Showing 30001 words to 33000 words out of 99881 words
da sukeyi komai nasa na musamman ne da ko mace kafin a samu me gudanar ir
in wannan classy rayuwar sai an tona.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#AMEENATOU BABBAH
#THE SEELAHS
#ROMANCE
#ZAFIN KAI
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadd
a zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp on
ly 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu
700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ay
i tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[2/24, 1:36 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
18
Shekarun Dr Jamaal Seelah Kusan 15 zuwa 16 da dawowa hannun Dad dinsa kwata kwata,
Kuma a wainnan shekarun abubuwa da yawa sun faru wainda suke akan wani matsayi na daba
n.
Tinda Jamaal ya dawo gurin mahaifinsa ya zama dukkanin wani abin alfahin Dad din sbd iliminsa da zafin kansa a komai daban yake Dana kowa dayake cikin ahalin seelahs,
Likita ne shi Kuma marikin dukiyar mahaifinsa ne shi Mai kulawa da kusan duka ka
mfaninsu batareda Saka hannun Haroon aciki ba sbd gaba Daya Haroon ya koma tamkar wani matsoraci kaman yanda Dad din ke fada shiyasa kwata kwata Dad din Baya wani yinsa.
Haroon shine yasan ciki da wajen huldodin su Dad sosai sbd shine lawyer dinsa a yan
zu Daya zama cikakken lawyer me zaman kansa Kuma kwararren Daya San aikinsa,
Yasan duka boyayyun illegal huldodinsu da Babu Wanda JEEY ya sbd tsananin taka tsantsan da boyewan da suke masa Dad Baya kaunar yasan ko aikinsa Daya mara kyau Dan kuwa JAMAAL di
n na sani zai iya barinsa har abada ya komawa Dr Aleena Kuma zai iya Jin haushi ko tsanarsa ko janyewa daga garesa Dan haka duk wata mummunan boyayyar harkarsu Babu wadda JAMAAL SEELAH ya sani suna tsananin kiyaye Hakan,
Haroon Daya San komai baida ikon
fadawa JAMAAL din bare Bude hanya komai kankantarta da JAMAAL din ze sani hakama shi Daya sani Yana taka tsantsan sosai akan bayyanar sirrinsu sbd sanin hukunce Sharia da shariar kanta,
Sharia da aikin shariar ya ratsasa sosai da yake kiyaye kaidojin aik
insa Baya shiga shiga huldodin Amma dai shine me riqe da mukullin rufe sirrin batareda barin hanyar fitarsa ko kadan ba hakama Baya taba barin kowace matsalar da zata bayyanarda huldar iyayensa ta aikin danyar zinariyar Dake tafiya da rayukan mutanen da Ba
su da adadi ba hakama da drugs masu tsananin hadarin gaske wainda BB ne akan wannan bangaren duk da shine riqe da sirrinsu na boye da babu Wanda ya sani Haroon din Shima baisan iyayen nasu sun taba dauka rayukan mutane da hannuwansu ba Kuma Yan uwansu tamk
ar jininsu Dan haka Bai taba kallan Dad dinsa ko daddy lameenu a matsayin komai ba face jajirtaccin Dake Gina ahalin seelahs a boye batareda sanin irin gwagwarmayar dasuke fama da ita ba.
JAMAAL SEELAH a yanzu da dukiyarsu da komai yake hannunsa Yana gu
danar dasu ne akan ilimi da kwarewa sosai dukiyarsu Daketa business din gaskia da duniya ta sani take sake habbaka da samun cigaba da nasarori Dan haka Dad ke sake Jin tsananin alfahari da farin cikin kasancewar Dr Jamaal Seelah dansa ne jininsa ne.
A c
an Poland a asibitin mahaifiyarsa yake aiki Amma anan din duk girma da tsari tareda dukiya me yawan da Dad dinsa ya kashe aka Gina masa asibitinsa ta kansa maidata yayi asibitin marasa karfi da tallafi Dan kuwa raayinsa ne gidan asibitin duba mara lafiya c
ikin tsananin sauki da Bada taimako sosai.
Hakan da yayi Dad Bai hanasa ba Bai Kuma nuna komaiba duk da Hakan yayi tsananin Bata ransa Se kawai sukai Hakan batareda saninsa ba ana kawo magani mara quality a asibitin Amma cikin ikon Allah Hakan Bai taba
bawa Dr JAMAAL din matsalaba saima sake daukaka da suna da mutunci harma da girma dayake samu gurin mutane sbd tausayinsa duk da kwata kwata baida sakewa ko kadan sai a gurin patients dinsa wannan zakaga ya sake musu kyakkyawar fuskarsa me daukan ido sosai
Amma badai ma'aikatansa ba harna asibiti harna sauran business dinsa.
Daga Baya Suma su Dad da sukaga asibitin sake qarawa SEELAHs girma da mutunci sosai takeyi tareda mutunci sai suka koma suna Jin dadin Hakan Amma dai a fili kawai cikin ransu Dad din
Babu abinda yake so da burin kaman Jamaal ya aje komai kwata kwata ya shiga cikin huldansu ya riqe komai sbd dagashi har
daddy lameenu kallan Jamaal sukeyi amatsayin sa'arsu Dan duk abinda ya Saka musu hannu Akai sai yayi musu yanda sukeso harma fiye Dan
haka suka rasa yanda zasuyi su sakashi cikin huldansu na boye sunada tabbacin zasu samu harma abinda basutaba tinanin samu ba karshe ma dukiyar Omar Dake kashesu da ransu a duk numfashin dasuke shaqa tasu zaso tafi tasa su Dena wahalarda kansu duk da ciwon
dukiyar Omar da rayuwarsa ma gaba Daya wani mummunan kurjin ciwo ne Da Babu ranarda zai fashe yabarsu saisun rufe kasa da idanuwansa.
Dr Jamaal Bai cika zama available sosai ba a Seelahs specialist da safe sai yamma Kokuma da daddare shine Asalin lokac
inda kake samunsa a asibitin Dan yafi samun nutsuwa sosai acan da dare zai zagaya patients nasu sosai ya duba su tareda Basu kulawa sosai.
Su kuwa a bangaren su Dad Hakan shine daidai yayi musu
Da safe Yana tareda su a gurin aiki da yamma zuwa dare Ya
na asibitinsa sukuma ana gudanar musu da tasu huldar lokutan.
********Rayuwa tayiwa kowa yanda yake so sosai harma da qari dan kuwa lokaci yaja ayau sunkai JAMAAL SEELAH yana musu huldodinsu da duk sukeso batareda yasan da yawa ayyukan dayake musu na
harkar banza bane sun taru sun rufesa duk da kulawansa sosai sun fisa kiyayewa sbd Bai taba tinanin wani abu Yana gudana a cikin familynsa ba da Bai saniba,
Sam Babu tsoro ko shakka ko rashin saa a lamarinsa saima izza da Kai tsayen da Babu acikin famil
yn kamansa,
Idan akwai abinda yafi farin ciki da Kwanciyar hankali tareda alfahari da Jin Babu kamansa to Dad Mam Yana ciki,ko sunan wani idan ba Jamaal ba bayason ana ambata a 'dansa,
A duniya ko asirinsa Baya tsoron ya bayyana ga duniya kaman yanda
shakkarsa Daya da tsoronsa Daya JAMAAL yasan su din su waye ne,
Me sukeyi a boye,
Ina suke zuwa,
Me suke hadawa da kuncewa uwa Uba abubuwan da sukai da rayukan da suka kawar ciki hadda na Dad Omar dinsa Daya kasa cire masa shi daga zuciyarsa kwata kwat
a duk kwata kwata haryanxu Babu Hulda tsakaninsu da Omar din.
Wannan kadai ne yake jijjiga zuciyarsu da tsoro da fargaba Amma bayan wannan ko Hukuma da duk wata sharia da masu yinta baima daukesu abin sakawa a lissafi ba Dan ya Dade da karbe wannan powe
r din a hannunsa dukkanin wata hukuma da sharia sune suke juyata yanda sukeso su Saka a kawar musu da Wanda duk sukeso da sunan sharia.
Yanzu cigaba da karfin da suka sake samu akan barnarsu shine da sharia suke amfani a kawar Dana kawarwa a rufe na ruf
ewa har karshen rayuwa,
Sun Dena Bata hannuwansu da jini Amma na Abinda Omar ya Haifa da Omar din shikam halastacce ne a gurinsu.
A bangaren Daddy lameenu ma kaman yanda Mam ke bugun gaba da alfahari da Jamaal haka yake wannan alfaharin dashi Dan kuwa
manyanci ya Saka da yawa fiyeda Rabin nauyin dayake kansu Jamaal din ya dauke musu hakama Bai taba banbanta matsayi ko kaunar Dad dinsa akanshi ba sbd sanin shi din qanin mahaifinsa dayake kallo uwa Daya Uba dayane Dan haryanxu kaf familyn Babu Wanda harya
nxu yasan ba uwa Daya Uba Daya SEELAHs suke ba.
Allah ya hore musu Jamaal din fiyeda yanda sukai tinanin samun ya dawo gurinsu dan haka Dr JAMAAL JEEY MAM SEELAH ya zama tamkar wani kofa ko bangon kariya da dukkanin ahalin seelahs Tako ina shi zaka fara
tinkara idan zaka tinkari familynsa musamman iyayensa.
Haroon seelah tini ya zama kaman wani shadow a gidan baka cika jinsa ba idan ba mugun abinsu da Jamaal Bai saniba bane zasu yi to shine zaa nemosa.
Kauna da shakuwa dayake tsakanin twins din wan
i irin karfi gareta da Babu ranar da Dad Baya bawa Haroon tabbacin kada Koda wasa Jamaal yasan meye sirrin dayake gudana a cikin seelahs Dan hakan daidai yake da rabasu da zaiyi har abada,
Shi kansa Haroon tsoro da shakkar bari Jamaal Koda tsautsayi yasan
wani abu ko fahimtar wani abu bare sanarda shi Dan gudu da shakkar fitintinu da tashin hankalin dazai iya biyowa Baya,
Shi kansa Yana shakkar Jamaal yasan cewa shi yasan komai Amma Bai sanar masa ba Dan haka Shima a cikin shakka da taka tsantsan din Jam
aal yake.
******Yau a gida ya kwana sbd tafiyan dayayi wani aiki da suke Gina sabuwar kamfanin qera karfe na Seelahs a Nasarawa ba a cikin gari ba can wajen gari sosai kusada wani kauyen da Baya nesa da cikin Nasarawa din hakama kusan filin Gina kamfani
n ya shiga garin sosai Dan haka kaman a garin ma zaa ce kamfanin take dan girmansa yaci kusan garin sosai.
Baccin ragewa jikinsa gajiya yayi na kusan awa uku bayan dawowan nasa kafin ya tashi sanyeda farar doguwar wandon TT me santsi ta kayan bacci.
Jikinsa Babu Riga daga doguwar wandon data zauna a qugunsa kaman zata sauka sai farar fatar jikinsa Dake glowing tana daukan ido hutun dayake cikin Yana bayyana.
Ba slippers a fafaren qafafunsa sbd saukowansa daga gado kenan Kai tsaye toilet ya nufa Kai
tsaye ya Bude ya tareda zira takarmin toilet din marasa nauyi da dadin takawa ya zare doguwar wandonsa Yana nufar shower Kai tsaye Dan wankan yake buqata kafin komai.
Ya jima a cikin toilet din ba sosai ba kafin ya fito daure da towel ash daure a qugun
sa kaman towel din zata Fadi sbd lazy daurin da yayi masa
qamshin shower gel na LE LABO SANTAL ne ke tashi jikinsa ahankali me sanyin dadin shaqa.
Ficewa yayi daga bedroom din nasa a yanda yake ya nufi hanyar dining room.
Fridge ya nufa Kai tsaye y
a Bude ya dauko energy drink din E-Bull ya Bude yakai bakinsa yasha Yana juyowa yaji an Bude kofar palonsa Kai tsaye an shigo batareda ya waiwayoba yasan Haroon ne sbd shi kadai ne me shigowa bangarensa Kai tsaye batareda buqatan kira a waya Dan Jin Yana N
an ko Neman izinin shigowa.
Haroon Daya qaraso tsakiyar palon tareda nufo inda Jamaal din yake Kai tsaye
Yana kallan yanayinsa Haroon yayi ya Dan dauke Kai Yana Bude fridge din shima ya dauko drink din me sanyi kadan ya Bude yafara Sha Yana son sanar
da Jamaal din son karban harkar sabuwar kamfanin nasu na Nasarawa.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#AMEENATOU BABBAH
#THE SEELAHS
#ROMANCE
#ZAFIN KAI
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina ne
man inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan
number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 090
33181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[2/26, 1:52 PM] MG: *_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
19
Haroon duk yanda yaso sanar da Jamaal kasawa yayi sbd shigarsa a aikin site din bazaiyiba tinda kwata kwata bayas
on aiki guri Daya da Jamaal inde na kulawa da harkokin Dad dinsu ne Dan tsoron bawa Jamaal daman fahimtar wani abin Koda tsautsayi ne Dan haka yauma hadiye zancensa yayi Yana dawowa Palo ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerun palon Yana cewa
"Amm
a yau din a gida zaka kwana tinda tafiya ka dawo ba buqatan zuwa asibitin ko?"
JEEY din baice komaiba Saida ya karasa shenye abinda yake hannunsa ya ajiye gwangwanin E-Bull din ya juyo Yana nufar hanyar bedroom dinsa Yana gyara towel dinsa kadan Daya ku
sa zubewa a qasa ya Bude Baki Yana cewa
"Inada patients Dake jiran dawowana na dubasu,
And inada ma da surgery da zanyi so meyasa zanyi kwanciyana a gida?
I can't even sleep or have a rest if ba hospital din naje ba you know that"
Yana kaiwa Nan ya
shige bedroom dinsa Dan shiryowa.
Bai wani jima sosai ba ya fito shirye cikin farar freesize Casablanca hoodie rigar data bayyanarda freshness dinsa sosai
sai half trousers fari Shima da slippers din Bally a kafarsa da haskenta da tsaftanta kaman ba
akai yake tafiya ba.
Qamshin turaren Allure ne na Chanel ya gauraye palon gabaki Daya daga fitowarsa Wanda ya tabbatarwa da Haroon ya fito ya Dan dago nasa fararen idanuwan Shima ya kallesa Yana ajiye remote dayake hannunsa Yana sauya channel Yana duba
time na agogon dayake daure a hannunsa yace
"Please kayi dinner damu mana to kafin ka tafi asibitin,Dad yayi tinanin zuwanka da Rana Kaci abinci tareda mu amma baka fito ba."
Zama yayi kusa da Haroon din Yana kunna wayarsa da tinda ya shigo gida ya k
asheta Dan samun hutun dayake buqata.
Zamansu guri Daya ne kadai wasu lokutan yake taimakawa kowa ganesu da tareda banbance waye Jamaal waye Haroon sbd fatarsu Daya Dan banbanta sai Kuma halayya da yanayi Amma suna rabewa basa guri Daya shikenan gane wa
ye wannan waye wancan zaiyi matiqar yin wuya har Dad dinsu kuwa musamman idan zaiyi maganar Sirri da Haroon ya ringa kokarin tantancewa kenan kada yaje yayi da Jamaal ya lalata aikin shekara da shekaru.
Cikin sauti me nutsuwa da Kwanciyar hankali ya Bud
e Baki yace
"Idan na tsaya Kaine zaka kaini asibiti bazan driving ba ka yadda da Hakan?"
Murmushi me kyau da nutsuwa Haroon ya sake Yana gyada Kai da cewa
"Har bakin office ma kuwa zan kaika DR JAMAAL SEELAH."
Murmushi Shima ya saki Yana kallan
Haroon din Dake Dora masa da bayanin yanda Dad zaiji dadin Hakan Dan farin cikinsa a rayuwa ya zauna table cin abinci da gabaki Daya iyalinsa.
Kiran sallan magrib ya Saka Haroon miqewa ya nufi hanyar Daya bedroom din dayake palon na Jamaal Yana cewa
"Kayi magana da mum kuwa?takira dazu tana buqatan sanin yanda ka dawo wayanka is off."
Shigewa yayi bedroom din batareda yaji amsan JAMAAL din ba,
Toilet ya nufa Kai tsaye yayo alwala ya fito suka fito tare zuwa masallacin gidan da suke sallah a ciki
tareda su Dad da masu gadinsu da securities.
Tareda iyayensu sukai sallah suna gamawa sukayo ciki gaba Daya Banda Dad Lameenu daya fita tareda drivernsa zuwa wani gurin.
Dad cikin kulawa ya Kalli Jamaal Dake cika masa ido tamkar bashine ya haifesa b
a ya tambayesa yanayin aikin Nasarawan Dan kuwa ba qananun dukiya zuka zubawa wannan aikin ba Wanda idan bakiyiba zasu tafka asarar da jijjigasu matiqa Dan haka Koda wasa bari kowa ya Saka hannu a aikinba sai Jamaal ne kadai project din da komai da komai y
ake hannunsa.
Cikin nutsuwa suke tattaunawa har suka Isa cikin main palon mansion din inda yake tsare da luxuries na Jin dadin rayuwa da asalin Hutu.
Hanyar dining room suka nufa dukkaninsu daidai fitowan mum Atey da itama Hutu da Jin dadin rayuwa ya
ke bayyane a tattareda ita.
Tana ganin Jamaal ta washe Baki cikin kulawa tana cewa
"Dr jeey tin dazu nake cewa kana hutawa baka fitoba bare muyi Maka barka da dawowa"
Dan kallanta tayi a gazarce Yana Dan sake fuska kadan batareda murmushinsa ya ba
yyana ba ya amsa da
"Eh na gaji ne Koda na iso Ina buqatan ishashiyan Hutu,.thank you"
Fitowan Ayesha 'yarta ne ya sakashi Dan daga girarsa Daya sama Yana Dan dauke kallansa daga gefen kwata kwata suna cigaba da magana da Dad akan abinda suke tattau
nawa.
Gurin Haroon ta nufa tana sake fuskanta gaba Daya da farin cikin ganin Jamaal din tace
"Dr sannu da dawowa."
Batareda ya waiwayoba yanda ya kamata ya Dan juyo kadan yace
"Yawwa thank you"
Zama tayi a kujeran kusa da Haroon tana gaida D
ad Shima kafin ta dawo da kallanta kan Haroon tana magana kasa kasa kada kowa yaji me take fada masa Yana dariya fuskansa a sake sosai sbd akwai shaquwa da kulawa sosai a tsakaninsu.
Mum kuwa gefen Dad ta zauna sai ya zamana gefen Jamaal din shi kadai n
e Daman Hakan shine raayinsa Dan haka take masu aiki suka qarasa kawo abubuwan da Babu a dining din su ruwa da drinks da cutlerys Dan Basu gama hada table ba masu gidan suka hau.
Mum Atee sosai takeson samun shiga kamar me gurin Jamaal sbd tini ta gama
da kame Haroon ta koma itace uwarsa komai da ita yakeyi a matsayin uwa shi kuwa Dr ko a mafarki ba'a Haifa macen da zata maye gurbi ko samun matsayin mahaifiyarsa ba bayan mum dinsa itace kadai tak dinta Dan haka duk tsananin dagiya da son nuna