Showing 15001 words to 18000 words out of 64149 words

Chapter 6 - Sartse Part 1 Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

150

na bi na damu kuma na yi al™warin zanyi masa biyayya akan komai ya sani, tun da harshi ya Wauki jahadin yi wa iyayensa magana akan yana son auren wacca ba ta kai ba, ni to me ya sa bazanyi ba. 



Wata ranar laraba da yamma ina zaune a Waki na Wauki wayar Hajiya na sake gwada lambarsa, ina kira ya katse ya kirani. Na ji wani mugun daWi a raina, ina Wagawa ya ce da ni. 



 Ina bayan gidanku.  



Ba shiri na mi™i na zura hijabi na yi waje, Hajiya na tsakar gida tana kaWa miya na ce da ita. 



 Zani gidansu Amina.  



 Da yamman nan?  



 Eyh.



Ina faWin haka na fice zuwa bayan layi, yana jingine jikin farar motarsa, yana sanye da light blue Win shadda, ina ganin fuskarsa na ji wani sanyi ya mamaye zuciyata, wata irin nutsuwa ta shigeni, duk wata fargabar da nake ji ta tafi. 



 Yanzu ma kin daina damuwa idan ban nemeki ba.



Ya faWa yana ™are min kallo. 



 Waya faWa ma, wallahi na damu sosai da sosai.



 Ban yarda ba, gashinan har wata ™iba kika yi.



 ˜iba kuma?  



 Eyh, ya maganar mu? Me kika yanke?  



 Zanyi magana da Alhaji ta yadda zai fahimta.  



 Good girl.  



Ya faWa yana buWe motarsa, ya Wauko leda ya mi™amin. Hannu nasa na amsa sannan na ce. 



 Na mene?  



 Naki ne, na yi magana da Daddy ya amince amma Mom ce abun sai addu a.  



Wani irin tausayinsa na ji ya ratsani, nasan irin wannan abun tabbas da wahala. 



 Allah Ya sa ta amince itama.  



 Nana na sha wahala akan lamarinki, sai na ji kamar zan ha™ura sai na ji bazan iya ba, amma ke  babu ruwanki Sata min rai kawai kike, maimakon ki nuna sakayyar soyayya amma naga babu abinda kike so sai Sacin raina.  



A tsorace na ce. 



 Ya zaayi naso Sacin ranka?  



 Gashi ina gani.  



Da irin waWannan abubuwan Fahad ya dinga amfani yana cusa min tausayinsa da wata iriyar soyayyarsa mai girma, wanda a kullum gani nake yana shan wahala a kaina, sai da fa na kasa tarar Alhaji ko Hajiya da maganar, duk son da nakewa Fahad bana jin ya kai tausayin da nake yi wa Alhaji ba. 



Shi kuma a kullum faWa min irin tashin hankali da suke yi da mahaifiyarsa da  yan uwansa a kaina, har cewa ya yi dani ya daina shiga sabgar sister Winshi, a ranar na yanke shawarar tunkarar Alhaji akan maganar. 





09:15pm. 

Alhaji na zaune a Wakinsa ya bayan ya yi wanka yana sauraren radio na shigo cikin Wakin. 



 Barka da hutawa Alhaji.  



 Nana barka dai, akwai abinda kike bu™ata ne? Ko kin shirya sanar dani damuwar da na ce tana damunki kike Soyewa.



GyaWa kai na yi sannan na fara magana cikin rawar baki. 



 Alhaji daman.. daman wani ne..  



Alhaji irin mutanen nan ne masu sauraron mutane, zai iya kwashe awa guda yana saurarenka ba zai katse ka ba, sannan kuma ba zai yanke ma hukuncin ba har sai ka kammala. 



 Wani ne.. tun da daWewa ya ce wai yana so ya turo iyayensa wajenka.  



Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce. 



 Su yi mini me?  



 Wai yana sona zai aureni, kuma na faWa masa kai bazaka aurar dani ba sai na yi karatu me zurfi na zama maaikaciya, ya ce wai ya ji ya gani zai barni na yi karatu duk wani waje da nake so.  



 Shi Win waye?  



 Sunansa Fahad Ta ambo.  



Wani murmushi Alhaji ya ™arayi sannan ya ce. 



 To ke me kika yanke, auren ko karatu Nana?  



Na yi shiru na rasa me zance. Allah Ya sani ina son Fahad ina tausayin halin da yake ciki a kaina, kuma bana son rasa shi, sannan kuma ina son cika burin mahaifina, amma kuma abu guda Waya da nake gani shine auren tun da Fahad zai barni na ci gaba da karatuna, domin a maganar mu ta ™arshe da shi ya ce da ni. 



 Idan kika ga zai™i sai ki faWa masa ni zan barki ki ci gaba da karatun naki.  



 Nana  



Alhaji ya kira suna na. 



 Na baki kwana biyu kije ki yi shawara, duk hukuncin da kika yanke zan amsa tare da nawa sharaWin akai.  



 Na gode Alhaji.  



Na faWa tare da tashi na fice, ko da na shiga Waki na kwanta abubuwa suka yi ta faWomin a rai, na sa™a wancan na kwance wancan. 



 Kalli su Yaya Radiya, da Rumaisa sunyi aure kuma suna cikin rufin asiri, ga Rumaisa nan ma ta koma makaranta tana karantar harkar lafiya, ke me kike jira zaki zauna wani zama idan kika gama karatun girma ya kama ki tsaf sai ki rasa mijin auren.  



Zancen zucin da na wayi gari da shi kenan, haka na yi ta abubuwa komai sukuku, dan ma yanzu ba makaranta muke zuwa ba WAEC zamu fara nan da sati biyu, shi ya sa bamu cika wani zuwa ba. Bayan Alhaji ya fita na shirya na lallaSa Hajiya akan ina son zuwa gidan Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duka a rana Waya. 



 Wai me zakije ki yi musu duka su biyun a rana Waya?



Hajiya ta tambaya cike da mamaki, ganin tana neman hanane ya sa na ce. 



 Alhaji ne fa ya ce na je dukkansu mu yi magana dasu.  



KuWi ta Wauka ta bani tare da cewa. 



 Kuma karki yi yamma.  





Ta gidan Yaya Rumaisa na fara, tun da shi yafi nisa, akan gidan Yaya Radiya. Shi ya sa na fara zuwa gidan Yaya Rumaisa, yanayin da na sameta ya yi matu™ar burgeni, ta yi ™iba abunta duk da karatun da take yi ga yaranta kyawawa guda biyu Afra da Affan.



Bayan mun gaisa ne na kalleta sannan na ce. 



 Yaya shawara nazo nema wajenki.  



 Ina saurarenki.  



Sai da na Wan yi jim sannan na ce. 



 Nasami Miji kuma dagaske aure na yake so ya yi, sannan ya yi min al™warin bari na na ci gaba da karatu da nuna masa Alhaji yana son karatun.  



 Rawasiya, kinyi magana da Alhaji.  



 Na yi, shi ya ce na yi shawara.  



Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta kalli ni cikin idanu tare da kamo hannuna, sannan ta numfasa ta fara magana cike da nutsuwa. 



 Nana zan gaya miki abubuwan da suke cikin aure na daWi da rashin daWi, idan na faWa miki sai ki yi tunani da kanki, ki ga wanne kika zaSa.  



 Tom Yaya.  



 Nana, aure ba kawai canza gida ba ne ko samun wanda zai ri™a lura da ke. Aure ibada ne, kuma makaranta ce da ba a yaye Walibi har sai mutuwa ta raba. Idan kika ga mace a cikin jin daWin gidam aure, to dole akwai matakan da ta bi waWanda suka kai ta ga wannan matsayin jindaWin. Nana abinda zaki fara sani a farkom farko shine, mene ne Aure kuma yaya Rayuwarsa take?

Aure haWaka ce ta rayuka biyu. Manzon Allah (SAW) ya ce a cikin Hadisin Al-Baihaqi Idan bawa ya yi aure, to tabbas ya cika rabin addininsa.... Don haka, rayuwar aure tana bu™atar ha™uri da juriya. Za ki ga daWi, za ki ga wuya. Amma mabuWin shi ne Biyayya da Fahimta. Sannan kisani akwai Abubuwan da ake so Mace mai aure ta yi, duk da suna da yawa amma bari na baki wasu daga ciki. Nana na farko akwai Biyayya. Ki sani Nana, biyayyar miji tana kai mace Aljanna. Amma fa muddin bai sanya ki saSon Allah ba. Na biyu akwai Kwalliya da Tsafta, Nana ki zama kullum idon mijinki yana ganin abin da zai faru da shi, hancinsa ya ri™a sha™ar ™amshi mai daWi. Sannan kuma akwai ri™e sirri. Kada ki yarda sirrin gidanki ya fita waje, koda ga mu  yan uwanki ne, muddin ba neman shawara ta lalura ba ne. Bayan wayannan akwai abubuwan da ba a so Mace ta yi. Misali Gasar Iko, Kada ki ri™a nuna wa mijinki ke ma kina da iko kamar sa. Shi ne shugaban gida, don haka ki ba shi matsayinsa. Sannan Yawan ™orafi Kada ki zama mace mai yawan gunaguni a kan kowane ™aramin abu. Sai kuma wani abu da muke yawan yi shine ™aryata Alkhairi. Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa yawancin mata suna shiga wuta saboda rashin godiya ga mazajensu. Don haka, ko kaWan ne ya yi miki, ki ce 'Na gode'."



Ta Wago ta kalleni yadda jikina ya yi sanyi, sannan ta ce. 



 Nana aure kala biyu ne, ko na ce zaman aure kala biyu ne, na farko akwai farin cikin aure idan aka yi dace. Nana, idan kika samu miji na gari, miji mai tsoron Allah kamar nawa, to za ki ji kamar kina Aljanna a duniya. Za ki samu abokin shawara, wanda zai kiyaye miki mutuncinki, ya kare miki rayuwarki, kuma ya zama silar ™arin kusancinki da Allah. Za ki ji wani sanyi a zuciyarki wanda ba shi da misali. Na biyun kuma shine akasin haka Idan ba a yi dace ba, Idan kuma aka samu rashin da ce wanda Allah Ya kare mu, to aure yakan koma kurkuku. Idan miji ya zama mara tsoron Allah, mai son kansa kawai, to zai ri™a amfani da ikon da Allah ya ba shi yana zaluntar mace. Zai iya raba ta da mutuncinta, ya raba ta da danginta, ya kuma mayar da ita tamkar baiwa a gidansa. Shi ya sa nake ba ki shawara Nana; Kada ki yi gaggawar aure don kawai kina son yin sa, ki yi shi don kin samu wanda ya dace, kuma ki tabbatar ba za ki daina karatun ki ba domin ilimi shi ne gatanki."



Jikina ya yi sanyi, ya mutu baki Waya. Tabbas duk wata shawara da nake nema nasame ta wajen Yaya Rumaisa, kuma dole na zauna na yi zurfun tunani akai sosai da sosai. 



 Nana karki yanke hukunci cikin gaggawa, ki sami lokaco ki nutsu, ki duba halayen saurayin naki Nana ki ga nagartacce ne ko akasin haka.  



 Shikenan Yaya Na gode sosai.  



Daga nan na yi mata sallama na wuce gida, ban ma je gidan Yaya Radiya ba, ko da Hajiya ta tambayi ya na dawo da wuri sai na ce da ita. 



 Iya gidan Yaya Rumaisa na je.  



Da ta cika ni da tambayar ya take ya gidan, kawai na tashi ma shige Waki. Kwata kwata ma bana son magana, so nake na nutsu na saurari zuciyata me take ce min, me ta hanga a tare da Fahad, sai dai fa ko mene ina matu™ar ™aunar Fahad, rabuwa da shi da wuya. 



Legendpen

08129553971

553*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001



Sadaukarwa.



RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 



Shafi na takwas

    (08)



Har dare ban iya ce da kowa komai ba, shiru kamar wacca ba ta da lafiya. Haka na kwana ina faman tunani har washe gari, gaba Waya ba mu haWu da Alhaji ba shima kuma bai neme ni ba, har zuwa yamma lokacim da nasan Sardauna zai zo, Hijabi kawai na sanya na fita dan bana jin zan iya wata kwalliya a yanayin da nake, sai dai tambayar da nake yi wa kaina.  Wai shin me ya dame ni?.  



Kallo Waya Sardauna ya yi min ya gane yanayin da nake ciki, tambayar farko da ya yi min. 



 Abban bai amince ba ne?.  



 A a ya ce na je na yi tunani akan aure ko karatu?  



 To Nana me kike jira? Kinsan abinda na yi fama da shi yanzu kafin na fito?  



A hankali na buWe baki na ce. 



 Jiya da daddare muka yi maganar da shi, jira nake ya dawo na ce mai na amince.  



Ya yi wani murmushi sannan ya ce. 



 Ko ke fa Hon.  



Nima na yi murmushi. 



 Kinsan sunana?  



Na Wago kai na kalleshi, ya gyaWa mun kai. 



 Wane suna?  



 Ban taSa ji kin kira ba, shi ya sa na tambaya ko kin sani?  



Sai da na yi murmushi sannan na ce. 



 Ya zaayi na kira sunan ka, ai babu ladabi.  



 To ai akwai sunan da nake so ki dinga faWan.  



 Wannene?  



 SARDAUNA!



Har cikin raina na ji daWin sunan, sai da na maimaita a raina sannan na ce. 



 Sunan ya yi daWi.  



 Ina som sunan &akata ce ta samin shi, shi ya sa na ce shine sunan da mata zata dinga kira na, kuma a yanzu naga komai ya kusa kammala, shi ya sa na faWa miki dan nima Mom ta fara amincewa.  



 Kai Alhamdulillah.  



Na faWa a fili, shi kuma ya ce. 



 Yanzu saura ke da Abba.  



Daga nan muka Wan taSa hira sannan ya tafi, abu Waya da na kasa sabawa da shi, shine duk sansa Sardauna ya zo wajena zai tafi sai na ji ba daWi, nifa ko ba zamuyi magana ba ya dinga kallona da ido kaWai ina kallonsa abun farin ciki ne. Daga nan gidansu Amina na shiga, abun mamaki na tarar da Fauziyya da Malaika duka a gidan. 



 Da banzo ba da ba zama a nemeni ba kenan?



Na faWa ina kallonsu. 



 To banza mun zo gidan naku aka ce kin fita, sai da muka zo Amina ta ce wai Fahad ne ya zo.  



 Eyh daga can nake.  



Na faWa ina zama. 



 Dagaske dai auren naki zai yi?  



Fauziyya ta tambaya, na kalleta sannan na ce. 



 Eyh wallahi, a yanzu ma  yan gidansu so suke su zo, Alhaji ne har yanzu bai gama amincewa ba.  



 Kai ma sha Allah, muna da shagali a gabanmu, amma ya zancen karatunki?  



Amina ta tambaya, kafin na bata amsa Malaika ta bata amsa da cewa. 



 Ke wai kin san gidan da zata shiga, to ™ila ma a ™asar waje zata ™arashe karatun na ta.  



 Kai Mailaka! Wai masu kuWin gaske ne?  



Amina ta tambayeta. 



 Wanne masu kuWi kika sani kaf Jigawa?  



 Gidan gwamna.



Amina ta bata amsa. 



 Ai gwamna kuWin jama a ne, wannan magana ake kan masu kuWin kan su, yarinya kin yi da ce za ki shiga cikin manyan mata masu aji.  



Ni dai jinsu nake har suka kammala hirar, na dawo gida. A bakin ™ofa na ga Yaya Ridwan yana kallona, ban kai ga shiga gidan ba na ji muryarsa na faWin. 



 Na ™ara ganin kin tsaya da wani Wan iskan sai na ci uwarki.  



Daga haka ya shige nima na shige ciki, sai dare sannan Alhaji ya dawo, sai da na jira ya kammala komai ya shiga ciki sannan na shiga Wakin na sa. 



 Alhaji Barka da dare.  



 Barka dai Nana.  



Ya amsa yana saurarena, sai dai na yu shiru na kasa magana. 



 Nana ya aka yi? Kin yi shwarar ne?  



Na gyaWa kai a hankali, ba tare da na yi maganar ba. 



 FaWi mana, ki yi magana ina sauraren kinji.  



 Al Haji.. da ma.. Daman Alhaji na gama ne.  



Na faWa a rarrabe, ya Wago kai ya kalleni sannan ya mayar da kansa ga abinda yake. 



 Kinga me?  



A hankali na ce.   Shwarar.   Muryar na ba ta fito sasai ba. 



 Tom me kika yanke, ina saurare.  



 Auren.  



Ya Wago kai ya kalleni kusan minti biyar sannan ya mai da kai ™asa. 



 Wannan ita ce shawarar taki?  



 Eyh Abba.  



Abba ya sauke numfashi bayan ya gama sauraro na, ya kalle ni da idanuwan da suka nuna damuwa amma kuma cike da soyayya, sannan ya fara magana



"Nana, na ji abin da kika zaSa. Kuma a matsayina na mahaifinki, ba zan taSa tilasta miki abin da zuciyarki ba ta so ba, domin aure ya fi ™arfin dole. To amma, kafin mu kai ga mataki na gaba, akwai wasu abubuwa da nake so ki sani, kuma akwai sharuWWan da zan gina aurenki a kansu nasan kinsan Aure, Nana, ba wasa ba ne. Mutuncinki shi ne mabuWin darajarki a gidan miji. Ina so ki sani cewa kowace mace ita ce take gina mutuncinta ko ta ruguza shi. Ki zama mai hakuri, mai biyayya, kuma mai kiyaye sirrin mijinki. Amma kuma, ki sani cewa Allah ya ba ki daraja a matsayinki na mace, kada ki bari wani ya take miki mutunci. Kamar yadda kika sani, burina ne ki karanta ilimin likitanci ko wani fanni da zai amfani al'umma. Tunda kin zaSi aure yanzu, to zan bar ki ki yi auren, amma a kan sharWi guda Lallai sai kin ci gaba da karatunki a gidan mijinki. Ba zan yarda ilimin ki ya tsaya a nan ba. Ilimi shi ne gatanki, shi ne haskenki, kuma shi ne zai ba ki  yanci koda bayan raina. Sannan, ina so in ga wanda ya sace zuciyar  yata har ta zaSi barin karatu a yanzu. Dole ne in ganshi, in tattauna da shi, kuma in fahimci wane ne shi, daga wane gida yake, kuma wane irin hali yake da shi. Ba zan ba da ke ga mutumin da ban yarda da asalin sa da addininsa ba."



Gaba Waya jikina ya yi sanyi, soyayyar da mahaifina yake yi min babba ce ba ™arama ba, kuma in sha Allahi sai na cika masa wannan burin nasa, nasan Sardauna yana sona kuma zai so abinda nake so. 



 Abba na yi maka alkwarin zan tsaya kai da fata akan karatuna, zan zama  yar da zaka yi alfahari da ita.  



Na faWa muryata tana fitar da wani irin sauti, kamar mai kuka. Alhaji ya yi murmushi sannan ya ce. 



 A kullum ina alfahari dake da dukkan  yan uwanki Nana, Allah Ya yi miki albarka.



 Amin Abba.  



Na faWa tare da ta shi na fice, ko da naje Waki ban wani iya bacci sosai ba, bawai ina cikin yanayin farin ciki ba ne da amincewar Abba ba, ba wai kuma ina cikin damuwa ba ne, kawai wata iriyar soyayyar Alhaji ce ke ratsa zuciyata, ina son Abbana so mai girma.



Washe gari. 



A wayar Hajiya na kira Sardauna na faWa masa yadda muka yi da Alhaji, maimakon naji farin ciki a muryar Sardauna sai tsoro. 



 Hon ina jin tsora gaskiyya, ba zan iya tunkararsa ba sai dai kawai na turu.  



 Alhaji fa ba shi da matsala, kuma ba wani abu zai ce da kai ba kawai tattaunawa zakuyi ku yi hira da shi.  



 A a Honey pls.  



Nasan dole aiki ne babba akaina, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login