Showing 1 words to 3000 words out of 52463 words
πκ¨
οΈ
πππππ
πππππκ¨
οΈ
(
ΚΚ
α΄α΄α΄
ΙͺΙ΄Ι’
Κ
α΄κ¨
οΈ
Κ
α΄
s)
β―
DΝAΝZΝZΝLΝIΝNΝGΝ SΝβ―TΝβ―RΝ'β―WΝRΝIΝTΝEΝRΝSΝβ―
β―
πππππππ
ππππ
.
(
π
ππ
πππ
)
πππππππππππππ
,
ππππππ
ππππ
π
π
ππππππ
πππ
πππππππ
ππ
πππππ
.
TALLA.
INA MASU SON YIN
BOOK COVERS,
LOGOS,
INVITATION CARDS
DAMA SAURAN SU??
KU KARZAYO @ASHANTY GRAPHICS KAN FARASHI MAI SAUKI.
π€
π
/1|5
Tuki take cikin nutsuwa fuskarta d'auke da murmushi. Yanayin garin shi ba zafafi ba, ba sanyi ba, ya k'ara sa mata nisha
Ι
i. Sauke glass din motar tayi bayan ta kashe AC wata irin iska mai dad'in gaske dake kad'awa ta
shigo motar. Kyakkyawar mace ce da a kalla za tayi shekara ashirin da biyar. Fara ce ba can ba ,zamu iya kiranta da brown skin mai haske. Tana da manyan ido da kwayar take bak'a wuluk da ita, sai dan siririn hancin ta daya tafi da cikakkiyar girar ta dake
ciki da gashi . Alamun hakan ya nuna tana da gashi sosai saboda goshin ta da gashin yake kwance luf- luf dashi gwanin sha'awa. Hannunta da yasha jan lalle ta miΖa ta d'auko had'addiyar Galaxy d'inta s23 dake ringing Sunan "HABIBIβ€" da Heart emo ya bayya
na jikin ta ra
Ι
au. Kai daga jin irin ki
Ι
an da wayar take kasan kira ne na musamman. Murmushi
tayi da dan Ζaramin bakin ta daya sha man le
Ι
e kafin ta
Ι
aga wayar tayi sallama da sassanyiyar muryar ta dake da mugun da
Ι
i .
"Slma Habibi "
Shiru ne ya ratsa wa
yar na wasu mintina kafin wata irin murya so deep tayi magana.
"Kina ina?"
Murmushi tayi na rashin amsa mata sallaman ta da bai yi ba. Idan da sabo ta saba da wannan Miskilanci nashi.
"On my way Habibi. Ka sauka ne?"
"My flight has been cancelled. Baza
n samu dawowa ba yau, maybe sai jibi ko next week"
Murmushin dake kwance kan fuskarta ne ya b'ace. Wata uku kenan da tafiyar sa kullum da irin excuse da yaka kawowa. Aiki kaza -aiki kaza. Sam bashi da time
Ι
inta dana yaran sa yafi bawa aikin sa muhimmanc
i . Fakin motar tayi a gefen titi murya a sanyaye tace.
"But Habibi gani nan ina hanya na kusa zuwa Airport "
"So, ya za'ayi kenan?. Ko kina so nayi tsuntsune nazo?, akwai aiki mai muhimmanci daya taso min. Saboda haka nayi cancelling zuwa sai next week
in sha Allahu. Ina babies d'ina?"
Wato ita baima damu da ita ba ta yaran sa yake?. Numfashi ta fesar mai zafi
"Suna gurin Ummi. Yanzu zanje na
Ι
auko su."
"OK, ina da meeting yanzu, let's talk anjima"
Kitt ya kashe wayar sa. Zubawa wayar ido tayi idan
ta cike tab da hawaye. ta rasa dalilin da yasa Maheer
Ι
in ta ya chanza. Da ba haka yake ba, cikin
Ι
an ΖanΖanin lokaci ya chanza. Shekara biyar kenan da auren su. Cikin shekarun nan babu wanda bai sheda so da kauna dake tsakanin su ba, a wannan watanni uku
n ya chanza,Bai damu da ya kira ta yaji yanda take ba ko Ζ΄aΖ΄an sa. Bai damu yazo yaga yanda suke ba, bata da ikon tayi fushi zai nuna mata zafi. Ajiyar zuciya ta sauke mai Ζarfi. Sam bata san sawa ranta zargi saboda haka ta bawa ranta aikin ne ya yi masa.
Maheer na santa, san da yake mata tasan babu wan gurbi da wata mace zata zauna a cikin sa. Numfashi ta Ζara ja mai Ζarfi ta lumshe ido ta bu
Ι
e a hankali bakin ta
Ι
auke da Addu'a. A take taji nutsuwa na zuwar mata. Motar ta tayar ta karya kanta ta koma inda
ta fito.
β¦β¦β¦
πππππππ
πππππππ
.
Unguwa ce data tara manya da shuni. Unguwa ce ta masu ku
Ι
i. Masu ku
Ι
in ma wanda suka amsa sunan kudi. katon layi ne ta shige dake shimfi
Ι
e da kwalta ga wasu fitilu da bishiyu masu shegen kyau da suka kara kaw
ata titin. sai da tayi tafiya ma
Ι
an nisa kafin ta fara hango wani katon gate saman shi an rubuta. ALHAJI BALARABE MAI DOKI MANSION. Katon mansion ne daya kunshi gidaje sama da hamsin. Kaf familyn mai doki suna cikin wannan Mansion tun daga kan y'ay'a da j
ikoki. Har tattab'a kunne. Basa auren bare sai nasu. Dalilin da yasa suka habbaka duniya tasan da Alhaji BALARABE MAI DOKI. Mai doki attajirin mutum ne daya tara dukiya da babu adadi. Har zuwa yanzu da jikoki da ya' y'a ke morar dukiyar tasa ,su kansu bas
u san adadin ku
Ι
in da mahaifin su/kakan su ya mutu ya bari ba. Alhaji mai doki yana d'aya daga cikin masu ku
Ι
in duniya.
B'angaren da yafi ko ina girma da kyau cikin mansion d'in ta shige wajen farking inda motoci wajen ashirin masu shigen tsada ke fake.
A guje wasu yara suka fito mace da namiji kyawawan gaske za kayi mamaki idan kaga yanda namijin keda uban gashi an tufke masa shi jelar ta kwanta bayan sa. Macen kuwa duda yarinya ce k'arama da bata wuce shekara biyu ba gashin ta har kugu bak'i mai santsin
gaske.
"Momy, Momy"
Da sauri ta fito daga motar tana murmushi ta durkusa ta bu
Ι
e musu hannu. A guje suka shige kirjinta suna dariya. ANNOOR ne ya d'ago ya kalle ta
"Momy ina Daddy?"
Murmushi tayi masa tana shafa gashin kansa mai shegen laushi da sant
si kaman ba namiji.
"Yana nan zai zo. Aikine ya yi masa yawa"
B'ata rai yaron ya yi kaman zaiyi kuka, itama Baby Ablah tayi narai-narai da nata manyan idon. Murmushi RIENA tayi mai ciwo ta k'ara rungume yaran cikin k'irjin ta.
"Daddy yana nan zai zo kun
ji, muje muyi sallama da Ummi sai muje, za kusha ice-cream da chocolate? "
Nan da nan suka saki ran su suna tsalle. Katon falo ne suka shiga komai nashi fari ne. Babu wasu tarkace a falon amma kallo d'aya za kayi masa kasan an kashe dukiya. Kayan da aka z
uba masa ko a k'asar waje Albarka. Babbar mace ce da a kalla za tayi shekara 55 zaune kan d'aya daga cikin kujerun hannun ta riΖe da husnul Muslim sai farin glass dake idon ta na karatu. Da sallam Reina ta shiga Annor da Ablah riΖe da hannunta. Murmushi ma
tar tayi ta rufe littafin da take karantawa ta d'ago tana kallon Reina dake durkushe a k'asa tana gaishe ta.
"RAHEENATU, sannu da zuwa har kin dawo?, ina Muhammadun bai dawo bane?"
"Eh wlh Ummi wai aikine ya riΖe sa yauma bazai samu damar dawowa ba"
"Hm
mm to ai shikenan Allah ya kyauta. Bari Rabi ta kawo miki Abinci ki shiga cikin Fadeela tana ciki"
Da d'an mamaki ta d'ago " yaushe Fadeelan ta dawo Ummi?"
"Jiya ta dawo Raheenatu"
Tana maganan ma sai ga ta ta fito. Kyakkyawar yarinyar ce da za tayi she
karun ta. Bak'ace mai haske da shek'i oily skin. Tana da tsayi babu laifi dan tafi Reina tsayi da kuma cika ido. Baza ka kalli Reina kace ta haifi yara biyu ba ,kai idan ma ba gaya maka aka yi ba baza ka yarda tana da aure ba. A guje Fadeela ta fad'a jikin
Reina tana dariya.
"Saukar yaushe?, kaga manyan mata ganin ku sai an cike foam"
"Kai Aunty Reina wlh ba haka bane"
"Toh yane, yaushe rabon ki da mu?, yanzu ma da ban kawo su Annor ba da bazan san kinzo ba sai dai naji tafiyar ki"
Y'ar dariya Fadeela
tayi bata ce komai ba ta mayar da hankali kansu Baby Ablah dake wasa tsakar falon.
"Raheenatu tashi ki shiga ciki mana. Narasa sai yaushe ne zaki dinga sakin jikin ki duk sanda ki ka zo sai ki yi ta rab'e-rab'e kaman ba gida ki ke ba."
Y'ar dariya Reina
ta yi. "Ai Ummi tafiya za muyi ma Wlh. Dama daga gurin aiki nake ne, toh kuma tunda yace bazai dawo ba yau bari kawai mu koma. Ina jummai take tazo mu tafi"
"Yanzu haka tunda ki ka jita shiru tana can d'akin su Rabi. Fadeela je ki kira mata Jummai d'akin
su Rabi"
Wayar Fadeela dake gefen Reina bayan tashin ta ta fara ringing. Kallon wayar tayi da sunan Uncle Maheer ya fito ra
Ι
au a jiki. Batasan me yasa ba taji gabanta ya yanke ya fad'i. Fadeela da Maheer d'in ta cousins ne ya'yan wa da kuma k'ani. Baba
n Maheer d'in ta Alhaji Muneer Mai doki shi ne Babba , sai Baban Fadeela Alhaji Ishaq Mai doki ke binsa. Iyayen Fadeela suna zaune ne a MOSCOW. Lokaci-lokaci suke zuwa gida hutu saboda y'ar tsaman da y'an uwan ke yi. Hajiya zuwaira matar Alhaji ishaq ita
ke hadda duk wata fitina dake faruwa tsakanin y'an uwan biyu. Bata san ganin Alhaji Muneer gaba da nata mijin, dalilin da yasa tayi duk abunda za tayi dan raba kansu ta kuma ci nasara. Sakamakon hakan suka koma Moscow d'in da zama. Sannu a hankali saida t
asa Alhaji Muneer ya barwa Ishaq kamfanin gaba d'aya yana juyawa. Tasowar Maheer ya fara bibiyar kamfanin na iyayen nashi. Kaf cikin y'ay'a n Muneer Babu wanda ya damu da maye gurbin iyayen nasu sai Maheer dake da interest kan kamfanin. Su hud'u ne maza sa
i mace guda d'aya da take autar su.
Akwai. ANWAR shi ne Babba yana zaune a US da matar sa sai yaran sa biyu shima dan kusan tare suka yi aure da Maheer. Likita ne shi Babba da US ke ji dashi. Shi yasa suka rike sa. Sai Maheer dake binsa, sai ADIL DA ANIL d
a suke twins suna karatu a jami'ar OXFORD UK. Autar su SAMHA tana can SAUDIYA tana nata karatun.
Zuwan sa Moscow yaga yanda Hajiya zuwaira ke b'ari da ku
Ι
in kamfanin iyayen nasu ya yi alwashin tsayawa tsayin daka wajen ganin ya gyara harkar kamfanin ,du
k da cewa bashi da ra'ayin irin wannan aikin shi burinsa ya zama soja, haka ya tashi kacakom ya koma Moscow d'in . Ba kasafai ya cika zuwa gidan kawun nasa ba sai da dalili mai karfi saboda halin kiyayya da Zuwaira ke nuna masa. Duk yanda take juya Ishaq
,Maheer tana masifar shakkar sa saboda kwarjini da Allah ya yi masa, bama ita ka
Ι
ai ba kusan kaf familyn nasu babu wanda baya shakkar sa, suna bala'in tsoron sa gashi Babban soja mai hatsarin gaske da duniya keji dashi. Dalilin da yasa duk wata masifar ta
da bala'in ta akan Ishaq da Muneer ya k'are. Taki jinin Ummi da duk wani abu daya rabe ta. A cewar ta ita ce ta dace da Alhaji Muneer, ita ya kamata ta zama matar sa. Sai kuma Allah baiyi hakan ba da aka tashi taron family na had'a aure da suke. Ta gama c
ika buri da tunanin ita aka zabawa Muneer sai akasin hakan. Ummi da aka kira AYSHA ita aka zabawa Muneer matsayin mata ,ita kuma Ishaq aka zaba mata a matsayin miji. Inda kiyayar ta samo asali kenan. Za kuma kusha mamaki idan nace muku da Ummi da ita Zuwai
ran uwa d'aya suke uba d'aya. Dalilin da yasa duk fitana da matsalolin da take haddasawa cikin family babu wanda yake d'aga kai ya kalle ta sai Maheer. Ganin Maheer na juya kamfanin tasan duk yanda za tayi ta tura Fadeela dake babba cikin yaranta Uku. FADE
ELA, ANITA, da SAPWAN. Tayi duk yanda za tayi aka bata matsayi mai girma. Ita ce CEO na 'MD DAIMON CASTLE ENT'. Shi kuma Maheer PRESIDENT .
Kusan zata iya cewa ta sanadin kawance da suke da Fadeela tasan Maheer da har soyayya mai karfi ta shiga tsakanin
su. A kanta ne aka fara karya doka ta family na auren bare. Dalilin da yasa da yawa daga cikin su har yanzu basu karbe ta hannu bibbiyu ba. Ita ba yar kowa bace iyayen ta nada rufin asiri dai-dai gwargwado. Baban ta tsohon d'an sanda ne da ya yi ritaya she
kara biyu da suka wuce. Babu wani aiki da Maman ta take sai yanzu ne ma da tayi mata hanya ake kawo mata sarin kaya daga k'asashe kuma Alhamdulillah akwai Albarka cikin sana'an. Bata dogara da dukiyar mijin ta ba ,saboda gori da take sha wajen familyn sa,s
hi yasa ta dage da neman na kanta. Babbar lauya ce ita dake kare hakkin Al'umma.
Har wayar ta katse ta kasa daina kallon fuskar wayar. Wani kiran ne ya k'ara shigowa daidai Fadeela ta shigo Jummai Nanny d'inta da Rabi mai aikin Ummi biye da ita. Da sauri
Fadeela ta k'araso ta d'auki wayar. D'auke kai Reina ta yi tana kallon Jummai
"Yauwa Jummai ,d'auki Baby Ablah muje. Ummi bari mu tafi sai da safe"
"Kin dai dage baza ki tsaya kici abinci ba ko?"
Y'ar dariya tayi ta miΖe. "Wlh babu komai Ummi a koshe n
ake ne" kallon Fadeela tayi dake waya a hankali duk da tana kusa da ita bata fuskantar abunda take cewa. Jira tayi saida ta gama wayar tace
"Toh mu zamu wuce sai yaushe zaki leko mana"
"Haba Reina, ai kinsan dole ne na zo. "
Juyawa tayi tana kallon Umm
i
" Ummi ina ganin jibi zan koma , uncle Maheer ke cemin akwai aiki mai muhimmanci daya taso dole ana buΖata naje, bari nabi sister Reina zuwa gobe zan dawo"
"Toh babu komai Allah ya tashe mu lafiya"
Gaba d'aya suka amsa da Amin. Har cikin ran Reina taj
i dad'in tafiyar daza suyi da Fadeela. Fadeela kawar tace sanadiyar ta kuma ta had'u da sanyin idaniyar ta. Annor da Baby Ablah sai tsalle suke Aunty Fadeela zata bisu. Hira suke sosai cikin mota na yaushe gamo. Anan Reina keji ashe gurin Aikin ta daya da
Habibi d'inta kamfanin ma da yake aikin kacakon na iyayen su ne.
Sai da suka tsaya suka yi tsarabar kayan ciye-ciye sannan suka isa gida ta dake nan unguwar Maitama.
A falo suka yada zango suka bu
Ι
e sabon shafin hira. Annor da Baby Ablah sun jima da yi
n barci jikin Fadeela . Kwasar yaran suka yi zuwa d'aki. Ruwa suka watsa suka yi salla sannan suka samu guri suka kwanta. Nanma dai hirar ce suke inda Reina ke tambayar Fadeela wai sai yaushe za tayi aure ne?. Dariya Fadeela ta yi
"Hmm Reina kenan, lokaci
kad'an ya rage kar ki damu"
Basu wani jima ba suka kwanta. Sun kwanta d'in ne amma Zuciyar Reina cike take tab da tunanin Habibi d'inta. Taso ace taji muryar sa kafin ta yi barci amma hakan ba mai yiwuwa bane.
Washe gari kaman yanda Reina ta saba bakwai
ta fita aiki, amma yau saboda Fadeela har karfe takwas ta kai tana shiri saboda hira da shirita da suka sa gaba. A gurguje ta fito cikin riga da sket na atamfa ta dora bak'ar doguwar riga a kai tayi rolling d'in mayafi. Kafarta sanye da flat d'in takarmi
fari da kuma farar jaka .hannunta sanye da farin agogo mai kyan gaske. Tayi kyau sosai dan baki bazai iya furta kyawun da tayi ba. REINA Kyakkyawar macece ta ko ina tayi. Bata da tsayi kuma baza ka kirata gajera ba. Tana da wani irin jiki mai daukar hanka
li. Daga saman ta zuwa kugun ta babu wata kiba ta arziΖia amma kirjinta a cike yake dam kaman balloons. Sannan cikin a matse yake baza ka tab'a cewa yara har biyu sun zauna cikin sa ba. Kugunta a mugun baje ga uban hips da in ka ganta sai kayi tunanin suna
rinjayar ta. A gaggauce ta fito bayan tayi sallama da Fadeela ta barta da su Annoor.
Tana mota kiran Maheer ya shigo wayar ta. Murmushi tayi mai kayatar wa ta d'aga wayar.
"Habibi, barka da safiya"
"How are you?"
Murmushi tayi tana Jin wani dad'i na
ratsa ta. A gaskiya ita kanta tana tsoron irin san da takewa Maheer.
"Lfy lau Habibi. Ya aiki? Munyi missing naka"
Wani irin murmushi ya saki ta cikan wayar har saida taji sautin sa.
"Kunyi missing d'ina ne ma?, bake ki ka yi missing d'ina ba"
Dariya
ta saki "no ai kasan nafi kowa missing d'in ka"
"OK, kina hanya ne yanzu?"
"Eh Habibi, yau ban fita da wuri ba saboda Fadeela "
"Hmm, OK drive safe za muyi waya later"
Har ya katse wayar tana murmushi. Ranta fes yau ya bata kuluwar da ya jima bai bata
ba. Harta a gurin aiki saida kowa ya fuskanci tana cikin farin ciki. Case d'in data tarar na wasu mata da miji shine yau ya