Showing 21001 words to 24000 words out of 52463 words
da Samha da suka kafe Maheer d'in da ido cike da damuwa.
" kuje ku kwanta. Gobe LAMEEN zai sauka. Anil kuje kai da Adil ku d'auko sa. InshaAllahu zai samu sauki"
Amsawa sukayi suka fice suka barshi ya cigaba da kulawa da Ma
heer. Washegari da safe kaman yanda yace suka wuce d'auko LAMEEN. Ummi da kanta ta saka Maheer a gaba yaci abinci da kyar ya gi loma biyu. Tana gama bashi Anwar ya sashi a gaba ya yi masa wanka. Minti talatin da fitar su Adil sai gasu sun dawo da wani bac
k handsome guy kyakkyawan gaske. Kusan idan ka ganshi sai kayi tunanin twins suke shida Maheer komai nasu kusan iri d'aya ne. Idan ka cire blues eye's da dogob gashin Maheer da kuma kirar karfi da Maheer keda shi. Shima LAMEEN a murd'e yake amma ba kaman
Maheer ba.
A guje ya fad'a jikin Anwar suna dariya kafin ya janye jiki ya durkusa yana gaishe da Ummi. Alhaji Muneer ya sauko fuska dauke da murmushi yake masa barka da zuwa. Kai tsaye dakin Maheer ya yi. Yanayin daya Maheer d'in yaji hawaye masu zafi su
n biyo kuncin sa. Baisan cewa haka abun ya yi worst ba. Rungume Shi ya yi yana godewa Allah daya sa yazo kan lokaci. Yanzu shima zai bashi kulawan daya dace.
✦✦✦
Salla take tana kuka har ta idar ta durkushe a gurin tana kuka mai cin rai. Muryar Khaleel
taji yana
"Yaya Ramlat ki daina kuka. Ya Reina tana can jannatul fiddausi da yardar Allah. Kowa ya yi mara sheda mai kyau har yau kuma ana yi."
Ajiyar zuciya yaja zuciyar sa ta karye. Da da hali shima kukan zaiyi amma yana so ya karfawa Yaya Ramlat gwiw
a suyi tawakalli. Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. Ita mutuwa tana kan kowa idan tazo za'ayi ta ko ana so ko ba'a so.
"Abba ne yace nazo na gaya miki Baban Haidar ne yazo yana waje yaki tafiya yana ta magiya kije"
Numfashi taja mai k'arfi ta j
uyo tana kallon sa da jajayen idan ta.
"Kaje kace masa bazan fito ba ya kama gaban sa"
"Ya ya Ramlat kiyi hak'uri babu yanda bamu yi dashi ba yaki tafiya. Wai magana yake so ya yi dake mai muhimmanci "
"Ramlat "
Suka ji muryar Mama cikin sanyin ta. Ha
nkali suka mayar kanta tana tsaye bakin k'ofa rike da charbi
"Tashi kije kiji abunda zaice"
Badan taso ba ta tashi tana share hawaye ta fito. K'ofar gida ta same shi kan mashin. B'ata rai tayi ta tsaya gaban sa babu sallama. Murmushi ya yi shi yanzu fa d
uk abunda za tayi masa tayi. So yake ya lalla
ɓ
ata ta koma dan a mugun matse yake. Shi bai iya zina ba kafin dai ya yi auren da zaiyi ya dinga sauke damuwar sa. Dan haka tayi duk abunda za tayi idan ta koma zataci ubanta ne.
"Slma abar kauna tunda ni kin k
i gaishe ni. Ya kike da yara na?"
"Me kazo yi nan?"
"Dan nazo ganin uwar y'ay'ana laifi ne?"
"Kaga Hamza, ba wannan nake tambayar ka ba me kazo yi ?"
Kaman ya rufeta da duka haka yaji amma ya cije lebe yana saisaita zuciyar sa.
"Kiyi hak'uri ki koma d
'akin ki Ramlat kodan saboda yaran mu. Nayi miki alkwari inshaAllahu komai ya wuce tsakanin mu"
Shek'ek'e ta kalle sa ta yi yar dariya. Baban Haidar na manta cewa tasan shi ciki da waje. Yanda ta sanshi shi kanshi baisan hakan ba. Da ace wannan maganan ha
r cikin zuciyarsa ya yi ta babu abinda zai hanata komawa kodan saboda yaransu amma ba haka zuciyar sa ke cewa ba.
"Zamana da kai har abada"
Ta juya da sauri ta koma yana kwala mata kira.
✦✦✦
UNKNOWN.
Sama-sama take jin magana kanta. Wani irin yare
ne take ji da ita kanta baza tace gashi ba. A hankali ta fara k'ok'arin bude manyan idanta. Dal haske ya haske idon tayi saurin mayarwa ta kulle. Maganan dai ta cigaba da ji kusa da ita da yanzu magana ta k'aru mutane sun k'aru a gurin. Sai taji kaman cou
rage suke bata ta bu
ɗ
e idon ta. A hankali ta fara bu
ɗ
ewa har ta bu
ɗ
e shi tar kan rufin bukka da take fuskanta. Juyowa da kanta tayi b'arin mutane da keta yare shiba larabci ba shiba fulatanci ba. Arba tayi da wasu mata sanye cikin kaya gashi dai kaman na b
uzaye dan har irin kitson su ne a kansu. Ido take binsu dashi d'aya bayan d'aya da tunanin ina ne kuma nan?. Meya kawo ta nan.?
Wata ce ta shigo sak inka kalle ta kaga fulanin usul. K'ara sowa tayi da murmushi sosai kan fuskar ta ,abunda batayi tsammanin
jiba shi taji tana yi.
"Alhamdulillahi baiwar Allah kin farka?, sannu bari a kawo miki ruwa kisha"
Da ido take binta ta kasa magana dan ji tayi bakin nata kaman an saka zare da allura an d'inke. Jikinta kuwa kaman an d'ora mata katon dutse mai shegen na
uyi. Me ya kawota nan? Ine nan?. Ina yaran ta ,Mama, Khaleel, yaya Ramlat da Abba. Ina Maheer.? Lumshe ido tayi kwakwalwar ta ta fara harbo mata abunda ya faru. Hatsari tayi abun mamakin shi ne ita tasan taga Fadeela a wani daki da take tunanin itama tana
ciki a kwance da wasu mutane suna magana. Ido ta bu
ɗ
e ta zaro shi zuciyar ta ta nanata mata .........
Phewwwwwwww
🧚
♀
️
hankali sai ya kwanta yanzu ko?
😂
𝐙ꨄ
︎
𝐂𝐈𝐘𝐀𝐑
𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌ꨄ
︎
(
ʙʟ
ᴇᴇᴅ
ɪɴɢ
ʜ
ᴇꨄ
︎
ʀ
ᴛ
s)
✯
D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯
R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
✯
𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘
𝐋𝐎𝐕𝐄
.
E|41/45.
FULL EDITED VERSION
THE HIDDEN SECRET.
ACCIDENT DAY. (RANAN HATSARI)
Lokacin da motoci biyun suk
a had'u saboda karfin impact d'in glass d'in motar Reina ya fashe gaba d'aya ta fice ta gaban motar sakamakon rashin saka seat belt da batayi ba. Yanda ta fice kaman iska yasa babu wanda ya lura da ita har ta mirgina can gefen titi tayi cikin ciyayi. K'arf
in Buguwar da tayi da sitiyarin motar yasa ta sume sai kafar ta da wajen fitar ta ta glass ya caki cinyar ta . Bayan wannan babu wani rauni data ji. Har aka gama kururuwar nan aka watse bata farfa
ɗ
o ba. Kuma Allah da ikon sa babu wanda ya lura da ita sai d
a kowa ya watse ana ta jimami. Gab da magriba ne wasu samari irin yan tashan nan sun tawo suna tangadi cikin maye d'aya daga cikin su yana bawa d'an uwan sa labarin had'arin da aka yi .
"Ina gaya maka Babaa wlh kurumus suka kune fa. Ya kamata mu tuba haka
ko ma samu k'arshe mai kyau. Ni ko k'ofar Aljanna aka ajiye ni ai na wuce sirad'i ko ba haka ba"
"Kai wlh kuma haka ne koda k'afa d'aya ne mu samu mu k'arasa"
Kai kana jin yanda suke maganan kasan a buge suke. Tsayawa ya yi da zancen ya zubawa guri d'ay
a ido. Kyefta ido ya yi ya k'ara Kyefta wa sai ya cakumo d'an uwan nasa da bai lura da abunda shi yake gani ba. K'arasawa sukayi inda yake tunanin kaman mutum ne a kwance. K'afa na rawa ya durkusa d'an uwan nasa da ya lura da abunda ya gani ya juya a guje
zai ci na kare ya riƙe sa.
"Kai Babaa ina zaka je. Ai inma mutuwar ce sai dai ta d'auke mu tare yasin baka isa ka arce va"
"Ka kyale ni Ilu. Nayi maka alkwari zanyi maka Addu'a. Idan na gyara hali na zan biyo ka yanzu ban shirya mutuwa ba. Don Allah ka s
ake ni"
"Wlh baka isa ba tare zamu je"
Kyem ya rike sa yana turjewa da magiya har suka k'arasa inda Reina ke yashe a k'asa. Ido suka zaro.
"Wai Babaa ko dai mun mutu ne?. Hurul'ain sun fara kawo mana ziyara"
"Kai fa ni matsala ta dakai ka cika yawa wlh
. Mutum ce fa"
Durkusawa sukayi kusa da ita suna haska fuskarta sosai. Hasken fitilar daya dalle mata ido yasa ta d'an motsa fuskarta amma bata bu
ɗ
e idon ba.
" Ilu da ranta fa. Taro moto mu kaita asibiti "
"Babaa idan aljana ce fa"
"Ka manta waye ni ne
. Kashina ko aljanu ai Albarka. Warin jikin mu kad'ai idan sun gammu su kansu Aljanun chanza hanya suke bare bil adama. Jeke samo mota Alhaji idan mum kaita asibiti sai a yi wadda za'ayi dan daga ni har kai babu ko kabo a jikin mu"
A hanzarce wanda ake k
ira da Babaa ya matsa bakin titin dan tarar mota cikin wanda suke wucewa. Taxi ya tsayar da taimakon matar dake ciki ta kama Reina suka shigar da ita cikin mota. Har suka je Asibit Babaa da Ilu suna bada labarin yanda suka ganta. Yau sunyi taimako sun san
zunubinsu zai ragu ko yane. Kaman fate asibitin da aka kai Maheer nan suka kai Reina. Suna fakin Ilu ya fito yana gyara ass down d'insa ya kalli mai taxi.
"Maza bari mu shiga. Kai ma yau kayi taimako Allah ya biya ka bari na samo nurse su shiga da ita cik
i"
"A'a kaga malam. Wai kana nufin baza ko biya ni ku
ɗ
in motana bane?"
"Taimako fa kayi . Munan daka ganmu ko kobo babu a jikin mu. Kaga ladan kaima sai a san maka ko ya kace"
Dariya sosai matar dake zaune cikin motar tayi. Ta kalli me taxin
"Kar ka da
mu ni zan biya ku
ɗ
in. Daga gani baiwar Allah tana buƙatar taimako. Bari na taimaka a shiga da ita ciki sai nazo mu tafi"
"Yauwa Hajiya Allah kema ya sammiki ladan nan. "
Dariya tayi tana girgiza kai ta gyarawa Reina kwanciya kan kujera sannan ta fito .g
aba tayi su Ilu na binta suna tafiya a karkace su dole tantiran y'an iska ga bak'in nasu yak'i yin shiru. Wata y'ar budurwa ce ta fito tana waya kaman wani take jira. Da sauri matar ta nufe ta su Babaa biye da ita.
"Yauwa Baiwar Allah don Allah ko ina ne
ake ganin likita? Mara lafiya ce muka kawo babu yanda take"
Kallon su tayi tana cewa
"Ki shigo kawai cikin asibitin Hasina gani a compound d'in ina jiran ki"
Kashe wayar tayi tana kallon matar da su Ilu dake washe jajayen hakoransu, su dole sunga budu
rwa zasu burge ta. Yatsina fuska tayi ta kai hannu ta toshe hanci. Allah ya gani tun kafin ma su k'araso inda take warin jikin su ya daki hancin ta. Da hannu ta nunawa matar.
"Ciki zaki shiga"
"Yauwa na gode Amma Don Allah in baza ki damu ba d'an taimak
a mun mu fito da ita"
Kaman ta rufe matar da masifa. Ta barta taji da abunda ke damunta sai ta k'ara mata wata damuwar. Hasin ta hango dake shigowa ta d'aga mata hannu.
"Muje ina mara lafiyar take"
" yauwa baiwar Allah mun gode. Tana mota"
Gaba tayi Fa
deela ta bita daidai Hasina ta k'araso. Kallo d'aya zaka yi mata kaga cikakkiyar yar bariki ko daga yanayin suturar ta da kuma uban bleaching data yi.
"Ina za kije kuma"
"Zoki tayani mu kamawa wannan matar mai jinya ta kawo "
"Hmmm. Ya jikin Maheer d'i
n? Ya farfa
ɗ
o kuwa?, da gaske dai ta mutun?"
Dai-dai suka k'arasa bakin motar ta sunkuya tana cewa
"Ga zahiri kina gan... REINA"
Ta kira sunan da k'arfi bata k'arasa abunda take niyar fad'a ba. Innalilllahi me take gani haka? Wani irin bugawa k'irjin ta
yake tana k'ara duba cikin motar da Reina ke kwance kaman mai barci. Hasina ta kalli Fadeela cikin rashin fahimta ta sunkuya itama dan taga abunda ya firgitata. Bata san Reina ba dan haka bata firgita kaman yanda Fadeela tayi ba sai kyan Reina daya firgit
ata matuƙa. Da sauri matar ta juyo tana kallon Fadeela.
"Baiwar Allah kin santa ne?"
Muryar Fadeela na rawa tace. " Y'ar uwa tace da muke tunanin ta mutu a hatsarin da aka yi d'azu "
"Ikon Allah wad'annan bayin Allah ne suka tsince ta gefen titi a sum
e. Kinga ikon Allah kenan"
Yak'e Fadeela tayi ta rasa abun cewa. Taya aka yi Reina ke raye?. Anya zata bari asan cewa tana da rai bayan kowa ya d'auka ta mutu. Idan Uncle yasan Reina bata mutu ba bazai tab'a daina sonta ba. Hasina dake karantar Fadeela ta
yi wani mugun murmushi ta kalli su Ilu da matar.
"Mun gode sosai, zamu karbe ta daga nan "
Ku
ɗ
i ta ciro har bandir biyu ta basu suka warce ku
ɗ
in suna godiya. Kai amma wannan yarinyar da suka taimaka akwai alheri duk inda take. Yanzu dubi daga sama Allah
ya basu ku
ɗ
i har bandir guda-guda?. Yoo su ai ko dubu basu tab'a riƙewa ba ta kansu. Godiya sosai Hasina tayi wa matar ta ja hannu Fadeela dake nan kaman mara laka suka fito da Reina. Maimakon suyi can inda y'an uwa suke ana jimami sai sukayi wani sashen d
a ita cikin asibitin. Nurse ce ta karbe ta aka dora ta kan gado suka yi wani d'akin da ita dan ganin likita.
Safa da marwa kawai Fadeela take bakin k'ofar kanta ya kulle ta rasa abunyi Hasina na binta da kallo har aka fito da Reina zuwa d'akin hutu.
"
Na shiga uku Hasina. Wannan mayyar taki mutuwa. Idan Uncle yasan tana raye burina bazai tab'a cika ba. Da naji mutuwar ta tunda nasan ta tafi kenan har ina tunanin dama dai bata mutu ba ko dan mutuncin da muka yi a baya. Amma a yanzu dana ganta Hasina fata
nake dama mutuwar tayi. Ta haka ne kad'ai zan mallaki Uncle "
Murmushin y'an iska Hasina tayi tana taunar cingam kas-kas.
"Kina bani mamaki wlh kaman ba wayayyiya ba. Tunda duniya ta sheda cewar ta mutu me yasa yanzu baza mu aikata lahiran ba?. Wannan s
olution ne mai sauki amma duk kin dauki chaji"
K'irji Fadeela ta dafe tana girgiza kai. Duk iskancin ta banda kisa. Baza ta dauki wannan nauyin ba.
"A'a wannan ba shawara bace .bazan iya kisan kai ba. Ki dai kawo wata shawarar "
"Hmm to ai shikenan tund
a haka ne. To ga wata shawarar, me zai hana a b'atar da ita kawai ta tafi can wata duniyar daban"
Da sauri Fadeela ta juyo " yanzu ki ka yi magana. Ya zamuyi"
"Abunda za ayi yanzu zan kira Don sai musan abun yi. Ku
ɗ
i kawai zaki kawo yanzu kiga aiki da ci
kawa. "
Abunda basu sani ba Reina ta dade da farkawa amma ta kasa tashi da bu
ɗ
e ido dan ba k'aramin buguwa tayi ba. Muryar Fadeelan data ke ji sama-sama yasa tadan bu
ɗ
e idon nata kad'an dan ta tabbatar. Duk taji maganan da suke ta fara k'ok'arin tashi ha
kan yaja hankalin su. Hankalin Fadeela in ya yi dubu ya tashi musamman ma kallon data ga Reina na aika mata dashi. Taji duk abunda suke cewa. Idan har asirin ta ya tonu Uncle bazai tab'a zama nata ba. Cikin rashin sanin abun yi ta dauko sandar k'arin ruwa
dake kusa da ita ta d'aga da k'arfin ta ta makawa Reina dake k'ok'arin miƙewa zaune. A take ta zube kan gadon a sume jini ya fara biyu gefen fuskarta. Yarda sandar Fadeela tayi ta dafe k'irji cike da tashin hankali. Hannu takai ta toshe bakin ta jikin ta n
a rawa yau ta shiga uku mai ta aikata.? Fito Hasina tayi tana wata mahuakaciyar dariya.
"Ke ke cewa banda kisa. Gashi yanzu kin kashe ta"
"Na shiga uku duba dan Allah. Wlh tsoro naji dan naga alama kaman taji duk maganganun da muka yi. Gashi dama kuma m
una y'ar tsama da ita me ki ke tunani zai faru idan ta samu lafiya?"
Matsawa Hasina tayi ta dafa k'irjin Reina dake buguwa a mugun slow.
"Shegiya gata da taurin rai taki mutuwa wlh. Bari kawai na kira Don yanzun nan "
Ko minti talatin bata yi da kiran
ba ya kirata yace sun iso. Nurse dake jinyar Reina suka bawa makudan ku
ɗ
i ta barsu suka fito da ita. Cikin mota suka sata Fadeela ta koma cikin asibitin cike da fargaba ta bar Hasina na yiwa Don bayanin aikin da zaiyi musu. Saida ta bashi makudan ku
ɗ
i san
nan ya amince ya fito daga asibitin da Reina bayan boot. Sai da ya yi tafiya mai nisa ya tsaya yana nunanin abun yi. Haka kawai yaji bazai iya aikata abunda suke son ya yi ba. Wani tunani ne ya fad'o masa ya zo nan bakin teku . Akwai wani bafullatanin mai
suna Hard'o. Irin mutanen nan ne masu safarar kayan marmari k'asa-k'asa. Idan bai manta ba shekaran jiya ya shigo gari dan ta teku yake yawon safarar sa. A yanzu haka yana zaune ne can k'asar MADAGASCAR dake yankin Kudu shida iyalen sa. Yana zuwa kuwa ya
tarar yana shirin hawa teku. Da azama