Showing 1 words to 3000 words out of 50955 words

Chapter 1 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2113

[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR




Story and writings by;
Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
📚✍🏽




Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina yi wa Allah godiya da ya bani ikon kammala littafina mai suna DA MAI RAI AKE RIKICIN DUNIYA
Littafi ne da ya yi duba akan ƙanne, iyaye da irin yadda suke shigo-shigo ba zurfi na ji daɗin yadda littafin ya samu karɓuwa.






Labari guda uku basira uku mahanga uku labarin ba iri ɗaya bane ko wani labari mahangar shi daban don haka ku shirya a sannu zaku gane
In da labarin ya dosa a wata mahangar


Yanzu ma muna tafe da wani littafi
mai suna WATA MAHANGAR ku buɗe kunnen ku zaku sha labari tare da faɗakar wa daga garemu littafi ne da zai haɗa marubuta guda uku, zamani uku, da tunani guda uku. Ina ma'abota karance- karance ku matso kusa don zaman jiran fitowar wannan littafi na marubuta
Amina maaji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam.


Paid book 400
Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984




Doka bamu yadda a juya mana labari ta kowace fuska ba yin hakan saɓa doka ce garemu duk mai matsala ko labarin yayi dai dai da rayuwar wasu mafita da gyara a ke nema duk da labarin a cikin kashi ɗari kashi sittin gaskiya ne ,ba munyi dan cin zarafi ko sawa wasu sunji sun tsani soyayya ba kowa da irin tashi ƙaddaran kai tsaye kakira_ kikira ɗaya daga cikin marubutan littafin mungode .




LAMBA TA ƊAYA


So shine ya ruguza min dukkanin tunanina ya ruguza min dukkanin ƙofofin daƙile wani gurbi na soyayya so ya yi min mungun saran maciji da son JB gara na sha guba lokaci ɗaya na bar duniya ashe maza sun daɗe suna yi mana lahani mai kama da ukuba na shiga garari tare da shiga tsaka mai wuya na tattara dukkan yarda da amana na bawa JB ashe mungu ne azzalumi, kuma mayaudari. ina rokon Allah da ya sakawa duk wacce ta faɗa irin tarkon da na faɗa wannan shine da na sanin da na fara yi na amsa tayin JB .da na barshi ya shiga cikin gararin rayuwa da tashin hankalin na godewa Allah da yasa ba a kan soyayyar shi na fara tsintar kaina da soyayya mai ruɗani ba sai in ce a cikin soyayya ni ce ban dace ba don an cutar dani .anyi mun lahani an sa natsani soyayya gaba ɗaya aguna bata da amfani don tayi mun illa a dalilin so narasa wasu abubuwa masu mahimmanci agareni.


Saboda soyayyar da muka yi da sauran ya sha banban da na JB duk da ƙaracin shekarun shi sai da ya yi min wayo yaci zarafina girma na bai amfane ni da komai ba sai cizon yatsa. so bai yi min adalci ba yasa na ruguza irin tarbiyyar da iyayena suka ɗaura ni akai Allah ka saka min.


A wani safiyar asabar ne ina cikin zama na na hau yanar gizo misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe 7:30am don ganin wani wainar ake toyawa na hau shafin sada zumunta wato wajen da ya haɗa mutane daban-daban wato facebook duk da a yanzu kasuwar shi ta kwanta yanzu yayin TikTok ake yi yawanci yan mata da samari nanne wajen samun nishaɗin su .amma hakan bai dame ni ba don duk in da kayi sabo to nan ne hanyar farin cikin ka.
ba da kowa nake mutunci ba bana yawan posting amma mutane da yawa sukan yi min magana kuma muyi mutunci da mutunta junanmu har ma da girmama wa a tsakanin mu.




Wani naga ya yi min magana ganin sunan yasa na amsa don kuwa sunan mahaifinmu iri ɗaya da shi mun gaisa sosai sannan na mutunta shi kwana biyu da faruwan hakan ranar Laraba ina zaune misalin ƙarfe tara na safe 9am naga wani baƙon number ya Kira ni da kamar ba zan ɗauka ba kawai wani tunani nayi na ɗauka can! sai naji ya yi sallama ta ɓangaren shi na amsa "kin san da waye kike magana?"cewa nayi gaskiya ban sani ba .


"JB ne kin gane ni" waye haka kenan?" wanda sunan mahaifinmu iri ɗaya "na gane amma waye ya baka number ta kuma waye ya baka izinin kira na?


"Ki yi haƙuri babu wanda ya bani kawai nine na samu ki yi haƙuri don Allah "shikenan yaya na ba komai na gode Ka ci darajar suna "godiya nake sosai gimbiya ta sarauniyar raina.
Murmushi nayi don gaskiya ya yi matuƙar bani dariya da Hausar shi irin ta Barebari.




Bayan mun gaisa shikenan ban ƙara jin labarin shi ko da na minti ɗaya ba a ranan haka ban sa komai a raina ba don ni ba komai a raina sannan nasan mutunci ne yasa ya ƙira ni ban san in da ya samu number ta ba tunda ni wajen shekaru hudu ban yi soyayya ba naso ganin hoton shi amma ba shi bane a kan dpn shi na Whatsapp ba, bayan
Kwana biyu naji ya yi min magana ya ƙira ni da sunan da ni kaina muddin a ka kira ni da sunan bana jin daɗin shi wato a kira ni da baby, a dama bai yi min amfani ba balle yanzu.


"Me yasa zaka Kira ni da wani sunan da gara guba ma da shi? '' subhanallahi! me yasa kika ce haka?"e babu wani suna da zai burge ni indai ta shafi soyayya ce "ki yi haƙuri nima da soyayya na zo miki sannan da maganar aure".


Aure kuma?


"bana jin soyayya a raina ka bar ni inyi rayuwa ta ba tare da wani ɓangare na jiki na ya samu matsala ba, don kuwa maza duk halinku ɗaya duk da sunan ku daban ne, amma hali kam duk ɗaya ne,"ka yi haƙuri na daina soyayya"ki taimaka mun ki karɓi tayin soyayya ta ba zan taɓa gudun ki ba zan kula dake da baki dukkan kulawa daga gare ni".


dogon numfashi naja saboda abun ya dame ni wallahi ko kalmar so bana son ji ko kaɗan saboda yana matuƙar ɗaga min hankali ba na kaɗan ba, na rasa dalili, a ranar ya kira ni yafi sau goma yace min sai mun yi video call ni kuma na kafe, bani da ra'ayin shi tunda ni ba ma'abociyar yin shi bane da safe ina buɗe waya ta da saƙon shi zan fara cin karo tun bana yarda har na fara sakin jiki da shi in ya kira mu zage mu yi ta hira da shi sosai
A nan ne nake sanar mishi nifa ba yarinya bace ya kamata ya gane nayi mishi bayanin yadda shekaru na shima ya gayamun na shi duk da ba a nan gizo ke saƙar ba don na ba shi shekaru kusan biyar ma'ana na girme shi kalman da yace min "wallahi shekaru ba za su taɓa ruguza mana soyayyar mu ba ko dai su hana mu auren junanmu ba. ''tura min hoton ki' don Allah' ba musu na tura mishi shima ya turamun nashi tabbas yaro ne sosai don wani zubin a hoton kaya ne ke sawa a ganshi kamar mai yawan shekaru da yawa tun daga nan muka yarda da juna har muka amince da juna ya yi min dukkan bayani a cikin Borno yake ni kuma cikin Damaturu nake ban ɓoye masa komai ba kamar na ƙara masa wutar so na a ranshi amma na sanar masa da irin lalurar da nake fama da ita na ciwon zuciya ya yi min fatan samun sauƙi. Akwai wani ranar da ya tambaye ni me ya raba ni da tsofin samari na a yadda ya ganni bazai iyu a ce banida samari ba .


Numfashi naja sosai
" Na farko mun rabu ne sakamakon shaye-shaye na biyu mun rabu saboda na kama shi yana soyayya da ƙanwata a ɓoye na uku saura sati biyu auren shi ban sani ba sai na ƙarshe Muhammad wanda har in koma ga wanda ya halicce ni ba zan samu madadin shi ba " Muhammad ya So ni ya ƙauna ce ni, in kuwa abubuwa zai yi wan da ya shafi jin daɗi tabbas baya barina a baya koda sutura ce ko da shadda zai ɗin ka to kala ɗaya zai ɗinka mana in anyi musu albashi zuwa yake garin mu muyi kusan kashe kuɗin in zai koma yabar min kuɗin kashewa .


kasancewar jinyar mu ta ciwon iri ɗaya ce ba ya ɓata min rai, bai taɓa gaya min abun da zan ji raina ya ɓaci ba yakan baro garinsu don kulawa da tawa lafiyar, mahaifiyar shi da sauran danginsa, suna mutunta ni a ganin su, haɗuwa dani yasa ya samu sauƙi don baya yawan kwanciya rashin lafiya a kan da, su biyu iyayen su suka haifa duk da suna da kuɗi amma baya garesu ni yake so yakan iya baro garin su yazo guna ya kama hotel don ya kula dani a gidan mu muke wuni
Gani yake yi kamar za a sace ni ko wani ya kwace mishi ni shekarun mu uku da shi an yi mana baiko kenan komai na akwati tare muka siya ina makaranta zaije department ɗin mu ya jirani na samu gata sosai, ban taɓa jin wani abu zai raba mu ba, ashe muna namu ne Allah na nashi wannan rana ta zame min wani ɓangare na jiki na da duk lokacin da na tuna sai na zubar da hawaye .


Kuka ne ya kuɓuce min sosai nai ta kuka na gagara daina kukan har yakai ga JB ya tambaye ni ki dai na kuka


me ya samu Muhammed?


tuna min da ya yi shine ji nake kamar zuciya ta zata fashe don fargaba da ruɗani .


"JB Muhammad ya rasu ciwon ciki ne sanadi ciwon zuciya bata zama ajalin sa ba duk da ita ce jinyar sa sanadin rabuwar mu ,ta har abadan don ranar Laraba shine ranar da Muhammad ya amsa kiran mahaliccin sa ,wajen misalin ƙarfe takwas ya kira ni mun sha hira sosai da shi wani kalmar da ta tasar min hankali da ya gayamun "yau ba kya son mu yi hira ki kasan ko mutuwa zan yi?




"ya Muhammad to sai me Allah ya jiƙan ka" ya dame ni da surutu gashi bacci nake ji yana yi min magana kamar wasiyya wajen ƙarfe tara yace min cikin shi na ciwo nace yasha magani yace babu nace ya kira maman shi yace ba kati a wayarsa dole na kira ta nace babanta cikin shi ciwo yake yi mishi a aika mishi magani zai sha ta bayar a ka kai mishi bayan wasu lokutan na kira shi don tabbatar da ya sha maganin, a daren mun yi hira sosai sai cewa ya yi "muddin nabar duniya ban yarda a ɗauki kayana a bawa Kowa ba don kayan auren mu da sunan ki na siya bada wata ba sannan ban san wa zai riƙemin ke amana ba ,ba lalle bane wanda zai soki ya kulamun da ke yadda ya kamata ke macece mai sauƙin kai naso mu rayu tare mu gina rayuwa kash zanyi tafiya gari mai nisa wanda ba lalle ne ki zoba ko da kinzo .a matar wani zaki zo in sha Allahu in dai baki cenza hali ba zaki samu mai irin halina ."kai dai Allah ya baka lafiya "Amin ya rabbi".


Har sha ɗaya kafin nayi bacci na barshi jin waya ta na ƙara neman agaji shine ya farkar da ni"ya Muhammad ka kwanta kayi bacci mana kaji "shikenan zan kwanta amma muddin kika ga ban tashi da wuri ba ki tasar dani kinji da to na bishi saboda bacci da nakeji sosai .


Washe gari


Shine ke zuwa ya tasar da iyayen shi sallah amma sunji shiru har kusan goma na safe aka aiki yaro yaje ya dubo shi yace yana bacci, "bacci kuma kodai bai samu yayi bacci da dare ba in ji mahaifiyar shi kabar shi zuwa anjima sai ka tasar da shi, yayan shi ne ya shigo don tambayar shi a na neman shi a office a kwai signature (saka hannu) ɗin da zai yi " ba shida lafiya kaje zan gaya mishi' in ji mahaifiyar shi da sauri ta wuce ɓangaren shi ta dinga kira babana ka tashi mana ayya kayi sallah kuwa jin shiru bai motsa ba ashe rai yayi halin shi ɗaga hannun shi ta yi ta duba saitin zuciyarshi ashe zuciyar ba lalle ne tayi aiki ba, ba a son yaushe ya rasu ba, addu'a ta yi mishi tare da hawayen da suka biyo kuncinta masu zafi yana ta zuba, ta gagara fitowa daga ɗakin ana cikin haka ne ya yi daidai da lokacin dana ke kiran wayar .


Mum ce ta ɗaga a take zuciyata ta tsinke jin kalmar haƙuri da take bani da kuma yi min nasiha, sunana ta kira Nusaiba nasihar da tayi min shine ya tabbatar min akwai babban matsala sosai .
Sai da taga na samu nutsuwa kafin ta gaya min rasuwar Muhammad na shiga fargaba tare da ruɗani, a lokacin muka haɗa kayan mu sai Bauchi mutane da ke zuwa yawanci a ni ake yiwa ta'aziyya, na rame sosai, so bala'i ne! akwai wata kalma da mom ta gaya min , akan in yi haƙuri Allah zai bani wani a madadin shi kwanan mu shida kafin muka dawo nasha wahala muna dawowa na kwanta jinya kamar ba zan yi rai ba don har aman jini nake yi sai da nayi wata biyu a asibiti kafin na dawo dai dai na sha fama da addu'a na fara mantawa .




"Ka ji waye mahaƙurci wanda yayi so tsakani da Allah babu algus a cikin ta ko".




jikin shi yayi sanyi sosai haka ya daure
ban taɓa jin labarin da ya tarwatsa tunani na ba, hakika na tausaya miki, Allah ya mishi rahama kin bani tausayi labarin akwai tausayi a cikin ta Allah ya bamu ikon yin gyara kuskuren mu


Amin ya rabbi




"Nusaiba zan riƙe ki tamkar jinina zan nuna miki gata sosai in sha Allahu zan kwatanta irin abun da Muhammad yake miki koda bai kai nashi ba kisa a ranki kin samu miji shekara huɗu da kika yi ba tare da soyayyar wani a ranki ba rabona ne ya tsaida ke daga kula kowa 'ki bani zuciyar ki zan mallaka miki ruhina da tawa zuciyar ".


Godiya nayi mi shi na kamu da son JB a kwanaki kaɗan a raina saboda kulawa da yake nuna min har jina nake na tafi wata duniyar sauran rayuwa ko, in ce na buɗe wata rayuwa mai tare da jindadi, JB ya So ni ya ƙauna ce ni sannan yana kulawa da ni amma ba zan taɓa haɗa soyayyar Muhammad da ta JB ba don shi Muhammad so mai tsafta yake min don ko ya tsana bai taɓa riƙewa ba. JB kuwa sai yasa in tura mishi suran jiki na in naƙi turawa ya yi fushi sosai ya daina kula ni duk da yawan shekaru na soyayyar JB ta yi min kamu amma abun da na lura da shi shine.


Suran jiki na yake so amma son bata da yawa gare shi son da nake mishi yafi nashi yawa nayi tafiya ya ce dole sai na tura mishi hoton ƙirjina naƙi kasancewar ina gidan biki shine yayi min fushi ya daina kula ni, duk hankalina ya tashi ba na kaɗan ba gashi na kamu da son shi wanda, raba mu zai yi mun illa tabbas .
Wajen sati ɗaya bai kula ni ba can dai na shiga fargaba sai da natura mishi' kafin yayi murmushi muka shirya...




Takun farko
[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR




MARUBUTAN JAHAR YOBE




Story and writings by Amina ma'aji
Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam 📚✍🏽




Paid book 400 zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068758984


LAMBA NA BIYU


*Masu karatu ku shirya wajen yin comments da sharhi marubuta guda uku zamani uku tunani uku karku sake ayi babu ku ,zaku sha karatu cikin aminci fatan alkairi gareku*.


Yanzu kenan na fuskanci bana ranshi wata ɗaya muka yi da shi wanda bai nemi komai daga gare ni ba yawan tura mishi hotuna na da nake yi cikin kaya masu daraja wanda kaman doka ne ya bani zan tura mishi guda uku a kowace rana da farko ya nuna min shi na Allah ne don baya son yawan sa gyalen da nake yi ko fita zan yi tabbas kamar mijina sai na tambaye shi .


a bu ɗaya na ɓoye mishi aiki da nakeyi amma shi kanshi ganin walwalan da nakeyi sannan ban taɓa roƙon shi ko mai ba ,bashida arzikin da zan roƙeshi ko mai wannan, ya samo a saline da irin kulawa dana ke samu daga iyaye na.yace kar in jima nace to, in kuwa ya kai awa ɗaya zai ta kira na ya dame ni in koma gida ya zo mun a kan shi na Allah ne tunda nake ban taɓa soyayya marar tsafta da kishin kaina kamar na JB ba, samarin da nayi duk sun girme Ni daga wanda ya bani shekara biyar sai shida Muhammad shekara biyar ya bani.a haka ban taɓa kallon shi a zahiri ba har muka yi kusan wata biyu.


Kamar wani ubana, ni nake fara kiran shi in ce mishi ina kwana mu gaisa baya aiki shago ne da shi na siyar da kayan ɗinki, ƙarfe tara yake fita na safe ni kuma muddin na tashi to tabbas zan tashe shi wajen kiran number shi dole ya tashi har zai ce min .


"wato ke in kin tashi sai kin tashe ni ko me zan yi miki ne kike yawan tashi na? "In kuwa baka son in tashe ka to ya zama dole ka rufe wayarka amma yau ina son muyi magana ".


A kan me kenan!


A haka ya yarda muka yi ta charting ina tambayar shi "don Allah ka gaya min baka taɓa soyayya bane sai a kaina naga kana yawan zumuɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login