Showing 1 words to 3000 words out of 64149 words

Chapter 1 - Sartse Part 1 Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

143



*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001



FUTURE WRITERS ASSOCITION (FUWA)



Sadaukarwa.



RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu)



Gaisuwar SARTSE zuwa gareku Iyalan Fam.

Alherin Allah Ya kai muku a duk inda kuke.



Shafi na Waya

(01)





Labarin Sartse irirarren Labari ne, ban a rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan akwai wanda ya yi shige sa yanayin labarinsa muna neman yafiyarsa akan hakan. Hain Mallaka nawane ni kaWai.



Kamar ko yaushe Book one zai kasance Free, Two da Three kuma zasu a paid, akan aramin farashi.



ShimfiWa



*Jihar Jigawa , Nageriya.*

Jihar Jigawa tana daya daga cikin jihohin da aka kirkira a karkashin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 27 ga watan Agusta, 1991. An ciro jihar ne daga tsohuwar Jihar Kano, inda aka ba ta sunan "Jigawa" wanda ke nufin kasa mai tudu ko yashi, yanayin kasar da ya shahara a yankin.

Jihar ta kunshi hadakar manyan masarautu guda biyar (5) masu tsohon tarihi, wadanda suka hada da: Hadejia, Kazaure, Gumel, Ringim, da kuma Dutse. Wannan ya sa jihar ta zama matattarar al'adu daban-daban na Hausawa da Fulani da kuma Mangawa. Ana yi wa jihar lakabi da Sabuwar Duniya saboda burin da aka sa a gaba na gina ta a matsayin jiha mai dogaro da kanta ta fuskar noma da kasuwanci.

*aramar Hukumar Dutse*

Dutse birni ne mai dadadden tarihi a kasar Hausa. Asalin sunan garin ya fito ne daga manyan duwatsu da suka mamaye yankin. Kafin kafuwar jihar Jigawa a shekarar 1991, Dutse tana karkashin jihar Kano ne kuma tana daya daga cikin tsofaffin gundumomi masu daraja.

Birnin na da sarauta mai karfi wato Masarautar Dutse, inda sarkin garin ake kiransa da "Sarkin Dutse." Tarihi ya nuna cewa mutanen farko sun zauna ne a kusa da wadannan duwatsun domin samun kariya daga makiya a lokacin yake-yake.



Yanayin Girman Garin a Taswirar Nigeria Dutse tana nan a Arewa maso Gabashin Najeriya. Haka A taswirar jihar Jigawa, Dutse tana tsakiya zuwa kudancin jihar. Ba birni ne mai matukar fadi kamar Kano ko Kaduna ba, amma yana bunkasa cikin sauri sakamakon zama babban birnin jiha.

Yanayin garin akwai zafi sosai a lokacin rani, sannan akwai hunturu mai ratsa jiki saboda duwatsu da kuma kusa da hamada.

Haka a bangaren Sana'ar Mutanen Garin

Mutanen Dutse galibi Hausawa ne da Fulani, don haka sana'o'insu sun hada da

" Noma: Shi ne babban jigo, musamman noman gero, dawa, wake, da kuma shinkafa a wuraren da akwai ruwa.

" Kiwon Dabbobi: Ganin cewa akwai Fulani sosai a yankin, kiwon shanu da awaki sana'a ce mai matukar muhimmanci.

" Kasuwanci: Akwai manyan kasuwanni inda ake hada-hadar amfanin gona.

" Aikin Gwamnati: Kasancewar sa babban birnin jiha, akwai ma'aikata da dalibai da dama (musamman saboda Jami'ar Tarayya ta Dutse - FUD).



Takur Site unguwa ce da ke zaman kanta a cikin birnin Dutse, wacce ta yi fice wajen tsari da kyawun gine-gine. Unguwar tana cike da manyan gidaje na zamani wadanda aka gina su da faffadan fili. Galibi gidajen suna dauke da fulawa da korayen bishiyoyi da ke kara wa unguwar kyan gani. Sannan Mafiya yawan mutanen da ke zaune a nan ma'aikata ne, manyan jami'an gwamnati, da kuma malaman jami'a. Wannan ya sa za ka iske mutanen cikinta masu ilimi ne da sanin ya kamata.

Babban abin da ya bambanta Takur da sauran anguwanni shi ne shiru. Babu hayaniyar yara a titi, babu kade-kade, kuma babu cinkoson mashina. Daga karar fankar sai kukan tsuntsaye; hakan ya sa ta zama gurin da mutum zai iya hutuwa cikin natsuwa. Sannan Tana da tituna masu kyau da hasken wutar lantarki wanda ya fi na sauran sassan garin tabbas saboda kasancewarta unguwar manya.





Da misalin karfe 05:40 na yamma.



Wani irin azababben zafi nake ji yana shiga jikina, kamar ana tafasa ni a cikin tandar gurasa. Kicin Win gaba Waya ya Wumame yana fitar da wani irin wuci, sakamakon girkin da nake a kurfoti guda biyu.



"Wayyo Allah!."



Na faWa a fili bayan na juya ga miyar da take tafasa akan Wayan kurfotin, tsumma na Wauka na sauke ta asa na fara juyata.



"Maggi bai ji ba! A'a ya ji Sardauna baya son maggi ya yi yawa."



Na faWa a dabarbarce, ina mai sa hannu na taSa wayata, allon wayar ya kawo haske na yi tozali da kyakyawan hotona ni da mijina a ranar Waurin aurenmu, a fili na furta.



"Ina sonka mijina, ina aunarka, Allah Ya kula mini da kai."



Ina faWin haka na maida kallona ga agogon, shida da rabi daidai. Nasan kowanne lokaci zai iya shigowa, aurin gurasar da nake gasawa ne ya daki hancina, ba shiri na mie tsaye na sa hannu a kan kaskon da nake gasawa da niyar juyawa, sai dai cikin rashin sa'a na kama dandarrayar kasakon maimakon gusar, wani irin zafi ya ratsani har tsakar kaina, na yi baya da sauri ina faWin.



"Wayyo Allahna."



walla ta cika min ido sakamakon raWaWin zafin da nake ji a 'yan yatsuna, ga kuma zafi da turirin da yake tashi daga cikin kicin Win.



Sake komawa na yi na kama gurasar a hankali na juya. Bayan na juya na ara Waukan wani curi Waya na Worashin akan abinda nake murzawa da shi na fara murzawa ina faWaWashi, har sai da ya yi falai falai, sannan na cire takan kaskon na Wora wannan, daga nan na koma kan miyar na Wauko plast mai kyau na juye ta a ciki gaba Waya, da niyar idan ya ci ya rage ni sai na ci. Domin azababben amshinta da ya cika mini hanci ya cire mini sha'awarta na lokacin, bayan na juye na Wauki plast Win na fito daga kicin Win zuwa makaken falona na alfarma da ya awato da kayan ado masu kyau da tsari.



angaren dinning na nufa, shi kansa abin tsayawa ka kalla ne, domin ni kaina lokaci zuwa lokaci na kan tsaya na kalli gidana da irin oarin da iyayena suka yi wajen cika shi da kayan alfarma, bayan oarin da Mijina Sardauna ya yi na gina makeken gida a anguwar Takur. Ina ajiyewa na koma kicin Win na juya gurasar dake kan wuta, sannan na fara oarin juye wutar dake cikin kurfotin da na sauke miya a cikin wani bukitin arfe, sabida bana son kashe wutar a cikin kicin Win toka ta Sata minin aikin da na yi, bayan na juye na Wauki Bukitin na fita bayan gidan ta aramar ofar kicin, aramin famfon na nufa na tara bokitin da wutar garwashin a ciki, bayan ruwan ya taru na zubar da iya ruwan da ya yi sanyi a bakin rariya, da sauri na koma kicin na sauke gurasar da ke kai na Wauki ta arshen na fara murzawa, bayan ta yi faWi na Wora ta akan kaskon, daga nan na koma na shanya gawayen da na kashe Wazu a asa, sannan na dawo kicin Win.



Daidai lokacin da motarsa ta fara horn, da sauri na dawo falo na buWe taga na fara kallonsa, tun daga parking Win har fitowarsa, yanayin yadda yake tafiya ma kaWai abin a tsaya a kallani.





"Wayyo Mijina, Allah Ya ara maka arzii, lafiya da nisan kwana."



Na faWa a raina, ina ja da baya.

amshin turarensa ne ya fara dukkan hancina kafin sassanyar muryarsa ta daki dodon kunne na.



"Sannu da zuwa."



Na faWa kamar zan durusa ma sa, tsabagen biyayya da auna.



"Yawwa! Sannu da gida."



Ya faWa yana mio mini jakar hannunsa, na russuna na amsa, ya ara ciro hulal kansa ya mia mini kana ya sami kujera ya zauna, Wakinsa na nufa zan ajiye cikin kakausar muryarsa ya ce.



"Ranki ya daWe takalmin fa."



Murmushi na saki sannan na ce.



"Ina shirin fara shiga da waWannan ne."



"Ko dai kin barni na cire?."



Na dawo kusa dashi, na tsugunna na cire masa takalmin, bayan na cire na kwaSe mai safar sannan na Wauka na shiga dasu cikin Wakinsa, komai a mazauninsa na ajiye su na ara gyara inda na ga kamar bai gyaru ba a Wakin sannan na shiga toilet na haWa masa ruwan zafi daidai yadda nasan yana so.



A inda na barshi na sameshi yana danna wayarsa. Sai da na gyara muryata yadda zata fito da zai sannan na ce.



"Ruwan wanka ya zama ready."



Ajiye wayar ya yi ya mii zuwa Wakin.



"Ki jera mini abinci kafin na fito."



Ya faWa cikin kakkausar muryarsa sannan ya shige ciki. Ina nan tsaye sai da naga ya yi kusan minti biyar a ciki sannan na sauke wata Soyayyiyar ajiyar zuciya, jin shi shiru ya bani ya bani tabbacin ruwan ya yi masa daidai.



Kitchen na koma na shiga haWo kayan abinci, a hankali a hankali na jera komai akan dinning Win bayan na gama na shiga nawa toilet Win nima na watsa ruwa a gaggauce na fito daga bayin na hau shiryawa.



"Nana! Nana! Nana!!."



Na ji muryarshi, ba shiri na zura Hijabi na fito.



"Na'am! Gani."



"Kina jina ina ta faman kiranki."



Ya faWa yana zama akan dinning.



"Yanzu na fito daga wanka ne."



Na bashi amsa.



"Okay i see, zuba mini."



Ya faWa hankalinsa yana kan wayarsa. Plate na Wauko na saka masa Gurasar guda uku, sannan na Wauki bowl na zuba masa miyar, sannan na ara Waukan wani bowl Win na saka masa farfesun tsokar rago, sai kuma kofi na zuba masa lemon citta da ya sa na yi masa. Sai da nagama gaba Waya sannan na ce.



"Gashinnan."



Wayarsa ya ajiye ya fara cin abinci, ganin ya fara cin abincin yasa na koma Waki na ci gaba da shiri na, sai da na taje dogon gashina sannan na fara shiri, sauaiyar kwalliya na yi, sannan na Wauko doguwar rigar abaya na saka, bayan na feshi jikina da haWin turarruka.



Ko da na fito falon ban ganshi akan dinning Win ba, sai da na arasa shigowa falon na hango sa acan kan kujera yana yana faman danna waya, kan dinning Win na nufa na zauna, buWe plast na yi zansa gurasar sai sai guda Waya na gani, murmushi na yi a raina na ce.



"Yau yallaSai anji daWin girkin kenan."



Na Wauki Wayar nasa a plate Win da ya gama ci, na buWe plast Win miyar zan zuba sai dai fa sam babu miyar a ciki ya shanye, karo na farko cikin abubuwan da Sardauna yake yi mini na ji babu daWi, buWe plast Win da farfesun naman ragon yake ciki na yi shima dai babu.



"Me ya faru haka?."



Na tambayi kaina, dan nasan dai Sardauna bazai taSa cinye duka wa'yannan ba, dole wani wajen ya kai ko ya kai kitchen.



"Ka kai ragowar kicin ne?."



Na tambaye shi, muryata na rawa kamar wacca ta yi tsaren gudu, ko dayake ba shakka tsare na yi, domin na yi tsere da zuciyata kafin bakina ya iya fito da wanann tambayar.



"Ban Wauke komai ba, ai aikin ne ko?."



Zama na yi akan dinning Win, gaba Waya raina babu daWi na rasa abinda ke mini daWi. Muryar shi na juyo ya na cewa.



"Me kike yi anan ne?."



Na goge wallar da ta fito daga ido na ce.



"Babu komai?."



"To tawo nan mana."



"Abincin zan ci."



Na faWa ba tare da na taso Win ba.



"Tom."



Kawai ya faWa ya ci gaba da abinda yake, na tashi na shiga cikin kicin Win, ban masan me zan iya dafawa ba wanda zansa a cikina, ga yatsu na sai wani irin zugi suke yi mini kamar wacca na taSa attaruhu.



Haka nagama zagaye na a cikin kicin Win na fito zuwa falo, na bude firij na Wakko biredi na dawo kan dining na haWa da ragowar romon farfesun naman na ci.



Bayan na kammala na Wauke komai na kai kicin, na gyara wajen tsaf sannan na nufo shi zan zauna na huce gajiyar da take cin jikina. Sai dai ban kai ga arasowa ba idanuna suka sauka kan abinda yake yi, ya zuge zif Win Waya daga cikin fulallukan kujera yana fito da katifar ciki yana gutsirawa a hankali, kamar aramin yaro yana wasa, sai da na haWiye wani abu a raina sannan na ce.



"Sardauna! Kujerar kake yagawa fa?"



Na fada ina kallon katifar da yake gutsirawa, gabana yana faWuwa ganin yadda yake Sarnatar da kayan gidan namu.



Kallona ya yi sannan ya kalli abinda ya watsar.



"To kin barni nan ni kaWai, ba dole na yi duk abinda zanyi ba dan ma banyi miki kuka ba."



Murmushi na yi sannan na zauna kusa dashi da faWin.



"Abinci fa na ci."



Cuno baki ya yi kamar aramin yaro zaiyi kuka sannan ya ce.



"To kuma sai ki bar mijin ki da yake sonki fiye da komai shi ka Wai, babu abokin ta ya shi zama."



"To ai gani nan nazo."



Na faWa ina shafa masa kai, ai kuwa ya kwanto akan cinyata.



"Daman kaina aiayi yake, ki gyara mini."



Ya faWa bayan ya kwanto, tare da janyo wayarsa ya fara dannawa, wani irin nauyi na ji kamar an Woramin dutse, kamar da gangan ya sakar mini nauyinsa, na fara shafa masa kansa, ina jin dumin gashinsa a tafukan hannuna.



"'Nana."



Ya kira sunana a hankali, idonsa har yanzu yana kan wayarsa.



"'Na ga yadda kika yi shiru Wazu da kika ga na cinye Gurasa, Ko dai kin fara gajiya ne da yi mini girki ne, ko gajiya da zama dani a cikin gidan? Rayuwar aure fa bauta da soyayya ne! Na Wauka kin fi kowa sanin cewa duk abin da yake nawa, naki ne... har da yunwar ki.'"



Na haWiye miyau me Waci da ya tsaya mini a mawogaro, na yi oarin yin murmushi duk da raWaWin da yatsuna suke mini na unar da na yi Wazu na ce.



"'Haba Sardauna! Kai fa mijina ne, ni kuma matarka ce mai aunarka, ai na ji daWi ma da ka cinye abincin, hakan na nufin girkin ya yi daWi kuma hakane burina."



Ya Waga idonsa ya kalle ni, wani kallo mai wuyar fassara sannan ya ce.



"Yauwa. Domin idan kika fara orafi a kan abinci, zan fara tunanin ko ni Win ne ba kya so... ko kuwa kin fara manta yadda iyayenki su ka gaya miki yadda mace ta gari take zama da mijinta?"



arar wayata ne ya katse mini maganar da na yi niyar yi, na kai hannu zan Wauka amma Sardauna ya riga ni.



"Wake kiranki a daren nan?"



Murmushi na yi sannan na ce.



"Bansaniba wallahi, amma bani na Waga."



Sardauna bai ba ni wayar ba, sai ma juyawa da ya yi ya fuskanci allon wayar, hasken ya haska kwayar idonsa da ta canza launi lokaci guda. Ya dade yana kallon sunan dake kan allon wayar kafin ya dago ya kalle ni, wani irin kallo nasa da yake mini wanda ni kaina bana gane me yake nufi dashi, sai kuma ya saki wani irin murmushi kana ya ce.



"Daga gida ne..."



Ya fada muryarsa na rawa kaWan.



"Radiya ce."



Ya kama sunan babbar Yayarmu kai tsaye, sannan ya ce.



"Me take nema gunki a wannan lokacin?"



Ban kai ga ba shi amsa ba, ya danna maSallin kin amsa kiran (Reject). Ya ajiye wayar a kan kirjinsa, ya kara gyara kwanciyarsa a cinyata yana kallon silin din dakin.



"Ita tai zaman aure, tana so ta hanaki kula da miji ko bawa mijinki lokacinki. Nana, kin san ina son ki ko? Kuma kin san ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Wannan gidan namu ne mu biyu, duk wanda zai kawo mana rarrabuwa, ko da kuwa danginki ne, to ba ya son mu."



Wani irin nauyi na ji ya ara danne ni, ba nauyin Sardauna ba, nauyin kalaman da ya jefo mini ne. Ya kama hannuna da ya kone dazu, ya matse shi a hankali sannan ya ce.



"Gobe me zamu karya dashi? Ni bana son cin biredi abinci nake son ci very special, ba irin wanda muka saba ci ba."



Na yi murmushi muryata na rawa sannan na ce.



"Tom Mijina na me kake so?."



"ZaSi yana wajenki, amma dai abu na daban, ko zan sami Vento cake wanda zan fita dashi ofis?."

Na gyaWa kai sannan na ce.



"Zaka samu mana."



Bansan ashe walla ta fito daga idona ba, sai ji na yi ya kai hannu gefen idona ya goge hawayen da yatsansa, sannan ya kai yatsan bakinsa ya WanWana.



"Hawayenki suna da WanWanon gishiri, Nana. Kada ki sake kuka... domin kukan mace a gidan miji, alama ce ta rashin godiya ga Allah ko kuma raina kulawar da miji yake ba ta."



Washe gari.



Gaba Waya jikina babu daWi haka na tashi, bayan na yi sallar asuba na shiga kicin, ba tare da sanin ainahin abu na daban da Sardauna yake maganarsa ba. Sai da na arewa kicin Win kallon sannan basira ta faWo mini, na tsugunna gaban kurfoti bayan na zuba gawaye na fara oarin kunna wuta, sai dai da na kunna hutar iska take kaWe ta, abu kamar wasa na kusa minti sha biyar a gaban huta amma tai kunnuwa.



Miewa na yi na nufi kan gas Wina yau kawai zanyi girki akansa, ina kunnawa na Wora tea kafin na Wakko fulawa na shiga kwaSa Fanke, amma wannan mai attaruhu da albasa da maggi ne a ciki, banda tabbaci amma nasan Sardauna bai taSa cin wannan ba, nima na ko yi sarrafa fulawane a wajen Anty Hadiza matar Isah Nadabo dake ita 'yar kano ce kuma a kanon ma wararriya ce a harkar sarrafa fulawa. Bayan kwaSa na rufe shi na shiga juye tea din a flask sannan na Wakko kasko na Wora akan gas Win na zuba mai.



Ina oarin fara saka fanke a cikin mai ya shigo kicin Win, har asa na tsugunna ina gaida shi kamar zan yi masa sujjada.



"Ina kwana, an tashi lafiya?."



Kallona ya yi sai kawai na ji ya ce.



"Me yasa baki da tausayi ne Nana, me yasa imaninki yake raguwa a ko da yaushe?."



Gabana yashiga faWuwa, irjina ya fara dukan uku uku, bansan tausayin da ya kaini kunna gas ba, duk da ba wani amfani nake dashi ba, sai na yi sati biyu banyi girki akai ba, hasali ma shi ke amfanin da shi wajen dafa ruwan wanka, ko tea idan yana sauri.



"Ka yi hakuri dan Allah, gawayin ne yai kamawa gaba Waya, na kusa minti goma ina kunnawa amma yai kamawa."



"Mitchewww."



Ya ja wani uban tsaki, sannam ya ce.



"Minti goma kacal? Ba zaki iya minti goma wajen kunnawa hutar da zaki yi wa mijinki girki ba? Nana bansan yaushe rashin imaninki ya kai haka ba, tabbas 'yan uwnaki zawara suna fara Woraki a turbar da suka bi suka kashe aurensu."



Hawaye na ji ya fara gangaro mini daga ido, cikin sanyi murya na ce.



"Ka yi hakuri dan Allah, nasan kana son fita da wuri kar na Sata maka lokaci, amma in sha Allahu bazan sake amfani dashi ba har Abada."



Na faWa muryata na rawa, alamun kuka ya fara cin arfi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login