Showing 75001 words to 78000 words out of 87292 words

Chapter 26 - Duk Kyan Takalmi Complete Hausa Novel

Eeshat   

16 Jul 2026

249

fice ta
barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau
karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin
ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta
danna da sauri sai taji muryarsa cike da
farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira
wayarki taki shiga sai da na aika yara suka
fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura
shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko?
Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi
murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar
ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti
abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta
mutu ne shine muka dungumo, muna nan
dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin
muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu
an samu rabin warakar ciown, tunda an
samu likita da ya gano matsalar. Barr
muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji
sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da
naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti
abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir
nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji
dadi ba.
Aisha farida ta dafe haba tayi dariya tace
albishir din meye? Yace alewar saka aurena
da janan na kawo miki. An bani ita har an
kai kudi da kayan sa rana , nan da wata uku
za a sha biki. Alewarki ta musamman ce,
bounty na kawo miki har jaka biyu saboda
matsayin ki a auren nan, sai gashi ba kya
nan. Ko 'ya'yan yayanki suna ciki a kirawo
mun su na basu? Aisha farida tayi dariya
tace Allahi abin godiya, amma na taya ka
murna yayana. Kuma na gode da
karramawar da kayi min. Babu kowa a 'yan
gidanmu, dukka muka taho. Nima kuma
yanzu zan zankado maka nawa albishir din.
Dr shuraim yana shagamu yazo da likita an
duba anti abida, ya siya mata magunguna ,
ya biya makudan kudi za a kai jininta kasar
waje a gwado. Sannan daga karshe ya
kunso kudin aurensa ya kawo yanzu yanzun
nan nima labari yazo min, suna can a kofar
gida shi da yayyena da tsofaffin maza. Barr
muazzam ya cika da farin ciki da mamaki,
ya kyalkyale dariya yace ikon Allah, Allah
mai yadda yaso. Wato auren namu ma tare
za'ayi kamar yadda muka fara nema tare.
Na taya ki murna kanwata. Baraka ma
komai ya daidaita, ita da mijinta suna cikin
farin ciki, ya rabu da nafisa , hankalinsa
kacokan akan baraka. Ciki ne ma da ita, sai
ririta cikin yake yi. Tace in gaishe ki da
kyau, kuma tana matukar yi miki godiya,
tana so ta ganki a rayuwarta. Tace in
gayyato ki suna idan ta haihu. Aisha farida
tayi dariya tace Allah Ya kaimu , idan dai ina
kano zanje. Sukayi sallama ya kashe waya.
3 missed calls din dr shuraim ta gani a
wayarta a lokacin da take waya yake kira,
sai ta fara kokarin kiransa, shima ya kirata.
Ta amsa sallamarsa cikin nutsuwa kafin ta
gaishe shi ya jero mata tambayoyi guda
uku, ta rasa wacce zata fara amsawa a
cikinsu. Farida da wa kike waya nayi ta kira
har sau 3 naji call waiting? Meyasa da kika
shiga gida dazu baki fito ba mun gaisa har
na tafi? Meyasa kwana biyun nan naga
alamar kin daina damuwa dani? Sai ta
lumshe ido tayi ajiyar zuciya sannan tayi
murmushi. Tace bari na fara amsa maka
tambayarka ta uku, sannan a gangaro ta
biyu, sai in gangaro ta daya. Zancen na
daina damuwa da kai wallahi ba haka bane,
tunda ina tuna ka a rana sama da dubu.
Sannan tambayarka ta biyu ina shiga gida
na bawa anti abida magani sai na zauna ina
saurarom fadan da goggo keyi mana ni da
yaya hussaini, wai mun kawo likitoci sun
duba ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini
ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda
nagama zan fita aka ce min kunja mota kun
tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake
waya dashi wani ne sunansa barr muazzam ,
bansan kai kira ba da na bashi hakuri na
katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi
hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar
da yakeyi yace waye barr muazzam? Na
fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki,
kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba?
A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa
ya kamata sannan tambayar ta daga mata
hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki
my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da
ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode
ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka
tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim
kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a
bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min
laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka
baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani.
Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah
Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a
lokacin da na shiga ukuba, sai muke
gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr
janan bai same ni ba, shine yake shaida
min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya
tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace
kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin
rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta
shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr
shuraim yace tabbas ta dade ana shariar
nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki
nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai
Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi
aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban
taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura.
Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki
bani labari mai dadi mana wanda zai sani
inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun
bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji
anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha
farida tayi dariya tace zanso nima ka
kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na
biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare
ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin
jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da
alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi,
yau farida ta zama ta shuraim, shima ya
zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace
bani labarin me ya faru? Haka dai suka
cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da
kauna har tsawon awa guda. Abida na
kwance ta kafawa farida ido sai murmushi
takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta
mike tayi rawa don babu hali ne. Tana
adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi
auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI
AISHA FARIDA!!!
BABI NA GOMA SHA TARA! Abu kamar
wasa karamar magana ta zama babba.
Auren farida da shuraim sai kankama yake
sake yi. 'Yan lungu yanzu sun gasgata, don
da jita jita akeyi ko kuma ana ganin abin ba
mai yiuwawa bane, wahalar da kanta kawai
zatayi, yaudararta zaiyi ya tafi don ba ajinta
bane. Sai gashi idan da a sati sau daya ake
ganinsa , yanzu a sati a kalla yazo sau biyar.
Ba sai an fada ba, rayuwa da tukunyar su
aisha farida ta canja gaba daya, sun fara
bankwana da talauci, dr shuraim ya tsaya
musu. Tun ba a yi auren ba ma har ta
kidime ta canza salo da yanayi, kai kace ba
wannan faridar bace ta da. A yanzu farida
ta zama gangariyar 'yar gayu. Komai nata
mai tsada ne (high class) , kama daga
suturunta, takalmanta, da jakunkuna,
mayukan shafawarta da kayan kwalliyarta.
Sai ta canja tafiya, ta canja magana ta kuma
canja tsarin rayuwarta. Bata wulakanta 'yan
lungu amma bata cika shiga cikinsu a yita
wasannin banza ba da surutai barkatai.
Zama da dr shuraim ta koya nutsuwa ga jan
aji , magana ma sai an daidaita baki. Haka
ba a cika dogayen jimla da hausa ba sai an
tottoshe da turanci. 'Yan lungu sunyi
gulmar, sunyi zumden, sunyi yaficen, abin
ya wuce tunaninsu. Sai cigaba suke gani
kala kala musamman da suka ga ta fara aiki
ya daukar mata mai adaidaita sahu ya kaita
ya dawo da ita.
DUK KYAN TAKALMI 3* 10
Abida na tsakar gida tana kallon bakinsu
bata ce musu komai ba suka gaji, har takai
ta kawo ma sun zo sun same ta don suji
wani labari game da wannan aure na farida,
sai ta nuna musu ba lallai sai dr shuraim ba,
duk wanda yafi alkhairi a farida shi zata
aura. Basu ankara ba sai suka ji tashinsu,
sai ana gobe zasu koma sabon gidansu suka
fada musu. Mamaki ya rufe jama'a, 'yan
rakiya mata lodi lodi suka bisu don su
ganewa idanuwansu. Gida mai kyan gaske
babu abinda ba'a zuba ba, tun daga gadaje
a dakuna uku da kujeru a falo duk shuraim
ya siya, gida gini bulo da bulo sama da kasa
duk tiles. Rayuwa sabuwa ta tabbata a
gidan hussaini, farida bata rasa kudi. Dr
shuraim yana bata, ta dauki albashinta
kuma. Babur ta fara siyawa yayanta, kuma
ta canja wa 'ya'yanta makaranta ta kudi
anan court rd, mai adaidaita ya kaisu ya
dauko su. Sun koma sabon gida ba dadewa
aka saka ranar kawo kayan sa rana da na
lefe gaba daya. Kudin mota baiyiwa su
aisha farida wuya ba, suka turawa
magabatansu a shagamu, mata bakwai
maza uku suka shigo mata suka zo kano
don karbar kaya. Abida bata mance da
kawayenta na tsohon gidansu ba, fiye da
bus uku suka ciko suka zo don su ganewa
idanuwansu. Tunda kan 'yan uwan shuraim
kallo ya fara kafin a bude kayan lefe. Masha
Allah! Tabarakallah! Kaya sun yi kyau.
Akwatuna shida da kit biyu. Da saitin
sarkokin gwal da awarwaraye hudu manya.
Wata uku kacal aka saka ranar bikin, kowa
yana sam barka tsakanin dangin amarya da
dangin ango, har aka watse.
An sha dauki ba dadi a bangaren dr
shuraim kan maganar aurensa, 'yan uwansa
mata da yawa basu son auren, kasancewar
sun iske dangin amarya basu da hali. Cece
kuce kala kala sukayi tayi amma shuraim bai
damu ba , tunda mahaifansa sun yadda,
sunyi masa fatan alkhairi , don haka suje
suce duk abin da zasu ce. Da farko dai
mahaifiyarsa taki yadda, amma da yake
tana jin maganar mijinta, kuma kaifi daya
ne, duk abin da ya fada ya zauna a gidansa
dole a bi. Amma a sanda guguwar rigimar
ta buso daga bangaren matar shuraim wato
faiza sai ta kore ta danginsa saboda tafi
karfi. A sanda shuraim ya shaida mata a
waya cewar zai kara aure aure cikin
lallabawa da tattausan kalamai, sai ta hasala
tayi ta zage zage har da koke koke wai bata
yadda ba. Ya shaida mata aikin gama ya
gama, saura wata uku, kuma ba zai fasa ba.
Haka aka tashi dai baram baram a wayar,
shi ba dadi, ita ma ba dadi. Bayan sati guda
da wayarsu sai gata a Nigeria ita da
mahaifiyarta. Ba sulhu ne ya kawo su ba,
rigima ce tsantsarta. Mahaifiyarta tace sai
dai ya saki 'yarta , dama can ita ba son
auren take yi ba. Tunda yace zaman nigeria
zaiyi tasan zai cuce su. Ta gangaro kan
mahaifansa tace dama sun tsani 'yarta faiza,
sune suke hadasu fada. Da kyar rigiman
nan ta lafa, su dai mahaifan shuraim ba su
rama ba, amma 'ya'yansu sun rama musu,
akayi ta cece kuce. Shuraim ne yayi ta bada
hakuri har aka samu hayaniyar ta sauka,
zuciyar kowa ta dan lafa aka zauna taro a
babban falon mahaifinsa aka fara bayanai
da yadda za'a gano bakin zaren. Kiri kiri
matar shuraim ta fada wa mahaifiyarta tana
son mijinta, ba zata iya rabuwa dashi ba.
Mahaifin shuraim yace to ki kwaso kayanki
kizo ki zauna da mijinki da 'yarku a
gabanku. Karatun fa? Inji mahaifiyarta ta
fada a fusace tana harararta. Tace saura
'yan watanni na gama, zanje na gama na
dawo na zauna. Ta sha adduoin albarka a
wajen mahaifin shuraim da shuraim din
kansa, gami da danginsa. Yayin da ta
sacewa mahaifiyarta gwiwa don ba haka
taso ba. Ta fusata tace to ko sau daya kada
kizo kice an miki wulakanci, kije can ki
karata.
A daddafe ta bari sukayi kwana uku sannan
suka koma london. Kafin su tafi kullum kuka
faiza take yi wa shuraim tana cewa baya
sonta yanzu tunda zai auri wata. Ya iya
dadadan kalamai masu kwantar da hankali,
gami da bayanai masu ma'ana ya hada da
yi mata alkawari zaiyi musu adalci a
tsakanin su. Sai taji sanyi a ranta, ta kuma
yadda da duk abinda yake fada mata.
Rabuwar lafiya yayi da matarsa, uwar ce dai
ko sallamarsa bata amsa ba a airport.
Hankalinsa ya kwanta a wannan bangaren
kuma bashi da sauran rigima. Duk dauki ba
dadin da suka yi aisha farida bata sani ba,
bai bari ta sani ba. A bangaren ta matsala
kadan ta samu daga musbahu, a inda ya
tayar da hankalinsa, ba ci ba sha da yaji
abar kaunarsa zatayi aure ta barshi. Ya hada
kayansa zai bar garin, zai shiga yawon
duniya a rasa shi har abada. Tunda ya rasa
farida, to shima mahaifiyarsa da matarsa sai
sun rasa shi. Hankalin 'yan gidansu da
mahaifiyar sa ya tashi, mahaifiyarsa da
kanta tayiwa aisha farida waya ta shaida
mata halin da musbahu yake ciki kuma suka
roke ta tazo ta bashi baki ko zaiji. Sai kawai
ta fashe da kuka ta kashe wayar. Abida tazo
ta iske ta tana kuka ta tambaye ta suka
zauna suka yi shawara. Ta bata shawara ko
bata je wajensa ba, ta saka kati a waya ta
kira ta bashi hakuri akan yayi tawakkali , ya
daure ya karbi kaddararsa , zai yiwu shi ba
alkhairi bane a gareta, itama haka. Ya zauna
kada yace zai gudu, baisan inda zai fada ba.
Kuma Allah Zai barshi da gudun tunda bai
yadda da hukuncin da Ya yanke masa ba.
Haka aisha farida tayi, sai bayan kwana biyu
ta kira shi a nutse tayi masa nasihu masu
ratsa zuciya. Har sai da yaji ba zai tafi ba,
ya fasa. Yana kuka, tana kuka, tanayi masa
fatan alkhairi da godiya. Shima irin
wadannan adduoin ya dinga zuraro mata
har ta kashe wayar.
Banbancin bikinta da na barr muazzam sati
uku ne, don haka sanda taje dinner party'n
bikinsu a tahir guest palace da daddare ta
tafi musu da katin bikinta ita ma. Barr
muazzam yayi farin ciki da ganin farida da
shuraim a wajen bikinsu. Da farko ma bai
ganeta ba, saboda kyan da tayi ta goge, ta
waye ta tsatso da wani kyau na daban. Duk
da dandazon taron nan kowa yana kokarin
ya gaisa da ango da amarya, sai da
muazzam ya taso ya tare su ya kamo
hannun amaryarsa ya gabatar mata da aisha
farida da ya dade yana bata labarinta.
Daman ta san shuraim har ta gayyece shi
bikinta, shuraim ma ya gabatar mata da
farida a matsayin amaryarsa. Daga karshe
muazzam ya kaisu wajen barr nuruddin suka
gaisa, suka zauna a kurkusa. Tabbas daga
gani babu tambaya, nuruddin yayi mamaki
da ganin farida, shi bai taba tunaninta ba
tun wacccan ranar, sai ya dinga tuno
wulakancin da yayi mata a baya, yana jin
nauyinta. Ya sake yin mamaki da yaga
matarsa ma ta santa, sun kebe sai hira suke
yi kuskus suna ta tuntsira dariya kamar sun
saba. Ya kalli shuraim ya sake kallonsa, ya
tabbatar ya hadu, Allah Ya tsara halittarsa a
nan ko ba'a fada masa ba yasan akwai kudi
da ilimi, kuma ita zai aura. Ya tara
tambayoyo jifgi guda a zuciyarsa yana so ya
samu muazzam ya jero masa su akan
farida. Baraka ta dubi aisha farida tayi
murmushi tace ina ta jin labarin aisha farida
kullum, sai yau Allah Ya nuna min ke. Babu
abinda zance miki ni da muazzam a duniya
sai dai godiya, kin ceci rayuka. Ni da na zata
ma soyayya kukeyi da barr muazzam, sai
daga baya na gane jininku ne ya hadu, ya
bani labarin ki da likita, kuma naji dadin
ganinku a tare. In Sha Allah kuma zanzo
bikinku duk da watan haihuwana ne
wannan. Farida tayi dariya tace nafi kowa
farin ciki da dukkanin mu Allah Ya amsa
adduar mu , Ya bamu wadanda muke so.
Ina nafisar ta sa take? Yaya suke a yanzu?
Baraka tayi dariya tace ai ko zancenta ba
yayi, ko kiransa tayi sai ya katse. Baya son
abinda zai bata min rai, yanzu duk abinda
nake so shi yake min.
DUK KYAN TAKALMI 3* 11
Tunda bikin farida da shuraim ya rage saura
sati guda basu zauna ba, daga ango da
amarya har danginsu. Sai shirye shirye
akeyi kala kala. Bayan yinin biki da
kowanne bangarorin biyu zasuyi, akwai
shagulgula har guda biyu da dangin ango da
amarya zasu hadu a waje daya ayi. Daya da
yamma za'ayi a tahir guest palace sai
dinner a Chinese dragon da daddare za'ayi,
kowanne kuwa sai da aka fitar da anko.
Kayan fitar bikin ango da amarya daban aka
dinka musu yadda zasuyi shigar kala iri daya
tsadaddun gaske. Asabar ce yau misalin
karfe biyar na yamma n shuraim ya sauke
aisha farida a kofar gidan kawarta khadija
sani dake sokoto td don ta mika mata katin
gayyatar bikinta ta fito su tafi. Saboda
akwai wurare da yawa da zata kai kafin
magriba ya mayar da ita gida,saboda dokar
da yaya hussaini ya saka mata cewar duk
inda taje ta dawo gida kafin magriba ko da
kuwa tana tare da shuraim ne tunda ba a
daura aure ba. 'Ya'yan abida dukka hudun
ne 'yan rakiya suna zazzaune a bayan mota
sunyi dai dai da kayan ciye ciye da shuraim
ya dau nauyin tulo musu. Suci biskit su kora
da alewa, sai su dora da ice cream da
shawarma. Ehm! Dadi kan dadi wai kunama
ta harbi gyambo, abinda basu taba ci ba a
yau gashi sun samu. Kada ki shiga ki zauna
kiyi ta labari fa a ciki. Shuraim ya fada a
lokacin da ya kashe mota dai dai wani bakin
gate. Ta dube shi tayi murmushi ta gyara
farin gilashin fuskarta tace bazan zauna ba
yayana, yaya za'ayi in iya zama inyi hira
alhali nasan kana jirana? Ina mika mata zan
fito. Ta juya ta dubi yara tace ku zauna
yanzu zan fito ba sai kun bini ciki ba.
Ta bude mota ta fito, takawa take a nutse
kafarta sanye da wani cogen takalmi mai
tsinin gaske, launin baki da bakar jakarsa.
Sai ya kara mata tsawo. Doguwar rigar
jikinta (gown) da aka dinka mata a jikin
super holland purple da baki ta sake fitowa
da kyauwn dinkin. Dr shuraim ya bita da
kallo saboda kyauwnta da yake gani, ji yake
tamkar zai hadiyeta don kauna. Tana shiga
gidan khadija ta iske ta a falo ita kadai tana
kallon MBC action, bayan ta amsa
sallamarta ta nuna mata kujera ta zauna,
sannan ta sake kallonta sosai, sai a lokacin
ta gane aisha umar ce. Khadija ta zabura ta
mike tsaye, ta jawo dogon salati ta dire, ta
rike haba tare da dafe kirji. Tace aisha
umar dama kece na kasa gane ki? Ikon
Allah kece kika zama haka? Daman maryam
ahmad tace idan na ganki yanzu ba zan
gane ki ba. Saboda kin sauya gaba daya kin
zama 'yar gayu. Dariya kawai farida ke
kyakyatawa, khadija ta matso kusa da ita ta
zauna ta shafa jikinta, ta sake nanikarta don
ta tantance kamshin turaren da take ji a
jikinta , tabbas designer ne. Kudinsa ba zai
gaza dubu ashirin ba. Ta janye dankwalinta
don taga gashinta. Sai taga waccan
cunkusheshen gashin na farida mai tauri da
ba a shamfo sai kitson zane kullum yanzu
ya sha mai (relaxer) yayi yalo yalo kamar na
larabawa, baki sidik da shi, ya warware ya
mike daman can mai yawan gashi ce da
tsawo, don haka ya wuce kafadarta. Babu
abinda khadija ke kira sai ikon Allah! Aisha
umar yaushe kika zama haka? Aisha farida
tayi sauri ta gyara daurin dankwalinta ta
mike tsaye tana dariya tace Khadija bana
son wulkanci, wane irin tonon silili kike yi
min haka? Ke dai wani labarin zamuyi shi
idan muka hadu, yanzu sauri nakeyi na bar
shi a kofar gida. Katin bikina na kawo miki,
rana ita yau yini da party. Ta zaro wasu
hadaddun katina guda biyu ta mika mata
daga cikin hadaddiyar jakar dake rataye a
kafadarta. Ta juya da sauri ta fara tafiya.
Khadija sani ta watsar da katunan akan
kujera ta biyo bayanta da sauri. Tace ke
aisha umar ko ruwa ba zaki tsaya ki sha ba?
Dan mai adaidaita sahu ba sai ki sallame shi
ba sai in mayar dake anjima da daddare
ba? Ko angon ne ya fara hana ki kaiwa dare
a waje? Lallai kina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login