Showing 63001 words to 66000 words out of 99881 words
sallama suka tafiyarsu Dan Basu guri da 'dansa batareda Haroon din ya fito ba Dan abinda Basu saniba Haroon din Yana jinsu Amma bazai iya fitowa a halinda yake ciki ba su gansa.
Saida suka fice siddeeq yaje rakasu kafin Haroon din ya fito hannuwansa n
a tsananin rawa kansa a qasa idanuwansa jajir Babu kyan Gani hakama a jiqe yake da zufa Mai tsananin gaske,
Babu inda yakejin azaba me tsananin gaske kaman a tsakiyar kansa da kirjinsa,
Jin muryan Dad dinsa a dakin ya karasa karya dukkanin Wani karfi
n halinsa shiyasa ya kasa fitowa Saida su Babbah suka fice Dan ganinsa a wannan halin na mafi Munin rauni zai karya zuciyoyinsu akansa gameda Basu auren macen da bayajin zai iya rayuwar Nan Babu ita su kuwa Ayanda suke tsananin kaunar Ameenatunsu bayajin z
asu taba bawa Wanda bazai iya tsayuwa a gaban mahaifinsa bama ya dago kansa aurenta sbd tinanin bazai iya Bata kariya ba ko kare martabarta.
Hannuwansa Dake rawa sosai kaman zasu qanqame yayi Baya dasu Yana kasa dagowa har lokacin kansa Juyewa yake Nema
n yi.
Zuba masa nasa jajayen idanuwan Mam yaji Yana kallansa sbd baisan ma me zai fara dashi ba sbd baqin ciki da damuwa me tsananin gaske Dan Shima Yana tsaka me wuyar da baisan ta inda zai fara bullowa zancen ba.
Tsadaddiyar wayarsa Daya ajiye gefe
nsa bayan ya zauna ya miqa hannu ya dauka tareda kunnawa ya Nemo hoton Ameenatou ya ajiyewa Haroon din kan centr table Dake gabansa batareda yace komai ba tukuna.
Haroon Daya kasa motsawa bare magana dago jajayen idanuwansa yayi ya Kalli wayar da Dad di
n ya ajiye masa idanuwan suka sauka akan hoton Ameenatou Dake bayyane a ciki tana murmushi sanye da hijab din islamiya.
Mummunan bugawa kirjinsa yayi ya dago idanuwan da sauri sai alokacin ya Kalli Dad din da Shima shi yake kalla Yana kokarin karantar y
anayinsa.
Hannuwansa Dake tsananin rawa ya sake kankamewa Yana sake kallan Dad din da kyau kafin ya Bude bakinsa Dake rawa da muryan Dake bayyanarda tashin hankalin dayafi wanda yake ciki yace
"Dad Kayi hakuri na.....
Katsesa Dad din yayi da cew
a
"Ka manta mace ce ta Raba Dan uwanka da mahaifinsa rabuwa ta har abada?
Ka manta matsalolin rayuwar da muke cikinsu duka ayanzu duk sbd macen da Dan uwanka ya so ne fiyeda kansa da ni mahaifinsa?
Wasu Hawaye ne masu tsananin zafi da radadi suka ga
ngarowa Haroon Dan Bai taba tinanin samun kansa a cikin irin yanayin da Jamaal ya samu kansa ba,
Gwara kaddarar Jamaal sbd shi yanada jarumta da karfin zuciyarsa fuskantar duk Wanda zai shiga tsakaninsa da farin cikinsa matars wadda ya tsayawa har ranar k
arshenta harma a bayan ranta ya tsayawa macen dayake so da dukkanin zuciyarsa.
Wasu zafafan hawayen ne suka sake gangaro masa Yana rintse idanuwansa sbd Yana fatan inama wannan jarumtar zata shigesa ya tsaya akan macen dayakewa mugun son dayakejin yafi
Wanda Dan uwansa yayiwa tasa macen.
Hawayen Dake zubawa daga idanuwan Haroon dinne masu bayyanarda tsananin radadin da zuciyarsa take ciki ya Saka Dad zubawa masa idanuwansa hankalinsa na Neman tashi Dan kuwa duk tsananin quncin da rayuwar Haroon din ta
ke ciki Bai taba zubar da Hawaye ba sai yanxu.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Gu
da biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki
bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[3/7, 7:04 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
38
Ahankali Haroon din yayi qasa sbd kasa riqe jikinsa Dake kakkarwa sosai da yayi har lokacin idanuwansa na kan hoton Ameenatou Dake kan wayar Dad din Yana tsoron me
Dad zeyi da hoton nata.
Zuciyar Dad Dake tsallen tafasa tana quna sosai akan abinda idanuwansa ke gane masa na azabbiyar Son yarinyar dayake hangowa a idanuwa da hawayen 'dansa kwalli Daya daya rage a hannunsa.
Cikin sanyi da tattara nutsuwansa dan
fahimtar komai yanda zai fishesa ya Kalli wayarsa shima tareda zubawa hoton Ameenatou idanuwansa zuciyarsa na shiga shakka da rarrabar tinani akan Aminta da ita ko sabanin Hakan sbd bazaiso tarihi ya Kuma maimaita kansa ba.
Dawo da kallansa yayi akan Ha
roon Yana dauke wayarsa daga kan table din yace
"Sbd itane ka tattarawa dukkanin nutsuwansa kayi Watsi da ita daga aikin dayake gabanka na cika mun alkawarin dakai na sakani alfahari dakai??
Kasan wane yaqin ne a gabanmu akan wannan masifar daka jefamu
akan mace?
Muryansa na kasa fitowa sosai yafara kokarin magana Amma zuwa lokacin ran Dad din ya gama tafasa Dan haka ko sauraronsa beyiba ya miqe tsaye Yana cewa
"Ka shirya a yau din zaka bar Nasarawa ban aminta da zamanka ananba bare sake ziyartar
Nan din,
Kasan me zai faru daga lokacin da na sake samun labarin ko 'dan uwan yarinyar Nan Daya ka sake muamala dashi???
Zasu bata ne gabaki dayansu danginta bazaka sake samun ko labarin Wanda ya taba saninsu ba bare sanin duniyar da suka tafi...
Qarasa zubewa yayi gaban Dad din Yana fashewa da wani irin kuka Mai tsananin tausayi da tashin hankali tareda Neman ficewa hayyaci Yana bawa Dad din hakuri jikinsa da hannuwansa na tsananta rawar Daya fara bawa Dad din mamaki da tsoro ya janye kafafunsa da
karfi cikin zafi zaiyi magana Haroon din ya sake rarrafowa wannan Karan Yana rokonsa da cewa
"Dad Dan Allah kayi hakuri kada ka hanani Ameenatou,
Itace ke bawa zuciyata karfin hali da zuciyan da Banda shi,
Dad nayi Maka alkawarin wanna Karan wlh zan
cika dukkanin buri da abinda kakeso idan ka barni da ita,
Dan Allah Dad ban taba tambayarka komai ba sai ayau din Ina rokon ka barni na aureta nikuma nayi Maka alkawarin zama duka abinda kakeso na zama,
Ka bani Daman karshe Dad zan gyara dukkanin matsala
n da aka samu a wannan aikin nayi alkawarin Hakan please Dad.
Tafasa zuciyar Dad din ke karawa yanajin kaman ya shaqe Haroon din da kansa ya qarasashi Amma Kuma zuciyarsa na yaqi da Hakan Dan bayason rasa Dan Daya rage masa.
Rikicewa Haroon yayi gani
n Dad din baida niyar sauraronsa hakama yasan kaman yanda Dad din ya fada batar dasu Ameenatou Abu ne me saukin gaske duk da Baya tinanin kashesu zaai ko makamancin hakan Amma dai koma Menene rabasa da Ameenatou kaman rabasa da dukkanin sauran Dan hankalin
Daya rage masa ne Dan haka yaji Yana Neman zaucewa gaba Daya Yana tino yanda Jamaal ya rasa fadila har abada sai kawai yaji kansa ya kasa dauka ya sake rarrafowa Yana biyo Dad din cikin matsanancin fita hayyaci daidai Nan siddeeq ya shigo sedai kafin ya k
arasa gurin Haroon din tini yafara wani irin jijjiga Yana buga kansa da kasa Yana ambatar sunan Dad din Dana Ameenatou batareda ma yasan meyakeyiba.
Jini hancinsa da goshinsa suka fara fitarwa harma da bakinsa Yana wani irin fizga take hankalin Dad din
yayi mummunan tashin da baitaba tinanin zaishiga ba ya dawo da sauri Yana Kiran sunan Haroon din da sauri sedai tini ya fice hayyacinsa dukkanin jikinsa na qara jijjiga sosai.
Siddeeq ma cikin matsanancin tashin hankali ya kamo Haroon din Yana janyo pil
low na kujera ya Saka masa Akai tareda birkitasa Yana hanasa bubbuga kansa a tiles da jininsa ke fita sosai.
Rasa abinyi Dad yai Yana shiga sabon tashin hankali da mamakin Menene yake faruwa da rayuwar Haroon din,
Badai shi Kuma haukacewa zaiyiba aka
n mace ba,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun"
Meke faruwa da yayansa?
Innalillahi wainna ilaihirrajiun.
Duk yanda Dad yake tsammanin lamarin ya wuce Nan sbd Haroon take ya koma tamkar me cikakkiyar tabin kwakwalwa duk tsananin zafi da bacin ran daya
zo dashi jin yayi kansa Shima Yana daukan matsanancin zafi.
Siddeeq drawers ya nufa na gado da gaban mirror Yana yamutsa hankali tashe Yana Neman maganinsa Amma kwata kwata ya kasa Gani.
Cikin daga sauti da kidima Dad yake cewa
"Meyake faruwa dash
i ne?
Menene Hakan nake Gani?
Ciwon hauka ya kamasa ne kokuwa?
Menene wannan din???
Duk a jere ciki daga murya da tashin hankali yake jero tambayoyi Yana kamo Haroon din Wanda yake jijjiga har lokacin.
A karkarshi pillow siddeeq ya sami maganin ba
yan ya haukata dakin cikin tashin hankali da mintinan da Basu Fi biyu ba ya iso da sauri yana Bude maganin ya kamo kan Haroon ya Saka masa
Tsaban rudewa Dad dinne da kansa ya dauko ruwa ya miqawa siddeeq ya basa rabi na shiga bakinsa Rabi na zubewa harya
hadiye maganin.
Sakewa jikinsa yayi Dad yayi gaggawan Bada umarnin a fito dashi zuwa asibiti shi kansa siddeeq a daidai wannan lokacin yasan likitocin gaske Haroon yake buqata Dan haka ba Bata lokaci aka kwashi Haroon din sai asibiti.
Suna zuwa aka
karbesa sbd duka jikinsa ya Dena rawa ko wani abin sai kawai aka miqasa da cewan faduwa yayi.
Dayake Mam yasan abinda zai iya faruwa na zuwan Yan jarida take ya Bada izinin securities kada su bar yan jarida zuwa ko sanin komai.
Har yamma sosai suna a
sibitin Haroon Bai farfado ba,
Dad magana yayi da siddeeq sosai yaji komai gameda ciwon Haroon da lokacinda ya fara take ya fahimci ba karamar illa maganinsu keyi masa ba Ashe Dan haka take ya sake shiga tashin hankali da damuwan kada Yan jarida ko kadan
Susan dansa Barr Haroon seelah na fama da tabin kwakwalwa.
A Daren suka koma Abuja dashi sbd hankalin Dad Bai kwanta ba anan din.
Su Babbah da suka samu labarin anbar Nasarawan da Haroon hankalinsu tashi yayi Dan kuwa ciwonsa kenan yayi tsananin gask
e haka suka ringa Kila mintina bayan mintina Dan Jin lafiyansa.
A cikin kwana da wunin Dad yayi sakawa da warwaran datafi dari da hamshin hakama Dad Lameenu ma hakanan ya lallabo ya taho sbd yasan Mam din na cikin damuwa da matsanancin hali Dan haka y
a taho su fuskanci lamarin tare duk da Shima ya kasa warware sbd Bai dawo daidaiba idan ba Jin yayi sun samu mafitan warwara ba.
A cikin kwana da wuni Dad ya tabbatarda irin tsananin so da kwallafa Rai da Haroon yayi akan AMEENATOU sunan Daya riqe Kai t
saye sbd Tinanin dasuketa yawo akansa.
A karon farko da zai sauya raayinsa zuwa wani raayin Dan cimma burinsa cikin sauri da samun mafita biyu,tasa data rasa 'dansa.
Shi kansa Dad Lameenu yashiga firgicin tarihin dayake Neman maimaita kansa,
Idan su
n rasa Jamaal sun tabarbare haka to Haroon dinma dasuke ganin baida amfani suna rasasa karasa tabarbarewa zasuyi komai yazo karshe shikenan.
Farfadowan Haroon Saida ya bawa dukkaninsu tausayi sbd yanajin jikin sosai Dan wanna Karan maganin ya Riga yayi
masa illa sosai da Babu wani abinda zaa iya yi sai ikon Allah.
Su Dad kasa barin kowa yaji zancen sukai sbd a nasu tinanin maganinsu ne yayi masa wannan mummunan illar.
Duk tsananin halin dayake ciki kallan Dad dinsa yayi har lokacin yanajin raunin b
atawa su Dad din Rai dayayi da asarar da shi kansa baisan ta inda zai fara gyara ba.
Rokonsa gafara da sake basa Dama shine abi farko Daya furta Yana rintse idanuwansa.
numfashi Dad din ya sauke tareda Gyara zamansa Yana kallansa cikin nutsuwa yace
"Zan sake baka Daman karshen Amma ba iya akan aikin kadai ba,
Zan nema Maka auren Ameenatou Amma sai idan ka cika alkawarinka ka gyara mummunan Barna da Tsaka me wuyan daka Saka SEELAHs gaba Dayanta aciki idan ba Hakan ba ka manta da maganar aurenta Dan
kuwa har abada bazaka auretaba idan ba Hakan ne ya faru ba"
Rintse idanuwansa yayi hawayen ciki masu dumi suna gangarowa ya gyada kansa cikin wani irin sanyin jikin da mutuwar jikin batareda ya iya cewa komaiba sai tsananin tsoro da shakkan Dayake mama
yesa.
Dad Lameenu da Baice komaiba gyara zama yayi Yana kallan Haroon din cikin nutsuwa Shima ya Bude Baki yace
"Haroon nayi Maka alkawarin bazamu bar garin Nan ba ayau sai munje munyi gaisuwar iyaye da iyayenta sbd Neman Maka aurenta idan har zaka n
utsuwa ka fuskanci nauyin dayake kanka sbd Kaine kaidai zaka iya gyara wannan Barnar data riskemu sbd kafi kowa sanin halinda muke Neman fadawa idan bamu farfado ba.
Tinda suke magana idanuwansa a rufe suka Hawaye masu zafi na gangarowa a acikinsu Saida
Dad Lameenu yayi masa alkawarin nema masa auren ya Bude idanuwan ahankali ya kallesa Yana sauke Kai kasa.
Dad dinsa ma Jin yayi yayi Naam da Hakan Dan shine maslaharsu ayanzu kada su maimaita kuskuren Baya gwara su nema masa auren su juyasa akan abinda
sukeso tinda zai iya komai akanta din.
Duk yanda wani zai samu Daman sanin matsalar ciwon Haroon Saida Dad ya tabbatarda Bata fita ba hatta siddeeq Bai bari likitocin sun bari yasan duk wani abinda aka bincika aka Gano ba har suka sake kwana biyu a gar
in Akai sallamarsa a ranar suka kwasa zuwa Nasarawa Dan Kai gaisuwan Neman auren.
#MAMUH#
[3/7, 7:04 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
****Su babbah da suka samu labarin zuwan da Dad din zasuyi gaisuwa tini aka gyara koina hatta kofar gidansa Saida ak
a share har kofar gidan makota aka shirya tsaf Dan tarbonsu da Aminansa guda biyu da zasu tayasa karban gaisuwan.
Dayake ranar su Dad din zasu koma da wuri suka iso guraren karfe daya na Rana Dan haka su Babbah suka tarbesu da girmamawa da mutuntawa sos
ai har cikin fara isowan gidan babban suka zauna a babbar dadduman da aka shimfida musu me kyau.
Dad Lameenu Dayake amsa gaisuwansu cikin girmamawa da kulawa sosai Shima tareda farin ciki me tsananin da tin anan aka fara farin cikin Samun Sirikai irinsu
da duk kudi da matsayinsu sunsan mutuncin mutane da iya mu'amalantarsu.
Babbah Dad Lameenu yayi kallan tsaf Mintina Yana tantance kamannin nasa da son tabbatarda idan shine Wanda yake tinanin shi dinne.
Ganin irin kallan da Alh Lameenu kewa Babbah y
a sakashi sai farin ciki yake sake shiga Yana sake musu barka da zuwa kafin ya tambaya jikin Haroon cikin kulawa sosai Yana dorawa da cewa sai anjima su Abdul su shiga dubasa Inshallah.
Abinda ya tarasu suka shiga gabatarwa Babu wani Bata lokaci suka ga
batar da kansu da Neman auren Ameenatou da suka zo nemawa dansu Haroon Wanda su Babbah sun sanshi kuma sunsan aikinsa da halayensa daidai gwargwado.
Naam su Babbah sukai kafin suka suka sake gabatar da kansu da shi babban amatsayin mahaifin Ameenatou wa
dda shine ya haifa abarsa da cikinsa Kuma yayi na'am da Hakan ya Kuma bawa Haroon aurenta.
Farin ciki da hamdala suka ringa miqawa ana sake taya juna murna Dad Lameenu ya cire kudin Neman auren Naira dubu dari biyar ya bayar kafin suka sake miqa godiyar
su har lokacin zuciyar lameenu wani tsalle takeyi cikin rudewa da rikicewa Dan kuwa ya sake tabbatarda Babbah ne suka tana Gani asibiti gurin Omar a lokacinda aka taba Kai masa attack idan Bai mantaba Kuma ya sake dubawa ya tabbata Babbah ne ya Gani Wlh.
Abdul da shine babban yayan Ameenatou Kuma dashi Akai zaman Neman auren Alh Lameenu ya kalla cikin kulawa Yana tambayarsa Aikinsa da karatunsa.
Cikin nutsuwa da ladabi Abdul din ya amsa masa matsayin karatunsa da aikin dayake yi.
Take Alh Lameenun
ya nuna raayinsa na Taimkawa yace Abdul din ya hada takardunsa zai Aiko a karba a aika masa Lagos.
Godiya Abdul din yayi su Babbah dasu Alh sabi'u makocin Babbah godiya sukai suna sake nuna Jin dadinsu kafin su Dad suka saki jiki sosai sukai fira da mag
anganu dasu babban anan ma sukai sallah azahar kafin suka Shirin tafiya su Babbah suka rakosu har waje inda motocinsu da securities dinsu suke suka shiga take aka bar gurin dasu.
Suna barin gurin Dad Lameenu zufan dayake hadawa tin acan yana shanye abin
sa a jikinsa ya zari tissue ya goge kafin ya Ciro wayarsa.
Hotunan da BB ya turo musu nasu babban ya Nemo hannuwansa na Dan rawa ya Nemo na Babbah ya zuba masa idanuwansa.
Mam da zuciyarsa kwata kwata Bata cikin dadi Baida energy din tambayar abinda
yake faruwa sbd bayajin zai taba barin ya hada zuria dasu Babbah
Ya nema auren ne sbd yana buqatan Haroon din sbd ya Jamaal ya dawo garesa Amma Badan Hakan ba bayajin zai tana yadda ya Kai kansa Neman auren.
Lameenu Daya sake goge zufansa miqewa Mam w
ayar yayi Yana cewa
"Wannan shine fitilar da zata kaimu ga sanin duk inda dangin matar Omar suke sbd samun Magajinsa"
Kallan wayar Mam yayi kansa na tsananin sarawa da nauyi Amma Jin Abinda Lameenu ya fada ya sakashi cire hannunsa daga goshinsa Daya
dafe idanuwansa a lumshe.
Kallan Lameenu din yayi bayan ya Kalli Babbah a wayar Yana jiran bayaninsa.
Cikin nutsuwa lameenu ya tinatar dashi ganin da sukaiwa Babbah a asibiti tareda Omar shekarun Baya.
A saninsu wancan lokacin daga kauyensu Omar y
ace musu babban yake Amma basusan Menene alaqarsa dashi ba Dan haka dole babba yasan waye yayan matar Omar Kuma bazasu rasa sanin komai ta hanyar Saba Daman a bagiren Neman ko mutum Daya daga kauyen suke amma tsawon shekaru ankasa samu.
Wani sanyayyan s
anyi ne ya ciked zuciyar Mam take yaji nauyin zuciyarsa na rayuwa sedai bayajin zasu samu yanda suke so idan suna nesa dasu Babbah din.
Lameenu Dayasan dalilinsa Daman kenan na buqatan daukan Abdul aiki take ya Saka kira yace a tanadarwa Abdul din aiki
me kyau da gidan zama a Lagos inda zai dauko iyayensa ya dawo dasu.
*********Su Babbah kuwa A nasa bangaren sunan jeden da Omar yake amfani dashi shine ya hanasa sanin shima Omar din seelahs ne Dan haka farin cikinsu kawai sukeyi.
Da daddare da kan
sa shi da su Abdul sukaje suka dubo Haroon