shiga da ita. Ya gyada kai yace okay, Allah
Ya ba da sauki. Ta fice cike da farin ciki,
tana fita ta dafe kirji tana ambaton Allah na
gode ma Ka, Allah Ka sake cika min burina
akan shuraim. Tana tafe tana fara'a tamkar
an biya mata kujerar makka. Sauri take ta
karsa wajen abida ta bata labari, amma da
ta tuna abida babu lafiya sai jikinta yayi
sanyi musamman data je ta iske abida ta
galabaita a inda take zaune, ta gaji da
zaman duk jikinta ciwo yaje. Hawaye kawai
ke fitowa daga idanuwanta. Ita kadai tasan
me takeji, sai dai duk wanda ya dube ta
yasan tana jin jiki saboda gaba daya
gabobinta a kumbure suke. Aisha farida ta
rike ta, ta gyara mata zamanta tana mai
lallashinta tayi hakuri likita yazo. Suna
zaune shiru aisha farida na ta sake
maimaito hirar da suka yi da rabin ranta, sai
tayi murmushin jin dadi ta waiwayo da
sauri ta dubi abida tana shirin ta bata
labarin dr shuraim sai taga mawuyacin halin
data ke ciki, sai taji hawaye ya cika mata
ido.
BABI NA GOMA SHA DAYA Aisha farida tayi
kuka, har ta godewa Allah a wannan rana ta
asabar saboda jikin abida ya matsa, babban
yayanta yaya lurwanu yazo da mota har
kofar gida, yace a bashi ita ya tafi da ita
shagamu ayi maganin hausa. Yaya hussaini
ya zama bashi da zabi kasancewar shima
yana ganin ciown bai yi masa kama da na
asibiti ba, don sunyi ta yin na asibitin babu
alamar jin sauuki, kullum ciow kamar kara
shi ake yi. Aisha farida ta dage wajen yi
musu bayani, sunki su fahimce ta, suna
ganin don ita 'yar boko ce kuma malamar
asibiti shiyasa take son a dauwama da na
asibiti don likitoci ba sa kaunar a hada
maganinsu dana gida. Sunfi karfinta, tana ji
tana gani yaya hussaini da yaya lurwanu
suka ciccibi abida tamkar 'yar jaririya da
kayanta aka saka ta a mota. Yaya lurwanu
ke tukawa, yaya hussaini yana zaune a
gefensa, yayin da ita kuma aka kwantar da
ita a bayan mota. Aisha farida ta mika
hannu ta tagar motar ta rike kumburarrun
yatsun abida a hankali yayin da hawaye ya
surnano daga idanuwansu su duka. Aisha
farida tace Allah Ya baki lafiya. Abida ta
girgiza kai tace ba zan dawo ba farida, ki
kula da 'ya'ya na, kada ki manta abu uku
dana fada miki. Ki zama mai yawan addua,
mai tsananin hakuri mai yawan kama
mutuncinki. Biyun kuwa ba yanzu zan fada
miki ba sai nan gaba idan ban mutu ba.
Yaya hussaini ya juyo da sauri yana kallonsu
ba tare da ya fahimci abin da suke ba, shi
da lurwan suka cika da mamakin jin
kalaman da marar lafiya ta ke furtawa.
Hussaini ya tambayi aisha farida meye
hakan kuma yake nufi? Zance me kuke yi?
Aisha farida ta goge hawaye tace a'a sako
take bani. Yace sakon me kuma naji ana
maganar soyayya? Ki koma gida ki kula da
yara, gasu can suna ta kuka, nima gobe
zandawo na bar miki dari biyar a daki akan
katifa. Idan anyi wa yara hutun makaranta
sai mu dunguma mu tafi shagamu, ni ina jin
ma gara ku kaura can kacokan, ni zan dinga
zuwa ina dawowa, gara mu hakura da
zaman kanon