Showing 39001 words to 42000 words out of 52463 words
Anwar ya girgiza ya miƙe " I'm sorry bazai Yiwu na tsaya d'in bane na kuma riga da nayi booking jirgi bacin hakama suna buƙatata ne cikin gaggawa "
Cikin fahimta suka miƙe duk
da sunsa cewa bawai saboda haka kawai yake son tafiyar ba. Rungume Shi sukayi gaba d'aya kafin suyi sallama ya wuce.
Washegari kaman yanda Lameen yace karfe goma suka fito tare da su Alhaji Muneer da iyayen sa harma da Ummi. Katuwar Motar Prado suka shiga
Lameen da Maheer a gaba. Lameen kejen motar su iyayen duk suna baya suna hira jefi-jefi. Gaba d'ayan su sunyi shiga ta kece raina sunsha manyan kaya kai kace an d'aura auren ma. Minti talatin ya kawo su k'ofar gidansu Reina. Suna baka motar su Hamza na f
aka mashin d'insa da yara gobe bayan sa. Daga Maheer har Lameen babu wanda ya lura saida suka fito daga motar yaran suka kwaso a guje suna kira
"Uncle Lameen, uncle Maheer "
Gaba d'aya suka juyo harsu Ummi suna kallon su. A guje suka fad'a jikinsu Lameen
ya sure Muniba da Aliyu fuskarsa cike matsanancin farin cikin ganin yaran. Soyayyar da yake wa Ramlat ta shafi yaran. Ba k'aramin kaunar su yake ba jiya ke kaman shida ita suka haife su. Duk da matsanancin kishi da yake a kanta wani ya riga sa, babu komai
yanzu tunda ta zama tasa za suyi ta haifan yara babu adadi. Wucewa ciki su Ummi suka yi suka bar mazan suna gaisawa da Abba daya fito jin hayaniyar yaran. K'ofar falon ya bu
ɗ
e musu ta waje suka shiga. Maheer dake jingine jikin mota yana kallon Lameen ya f
ad'a duniyar wasa suna tayi da yaran ya saki mugun murmushi yana kallon Hamza dake kallon Lameen kaman zaiyi bingida. A kausasashe ya kwalawa su Haidar kira.
"Kai Haidar kuzo nan?"
Sai a lokacin Lameen ya kula dashi. Ya kuwa b'ata rai yana kallon Hamza
tun daga k'asa har sama. Haidar ya k'arasa kusa da uban nashi a dan rab'e kaman mai tsoro kar ya kai masa duka. A kumbure yana kumfar baki yace
"Shiga ka kira min Maman taku"
Bai musa ba kuwa yaron ya kwasa a guje ya shige gida. Kar kuso kuga zuciyar Lam
een kaman za tayi bindiga. Daga shi har Hamza babu wanda ya yi yunƙurin motsawa daga inda yake sai mugun kallo da suke jefawa juna.
Suna can kuryar d'aki lokacin da Haidar ya shigo yana kiran Momi. Shigowar su Ummi ne suka koma d'akin amma da suna nan kit
chen suna taya Mama girki tunda sunsan da zuwan bak'in. Tun wajen bakwai na sace aka dora sanwa da su snacks da kuma lemukan gida na hannu na musamman da suka yi.
"Momy kije inji Daddy yana waje"
"Kaje kace masa bazata zoba"
Reina ta yi saurin bashi am
sa tana saka kaya kafin Ramlat d'in ma ta bu
ɗ
e baki. Ashe Mama taji ta shigo ne danta kira su
"Wane irin baza tazo ba?,Raheenatu bana san rashin kunya. Kai Haidar je kace masa gatanan zuwa ko dan Albarkacin yaran da kuke tare ai aji me yazo dashi. Idan k
i ka yi aure ai bashi da wani ikon k'ebewa dake. Maza kiyi sauri ki dawo"
Baki Reina ta turo ta cigaba da saka riga bata ce komai ba. A ranta kuwa cewa take tunda su Haidar suka zo to babu inda zasu sunzo kenan. Hijabi Ramlat tasa kan doguwar rigar dake j
ikin ta ta fito. Tana sawo kai kofa suna had'a ido da Lameen dake fuskantar k'ofar gidan. Gaban ta ya yanke ya fad'i. B'acin rai ne da tsantsan kishi kwance kan fuskarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tayi saurin d'auke kai tana kallon Baban Haidar dashima ya zub
a mata ido . Fuska a ha
ɗ
e ta k'arasa inda yake tsaye babu sallama tace
"Gani"
Murmushi ya yi " love wai har yanzu fushin ne?, don Allah kiyi hak'uri ki bani dama a karo na biyu ki koma d'akin ki wlh ina sanki Ramlat bazan iya rayuwa babu ke ba kodan sabo
da yaran mu"
Kafin ma tace wani abu suka tsinkaci muryar Lameen kan su
"Baza ta koma ba"
Shek'ek'e Hamza ke kallon sa "kai kuma waye ka ke shiga tsakanin mata da miji?, har ka isa kace Matata baza ta koma d'akin taba?kai a wa?"
"Mijinta.. kar ka kuskur
a ka k'ara kiramin mata da matar ta. Cewa za kayi tsohon mijin ta. Know backup she's mine"
Kasa cewa komai Hamza ya yi yana kallon Lameen daya kere shi a tsaye ya kirar karfi da Allah ya bashi. Duka d'aya zaiyi masa ya zube a gurin. Shi bama wannan ba bur
in sa ya Labba Ramlat ta koma d'aki ta. Yanzu yasan daraja da kimarta. Amaryar daya yi tun ba'a je ko ina ba ta fara gasa masa gyad'a a hannu. Sai yanda tayi dashi mugun tsoron ta yake ji kaman. A cikin watan shidannan da ya yi aure in aka cire sati biyu d
aya kwashe yana shan amarci babu ranan da zata fito ta fad'i bai fuskanci tashin hankali ba gurinta. Gata jibgegiyar mace idan ya bata haushi ta haukan shi ta zaune. Ya k'ara figewa ya lalace sai d'an hanci do ido kawai zaka gani. Kan Ramlat ya juyo ya ma
rairaice murya
"Don Allah kiyi hak'uri Ki koma d'akin ki don Allah. Badan hali na ba. Na tuba nabi Allah walh ina sanki Ramlat "
Cikin matsanancin kishi Lameen ya yunƙura kaman ya kifeshi da mari Maheer ya yi saurin tare shi.
"Dude relax mana"
A zuciye
ya juya kan Ramlat " Baby wuce ki koma gida"
Ikon Allah babu musu Ramlat ta juyo ta koma ciki. Hakan kuwa ba k'aramin dad'i ya yiwa Lameen ba ya juyo kan Hamza
"Kagani she's mine so backup"
"Karya ka ke wlh. Ai baka aureta ba har yanzu kaman allura ta
ke cikin ruwa mai rabu ya dauka. Kana manta cewa ni mijinta ne kuma uban y'ay'an ta"
"Tsohon mijin ta. Ka dinga gyara zancen ka. Eh kai uban y'ay'an ta ne na baya. Ni kuma zan zama uban y'ay'an ta daga yanzu har k'arshen numfashi da yardar Allah"
A zuci
ye Hamza ya burga mashin d'insa zuciyarsa na tafarfasa ya watsa musu mugun kallo ya fisgi mashin d'in kotakan yaran baibi ba. Dama kuma ya kawo sune su kwana biyu dan Hansa'u tace baza ta yi rainon y'ay'an wata ba. Y'ar dariya Maheer ya yi yana kallon Lame
en dake huci ran maza ya b'aci. Harara Lameen ya zuba masa yana taune harshe yace
"Dude a yau d'innan za'a bani auren ta I don't care bazata tare yanzu ba, ina so na ganta karshin inuwata nasan cewa nike da iko da ita"
Yana gama fad'in haka ya wuce ciki
Maheer ya biyo sa. Abinci ne baje gaban iyayen suna hira cike da nisha
ɗ
i kaman sun dade da sanin juna. Guri suka samu suka zauna babu kun Lameen ya bu
ɗ
e baki.
"Dad why not a d'aura auren yau kawai in yaso daga baya ayi bikin"
Ido duk suka zuba masa kaman
wanda keda kai hudu. Maheer ya guntse dariya. Alhaji Muneer ne ya yi k'arfi halin cewa
"A daura aure fa Lameen? Yanzu yanzu daga zuwa tambaya sai a daura aure?"
"Eh Dad ai naga ba wani taro bane za'ayi idan ma za'ayi taron sai ayi daga baya ko in na daw
o daga UK. "
"To mai zaisa ka bari idan ka dawo sai ayi komai a nutse mana"
Kaman wani k'aramin yaro yace "A'a dad ni gwanda kawai a daura kafin na tafi"
Ikon Allah. Dariya Abba ya yi ta manya yaran zamani sai Addu'a.
"Kaga Alhaji tunda har ya nuna ha
kan yake so ni a guri na babu wata matsala. Ramlat ai ba yarinya bace a d'aura auren kawai dama kuma kaga yau Juma'a, sai ayi a masallaci. Batun biki kuma babu wani biki saidai kai ango ita ai ba yanzu ta fara auren ba"
Ai ji yayi kaman an masa albishir
da aljanna. Ya saki murmushi bakin har kunne. Kai iyayen suka girgiza fuskarsa dauke da farin ciki suna k'ara jinjina halin dattako irin na Abba. Juyawa Abba ya yi kan Maheer
"In yaso kai Maheer sai ka shirya ka juya da matar ka yau ko?"
Kai ya sunkuyar
baice komai ba amma kar kaso kaga zuciyarsa. Sai suka ci suka sha suka wuce babban masallaci na garin Abuja. Kafin a tada sallah Alhaji Muneer yasa aka sanar akwai d'aurin aure bayan an idar ana gayyatar kowa da kowa. Gashi yau masallacin ya cika da dubb
an Al'umma. Ana idar da sallan kuwa aka d'aura auren Ramlat da Lameen kan sadaki Naira Million biyu cus ya bada kash a hannu. Inda zaka san dama da shirin yake. Garin Abuja ya d'auka abune sa aka jima ba'a yi ba.
Haka kawai tun bayan tafiyar su ta Kejin j
ikinta kaman wadda aka yiwa duka. Daga ita Har Reina babu mai kuzarin kirki. Ummi da Mama da Momyn Lameen suna can tsakir gida suna ta hira abun. Sai ga Khaleel niki-niki da kayan alawa da dabido kwali-kwali. Gaban su ya ajiye ya juya ya fice ya k'ara dawo
wa da wasu. Da mamaki suke kallon kayan daya ajiye gaban su kafin Mama tayi magana sai ga Abba ya shigo da jakar ku
ɗ
i . Sa sauri Maman ta shimfi
ɗ
a masa abun zama ya zauna bakin sa ya kasa rufuwa.
"Ina Ramlatun da Raheenatun suke?"
Da sauri suka fiti suna
amsawa.
Murmushi ya yi ya miƙawa Mama jakar ku
ɗ
in yana cewa
"Karb'i nan wannan sadakin y'ar kine Ramlat, yanzu a masallaci na daura mata aure. Hukuncin Allah kenan. Allah ya riga da ya kaddara yau zata zama matar Lameen. An d'aura aure tayi duk wani
shirye -shirye da zatayi don yace nan da kwana biyar zasu bar k'asar."
Gud'a Ummi ta saki da dariya a tare "Kai Alhamdulillahi nafi kowa farin cikin wannan abu. Ai Mama bani ita za kiyi mu tafi tare muje mu shirya ta a gida. Dama da Raheenatu zamu tafi ai
kinga sai na shirya su gaba d'aya "
Da saurin Ramlat ta tashi ta shige d'aki Reina ma ta bita. Gaba d'ayan su babu wanda ya cewa d'an uwan sa komai. Har yanzun Ramlat ji take kaman a mafarki wai ta zama matar Lameen?. Har wajen Magriba daga Reina har Ram
lat babu wanda ya k'ara yunƙurin fitowa sai da su Ummi zasu tafi ta shigo har uwar d'akin ta sasu a gaba suka fito da kayan su. Da kyar ta bari sukayi sallama sa Mama da Abba suka fito kan kowa a k'asa. Mota suka shiga tare da Ummi da Momy su kuma mazan s
uka shiga guda da Maheer yasa aka kawo. Har suka je gida sun kasa sake jiki musamman Reina dake ji komai ya zame mata sabo , sun zame mata tamkar bak'i. D'aki Ummi ta basu ta hana daga Maheer har Lameen su gansu. Sosai tasa su a gaba da gyara babu kama ha
nnun yaro. Cikin kwana biyu suka cika suka batse har diga suke ga maaifaffen kamshi da suke mai shegen dad'i a koda yaushe sunyi wanka ko basuyi ba. Tun daga India ta dauko mai kunni aka rangad'e su da henna kaman ka sace su ka gudu ga body shape nasu ya k
'ara fitowa kaman y'an tsana.
Yau ya kama tafiyar su Ramlat tun asuba Ummi ta sasu a gaba ta wanke da ruwan turare dana hayak'i. Aka shirya su cikin wata doguwar riga y'ar India sunsha tsarka ta gwal. Sannan ta fito dasu kowa aka sashi cikin motar mijinta
. Kamshin turaren Maheer ya daki dodon kunnen ta. A hankali ta d'ago suka had'a ido yaja wani irin numfashi kaman zautacce. Kyan data yi bazai misultuba. Yana sanye cikin wata three pieces suits dark ashe data kamashi ya yi masifar kyau da ponytail d'insa
idan sa sanye da farin glass ga hadedden wrist watch na DAIMON dake daure tsintsiyar hannun sa. Duk wannan kyan daya yi mata tayi mugun ha
ɗ
e fuska ta matsa can gefe kaman wadda taga kashi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya yi magana kaman maijin tsoro
"
You are so beautiful "
A zafafe tace "basai ka k'ara sanar dani abunda na riga na sani ba"
Murmushin gefen baki ya yi yana san wannana sass nata is turning him on that is so painful and hurts at the same time. Baice komai ba ya shiga da kallon ta yana m
urmushi tana zuba masa hara kaman zata cire don ta ta bashi.
Bangaren Lameen kuwa ai kasa jurewa ya yi da azamarsa ya rik'o ta ya matse kan faffa
ɗ
an kirjin sa yana sauke ajiyar zuciya. A kunyace ta kwanta kan kirjin data jima tana mafarkinsa.
"Finally
Baby, I get to see you. Haba wannan rashin ganin naki is to painful. Hope dai kin shirya ko dan wannan mijin naki babu wasa ina so a yau mu samu first baby namu nida ke"
Ido ta zaro tayi saurin kwacewa ta koma gefe tana jin kaman motar g ta rabe biyu ta s
hige k'asa. Y'ar dariya ya yi da husky voice nashi.
"What, wai kunya ki ke ji? ,mijin ki bashi da kunya ki ajiye ta gefe"
Bata ce komai ba kanta a k'asa amma tanajin irin kallon kurillan daya ke mata. Saitin fuskarta taji saukar numfashin sa kafin taji
ta kirata da sunan data tsana
"Guntul"
Aikuwa ta d'ago ta juyo a zafafe zata kwaba mishi magana ya had'e bak'in su. Bakinta daya sha janbaki ya damke da nashi yana bata wata irin zazzafar sumbaci kaman zai cinye bakin. Duk wani k'arfi da kuzari na Ramla
t ya fece. Tunda take da Baban Haidar bata tab'a jin abunda take ji ba yanzu. Saida ya sumbaceta san ranshi duk ya shanye janbakin Sannan ya sake ta yana sauke ajiyar zuciya. Finally he has being longing to taste those lips. Kunya wajen Ramlat ba'a cewa ko
mai sai muzurai take yana murmushi yana binta da predator eye's.
Had'addan reception ka yi. An kawara gurin kaman a k'asar waje. Babu wasu mutane da yawa dan basu fi hamsin ba. Abun ya k'ara tsari matuƙa komai anyi shi a gayance. Amarya da ango sun dan
taka sunsha b'arin ku
ɗ
i ga cima kala-kala sai ka ture. Karfe biyu daidai aka tashi kowa ya watse. Reina da Ramlat suna rike da hannun juna dan sunsan sallaman kenan daga nan ita Ramlat zata wuce idan taje tayiwa su Mama sallama. Su Haidar yace daga baya za
i turo a kaisu dan a can UK zata zauna.
Kuka suke angwayen kowa tsaye bayan tashi. Ganin kukan nasu bazai k'are ba Lameen ya yi magana yana kallon agogon hannunsa.
"Baby jirginmu zai tashi nan da 1hr kiyi hak'uri mana haka."
Babu wanda ya kula shi sai
ma k'ara rungume juna da sukayi suna kuka. Kai ya girgiza Maheer kuwa ya kasa cewa komai sai kallin Reina da yake da longing. Ji Ramlat kawai tayi ya yi sama da ita kunya yasa ta maida kai ta kifa kan kirjinsa. Tanajin suna sallam da Maheer kafin ya wuc
e ya sata a mota suka bar gurin.
Ajiyar zuciya Reina ta sauke bayan b'acewar motar su. Muryar Maheer taji bayan ta
"Let's go"
Ya mik'o mata hannu ta kama saboda rigar jikinta data kamata take tafiya a hankali. Mugun kallo ta watsawa hannun yaga d'azu y
ana ta rungumarta cikin mutane ta kyale shi saboda ido shine yake tunanin yanzu zai iya tab'a ta ta kyale shi?. Tsaki taja mai k'arfi ta wuce tana tafiya a hankali ya bita da kallo yana murmushi. Kai ya girgiza ya yi saurij binta suka jera har wajen mota y
a riga k'arasawa ya bu
ɗ
e mata ta shiga tana banka masa harara.
Tayi tunanin gidanshi na Maitama zasu sai taga sun dauki wata hanya daban. Har ta fara tunanin yanayin data riske shi da Fadeela. Wai ina ma Fadeelan ne? Ta yiwa kanta tambayar da babu mai b
ata amsa. Katon gida suka shiga mansion guda ta ko ina sojoji ga wasu shegun karnuka na waje da aka zuba lungu da tsako. Dole kuwa dan ita kanta zata shaida duk Abuja babu gida kaman shi. Za kayi tunanin daga waje aka dauko gidan aka dasashi .komai da glas
s aka yi shi. Galala take kallon gidan .aljannar duniya kenan. Ashe abun kallon yana ciki. Duk irin wayewa ta Reina saida ta saki baki da hanci tana kallo ta manta da Maheer dake binta kaman jela duk inda tayi. Yanda kasan tasan gidan ta shiga nan ta fita
nan har ta shiga wani shegen d'aki mai masifar kyau da Sam bazai kwatantu ba. Tuni ta gama sawa a ranta ya zama nata dan haka kai tsaye ta nade gadon saboda gajiya. Miƙewa tayi ta fara k'ok'arin cire riga bayan ta tub'e dogon takarmi dake k'afarta. Ido suk
a had'a dashi jingina jikin koma ya harde hannu da k'afa ya zuba mata tsumanmun idan sa. Wlh tuni ta manta dashi. Kici-kicin tayi da rai tana kallon sa da fad'a tace
"Lafiya dai?, kaja ka tsaya kana kallo na? "
Murmushi ya yi " kiyi hak'uri me zakici na
d'ora mana"
A dak'ile tace "bana san shiga sharo babu shuni. Ka dafawa kanka abunda za kaci nima ina da kafa da hannu zan dafa nawa"
"Hmm, ok"
Ya bita da wani shegen kallo data kasa gane shi ya fice daga d'akin. Tsaki taja mai k'arfi. Ta miƙe ta banko k
'ofar tana mita. Mutum sai shegen naci kaman maye haba. Kayan ta cire ta shige ban
ɗ
aki ta watsa ruwa da alwala