Showing 3001 words to 6000 words out of 87292 words
sunan zama ba
sai dai inje da sunan ziyara. A wata unguwa a
cikin kano mai suna sharifai zauran tudu, yaya
hussaini daman ya kama mana haya tun kafin
muzo, a gida mai dakuna bakwai muka kama
dakuna biyu. Don haka mutane ne da yawa a
cikin gidan, bandakin daya ne kacal, kicin daya
da tsakar gida daya ake amfani dasu mata da
maza, yara da manya. Abunka da gidan yawa,
kazanta ba'a magana. Gashi daman gidan ya
tsufa ya farfashe ba gyara sai warin bola da
kwata kowa kyashi ya hana shi gyarawa. Idan
ka share cikin dakinka da kofar dakinka ka
gama shara babu wanda zai share tsakar gidan
da zaure balle kofar gidan. Ga gida a lungu ko
mota bata shiga lokon, ga wata tafkekikyar
kwalbati da ta cinye fadin lungun, kowa a
tattakure babu sakewa, yara basa iya wasan
guje guje su more sboda matsi. Haka kowacce
mace ta baza kayan san'arta a cikin gida, cikin
zaure ko kofar gida saboda sai an taimakawa
mazan rayuwar zata tafi dai dai. Daman mazan
da yawansu buga buga sukeyi, wani sai ya
dawo gida babu abinda ya samo, da dan kudin
sana'ar natar za'a yi cefane kuma ta bawa
yaranta kudin makaranta. A gidan ma har gara
yaya hussaini tunda yana daukar albashi duk
tsiya dai karshen wata zai samu duk da dai dan
albashin bashi da yawa kuma rabin kudin a
acaba yake tafiya, kafin wata ya kare sai anci
bashi dole kafin a biya an jigata. Duk da haka
dai munfi sauran, muna dan cancanawa dai
muna rayuwa. Ni da abida muka fara sana'a,
muna soya wainar fulawa a kofar dakinmu,
kuma ana saya ba laifi duk da cinikin naira
biyar biyar ne, duk da haka muna samun na
sayan maggi, gishiri, a ciki ake bani kudin
makaranta da kudin dinkin tsummokaran mu
idan sun yayyage. A makarantar bokon cikin
unguwa aka saka ni, kamar sauran yaran
unguwar haka aka saka ni a makarantar allo da
yamma ta islamiya da daddare. Bana fashin
zuwa makarantar kullum saboda ina tsoron
yaya hussaini sosai, baya yi min wasa koda
yake matarsa ma baya sakar mata fuska ,
mutum ne mai zafin zuciya. Lallaba shi muke
kamar kwai. A daki daya nake zaune babu
komai a ciki daga 'yar karamar katifa sai 'yar
jakar kayana ta buhu a gefe ko ledar daki ba'a
shimfida ba sai tsurar ragargajejjen siminti da
wani yagulallan labule. Dakin su abida da
mijinta ne mai labule mai kauri, an shimfida
leda a kasan da katuwar katifa sai akwatin
kayansu a gefe. Kayan kitchen da danyan
abinci suna dakina wasu a dakinsu. Haka muke
rayuwa amma muna farin ciki saboda mun
sami ci gaba fiye da a garinmu tunda daman
can a cikin talauci aka haife mu. Bayan
kaurowar mu da shekara daya mahaifiyata ta
tara kudin motarta da guzurinta tazo ganina
sabida tun kaurowarmu bamu je shagamu ba,
saboda matsalar tattalin arziki sai ita tazo dan
taga yadda muke rayuwa don koda yaushe
magana ta takeyi don tana sona sosai har fiye
da 'yar autarta. Nayi murna matuka da ganinta
har ita ta fini murna, yaya hussaini da matarsa
ma sunyi murna da ganinta kuma sunji dadin
tsarabar da ta kawo mana. Ni da abida atamfa
dai dai ta kawo mana, yaya hussaini ta kawo
masa yadi, sannan ta kawo mana doya,
dankali, ayaba da lemo jifgi guda. Allah cikin
ikonsa cikin daren data zo muna kwance da ita
a dakina ciwon ciki ya turnuke ta kafin in
bugawa yaya kofa ya fito don a kai ta asibiti
rai yayi halinsa. Ummata ta mutu a gabana ina
kallonta ban isa in hana ta tafiya ba, Ubangiji
ya nemi kayanSa. Sai na tuna wasiyyat da ta
bar min cewar idan ta riga ni mutuwa inyi mata
addua kamar yadda na yiwa mahaifina. Nayi
mata addua sosai kuma ban manta ambaton
innalillahi wa'innalialhir rajiun ba har gari ya
waye. Sai dai nayi kuka mai yawa saboda na
kara wayo na san zafin mutuwar sosai ba
kamar da ba, na tausayawa kaina sai nafi
tausayin kanwata munauwara. Gata karama ita
kadai ta rage babu uwa, babu uba, babu ni 'yar
uwarta. Nasan a gidanmu 'yan ubanci akeyi
kowa yana tattalin 'yan dakinsu, nasan sai dai
dangin mahaifiyta ne zasu dauke ta suma
kuma duka kanwar ja ce, talauci ne tsagoronsa.
Rashin kudin motar da za'a kai gawarta
shagamu shi ya hana yaya ya kai ta can a
binne sai kawai ya buga waya ya sanar dasu
wannan mummunan labari. Sun kuwa gigice da
jin haka sai suka yanke shawara gara wasu su
taho kanon ayi jana'iza a binne ta anan. Allah
Ya rubuto anan kasarta take. Da suka iso sai
akayi mata sallah aka binne ta. Kafin kwana
bakwai wasu daga cikin danginmu sai da suka
zo kano sukayi gaisuwa sannan suka koma,
wasu da yawa basu sami damar zuwa ba, da
yake a can ma ana zaman makokin don ba
kowa yake da kudin zuwa ba. Da akayi albashi
ni da yaya hussaini da matarsa mukaje
shagamu don yin gaisuwa da kuma zancen
abinda ta bari. Baiwar Allah bata da komai
daman mijinta bai bar mata komai ba, dan
matan basu samu gida ba! Basu samu gona
ba. Ko mu 'ya'yan kudi kadan aka bamu da
akayiwa gidan da gona kudi wani yayanmu ne
ya saya dan ba zai rabu ba. Daga ragargajejjen
gadonta sai tsumokaren kayanta aka ajiye
mana shine gadonmu. Na kasance marainiya
babu uwa ba uba, sai ni sai halina sai kuma
yayana hussaini da matarsa sai Allah. Kuma
ina godiya ga Allah a kowanne lokaci don ban
mantawa da nasihohin da mahaifina yayi min
ta karshe. Allah yana ganina, kuma Yana
taimakona, Bai bari na tagayyara ba. Babbar
baiwar da Allah ya min itace daya bani jama'a,
masu sona suna da yawa a duniya, mata da
maza. Yara da manya kowa yana yabon
halayyata koda kuwa an kushe ni sai kaji ana
yabona. Na godewa Allah Shine gatana shine
majibancin al'amurana. Aisha farida ta rushe
da kuka hade da hawaye mai radadin fita.
Hawaye ne yake ta kwaranya tamkar an bude
ruwa a famfo. Barrister Mu'azzam ya juya ya
dubi abokinsa barrister nuruddeen shima ya
kalle shi sannan suka juya su dukka suka sake
duban aisha farida, suka cigaba da mamakin
wannan yarinya mai surutu da zazzakar murya,
ga iya magana tana fitar da kalamai dalla dalla
a jejjere tamkar wacce wani ya labe yake rada
mata. Wannan itace fadi ba'a tambaye ki ba,
amma fa sunji dadin sauraron labarinta, yayi
ma'ana kuma sun karu da abubuwa da yawa
na game da zamantakewar rayuwa. Sannan sun
tausaya mata, ta cancanci a tausaya mata
domin rayuwarta tana cike da abubuwan ban
tausayi. Daga ganin ta a kidme take a dimauce
ta fado musu ta gaishe su, kafin su amsa ta
sami kujera ta zauna ta hau basu labari. Yau
ne rana ta farko da suka fara ganinta a
rayuwarsu itama haka, farida batasan wacce
irin damuwa bace ta hana su zama a gidajensu
suka fito a cikin daren nan suka zauna a wajen
shakatawa mai suna "fish park" dake
nassarawa GRA. Barrister muazzam ya zaro
dan karamin handkerchief fari kal daga gaban
aljihun rigarsa (suit) ya mika mata ba tare da
yayi magana ba, ta dago da jajayen idanuwanta
tana gogewa wani sabon hawaye fil yana
bulbulowa daga idanuwanta. Barrister
muazzam ya mika hannu a sanyaye kan teburin
dake gabansu ya dauko wani kwalin lemo ya
tsiyaya a cikin kofuna biyun da suke gabansu
ya mika mata, sai ta karba sannan tayi godiya
ta fara kurba a cikin nutsuwa yayin da shima
ya dauki daya kofin ya kwankwadi lemon a
cikin kofin ya mikawa abokinsa shima ya karba
ya fara sha ba tare da wani daga cikinsu yace
uffan ba. Sai aisha farida ta fara tunanin ko
kurame ne bata sani ba tazo ta hau su da
surutu, saboda tun sanda ta zo ta zauna ana
fiye da mintuna talatin babu wanda yayi ko tari
a cikinsu har yanzu sai kallonta kawai sukeyi
da ido. Ta kurbi lemo ta ajiye kofin akan teburi
ta sharce hawaye da hankicin dake hannunta
tayi murmushi. Tace bayin Allah shin baku
magana ne, ko kurame ne?
Kallonta kawai suke yi har yanzu babu wanda
ya tanka mata, su kalleta su juya su kalli
junansu. Sai taji hankalinta ya tashi, tayi ajiyar
zuciya tace yaya sunanku? Barista nuruddeen
ya dubi barr muazzam ya kifta masa ido
alamar kada yayi magana. Suka ci gaba da
sauraronta tana ta magana ita kadai, sai taji ta
zama tamkar wata mahaukaciya wacce bata
san ma abinda take yi ba, taji duk ta tsani
rayuwarta, sai ta tashi a sanyaye ta juya zata
tafi. Barr muazzam yaji tausayinta sai yace
aisha farida meyasa zaki tafi? Ta juyo da sauri
ta dube shi sai ta girgiza kai tace kuyi hakuri
ban san na takura muku ba, na shiga masifa,
na shiga kunci har na dimauce ban san dalilin
da yasa nazo wajenku na dinga zazzago muku
labari baku tambaye ni ba. Na ganku
kammalallu dan haka na zata zaku karbe ni
hannu bibibuy , kuba bani shawara dan ban san
abinda zanyi ba anan gaba. Barr muazzam
yace dawo ki zauna, shirun da mukayi miki don
bamu sanki ba kuma bamu san manufarki ba
kinsan duniya abar tsoro ce bai kamata nan da
nan ka yarda da mutumin da baka taba gani
ba. Kuncin rayuwar kuwa mun fiki shiga shine
ya fito damu nan ko Allah zaisa muji dan
sanyi. Ta dawo ta zauna a sanyaye ya yin da
take tuhumar kanta da laifin rashin hankali,tana
jin haushin kuskuren data tafka daga ganin
mutane bata san su ba kawai ta zo ta zauna ta
hau basu labari,ta fadi sirrinta bayan ba'a
tambaye ta ba,lallai dole suyi mata kallon wata
sakarya. Ta tambayi zuciyarta shin ko cutar
tabin hankali ce ta kama brain din ta domin
sanda ma ta fara magana bata sani ba.
Mu'azzam ne ya ktse tunanin da take yi ya ce
"ni sunana Barr Mu'azzam,abokina kuma Barr.
Nuruddin. Mecece takamaimiyar matsalarki?
Menene dalilin da ya fito da ke daga gidanku
zuwa nan a cikin daren nan? Naga ba tare da
mijinki ku ka zo sayan kifi ba kamar yadda
nake ganin wasu ma'auratan hausawanmu na
yi? Me kika fito nema? Wanne irin taimako kike
nema daga garemu? Kina so mu saya miki kifi
ne ko kuwa kudin mota ki ke nema? Ta yi
murmushi ta ce "gaskiya ne,na cancanci a
tambaye ni domin ban yi kama da mai kamun
kai ba. A rude na shigo nan dan yau ne rana ta
farko dana taba zuwa nan,ban san inda zan
nufa ba sai na hango ku kawai na ji a raina
tamkar naga yayyena,wadanda zasu iya
taimakona shine na taho wajen ku ko Allah zai
sa ku kwace ni daga mugun dan sandan da
yake shirin cutar da rayuwata. Barr nuruddin ya
dubi abokinsa ya tsuke fuska ya ce "kai kada fa
ka yayumo mana ruwan dafa kanmu,ka bar
yarinyar nan ta kama gabanta. Me yasa ka
dawo da ita har ta yi niyyar tafiya? Ka cika
kwashe- kwashe kamar baka san irin yan
matan nan ba ne yan club? Idan ba yar club ba
wacce budurwar kirki ce zata baro gidan
iyayenta ta shigo wajen nan da dare? Ka duba
ka ga nisan unguwarsu tun daga cikin gari
zuwa nan? Zuwa ta yi ta tsara mu ko daya
daga cikinmu zai dauke ta. Ke yarinya ki kama
gabanki mu ba irinki bane,je ki can ki sami yan
uwanki irin ki. Shawarar da zan baki kuma ita
ce ki koma skul ki taimaki lyf din ki don yawan
duniya ba riba sai asara,akamr yadda kika ce
mahaifinki ya yi maki wasiyya kafin ya rasu"
aisha farida tayi dariya maimakon ta ji haishi
sai ta gyada kai tace "gaskiya ne yayana na ji
dadin shwararka kuma zan dauka insha Allah
zanyi amfani da ita. Sai nauyi da kunya ya
kama barrista mu'azzam ya ji kamar ya nutse
a cikn kasa saboda baranbaramar da abokinsa
yake yi,baya kara,ba kunya balle jin nauyi yake
maganarsa,ya harare shi yace haba nuraddin
kai fa mtsalata da kai kwaba mahgana babu
taunawa. Ka bari ka ji uzurinta idan ka gama
jin inda ta nufa sai ka yanke mata hukunci.
Kamar ba lauya ba ai sai ka gama sauraron
labarinta tun daga farko har karshe sannan ka
gama jero mata tambayoyi ta gama amsawa
ka kula da inda ta nufa sannan ka yi mata
nasiha ba fada ba. Yanzu da a kotu muke sai
ka fadi a sharia dan kawai kana jin haushin ka
sai ka huce akan yar mutane,to ba ita ta kar
zomon ba ko rataya ba'a bata ba.
Posted by Bashir Sani Mahmud on 22 Aug 2017
Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai
laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai
ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi
muku surutu, nasan ba'a son mace marar
kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace
zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna
a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya
zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi
mana sallama duk da tun kafin mu amsa har
kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar
mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika
zarce da bamu labari shine abinda ya daure
mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna
yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin
ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman
abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu
matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada
mana mu dake sai mu taimaki juna da
shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike
tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama
kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba
zan iya zama ina sauraron wannan shirmen
naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba,
daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da
ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji
matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama
bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta
bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci
sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka
matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina
fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga
hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha
farida da barr muazzam suka bishi da kallo har
sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da
kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga
idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da
komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani
labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin
mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi
murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko
kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai
abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar
tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum
na farko a rayuwata daya taba jifata da
wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni
ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr
muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da
bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki.
Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura
gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da
irinkukannan yaukimani wata takwas
kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa
kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi
yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake
zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki
da daukakardakikasamu kozansamisukuni
yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI
NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai
yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen
sabongari na zana jarabawar common entrance
ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa
sai naci jarabawa aka turani makarantar da na
zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya
karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden
makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya
barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo,
gashi bansan kowa ba a makarantar amma
daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai
na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a
na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi
da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son
ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na
yi suna a makarantar nan da nan malamai ma
suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya
magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga
aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu
sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min
siyayya ba da biyan kudin makaranta ba
kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba
kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na
farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar,
sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a
jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin
haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci
ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya
kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan
koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya
harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da
ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani
hakuri cewar zai mayar dani makarantar
gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na
koma makarantar shekara naci gaba da karatu,
daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin
dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a
FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa
da yaran hausawan da suka sami horon turanci
tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science
class) har Allah ya kaini aji shida aka bani
shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara
ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni
nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan
babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar
makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana
kwatance dani saboda kokarina. Da muka
gama makarantar ita da malamai sai da sukayi
takaicin rashina saboda ba'a sami madadina
ba. Bayan gama makarantata da wata uku
yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani
kudin mota da guzuri na zuwa shagamu,
saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da
'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani.
Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da
tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu
daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba.
Ina samun wasikun kanwata munauwara akai
akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai
ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar
an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3
anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai
yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu,
dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba
zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan
'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya
suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk
da rashin wadatar da muke ciki a kano sai
naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da
gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa
har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda
yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege
a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi,
gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye
da ashirin, yare kala kala kamar hausawa,
yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban.
Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara
layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan
shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita
kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin.
Saboda tausayin halinda na same ta kusan
dukka kayana na sakawa na bata kyauta,
sannan na hada mata mayafai, sarkokina,
takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk
kudaden dana samu na bata dukka kudin mota
na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha
kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na
tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan
rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake
haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu
komai duk na rabar da kyana kuma da masu
kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin,
yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na
dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan
haka na daina zuwa taron biki ko gidan
kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi
garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye
wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min
wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta
kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka
inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da
cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da
shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan
zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya
kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna
bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana
suka ga