Showing 21001 words to 24000 words out of 64149 words

Chapter 8 - Sartse Part 1 Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

148

jawo ni, ya rugume ni jikinsa a hankali bacci mai daWi ya Wauke mu. A raina ina faWin haka ake aure? Haka rayuwar take da daWi? 



Kiran sallar asuba ne ya tashe ni na buWe idona, idan da sabo na saba dan dama shine daidai lokacin tashinmu. Ina matsawa daga jikinsa ya buWe ido.



 Come on Nana.  



Ya faWa cikin magagin bacci. 



 Kiran sallah ake.  



Na faWa a hankali. 



 I know, matso!  



Ya faWa yana kamo ni, ba shiri na koma na kwanta ya sake rungume ni bacci ya sake Wibansa, ni kam idona biyu ina ta faman sa™e sa™e. Ba shi ya farka ba sai 6:30. 



 Honey! Baki san irin gajiyar dake jikina ba.  



Ya faWa yana kamo hannuna, na yi murmushi sannan na ce. 



 Ina kwana.  



 Mu fara sallah mana.  



Toilet na shiga, sai kawai na ga shima ya biyo ni. 



 Mu fara yin wanka, sai mu yi sallah.  



Abu kamar wasa  Sardauna ya ce tare zamuyi wanka, haka kuwa akayin, daga nan mu ka yi alwala mu ka gabatar da sallah. 



Bayan mun gaisa ne ya ce. 



 Ya kwanan sabon gida?  



Na yi murmushi sannan na ce.



 Da godiya.  



 Nana i really love you, i love you smile please keep it.  



Muna zaune muna hira ya hanani tashi naga shiga kicin,  sai da aka yi masa waya sannan ya tashi, can ya shigo yana cewa.



 Je ki haWa mana breakfast.  



Na tashi na fita, wani babban kwando nagani ya ajiye akan centre table na Wauka na kai kan dinning sannam na shiga kicin. Ba ™aramin mamakin irin girman kicin Win na yi ba, dan zai iya fin girman wani Wakin a gidanmu, amma duk da haka an zuba kaya masu yawa a ciki. 



Da kansa ya zagaya dani ko ina na gidan, ya nuna ko ina har da Wayan part Win, da kuma Wakinsa na nan. 



Sai can yamma sannan  yan uwana suka yi min zuwan nan da suke yi, da daddare ma cikin irin yanayin jiya muka sake kwana da Sardauna. 



Har tsawon kwana goma da aurenmu muna zaman jin daWi da soyayya da Sardauna ina samun soyayya da kulawa a wajen Sardauna, yana riritani kamar jaririya, ko ™wai da ake tsoron fashewarsa. 



Ranar juma a su Malaika, Amina da Fauziyya suka shirya zuwa, tun safe nake rawar jiki da zuwansu, na faWawa Sardauna ya kai sau goma, tun yana kulani har yafara min banza, haka har ya tafi ofis, girki wajen kala uku na yi musu sabida murnar zuwansu. 



Wajen ™arfe Waya suka zo, har wani tsalle na yi da na gansu, suma cike da farin ciki suka tarbeni suna murnar ganina cikin farin ciki, bayan sun zauna na shiga yi musu safarar abun sha, lemo kala kala na gora da na kwalli, sannan kuma wa yanda na yi da kaina. 



 Oh my, Nana kinga yanda kike glowing.



Malaika ta faWa tana kashen ido. 



 Nana duk waWannan abun shan namu ne mu kaWai, duniya sabuwa.  



Amina aminu ta faWa, na yi dariya sannan na ce. 



 Ku yara ashe haka aure yake da daWi? Haka ake rayuwar auren, ai wallahi aure yafi komai daWi idan kuka sami irin mijina. A shawarce karku ce zaku zauna, wallahi kuna komawa gida ku ce sai anyi muku aure.  



Legendspen

08129553961

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001



Sadaukarwa.



RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 



Shafi na goma

    (10)



Dariya suka kece da ita sannan Malaika ta ce. 



"Yarinya ta ji daWin aure." 



Ni kuwa na ce. 



"Ba dole ba? Mene wanda nake so mijina ba ya yi min, a zaman nan namu sau uku yana fita dane manyan wajen cin abinci, gaskiyya  duk wacca ta yi dacen miji ta yi riba." 



Haka muka yi ta shan hirar mu muna dariya, wajen ™arfe biyar Sardauna ya kirani a waya, a gabansu na Wauka ya ce dani yana son na yi masa cous-cous da miyar kaza. Ina gama wayar na kallesu sannan na ce. 



"Bara na shiga kicin." 



"Kaga matar aure." Suka faWa suna dariya, suna nan zaune na shiga kicin na fara haWa masa girki, sai dai sanda na duba friza Waukar kaza babu kaza, sai a lokacin na tuna gaba Waya na yi amfani da ita, waya na Wauka na kirashi sai dai bai Wauka ba. Sai kawai na Wora cous-cous Win. Ina cikin Kicin Win Fauziya ta sanar da ni cewar zasu tafi, haka na fito falon mu ka sake taSa hira kafin su ka tafi, Naira dubu biyar na basu na ce su hau mota, ni kuma na dawo kan girki na.  Ashe Sardauna ya kira ni ban kula ba ina kicin wayar na falo, ganin lokaci zai ™ure sai kawai na Wora miyar na yi masa ta nama, amadadin kaza tun da duk nama sunansa nama. 



BandaWe da gama abincin ba ya shigo, da murna ta kamar ko yaushe na je na tare shi, na yi tsalle na faWa jikinsa ya rungumoni yana faWin. 



"Hon yau bana jindaWi." 



"Meke damunka?"



Na tambaya ina amsar jakarsa hannunsa, zama ya yi kan kujera tare da mi™amin ™afarsa na fara cire masa takalmi. 



"Wane mistiyacin yaro ne a family, ya dawo ™asar shine yake neman yi min rashin kunya." 



Ya faWa yana taSe baki, sai duk na ji ba daWi.



"Ka yi ha™uri ka ™yaleshi kawai." 



"No! Turaki bai isa na ™yaleshi ba, dole na Wau mataki zan nuna masa ni ba sa'ansa ba ne." 



"Kai Sardauna shi Turaki?" 



Tambayar da na fara yi kenan, kallona ya yi sannan ya ce. 



"Granny ce ta sama na sunan dukkanmu, sa'a na ne, kusan lokaci Waya aka haife mu da shi, amma na girmeshi. But seriously Nana tun ina ™arami bana son yaron nan, abokin dabi na ne, komai na yi sai ya ce zaiyi, natsani na ganshi da abuna ma gaba Waya." 



"Ka daina faWin haka Hon, ba a cewa antsani musulmi, mussaman shi da yake Wan uwanka." 



"˜yale wannan maganar Hon! Yunwa nake ji."



Ya faWa yana tashi zuwa wajen dinning, nima na ta shi na shiga da takalmi da jakarsa Waki. 



"Me ya sa ma bazan yi biyyar aure ba, bayan Yaya Rumaisa da kanta ta ce Biyayya na ™ara soyayya kuma gashi ina gani, ni ina mamakin matan da basa yi wa mazajensu biyayya. Me suke nema a duniyar?." 



Na faWa bayan na ajiye kayan, sannan na fito falon yana zaune kan kujerar dinning yana jirana. Plate na fara ajiye mai sannan na buWe cous-cous Win na fara zuba mai, sai bayan na gama na buWe miyar na fara zubawa. 



"What is this?" 



Ya katseni. 



"Abincin." 



Na faWa muryata na rawa, le™a miyar ya yi sannan ya kalleni. 



"Bance miki chicken nake so ba, me ya sa naga beef?" 



"Ahm. Daman kazan ne babu, da na duba sai naga saura nama shi ya sa na yi na nama" 



"Me ya sa baki sanar dani ba?" 



"Na kiraka baka Wauki wayar ba." 



"Ban kiraki ba bayan nan? Me ya sa baki Wauka ba, sabida kina can ™awayenki sun zo ko? Ni ban isa na sa ki abu ba? Ban isa na ce ga abinda nake so ba ni da gidana?" 



Ya yi maganar cike da tsawa kamar zai dake ni. 



"A'a ba haka ba ne, ka yi ha™uri wallai gobe zanyi." 



"Dalla malama rufemin baki, shashasha marar hankali, abinda zaki fara yi min kenan? To wallahi Nana baki isa ba." 



Yana gama faWin haka ya yi fatali da abincin ya yi waje, wani irin zafi na ji ya mamayeni, kamar ba wacca take cikin Ac ba, jikina gaba Waya ya fara rawa ba shiri na tsugguna ™asa na fara raira kuka, sai da na yi kusan minti talatin ina kuka na babu mai rarrashina sannan na tashi daga baya na shiga kwashe kayan, sannan na gyara wajen na koma kan kujera na zauna.



Ba Sardauna ya shigo ba sai wajen ™arfe tara, kallo Waya ya yi min ya Wauke kai, da sauri na tashi ina faWin. 



"Dan Allah ka yi ha™uri." 



Šauke kai ya yi ya shige Wakinsa, ya tura ™ofar ya murWa mukulli, haka na yi ta faman bugu amma bai buWe ba, sai wajen ™arfe 12:30 na je na kwanta ganin Sardauna bazai buWe ba. 



Wannam shine karo na farko da muka sami saSani da Sardauna tun zuwana, wannan ta kasance ba™ar Rana a wajena domin naga abubuwa kala kala, ko baccin kirki ban iya ba. 



Washe gari da safe tun da na yi sallar asuba ban koma ba, na shiga kicin haWa masa abincin kari mai kyau da lafiya, sabida ina son na burgesa kuma ya yafe ni. Gurasar da na koya wajen Anty  Adiza na yi masa da miyar farfesun naman rago, na juye a plast na kawo kan dinnig Win. Na shirya na dawo falon na zauna jiranshi, bai fito ba sai ™arfe tara kasancewar yau Asabar ne kuma babu aiki. 



"Ina kwana?" 



Kallona ya yi sannan ya kalli dinning Win, ya nufi wajen ba tare da ya ce da ni komai ba. Na bi bayanshi ina kuka ina faWin. 



"Dan Allah ka yi ha™uri, wallahi bazan sake ba dan Allah."



"Uhm." Ya faWa yana zama kan kujerar, ya fara zuba abincinsa, in tsaye akansa ina faman zubar hawaye amma ya yi banza dani kamar bai san ina wajen ba, har ya kammala sannan ya kalleni. 



"Ki biyo ni." 



Ba shiri na bi bayanshi zuwa falo, ya zauna akan kujera ni kuma na zauna a ™asa, sai da aka kusa minti biyar sannan ya ce. 



"Nana!" 



"Naam." 



Na amsa masa. "Nana wanene ni a wajenki?" 



"Mijina." 



Ya kalle ni sannan ya ce. 



"Shine matsayina a wajenki?" 



"Eyh." 



"Nana" 



Ya sake kiran sunana, na sake amsa masa. 



"Nana,  ina so ki canja min matsayi daga na mijin da kika ba ni. Ina so ki bani matsayin da yafi kowanne matsayi a wajenki, ki bani matsayin Uwa, Uba, dangi, Nana ina so ki Wauke hankalinki daga komai daga kowa ki mayar dashi kaina, Nana ni kaWai. Nana irin son da nake yi miki bana so naga kina mu'amala da kowa a duniya, Nana ina jin kishin akan kowa ciki har da 'yan uwanki, Nana ko da mace naga kina magana ina jin zafi a cikin raina, ina jin duniya ta yi min zafi. Nana zaki iya yi min wata alfarma?" 



"Eyh zan iya." 



"Nana ina so ki cire kowa a rayuwarki, ki cire komai sai ni Nana, ni kaWai zaki gani, ni ka Wai zaki ji." 



"Na yi maka al™warin." 



"Ta shi ki zauna anan." 



Ya faWa yana nuna min kusa da shi, na mi™i na zauna ya kama hannuna. 



"Nana ni mijinki ne, mai sonki! Da ya sadaukar da dubban farin ciki dan ya rayu dake, Nana ina son sakayya mai girma dan Allah." 



Da irin waWannan kalaman Sardauna, ya dinga dasa zazzafan tausayinsa a zuciyata, har na ji babu wani a rayuwata sai Sardauna. 



Daga nan komai ya dawo daidai tsakanina da  Sardauna, muka ci gaba da rayuwa cikin soyayya da farin ciki. Sardauna yana yawan magana akan ayyukan gida sun yi min yawa, hakan yasa ya kawo 'yar aiki me ta ya ni aiki, a farko mun fara zama tare da ita tana ta ya ni aiki, amma daga baya na fara fuskantar abubuwa sun fara yi wa Sardauna yawa, mussaman yadda wata rana ya fara magana akan yawan kuWin wuta da aka kawo masa bill. Hakan ya sa na sallami 'yar aikin, da ya yi magana na ce masa bana son yana yawan kashe kuWi, amma bayan kwanaki ya sake dawo da ita na sake sallamarta, a haka ya kawo har guda uku ina sallamarsu, daga baya ya daina kawo wa. 



Haka mu ka ci gaba da rayuwa cikin so da ™aunar juna, Sardauna yana riritani tamkar ™wai akan cokali wanda ake tsoron faWuwarsa. Ina rayuwa ta cikin farin ciki kowa yana ta ya ni murna, na je gida sau biyu sannan na je gidan yayuna sau Wai Wai, suma sun zo baki Waya har da Ra'is amma banda Yaya Ridwan.  



Ranar wata juma'a bayan ya dawo, yake sanar dani wai ™arshen wannan satin ranar Lahadi suna da baban family meeting, kuma ana bu™atar kowa yaje har da iyalansa. 



Tun da Sardauna ya faWan na fara tunani, danni ban taSa haWuwa da 'yan uwansa ba tun lokacin biki, sai dai 'yan gidansu da ya kaini sau Waya. Hajiyarsa mutuniyar arzi™i da ™annensa duk ba su da matsala, amma fa wannan ya ce wai babban famili meeting, duka 'yan uwansa zasu je. 



Washe gari na kira Yaya Rumaisa a waya na faWa mata bayan ya fita, nan ta bani shawarar irin yadda zan shirya, yadda zan kama kaina a cikinsu, da sauran abubuwa.



Ranar Sunday tun safe, na fara shirina amma ina yin komai cikin nutsuwa sabida kar ya ga rawar kaima, kamar yadda Yaya Rumaisa ta faWa. Bayan munyi breakfast ya ce dani. 



"Ki shirya muje da wuri, zan ajiye ki sai na fita zuwa 12:00 ake farawa, zan dawo kafin lokacin." 



Tashi na yi na shiga Waki, na ™arasa shirina daga nan na dawo falo lokacin shima ya gama shiryawa. 





FADA AREA

09:30am. 



Babban gidane na gaske da ya ji kayan more rayuwa, mutane ne tsilli tsilli cikin gidan sabida basu gama hallara ba, yana gaba ina binsa a baya ya yiwa wayanda ya ga dama magana, ya yi banza da wayanda ya ga dama, har ya kaini inda Hajiyarsu take tare da 'yan uwansu. Dukkansu na gaishesu kamar yadda na ga ya yi, suna ta samin albarka kowacce fuskarta washe da fara'a. 



Bayan mun gaisa ne na koma gefe na zauna a babban falon inda naga Lubna ™anwarsa ta zauna, shi kuma ya tashi ya fice. Kowa sabgar gabansa yake masu danna waya na dannawa masu hira na taSawa cikin harshen turanci, ba ruwan kowa da ni, hakan ya sa nima na ja waya ta na fara dannawa, nan ga message Win Amina Aminu cewar an fara cire WAEC, sun cire tasu a cafe kuma sun sami 8 credit, sannan an fara registration Win Jamb. Na yi mata reply da cewar Okay idan ya shigo zan faWa masa sai ya ciro min. 



"Salamu alaikum."



Da sauri na Waga kai sabida yadda na ji muryar kamar ta Sardauna sai da ba shi ba ne, wannan wani matashin ne daban shima Wan gayu amma Sardauna yafi shi kyau nesa ba kusa ba. 



"Uncle Turaki Welcome." 



Na ji muryar wata yarinya ta faWa tana nufo sa. 



"Dotti, how are you." 



Ya faWa cikin wani irim ™warewar turanci, kamar ma bai iya hausa ba, a raina na ce. 



"Wannan shine TURAKIN? Duk rashin girman SARDAUNA da nake gani, sai naga wannan yafi ™an™antar jiki." 



Na faWa a cikin raina, ™arasowa ya yi inda iyayensu suke ya fara gaishesu cike da girmamawa, ya Wan fi Sardauna sakin fuska amma Sardauna yafi shi komai na duniya, haka kawai sai na ji bai yi min ba sabida yadda suke da mijina. Daga nan ya juyo inda sauran yayunsu suke suka ya fara gaishesu, yadda yake Wan wasa da su Sardauna duk ba ya haka, dan ko da yazo daga Ina wuninku, Ya iyalai shikenan ya tashi ya fice. Amma shi gashinan sai hira suke har da wasa da yaransu, suma sai jan shi suke da hira mafi akasarin hiran na su ma cikin harshen turanci suke. 



A raina na ce. "Su waWannan sun maida turanci yaren uwarsu da ubansu, ba ga yaran ba ga iyayensu ba." Daga nan kuma ya juyo inda muke nan kowa ya fara gaisheshi, nima na gaisheshi ya amsa ba tare da ya kula da ni ba™uwa ba ce a cikinsu. Wata da na ji suna cewa Sister Seemah ta ce. "Blood meet your Amarya." Ta faW tana nuno ni, gaba na ne na ji yana faWawa sabida irin kallo daya ke min, sai da ya kalleni tas sannam ya dawo inda nake. 



"Daga ina?" 



Ya tambayeta, Sister Seemah ce ta matso sannan ta ce. 



"Sardauna's Wife." 



Kallona ya sake yi tare da jijjiga kai, sannan ya ce. 



"Matar ™anina kenan? Me sunanta?" 



"Nana." Lubna ta faWa. 



"Sannu Amaryarmu, sunana Turaki yayan mijinki Sardauna, kuma babban abokinsa." 



Na yi murmushi sannan na sake cewa. 



"Ina kwana?" 



"Lafiya ™alau, ina Wan uwan nawa?" 



"Yanzu ya fita zai dawo."



Na faWa a raina na fara mamakin me ya sa to basa mutunci da Sardauna, amma shi ga shi anan yana sakar min fuska har da cewa matar ™aninsa. 



"Okay zan jirashi a main falo, ya gidan?" 



"Lafiya lau." 



"To Allah Ya sanya alheri, Allah Ya bada zaman lafiya." 



Na buWe baki da niyar cewa Amin, muryar Sardauna ta cika Wakin. 



"Malam matsa daga kusa da matata." 



Legendspen

08129553971.



*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001



Sadaukarwa.



RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 



Shafi na sha Waya.

    (11)



"Kai yaro gyara bakin ka." 



Turaki ya faWa yana kallon Sardauna. 



"Ni kake cewa yaro?"



Sardauna ya faWa yana ™arasowa wajen. 



"Relax boy." 



Turaki ya sake faWa, hannu Sardauna ya sa ya fisgo ni na faWi ™asa, da sauri Matar da na ji suna cewa Hajiya Maama ta shi tana faWin. 



"Sardauna bita a hankali, ba ita a lamarinku."



"Maama me ya sa zai zo kusa da iyalina, mene haWin shi da ita." 



"Shut up malam, bansan har yarintarka ta kai haka ba, na yi tunanin duk wani abu da yake tsakaninmu zai ™are a tsakaninmu ba sai ya shafi iyalanmu ba, amma na fuskanci har yanzu da yarinta a kanka." 



Cike da wani irin fushi Sardauna ya yo kansa, Hajiya Maama ta ce. 



"Dakata Sardauna, anan kaine baka da gaskiyya. Duk wani abu da yake between you guy's ku tsayar da shi iya ku biyu, karku sanya familinku."



"But she is not our family she is mine, my family, so ya yi baya da ita." 



"Sardauna karSi wannan, ka ce she is not our family she is yours?" 



Wata dattijuwar mata ta faWa, ni mamakina ma yadda aka yi ta iya turanci har haka. 



"Dada wasa yake." 



Turaki ya faWa, sai a lokacin na fuskancin yafi Sardauna wayo ne. 



"No let him, allow him to say his mind." 



"Dada wasa nake." 



Sardauna ya faWa. 



"Are you kidding your parents?" 



"Wannam tsohuwa da mita take."



Na faWa a raina. 



"Kar nasake jin irin wannan." 



Ta faWa tare da komawa ciki, ni kuma na tashi zaune, Sardauna ya fice sauran kowa ya koma ya zauna. Haka su ka yi ta fira har zuwa 12 iyayensu maza su ka shigo suka tattauna abinda zasu tattauna daga nan aka ci gaba da hirarrakin su, banda Sardauna da ya fice. Duk lokacin da na Waga kai sai na ga munyi ido huWu da Turaki, wani lokacin ya yi min murmushi wani lokacin kuma ya yi kamar bai ganni ba. 



Haka aka gama zama kowa ya watse ya tafi, Sardauna ko a mota baice dani ™ala ba, bare kuma da aka koma gida. Nima dai ban ce masa ci kanka ba haka shima bai ce min ba, sai zuwa dare bayan ya sake dawowa na yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login