Showing 12001 words to 15000 words out of 52463 words
shi yasa bayasan matsalan mata wlh sun cika kishi. Yanzu fisabillahi dan ya kasance da matar sa dubi irin kallon tuhumar da
take masa ko zina ya yi ai iya kaci kenan. Ya Reina za taji idan tasan alakar dake tsakanin sa da Fadeela bayan ta y'an uwanta taka da take tunanin babu wata bayan ta?.
Fitowar Reina ya samu saukin mugun kallon da Fadeelan ke jefe masa. Kai ya girgiza y
a tashi ya haye sama ya barsu nan falon Reina na baje mata kayan motsa baki gabanta. Sama-sama take jan Fadeela da hira du da ta lura kaman hankalin ta ya yi wani gurin. Tsawon minti talatin suna zaune jefi-jefi Reina na kawo mata hira tana bata amsa da Eh
ko A'a. Fitowa ya yi sanye da kananan kaya. Gajeren wando da riga mai yankakken hannun gashin kansa ya yi masa ponytail a tsakiya wasu sun zubo goshin sa da bayan sa. Da ido Fadeela ta bishi kaman ta had'iye ita Reinan ma bata lura da fitowar tasa ba han
kalin ta ya yi kan waya suna chat da Yaya Ramlat. Yanayin kallon da sukewa juna shida Fadeela kasan magana suke da ido ko daga yanda ta turo baki ta d'auke kai gefe.
Sai da ya zauna sannan Reina ta d'ago tana murmushi.
"Habibi barka da fitowa"
Kafin y
a kaiga bata amsa wayar sa ta hau ringing. D'aukan wayar ya yi da sauri ya bar falon. Jim kad'an sai gashi ya dawo.
" Abu ya taso yanzu gurin aiki. Zan koma MOSCOW yanzun nan daga can zanje CANADA suna buƙatar taimakon gaggawa na wani terrorist attacks da
aka kai musu d'azu . Ana buƙatar bincike da gano inda suke saboda sunyi garkuwa da mutane"
Daga Reina har Fadeela jikin su ya yi sanyi suka bishi da kallo ya haura sama a guje. Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka kalli juna kowa da abunda ke cikin ransa
. Ko minti biyar baiyi ba sai gashi cikin kakin sa na Sojoji bayan sa da katuwar jakar makamai. Miƙewa Reina ta yi ta nufe sa tana k'ara jinjina irin kyau da kyan suke masa idan sa kawai dake a bu
ɗ
e ya kara haska shi. Kam ta rungume sa tanaji kaman kar ta
barshi ya tafi, a duk lokacin da irin wannan abu ya taso mai had'arin gaske bata iya runtsawa har sai ya pkirata ya sanar mata da samun nasarar sa. Goshin ta ya sumbata ya wuce da sauri suka biyo shi ita da Fadeela. Idan kaga yanda Sojojin nan suka yi layi
suka k'ame masa kowa sanye da kayan sa sai abun ya baka shawa'a da kayatarwa. Baza ma kace suna numfashi ba. Suna tsaye ya gama musu jawabi suna bashi amsa da "YES SIR " a tare. Suna gamawa suka k'ame tare da sarawa kafin a guje suka shige mota. Juyowa ya
kalli Reina da idanta ke cike tab da hawaye. K'ara rungume ta yai kan kirjinsa murya k'asa-k'asa ya ce.
"Take care Alright, I love you"
Kai ta d'aga masa hawayen idan ta da take k'ok'arin hanasu zubowa suka biyo kuncin ta. Hannu ya kai ya goge su ya k'
ara sumbatar goshin ta. Da ace Reina zata juya taga kallon da Fadeela ke mata to da tabbas babu abunda zai hana k'asar gurin ta tsage ta nutse cikin ta. Shi dake fuskantar Fadeelan shi ka
ɗ
ai ya lura da kallon nata. Ajiyar zuciya ya sauke ya janye Reina dag
a cikinsa yana kallon Fadeela.
"Yanzu zaki tafi muje na sauke ki ko sai anjima?"
Bai ma gama maganan ba ta wuce fuu ta shige motar sa. Da ido suka bita gaba d'aya ya taune harshe. Wai what is wrong with this girl dake k'ok'arin tona musu asiri?. Bai shi
rya fuskantar Reina da wannan bom d'in ba. Yana tsoron ranan da wannan asirin zai tono. Shi ba ma'abocin zina ba. Amma Fadeela ya rasa dalilin da yasa duk lokacin da suke tare baya raba kanshi da ita. Murmushi ya yi mai kama da yak'e
"Bari muje Baby zan
kira ki alright?"
Kai kawai ta d'aga masa tana kallon sa har ya shige mota suka fice daga gidan. Sam bata damu da tafiyar Fadeelan ba saboda tana cikin alhinin tafiyar Maheer da kuma inda zaije .
✦✦✦
Yau tsawon sati biyu kenan da tafiyar Maheer. Duka du
ka cikin kwanakin nan zaka kirga wayar da suka yi. Bata damu kanta sosai ba saboda itama kanta tayi busy da wasu case's da suke buƙatar taimakon ta. Baby Ablah da Annoor bata d'auko su ba gurin Mama ta barsu can dan bata samun zama sosai. Cikin case's d'in
da zata kare akwai wanda yafi daukan mata hankali tun daga KANO suka yi tattaki suka neme ta dan ta tsaya a kai. Yarinyar ce k'arama da bata wuce shekara goma sha bakwai ba dake zaune da matar uba dake gana mata azaba. Bayan rasuwar mahaifiyar ta ya k'ara
aure. Shekara biyu da auren Baban nasu ya fara neman wani auren dan sai yake ganin mace guda baza ta maye masa gurbin tsohuwar matar sa ba. Rana d'aya aka wayi gari uban Yarinyar ya mutu ta sanadin abinci da ake tunanin ita y'ar tasa ta bashi yaci. Da aka
yi bincike aka gano ugaba ce mai karfi aka zuba cikin abincin nashi da tayi sanadin ajalinsa. Matar uban ta tara jama gida tana ihu da kururuwar Yarinyar ta kashe mata miji tana cewa dama yana kuka da ita saboda tana jawo masa abun magana. Ta daina ganin
mutuncin uban ta gashi yanzu taga bayan sa kaman yanda tasha furtawa.(kunji makircin )Yanzu bincike da ake ita Yarinyar tana can kulle a cell za'a fara zuwa kotu. Lawyers wajen biyu ne suka tsaya mata da suka gaza saboda rashin kwararan hujjoji da zasu kar
e ta. Saboda yanda ta shiga cikin trauma bata iya fura komai sai ba ita ta KASHE MAHAIFIN TA BA. bata ci bata sha sai kuka.
Sosai Reina ta tausayawa yarinya ta kuma ci alwashin tsayawa kan shari'ar har Allah ya basu nasara. Ta tara hujjoji masu tarin yaw
a dake nuni da matar Baban ke da sa hannu cikin kisan. Dangin iyayen yarinya suna cikin matsanancin tashin hankali matuƙa don basu da komai sai Allah da suka dogara dashi.
Kaya take had'awa cikin k'aramin akwati tana waya.
"Yaya Ramlat tafiyar ta kama do
le sai naje ne. Jibi za'a shiga kotu ina buƙatar naje da kaina dan samun amsan wasu tamboyi game da case d'in "
Murya ce mai sanyi tayi magana daga d'aya b'angaren dan har tafi ta Reina sanyi.
"Yaushe zaki dawo?"
Agogon hannun ta Reina ta kalla dake nun
a mata karfe goma na safe. Sha biyu jirgin ta zai tashi
" InshaAllahu da zarar mun gama da case d'in zan dawo. Ku tayani da Addu'a Allah ya bani nasara"
"InshaAllahu zaki samu nasara. "
D'an jim Reina tayi tana sauraran ta. Akwai tambayoyi da yawa da t
ake so tayi mata amma ta barsu cikin ranta. Zama tayi tana jan numfashi mai k'arfi ta fesar a hankali tace.
"Ya ya naki jikin?, hope babu wata matsala yanzu ko?"
Saida ta dauki wajen Minti biyu bata ce komai ba sai fitar numfashin ta kawai da Reina keji
ta cikin wayar. Babu abunda RAMLAT ta bari na mahaifiyar su tun daga sanyin su ,hak'uri, da rashin magana.
"I'm fine. Kawai ina craving d'in nama ne Baban Haidar zai tawo min dashi idan ya taso"
K'arya , K'arya . Shine kalman da Reina ke maimaitawa cikin
ranta.Tasan babu wani Nama da zai kawo. Da ace zai kawo da baza ta furta mata buƙatarta ba.
"Yaya Ramlat wai dole ne zama dashi?, ki rabu dashi mana, ko ana dole ne"
Murmushi Ramlat tayi .Reina har yanzu yarinyar ce. To idan ta fito taje ina?, yara uku
ne ke gaban ta yanzu ga ciki. Shikenan kuma sai ta kwaso yara ta dawo gida ta d'orawa iyaye nauyi suna fana da kai. Ga wanda ya zama dole ma ya yi musu bai damu dasu ba ina kuma ga wani?. Aure ai komai rashin dad'in sa rabuwarsa babu dad'i bare ita dake d
a yara. Bata ce komai ba sai Murmushi data cigaba da yi hakan ya tabbatar wa da Reina bazan tace komai d'in ba. Ajiyar zuciya taja mai k'arfi. Yanzu idan tace ta turo account ta tura mata ku
ɗ
i Babu amfani tunda baya bari tana fita bare ta samu d'an aike t
a siyi abunda take sha'awar ci. Wani lokacin sai dai Reina ta aika Khaleel yaje da kanshi ya kaiwa Ramlat d'in idan Baban Haidar d'in baya nan.
"Zan aikawa Khaleel ku
ɗ
i ya siyo miki ya kawo miki gida. Baban Haidar baya nan ko?"
"Eh yana gurin aiki. "
"T
o shikenan zan bashi mota dan ya yi sauri. Ki kula da kan ki dasu Haidar "
"To na gode. Allah ya..."
Kitt Reina ta kashe wayar zuciyar ta na zafi har wasu hawaye ne ke bin kuncinta. Halin da Yaya Ramlat ke ciki abin a tausayawa ne basu da ikon yin wani a
bu a kai. Mama ta kira tace Khaleel yazo maza ya d'auki mota yaje gidan Ramlat ya kai mata sako kafin ta tafi. Itama Maman bata ce komai ba dan tasan kwanan zancen. Addu'a ta karayiwa Reina kan tafiyar da zatayi ta bawa su Annoor suka gaisa. Ko cikakken mi
nti Ashirin Khaleel baiyi ba ya k'araso. Ku
ɗ
i ta bashi da yawa tasa ya siyawa Ramlat kayan ciye-ciye da sauran su . Tana hanya ta kira Maheer da basuyi waya ba tun shekaran jiya sai text da suka yi yake ce mata suna gurin aiki ne can Afghanistan. Yasan da
tafiyar dan haka shima fatan Alkhairi ya yi mata da samun nasara suka rabu.
Sha biyu daidai jirgin ta ya d'aga zuwa KANO.
𝐙ꨄ
︎
𝐂𝐈𝐘𝐀𝐑
𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌ꨄ
︎
(
ʙʟ
ᴇᴇᴅ
ɪɴɢ
ʜ
ᴇꨄ
︎
ʀ
ᴛ
s)
✯
𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘
𝐋𝐎𝐕𝐄
.
𝐄
/26/30.
A can bangaren Ramlat cikin sanyin jiki ta janye wayar daga kunnen ta ,ta zuba mata ido tana jin kaunar y'ar uwar ta ta. Hak'ika duk y'an uwan da suka kasance kaman Reina masu damuwa da damuwar y'an uwan s
u, to tabbas babu wani bara gurbi da zai shiga tsakanin su. Su Haidar dake cin abinci Farar shinkafa da mai tsakar falon ta kalla. Shikenan dai abincin a koda yaushe. Allah ma ya taimake ta ya ajiye musu buhun shinkafar da man. Babu zanchen magi sai gishir
i. Inda Allah ya taimake ta tana da d'an chanji ne take fita ta siyo musu d'an dunkule su barbada kan abincin. Yanda suke cin abincin cikin nutsuwa fuska babu annuri zaka san su kansu yaran sun gaji da cimar da ake basu a kullum babu sauyi. HAIDAR ne babba
dake da shekara biyar ,sai MUNIBA dake binsa, sai ALIYU wanda shi ne ta d'an samu tazara tsakanin sa da Muniba.
Babu zato taji k'arar mashin. A firgice take kallon tsakar gidan ta wandon d'akin. me ya dawo da Baban Haidar kuma.? A sanin ta bai cika dow
awa ba idan ya fita sai dare wani lokacin ma sai sunyi barci. Su kansu yaran sai suka yi wani tsuru-tsuru dasu alamun idan mahaifin nasu nanan basu sakewa, a takure su. A hanzarce ta tashi cike da fargaba tana Addu'a Allah yasa Khaleel kar yazo yanzu. Sall
aman Baban Haidar cikin falon ta k'ara rikicewa.
"Sannu da zuwa Baban Haidar "
Ta nufe sa tana k'ok'arin karb'an ledan dake hannun sa. Tsawa ya daka mata ya janye ledar da take k'ok'arin karb'a.
"Ke mene haka?, kauce ki bani guri mayyar banza da wofi"
A sanyaye ta koma gefe ta bashi hanya ya k'arasa shigowa falon. Guri ya samu ya zauna rik'e da ledan kaman za'a kwace. Haidar dake da wayo sosai ya tab'a y'an uwan nasa suka had'a baki suna masa sannu da zuwa.
"Daddy sannu da zuwa"
"Yauwa"
Ya furta b
abu wani kulawa bare yaji ya yaran nasa suke. Ramlat ya kalla dake tsaye har yanzu ta kasa zama. Tsaki yaja mai k'arfi da fad'a yake magana
"In ance mata matsala ne daku kuce ba haka ba. Kinja kin tsayamin kerere a kai. Ko ni ki ke so na d'aukawowa kaina
ruwan shan ne. Ke har yanzu baki iya tattalin miji ba sai iya d'aukan ciki kawai ki ka iya?"
Ajiyar zuciya ta sauke da murmushi kan fuskarta amma kallo d'aya za kayi mata ka hango tsantsan fargaba da tashin hankali dake tattare da ita. Addu'a kawai take c
ikin ranta Allah yasa kar Khaleel yazo.
"Ka yi hak'uri Baban Haidar "
Juyawa tayi da sauri ta fice . D'an kitchen d'in su dake nan tsakar gidan ta shige ta d'auko masa ruwa da cup ta dora kan plate. Gaban sa ta ajiye kayan ta koma kusa da yaran da suka
kafe Baban nasu da ido sun takure guri d'aya. Lafiyar yar gashin kaza ya juye kan plate d'in data ajiye masa. A take falon ya kaure da kamshi. Daga Ramlat har su Haidar saida suka had'iye yawu idan su kur kan plate d'in. Haka suka zuba masa ido yana yaga
r kazar nan hannu baka hannj kwarya yana korawa da lemo mai sanyi. Duk loma d'aya idan ya yi sai sun had'iye yawu. Saida yaci ya yi nak sannan ya tura musu d'an kafar kazar da hanji sai y'ar tsoka ta fiffike guda d'aya.
"Gashi nan ki raba musu kun zubam
in ido kaman wasu mayu. Haba wannan masifa. Na baku na safe,rana,dare baku godiyar Allah. Na fita nayi yawo y'ar k'azar ma ku barni naci kun sani gaba salon na kware. Kina koyawa yarana kwad'ayi. Tun wuri kisan irin tarbiyar da zaki bawa yara na. Bazan lam
unci wannan ba"
Batace komai ba ta d'auki plate din ta dan kwacaccala shi ta bawa yaran . Yana k'ok'arin miƙewa zai fice sai ga muryar Khaleel yana rafka sallama ya shigo kai tsaye da kaya niki-niki. Gaban Ramlat in dubu ne ya fad'i har wani gumi ke zubo
mata ta miƙe da sauri zata fice ta tareshi Khaleel d'in ya sawo kai cikin falon. INNALILLLAHI WA INNAILAIHI RAJI'UN kalman da take ta furtawa kenan cikin ranta. Turus ya tsaya yana kallon Baban Haidar daya bata rai tun shigowar Khaleel d'in .jinin su Sam
bai had'u ba yanda Khaleel ke ji da kuruciya baya ganin girman Baban Haidar saboda halin daya Yayar tasu ke ciki. Mugun ha
ɗ
e rai Khaleel ya yi ya k'arasa shigowa cikin falon da wata izza kace d'akin Mama ne. A guje su Haidar suka nufe sa ya ajiye kayan yan
a dariya ya rungume su. D'agowa ya yi ya kalli Ramlat dake kallan Baban Haidar da ke bin Khaleel d'in da mugun kallo fuskarnan tayi jazur da ita saboda b'acin rai .
"Yaya Ramlat ga sako inji Ya Reina"
"Khaleel me yasa baka da kunya ne?, baka ga Baban Hai
dar bane baza ka gaishe shi ba?"
Fuska babu walwala bai kalleshi ba a cunkushe yace
"Barka dai"
Ji Ramlat tayi kaman ta nutse a gurin saboda kunya ,tasan khaleel da taurin kai. A fusace ta rufe shi da fad'a inda take ciga banan take fita ba. Iya fusat
a kuwa Baban Haidar ya yi bakin sa na kumfa ya rufe Ramlat d'in ita ma da fad'a babu ruwansa da d'an uwanta da kuma y'ay'an ta dake gurin don shi laifin ita Ramlat d'in yake gani .
"Fad'an me ki ke masa?, idan baki nuna masa bani da daraja gurin kiba ai b
azai rainani ba bare ya dunga tunanin had'a kafad'a dani tunda yana ganin kanmu d'aya. Duk munafurci ki da kulle -kullen da ki ke ina sane. Ki cigaba da nunawa y'an uwanki na gaza dake da yarana. Annamimiya mai bakin hali da farar kafa. Nayi dana sanin au
ren ki"
A zuciye Khaleel ya tashi zai mayar masa da martani yana wani huci Ramlat ta daka masa tsawa.
"Ka fice a nan Khaleel "
Fuu ya juya a zuciya ya fice zuciyarsa na tafarfasa. Ajiyar zuciya Ramlat ta sauke ta juyo tana kallan Baban Haidar dake zuba
uban huci jikinsa har rawa yake saboda bala'i. Baki ta bu
ɗ
e zata k'ara bashi hak'uri ya d'auke da wani mahaukacin mari.
"Baki isa ki tozar tani ba. Duk abunda nake miki baki gani ba sai kin sa duniya tana min kallon mara imani? ,wlh daga yau ki ka k'ara k
iran wani ki ka ce ya kawo miki wani abu a gidan nan sai na lahira ya fiki jinda
ɗ
i. Mara mutuncin banza da wofi"
Hankad'e ta ya yi da mugun k'arfi ta kuwa ta fi ji ka ke kum tayi mugun ha
ɗ
uwa da bango. Zubewa tayi k'asa rike da cikin ta da take ji kaman a
na tsinka mata hanji. A fusace ya fuce yana huci bai damu da kukan su Haidar ba bare ya juyo yaga wane hali take ciki. A guje suka nufi Uwar tasu dake kwance a kasa tana murkususu. Da kyar ta d'ago tana kallan yaran dake kuka kaman ransu zai fita. Murmushi
k'arfin hali tayi ta yunkura da kyar ta miƙe zaune tana cije