Showing 33001 words to 36000 words out of 52463 words
ya watsa ruwa tare da d'auro alwala. Farar jallabiya ya saka ya fashe kanshi da turarurruka masu sanyin kamshi kafin ya tada sallah kaman yanda ya sama ya kuma zame masa jiki.
Washegari
ma bai shigo ba daga masallaci sai da gari ya yi haske sosai yana tilawar Qur'ani shi da A Muneer da sauran mutane dake zama. Wannan karon Harda Lameen da Anwar . Ba kullum Lameen ke tsayawa ba. Gab d'aya suka shigo falon bakin su dauke da sallama. UMMI s
uka tarar cikin shiri ita dasu Annoor dake ta doki zasu unguwa. Kallon su tayi tana gyara mayafi.
"Yauwa kun shigo?, ni zanje naga Ya'ta ga abinci can kan dinning, sai na dawo"
K'ok'arin wuce su take duk suka bita da ido. Dariya Dad ya yi yana girgiza
kai ya yi saurin tare ta.
"Ki bari mana ki karya dan nasan baki karya ba sai mu tafi gaba d'aya ko?"
Zama Ummi tayi badan taso ba tana cewa
"To kuyi suari don Allah naje naga Raheenatu. Har yanzu ban yarda ita ce ta dawo ba sai na ganta da ido na"
Mur
mushi suka yi gaba d'aya duk suka haura sama Maheer ya wuce gurin su Ablah dake wasa ya rungume tare da sumbatar goshin su ya wuce da sauri ya haura sama. Yafi kowa buƙatar ganin Reina a gaggauce ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin shadda dakakkiya mai t
sadar gaske data yi masa masifar kyau ya d'ora hula kan jikakken bakin gashin sa daya sha mai ya k'ara zama wani coily ya kwanta luf bayansa da goshin sa. Murmushi ya yi yana kallon kansa cikin mudubi. Yasan yanda Reina ka son ganin sa da manyan kaya sabod
a ba k'aramin kyau suke masa ba. Rigar doguwa ce da wandon ta ya saka bak'in takarmi mai yatsa sai Agogob Rolex mai shegen tsada daya amshi fatar sa.
A hanzarce ya fito falon yana duba agogo. Da ido Ummi ta bishi tana tasbihi cikin ranta. Hak'ika Allah y
a basu yaro mai kaman dubu cikin Al'umma. Maheer nata ta ko ina ya cike d'ari. Ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba. Kan d'an ta Maheer kan ya cike shi tab tamkar shi ya hallici kansa dan kyau. Fitowar su Anwar da Dad ya dauke hankalin ta daga kan Mah
eer ta miƙe da sauri da nufi tebir ta shiryawa kowa abinci suka hauci a gurguje saboda azalzala da Ummi ke musu. Maheer kuwa ya kasa ci dan yafi Ummi matsuwa yana dakewa ne kawai. Da kyar ya yi cokali biyu ya ajiye yana duba agogo a kai a kai.
Gaba d'aya
suka miƙe suka fito. Mota biyu suka yi Ummi da Dad cikin guda, Anwar, Lameen da Maheer a bayan su. Tunda suka d'auki hanya gaban Maheer ke bugawa. Kar suje yauma tace bata sanshi ba, amma su Ummi fa suma ta manta su?
✦✦✦
Saboda yanda suka raba dare ba
suyi barci ba yasa tunda tayi sallan asuba take barci saboda gajiya. Babu wanda ya yi yunƙurin tashin ta suka hau gyara da dora abinci. Sama-sama takejin magana kanta da shakkekar kuka. K'ok'arin bu
ɗ
e ido take taji an fado kanta ana
"Momy, momy"
Ai tuni
ta manta da kukan da take ta tashi a sukkuwanne ta rungume Annoor da Ablah dake kuka jikinta. Tuni ta manta da plan d'in daya shirya. Doga yaran tayi tana kallon yanda suka k'ara wayo da kyau abunsu. Dariya tayi mai hade da kuka ta k'ara matse su cikin k
'irjin ta. Idanuwan data keji kanta yasa ta d'ago suka had'a ido da Ummi dake zaune gefen gadon tana kuka da murmushi a tare. Kunya ce ta kamata ta sunkuyar da kai tana gaishe ta. Rungume ta Ummi tayi tana Hamdala.
"Alhamdulillahi, kinga ikon Allah ko Ra
heenatu, Allah ya dawo mana dake Anwar ya sheda mun komai. Mun gode alherin wannan mutane Allah ya saka musu da aljanna "
Ramlat da Mama suka Amsa da Amin. Miƙewa Ummi tayi tana goge hawaye tace
"Idan kin gana kizo falo tare muke da Baban Maheer "
Ai t
anajin sunan ta b'ata rai kaman wadda aka gayawa sakon mutuwa. Ba Mama kad'ai ba har Ummi mamaki ya kama su na ganin chanjin fuskarta lokaci gudu. Abun tambayar anan shi ne, Fitowar ne bata son yi ta gaisa da Baban Maheer ko kuwa Maheer d'inne bata son gan
i?. Kai Ummi ta girgiza ta fice da sauri koma mene za suji. Mama ma ficewa tayi tana jefawa Reina kallon tuhuma. Bayan sun fice Ramlat ta zauna gefen gado tana kallon ta tana wasa dasu Annor dake cewa ta tafi ta barsu karta kara tafiya ta barsu.
"Wai mene
matsalan ki da Maheer ne?,ni dama nasan jiyan kina sane duk abunda ki ke. Me ya yi miki haka mai zafi daya kasa wucewa har yanzu"
Duk yanda suke da Ramlat tsintar kanta tayi da kasa gaya mata abunda Maheer ya yi. Bata rai tayi tana tabe fuska .
"Nifa ka
wai yanzu bana sanshi ne Yaya Ramlat. Bazan iya zama da mutum da yake rayuwa can wata duniya daban ba, bashi da cikakken lokacin da iyalen sa"
Kallon da take bin Reina dashi ya tabbatar bata yarda da abunda tace ba amma tayi shiru bata ce komai ba. Numfas
hi taja mai karfi ta fesar.
"Annoor ,Ablah kuzo muje Momy ta shirya ko"
Babu musu yaran suka bita Reina ta bisu da kallo tana murmushi. Miƙewa tayi bayan sun fice ta cire hajibin dake jikinta. Tsabar yanda barci ke idon ta d'azu ko cire hajabin bata yi b
a kan doguwar rigar dake jikin ta mai tsantsi fara mara nauyi. D'an pant ne kawai a ciki dan rigar da gidan bra d'inta gata shara-shara. Mik'a take cike da gajiya ko ka
ɗ
an bata lura da mostin shigowa ba sai dataji wani irin kamshin turare mai masifar dad'i
da saka nutsuwa ga duk wanda ya shak'eshi. Hannun ta dake sama tana mika ta ajiye da sauri ta bu
ɗ
e ido ta juyo bayanta dan ganin mammallakin shi duk da zuciyar ta ta bata ko wane dan shi ka
ɗ
ai ke irin wannan kamshin.
Ido suka had'a da Maheer dake jingina
jikin bango kwayar idon sa dauke da tsananin so da bege da kuma wani abu data kasa gane shi. Nan da nan fuskarta ta chanza ta mugun ha
ɗ
e rai tana jefe masa kallon tsana. Murmushi ya ya k'arasa shigo cikin d'akin ya tako a hankali har inda take tsaye.
"I
know baki manta ni ba, kina pranking d'ina ne. Nasan girman laifin dana yi miki ya chanchanci ko wane irin hukunci zaki d'auka a kaina. A shirye nake da karb'ar sa matsawar hakan zai sa kiji a ranki zaki yafe min wata rana ko ba yanzh ba After all har yanz
u ke Matata ce Right?"
A zafafe tace "Am not your wife, divorce me yanzun nan, ko hukuncin dazan yanke bazai maka dad'i ba da kai da duk wani mai kaunar na. Zan maka ka a kotu na kuma karb'i costudy na yara na. I'm a lawyer zan iya fidda wasu hujjoji na
bogi da zanyi restraining order a kan ka. Dan haka tun muna mubiyu ka sake ni kaje ka aure wadda ka ke so. "
Tunda ta fara maganan ya kafe d'an k'aramin bakin ta da ido. Fad'a take amma saboda sanyin muryar ta baza kace fad'an take ba sai in fuskarta tayi
jaa. Murmushi ya yi yanajin d'acin maganan rabuwa da take furtawa. Tabbas Reina da yasani a da ba ita bace wannan. Waccan tana masa so da baza ta iya Rayuwa babu shi ba, amma wannan ta kalli kwayar idansa tace ya rabu da ita. Abu ne da bazai tab'a faruwa
ba. Ya gu loosing d'in ta once yanzu kuma ta dawo gareshi babu wani chance da zai yarda ya k'ara loosing d'inta. His ready to fight.
Wani irin intense kallo ya bata yana jin wani d'aci cikin ransa. Da kyar ya iya bu
ɗ
e baki ya bata amsa.
"Never, I will n
ever divorce you sai in mutuwa nayi"
Tuni ta k'ara ganin hayak'i .juyawa ya yi zai fice tasha gaban sa . Tsabar yanda masifa ke cinta jikinta sai tsuma yake. A zafafe bakinta na kumfa ta fara magana k'asa-k'asa tana nuna k'irjin sa da yatsa.
"Idan ka isa
d'an halak ka sake ni yanzun nan. Na tsane ka na tsani duk wani abu da zai rabe ka. Ka sake ni nace"
Ido ya zuba mata zuciyar sa na gaya masa she's change and their is no why in he'll zai k'ara yin thesam mistake daya yi a baya. A hankali ya furta mata k
alma d'aya ya wuce ya barta tana tsuma kaman tayi bindiga.
"Never"
Cije baki tayi ta wuce fuu ta shige ban
ɗ
aki zuciyar ta na suya tayi wanka ta fito. Cikin fushi take shirya wa harta gama ta fito sanye da riga da sket da suka kamata sosai saboda Hips na
ta daya k'ara bu
ɗ
ewa. Kayan Ramlat ne kusan basu da banbanci wajen k'iba amma yanzu Reina tafi Ramlat jiki. Katon mayafi yafa ta fito. A falo ta same su gaba d'aya ana ta raha. Da sallama ta shigo kanta a kasa. Kusa da Ramlat ta rakub'e tana gaida Alhaji
Muneer dake amsawa fuska cike da murmushi. Tanajin yanda ido ke binta kaman masu ganin hanjin cikin ta. A hankali ta d'ago sai karaf suka had'a ido da Anwar dake kallonta tun d'azu. Murmushi ya sakar mata tayi saurin maida kai ta ta sunkuyar cike da haushi
. Ita yanzu duk wani abu daya shafi Maheer bata so.
Maheer dake gefe kaman zaiyi bindiga zuciyar sa ana wani irin tafarfasa. Duk wani exchange daya faru tsakanin su kan idansa. How dare Anwar zaima matar sa murmushi?. Dunkule hannu ya yi ya yunƙa zai dan
nawa Anwar zagi Lameen dake zaune kusa dashi yana nazarin sa ya yi saurin dafa hannun daya dunkule . Ajiyar zuciya ya sauke ya rintse ido yana fesar da huci mai zafi. Muryar Lameen yaji yana magana kafin ya miƙe ya kama hannun Maheer suka fice daga falon.
Waje suka yi Lameen ya juyo cikin fushi.
"Kana da hankali kuwa mai ka ke shirin aikatawa ne?"
"Kai baka ga kallon da yake mata ba?, Matata ce fa har yanzu, bashi da hurimi da ita da zai tsaya yana kallon ta yana mata murmushi "
"Kai ma kaji abunda kace
ko? Matar ka. Ka kwantar da hankalin ka please ka nutsu ka ajiye wannan kishin aside. Anwar dan uwanka ne, kuma ya bada gudunmawa mai yawa wajen ceton rayuwar ta. Ko babu komai wannan ya isa ya kulla zumuncin mai karfi tsakanin su bare kuma tana matsayin
matar ka. Yanzu kamata ya yi ka maida hankali wajen winning d'inta back"
Ajiyar zuciya yaja mai karfi k'afad'arsa ta saki. A sanyaye kaman zaiyu kuka yace
"She hates me"
"What do you expect Maheer?, you cheat on her da friend d'inta kuma cousin naka. A
kwai ciwo but that love yana nan .can kasan zuciyan ta bunne sa ka hak'o sa ka nuna mata hau sorry you are and regret your actions "
Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido. Tabbas zaibi shawarar Lameen. Why yake son Lameen kenan his a freaking genius y
asan takan sarrafa harshe ya baka calmness da ka ke nema. Komawa suka yi aka cigaba da hira .da suka koma ya tarar sun koma d'aki ita da Ramlat ya yi ta zuba ido har suka fito zasu tafi amma shiru ka ke ji. Annoor da Ablah dama sun mak'ale gurin Maman su.
A sanyaye ya shiga mota yaso ace ya ganta koda zata zageshi ne hankalin sa ya kwanta.
✦✦✦
Suna shirin kwanciya wayar Ramlat dake gefen drawer ta hau k'ara hannu ta kai ta d'aga wayar sai taga bak'uwar number. To wane haka. Ita dai tasan babu wanda yasa
n number d'in ta sai Baban Haidar. To ko shine ?,amma ai in shine tana da number d'insa. Waye haka cikin daran nan?. Ajiye wayar tayi ta gama ringing bata d'aga ba tana katsewa kuwa wani kiran ya k'ara shigowa nan maki d'agawa ta k'ara katsewa wani kiran y
a k'ara shigowa. Reina dake kwance dasu Ablah tayi zurfi cikin tunanin yanda zata maka Maheer da Hamza kuto su basu takardar saki da kuma karb'awa Ramlat y'ay'an ta. K'arar waya ta dameta ta juyo cike da haushin Maheer
"Wai ki d'aga mana haba, koma waye
yabi duk ya ishi mutane da naci. Mtswww "
Murmushi Ramlat tayi ta d'aga wayar bakinta dauke da sallama. Ba'a amsa ba sai ajiyar zuciya dataji an sauke.
"Finally woman. Me ki ke nake ta kira kinki dauka, kashi?"
Cije baki tayi wane dan iskan ne kuma wan
nan. Tambayar ta ta samu amsa a take
"Guntul"
Wai ji tayi kaman tayi jifa da wayar saboda haushi. Da cijajjen baki tace
"Ina ka samu number na?
Dariya ya yi da take jin sautin ta
"Ina ruwanki da inda na samu?, inna gaya miki me zaki bani?"
Cire wayar
tayi daga kunne a zafafe zata kashe taji Muryar sa
"Allah idan ki ka kashe wayar nan baza kiyi barc..."
Kitt ta kashe wayar tayi jifa da ita kan gado . Kaman yanda yace kuwa ba suyi barcin ba dan wani irin mahaukacin kira ya dinga jero mata ga shigiyar w
ayar bata mutuwa gurin switch d'in ya lalace ta sata silent ta dame su da uban vibration. Ai kuwa Reina ta cika tayi fam. Ga haushin Maheer gana Suarayin Ramlat. A fusace ta d'auki wayar tayi jifa da ita. Haba maza sai shegen naci da jaraba.
𝐙ꨄ
︎
𝐂
𝐈
𝐘𝐀𝐑
𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌ꨄ
︎
(
ʙʟ
ᴇᴇᴅ
ɪɴɢ
ʜ
ᴇꨄ
︎
ʀ
ᴛ
s)
✯
D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
*AMMEY LAYLERH DETA SERVICES*
*Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa
👌🏻🤗
*
*MTN*
500MB-180
1GB -280
2GB
- 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500
*AIRTEL*
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600
*GLO*
200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600
*9MOBILE*
500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB
- 2500
Account number: 3206656358
Account name: Maryam Nasiru first Bank
*MORE Information 08104493215*
✯
𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘
𝐋𝐎𝐕𝐄
.
E|61/65.
Not fully edited!
Washegari karfe takwas
tayi wa Maheer da Lameen k'ofar su Reina. Abba ne ya shigo yake cewa Mama sunzo suna waje dan haka a dora abincin dasu. Kira Mama ta kwalawa Reina dake shirya su Annoor bayan ta musu wanka. Amsawa tayi fito sanye cikin doguwar riga baka mai mad'auri. Kanta
d'aure da mayafin rigar. Bakin k'ofar kitchen d'in ta tsaya tana kallon Mama da Ramlat dake soya Kosai da kunun gyad'a.
"Gani Mama"
"Yauwa kije ki kimtss falon anyi bak'i "
Da mamaki tace to kusa waye yanzu da sassafen nan. Falon ta wuce ta k'ara kimts
ashi ta kunna turaren wuta. Tana k'ok'arin fitowa taji muryar Abba nawa bak'in iso. Sa sauri ta fito har suka kusa cin karo da Maheer daya sawo kai. Baya taja fuska a ha
ɗ
e ta koma ta basu wuri. Ja ya yi ya tsaya shi bai wuce ba bai kuma bata hanyar wucewa
ba. A zafafe ta d'ago zata yi masa rashin mutunci suka had'a ido da Abba dake tsaye bayan su. Cikin kunan rai ta gaishe su murya k'asa-k'asa yanda baza suji amma da yake hankalin sa kacom yana kanta saida yaji. Nan da nan fuskarsa ta cika a annuri ya kauce
ya bata hanya ta wuce da sauri kaman zata kifa. D'aki ta koma tana mita cikin ranta. Maza da shegen naci suke wlh. Su Annoor ta k'ara shiryawa tace suje Baban su yazo ai kuwa suka kwasa a guje suna kiran Daddy. Ramlat ce ta shigo da d'an flasks na abinc
i da wanda suka zuba kunnun gyadan a ciki. Kosan ya yi jajur dashi yaki albasa da nama. Ga kunun gyadan dayaji madara sai gard'i yake. Zagewa suka yi suka kwashi abincin nan kaman zasu cinye kwanan sai santi suke zubawa. Khaleel ne ya shigo rike da nashi k
wanan sai hamma yake sai yanzu ya tashi. Samun gurin ya yi ya zauna ya fara kai loma cikin bakin sa. Muryar Mama suka ji tana kwalawa Reina k'ira. Turo baki tayi dan tasan kwanan zancen. To ai ba ita ka
ɗ
ai ce a gidan ba da sau ita Mama ke turawa wajen su.
Fitowa tayi tana turo baki ta samu Mama tsayr bakin k'ofar kitchen da wani flask mai kyau a hannun ta.
"Ingo wannan ki mik'a musu zasu k'ara. Yanzu Abban ki yace sun basu koshi ba a k'ara musu"
Ikon Allah kaji fa. Su ko irin alkunyar nan Babu. An basu ab
inci sun cinye harda neman k'ari?.
Karb'an abincin tayi ta koma falon bak'in ta da y'ar sallam dan tayi tunanin Abba ma yana ciki. Lameen ne ya amsa bakinsa cike da kosai yana