Showing 27001 words to 30000 words out of 99881 words

Chapter 10 - AMEENATOU BOOK1 COMPLETE

MAMUHGEE   

07 Oct 2026

810

mahaifiyarta Dan haka

yarinya taci sunan mahaifiyarta AMEENATOU

Banbanci kawai shi mahaifinta ya kirata da AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH shikuwa Babbah ya ambaceta da AMEENATOU NUHU BABBAH.

duk wani taurin zuciyan Babbah da rashin hakurinsa dawowa yayi sabo fil a take Dan h

aka da karfin hali ya kwana gari na wayewa yasa aka sallamesa batareda ya warke yanda ya kamata ba Amma yanda yakejin zuciyarsa idan ba abinda zuciyarsa keso yayiba zai iya samun bugawar zuciya Dan haka Kai tsaye gida suka nufo.

Suna dawowa wanka kawai

yayi ya fice daga gidan.

Bai dawo ba sai dare.

Yana dawowa ko abinci Bai iya ci ba ya shige dakinsa haka suka kwana jigum jigum kaman gidan zaman makoki.

Da sassafe sai ga baqi sunzo gurinsa.

Dadah na daki tanaji Akai cinikin gidan aka Kai karshe

batareda tsayawa lissafin komaiba Babbah ya sallama gidan take aka Saka masa kudin a banki tareda rubuce rubuce da shedu ya miqa takardun gidan.

Suna wucewa ya sanar da Dadah duk abinda sukeyi a siyar da komai yau washe gari zasu bar garin.

Da farko

hankalinta ya tashi Amma duba da yanda komai yake tafiya da abinda ya faru itama taji zatafi samun nutsuwa Subar inda aka Sansu su koma inda Babu Wanda ya Sansu su Gina sabuwar rayuwa tareda Ameenatou Dan Bata cikakkiyar rayuwar yancin data cancanta.

Tin a ranar suka fara shirye shiryen barin gari sedai Basu samu wucewa washe garin ba Saida Babbah yayi tafiyar kwana shida ya dawo yaje ya Siya musu gida a inda Babu Wanda ya Sansu Kuma baa birni sosai ba a local government sbd samun nutsuwa.

Sunyi ba

nkwana da makota da abokan arziki da kasuwanci sun bar garin gombe batareda sanarwa kowa inda zasu komaba sbd ita kanta Dadah babban Bai sanar da ita ita zasu koma dinba sbd tsaro sedai sunje ta Gani.

Tafiyar wuni guda Mai Nisan gaske sukai sai gasu a w

ani garin da Dadah Batama tantance sunansa ba Amma dai akwai Fulani sosai a garin dayake a gajiya sosai Bata damu da tsayawa tambayar babban ba gashi dare yayi Dan haka Kai tsaye Dan karamin gidansu Daya Siya musu suka Isa Wanda yake sabo ne daidai misalin

rufin asiri Kuma ya Siya komai ya zuba tin daga kan katifun Kwanciya da Yan abubuwan amfani.

Ruwan zafi ya fita ya siyo sukasha shayi da bread sai indomie,

Hakama ya sake fita ya samo ruwan zafi a gurin me shari Wanda bana shayin ba akaiwa Ameenatou w

anka aka gasata sosai sauran su Hafiz suka sukai wankan,

Shima babban wankan yayi Dana sanyi itama dadah Dana sanyi tayi

Dayake sun Riga sunyi sallolinsu tini suka kwanta sai baccin wahala da rashin dadin Rai.

Washe gari duk wani sauran abinda basuda

Saida ya fita ya siyo musu shi ya kawo,

Abinci ma haka ya Siya Wanda zai Dade musu Bai qare ba ya ajiye,

Bai taushe hannu ba ya bazama yaje ya nema makaranta ya Saka su hafiz a a biya kudin da komai daga bokon har Arabic sbd so yake Kai tsaye ya fusk

anci rayuwarsa shida iyalinsa,

Kayan baby Ameenatou kuwa tin daga kayan sakawa har Madara da abubuwan buqatanta Babu abinda Bai siyo ba Dan haka dadah itama ta sake jikinta yanda ya kamata tana kulawa da ita tamkar ma itace ya haihu Dan duka makota da W

anda suka ringa shigowa suna gaisawa sun dauka itace ta haihu din itama Bata Musa din ba sai aketa mata barkan haihuwan ana tambayar sunan yar.

Dayake baai mata yankan suna ba sai da sukai kwana biyu sun gama hutawa da gyaran gidan kafin Babba ya yankaw

a Ameenatoun tasa rago Akaci Akai sadaka.

Tin dukkaninsu sunata fama da kadaici da bakunta har suka fara sabawa tini dadah tafara Yan sana'ointa data Saba Yara ma sun fara zuwa makaranta tini,

Babbah ma shago ya Bude a kusa ba nesa ba na siyarda hats

i Dan haka suka dauki hanyar zama Yan gari musamman Babbah Daya danne komai ya koma babbansa na Baya sbd kawai su zama cikin farin cikinda idan Ameenatou ta tashi itama zata tashi cikin farin ciki tsakanin iyayenta Dan baida niyar tasan basune asalin waind

a suka haifetaba duk da sunyi mata tsufa a iyayen Amma dai sune suka haifetan kawai.

Dan haka ahankali suka nitsa rayuwa na tafiyar dasu cikin Kwanciyar hankali da amince Dan tini ya rufe Babin Omar a rayuwarsa data iyalinsa Dan kuwa bayajin har abada z

ai bari Omar ma yasan inda suke bare tinanin ma yanada 'ya a hannunsu.

*******

Lagos

Zaune suke duk inda jini yake yawo a jikin Mam seelah tafasa yakeyi Yana Jin kaman kansa zai rabe sbd baqin ciki da damuwa.

Shikuwa lameenu tini yafara ficewa

hayyacinsa sbd kansa Bai sake cikakkiyar lafiya ba tinda lamarin Nan ya faru sbd ya kasa tantance gaskiyar abinda yake gudana a Kai da zuciyar Omar Wanda har lokacin baida alaqa da kowa Babu labarinsa.

Ga dukiyar dai ya tafi yabarta kusan a hannunsu Dan

duka kadarorinsa yanzu kusan a hannunsu suke amman Sam basuda nutsuwan cinsu tinda basuda tabbacin Shirun nasa na Menene,

Amma dai ko na Menene Abu Daya suka tabbatarda shi shine fitowarsa Koda zasuyi gaba da gaba ne saisun kar karshen matsalarsu Dan yan

zu rayuwarsa ma itace abin buqatan tinda yasan Menene sukai masa.

Shigowar BB babban Dan hannun damarsu Mam dinne ya Saka Lameenu dagowa da idanuwansa dasukai ja ya kallesa kafin yayi magana cikin girmamawa BB ya Kalli Lameenun kafin ya Maida kallansa

kan Mam Yana Dan sauke Kai cikin nasa zafin zuciyar da fargaban abinda zai fada yace

"Ranka ya Dade binciken da muketa son tabbatarwa akan gawawwakin da jamian tsaro suka fitar bayan kashe gobarar gidan gaskia ne gawa uku kadai aka samu daga cikin gida

sai gawar security dinnan Daya daga waje bayan Kuma idan aka cire Sir Omar da Ahmed gawa BIYAR ya kamata a Gani a cikin gidan.......

Wani mugun zufa me zafin gaske ne ya tsinkowa lameenu kansa na sarawa

Shikuwa Mam wata mummunan sarawa kansa yayi ya d

auki ruwan Dake gabansa yakai bakinsa Yana Sha sbd Jin koina jikinsa kaman Yana ci da wuta.

Dan gyara tsayuwa BB yayi Yana kallan Lameenu Daya zuba masa ido Yana jiran sauran bayanin yaji Shima wani zufa ya tsitsifo masa sbd abinda zai fada yace

"Cik

in gawawwakin da aka samu an samu tantancewa da tabbacin akwai ta matar sir Omar din Amma Kuma Babu ciki a jikin gawar Wanda ni Kuma ta tabbatarda naga tsohon ciki a tareda ita a Daren........

Ruwan da Mam ke Sha ne suka dawo ta hancinsa gaba Daya ba sh

iri sbd mummunan tashin hankalin da Bai taba Jin irinsa ba.

Lameenu kuwa take bugun zuciyarsa ya Nemi tsayawa cak sbd firgicin da Bai taba samun kansa ciki ba.

#MAMUH#

#AMEENATOU

#DR J SEELAH

#DESTINED

#LOVE

#ROMANCE

#LIFE

#REVENGE

#HAROON SEEL

AH

#IDENTICAL TWINS

#ZAFIN KAI

#THE SEELAHS

ASHNA BEAUTY SKINCARE

Free class free class 

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu

muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta

Carwash

Airfreshner

Liquid soap

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*

_M

amuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_

Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_

ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

[2/22, 1:30 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

17

Shi kans

a BB zufan yaje hadawa zuciyarsa na tsalle Dan yasan ansamu babbar matsala data jawo musu wani Sabon aikin me girma daban.

Mam kuwa bayan ta hanci da ruwan suka biyo bar cikin kansa sukai yaji Yana Neman zaucewa da sauri ya dago idanuwansa da suka sauya

take zuwa jajir ya Kalli BB dukkanin jikinsa na Neman sakewa daqyar ya hado kalmomi a bakinsa cikin sanyi da nutsuwan son fahimtar komai daki daki yace

"Wane ciki kake Bada tabbacin ka Gani a jikin matar Omar?

Na haihuwan Dan mutum kokuwa na samun qos

hi datai a gidan??".

Kansa ya saukar kasa bayan ya Kalli lameenu Wanda shi kwata kwata Neman rasa gane komai yakeyi

Ya Dan sake saukar da kansa qasa yace

"Tabbas cikin haihuwa ne a jikinta,

Kuma kaman yanda Daya daga cikin securities dinmu Dake g

anin gidan ya tabbatar mana tabbas tana daukeda juna biyu tsoho matar Sir Omar din..

Hakama a Daren Koda muka shiga ni naga cikin da idanuwana sedai abinda yasa ban fada ba na dauka ba amfani tinda itada cikin sun tafi kenan sai gashi ance Babu ciki a j

ikin gawarta hakama baa samu gawar baby Koda konanniya ce a gidan,

Gashi Babu sauran mutum biyu Daya kamata Suma ace an samu gawarsu a gidan,

Dame aikinta Daya Wanda kowa ya tabbatarda masu aikinta biyu ne hakama a Daren ranar shi Sir Omar din yayi baqo

Wanda bamusan ko wayeshi din ba a gun sir Omar din

a cikin gidan ya kwana muma da idonmu mun gansa mun sumar dashi Amma baa samu gawarsu ba.....

Jinin Mam da lameenu wata irin qunar masifaffen tashin hankali sukeyi musamman Lameenu da idanuwansa suka

rufe baiga cikinba da Saiya tabbatarda a tsakiyar cikinta zai kutsa azabbiyar wuqarsa me barka kayan cikin mutum ya tabbatarda mutuwar haihuwar magaji ko magajiyar Omar jeden seelah.

Mam kuwa a Karan farko da zufar tashin hankali mara misaltuwa ta rufes

a sbd babbar babbar uwar matsala da budaddiyar masifa ta riga ta fadowa rayuwarsu tinda Omar ya rufesu akan samun haihuwarsa hakama idan har Babu ciki a jikin gawa Kuma Babu gawar baby a gidan to ta tabbata Omar ya boye abinda aka haifar masa hakama idan y

a boye abinda ya Haifa Hakan na nufin ya San wani abu Dan bazai yiyu Babu komaiba Omar ya boye musu haihuwarsa ta farko daya kamata ace sune sukaiwa abinda aka haifar huduba Dan shine kaf yakewa nasu yayan huduba.

Wace sabuwar masifar ce wannan ta bullo

musu?

Me Lameenu yayi?

Tayaya zaace yaje yayi aiki irin wannan da kansa Amma ya kasa tantance ciki a jikin Amina..

Cikin wani irin mafi girman tashin hankali da sake jiquwa a zufan gaske duk ac Daya gama cika palon Lameenu yace

"Kenan nakudar ha

ihuwa takeyi a Daren Kokuma wani abin na damunta sbd a dakinta me aikinta Daya take tareda ita hakama Shima Omar ya fito a cikin Daren har harabar gida...... innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Wani kallan baqin ciki da tashin hankali Mai tsananin gaske M

am yayiwa Lameenun Yana Jin inama dashi su BB suka hada suka kashe cikin duhun ya huta da baqin cikin dayake ji yanzu akan wannan shirmen da baqar ranar Daya nuna musu Dan samun haihuwan Omar itace babbar baqar kaddarar data sake Hawa kansu tinda Babu yand

a zaayi ko sun kashe Omar dukiya ta zama tasu yanzu yanada me gadons gaba Daya,

Kashe Omar batareda sun tabbatarda sun gane inda abinda aka haifar masa yake ba kaman aikin banza ne Dan haka dole saisun fara kawar da magaji ko magajiyarsa sun tabbatarda

babu me gadonsa bayansu kafin su kawar dashi,

Gaba Daya yanzu lameenu ya jiqa masu aiki ya dawo musu dashi Baya,

Ta Ina zasu fara da sanin inda ma zasu Gano mutanen biyu Dan idan ma akwai haihuwan ko Babu a bakinsu zasu tabbatarda komai a zahiransa.

Lameenu ma Jin yayi zuciyarsa da gangar jikinsa na rawa sosai akan ta inda zasu fara Neman wannan haihuwar da itace tayi musu shamaki yanzu da cikar buri bama Omar din ba Dan kuwa shi fitowarsa kadaice ta shiga tsakaninsa da mutuwarsa Dan kawar dashi ya z

ama dolen dole tinda yasan komai dabai kamata ya sani ba akansu.

BB kansa ma cikin baqin ciki da zafin zuciyar samun wannan babbar matsalar a aikinsu yakeji duk da yanzu ko zasu rayukan mutane dari saisun Nemo inda mutum biyun Nan suke Dan wannan Karan

Mam seelah ne da kansa sai cike aikin batareda barin matsala ya kawar da matsalarsu.

Dayake Lameenu yasan shine ya Bude kofar wannan sabuwar masifar data samesu Kuma yasan Mam Bai taba samun matsala a abu ba idan ya tashi aiwatarwa a natse yake cikakkiy

ar aikinsa ba damuwa Dan haka duk yashiga damuwa kan tashin hankali Amma dai koma yayane yasan bazasu taba samun baccin nutsuwa daga Nan har shekaru masu zuwa matiqar Mam Bada hannunsa ya kawo karshen jinin Omar ya batar dashi a duniya ba.

Babban arziki

n Omar yaci shine Basu taba sanin qanwar mijin Ayshatu kanwar kasim yake aure ba,

Hakama Basu taba sanin waye ma mijin Ayshatu din ba bare inda yake Dan haka suka bazama sakin mahaukaciyar dukiya Baji ba Gani Mai aikin gidan Omar jeden suke nema da baqons

a,

Amma dai me aikin sukafi Maida hankali nema itada aka sani sbd shi baqon haryanxu basuda tabbacin wayeneshi?

Daga Ina yake?

Meye alaqarsa da Omar din?

Yaya kamanninsa suke?

Dan haka Maryama suke nema ido rufe Baji ba Gani,

Ta bangare Daya kuwa su

aje matsalar Omar a gefe saisun gama data abinda ya Haifa din Wanda suke da tabbacin Yana sane ya boyesa koma inane sbd kada su sani.

**********Ahankali ahankali Suma cikin tsananin rashin Kwanciyar hankalin zuciya da tsananin son cikar buri lokaci

da shekaru suka ja musu batareda sun samu sanin inda Maryama take ba Amma dai Basu taba cire Rai kona daqiqa bane daga tsananta bincikensu Wanda duk tsawon shekarun da aka dauka wannan burin koyaushe karfi da zaquwa yake qarawa ransu sbd kullum dukiyar Oma

r tamkar hakin da ake bawa ruwa takeyi sai yaduwa take sake yi tsananin Sonta da maitarta na karuwa ransu tana yaduwa a jini da gangar jikinsu tareda tsiruwa a zuciyarsu duk kuwa da daukaka da tarin arzikin da Suma suketa qaruwa a rayuwarsu.

*********

********

Shekaru sun tafi a yanzu Sunan SEELAHs Babu inda Bai shiga ba Dan kuwa sunyi wata irin kafuwar da Babu Wanda zai iya girgizasu idan ba ubangijin Daya Basu ba,

Sunyi suna me karfin gaske,

Sunada power fiyeda yanda ake tinani,

Sune masu fada a

ji,

Masu taka Wanda suka so,

Masu yin yanda suke so,

Nera da dollar sun zaunu a SEELAHs kaman basusan meye matsala ba a rayuwarsu,

Tin shekarun da suka gabata suka tashi daga inda suke suka sauya anguwar datafi kowace anguwa tsaro da tarin asalin mas

u nerar data amsa sunanta nera,

Kaman yanda gidajensu suke a jere acan Baya hakama yanzu mansions dinsu a jere suke guda uku sbd duniya su uku ta sani haka zasu cigaba da zama su ukun har sai Omar yabar duniya Dan haka Koda suka tashi barar da dukiya ak

a Gina mansions din da Omar sukayi duk da har lokacin Bai taba dawowa Nigeria ba duk da ya bayyana Amma inda yake rayuwa yanzu komai dukiyar dasuke ji Dan ita Basu Isa su tinkaresa da matsala ba a gurin sbd shi kansa ya goge sosai yanzu baida wani sanyi ko

kawaici kaman Omar din Baya sosai yake tafiyarsa business dinsa da rayuwarsa batareda ya waiwayo Nigeria hakama Yana sane yaqi waiwayo yarsa yafison yagama ganin gudun ruwan Yan uwansa Dan Yana bayyanarda ita zata zama cikin hadari duk tsaron dayakeda shi

bazai iya wasa da rayuwarta ba ya daukota ba Dan yasan ko Babbah zai rasa ransa Yana can Yana kulawa da ita cikin Kwanciyar hankali da tsaro musamman dasuka samu tabbacin su kawun sun bace Babu me labarin inda suke duk bincike kuwa su kansu Basu Gano inda

suke ba Dan haka ma ya kyalesu sai koma ya lafa zai nemeso duk inda suke.

***********

DR JAMAAL SEELAH Wanda aka Fi sani da DR JEEY SEELAH matashin likitan daya qware sosai a aikinsa,

Likita ne da ba iyayensa kadai ba dukkanin mutane suke tsananin

alfahari dashi sbd qwarewansa akan aikinsa duk da ta bangare Daya mutum ne Mai tsananin

zafin Kai da Baya daukan reni barema kallan kadai idan kayi kaine kake Rena kanka sbd asalin abinda ake kira da kwarjini da Asalin class me sakaka kama kanka kawai daga

ganinsa.

Duk duniyarsa mutum uku ne kadai suke ganin Asalin dariya ko kyakkyawar murmushinsa Dake kashe me kallansa,

Daga mahaifiyarsa Rabin ransa da Babu Wanda ya Kai masa ita a duniya,

Sai 'dan uwansa Rabin jikinsa Barr Haroon seelah sai patients

dinsa Suma ba duka ba,

Bayan wainnan ko mahaifinsa dayake tsananin sonsa fiyeda duk abinda ya mallaka Baya ganin wainnan abubuwan daga garesa.

JEEY SEELAH shine Asalin definition na SEELAHs kaman yanda Dad dinsa me fada sbd rashin tsoronsa da zamana

Dan Kai tsaye hakama reni Baya tinkarosa,

Izzarsa da nutsuwarsa tareda class me sanyi ko su iyayensa sun shafa masa lafiya kwarjininsa suke Gani suna daga masa kafa ba kamar Haroon ba duk da idan ba nutsuwa kayi ka tantance kamewan JEEY ba kwata kwata ha

ryanxu baka taba ganesu sbd kamanninsu sosai suke sake kamewa Dana juna.

DR JEEY SEELAH shi gaba Daya kusan rayuwarsa a Poland yayita da mahaifiyarsa harya gama karatu ya fara aiki acan kafin ya tattara ya dawo Nigeria sbd takurawar Dad dinsa da Dan uwa

nsa Amma dai Yana yawan zuwa duba mahaifiyarsa,

Akwai rayuwar turai sosai a tattareda shi musamman duba da yanda yake gudanar da rayuwarsa Dan kwata kwata baya iya rayuwa gida Daya da iyayensa Dan haka Akai masa part dinsa daban a cikin mansion din Wand

a yakeda Dan nesa da bangaren su Dad da Haroon.

Bayan banbancin halayya da rayuwa tsakaninsa da haroon akwai na hasken fata Wanda shi yafi Haroon sbd banbancin tsadaddiyar rayuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login