Showing 51001 words to 54000 words out of 161911 words

Chapter 18 - AUREN WATA TARA COMPLETE

18 Oct 2026

829

irin kasalalliyar murya Amera ko Mikewa tayi tare da cewa "nidai wlh na gaji Haba Ayi

mutum bashi da aiki sai Abu d'aya wannan jarabar dame tayi kama.shekara Tara ai yaci ace yanzu ka fara hakura da abunnan kai dama baka gajiya" ta fad'a cike da

Rashin kunya"MD ko ranshi ne ya b'aci sosai Cikin fad'a ya ce "Get out Ki fitarmun daga daki Kum

a ki rubuta ki Aje daga rana irin ta yau Bazan k'ara neman wani Abu wajenki ba zakisan ni in d'ane ki jika jikin naki kisha me nake moruwa da jikin naki daman stupid kawai marar Ilimi ko aikin Ubanme kikayi da zakice kin gaji in banda yawan birthday da di

nner da yawo gidan kawaye da bama musulmai ba ubanme kika iya ibadarma yinta kike yanda ya kamata "kuka Amera ta fashe dashi Tare da cewa " Ni kake cewa haka yau MD Daman nasan zuga ka ake kwanannan kakemun Rashin mutunci to duk ubanda ke zuga ka dinma za

nganshi sannan jiki ai nawa ne kuma nace banaso daman ance d'an Adam butulu shekara Tara kana moruwa dole ka fad'i haka idan bani ba wace mace ce Zata zauna dakai a irin wannan yanayin naka kullum Abu d'aya ba sassautawa in banda ina da kwarin arziki ta tu

ni ban rarakeba To wlh bazan iya ba Ai bani kadai bace mace a duniya"ta k'arasa fad'a ta na Jan tsaki"Idan ran MD yayi dubu ya b'aci baisan lokacin da ya wanke ta da Mari ba tare da nuna ta da yatsa ya ce "Ni kike fad'awa haka Amera Dan baki da Ilimi mijin

ki na Aure na sunna Aiko zakisan na haihu zakisan ni d'ane sannan zakisan ba ke kad'ai bace mace a duniya " Sosai Amera ta tsorata da mijin nata abar kaunarta Tsawa ya k'ara daka mata ba shiri ta bar d'akin hada tuntube MD ko ranshi ne yayi mugun b'aci ran

ar bacci sai barawo yana dawowa daga Sallar asuba Bayan yayi wanka Ya shirya tare d'aukar password d'inshi ya bar gidan Gaba d'aya baima waiwayo Amera ba Dan ta gama bata masa rai Kai tsaye Aiport ya nufa.

<Zaria>

zaune take Gaban Lecturer d'insu Bayan k

iranta da yasa akayi tunda Ta shigo tayi k'asa da kanta ta na wasa da y'an yatsun hannunta shiko wani irin kallo yake binta dashi Na kurulla har wani Had'iye yau Yake "ya ce " Zarah Yusuf ko"?eh"ta fad'a gabanta na fad'uwa Dan kar ace wani abun tayi "Murmu

shi Sulaiman yayi ya ce "Ki saki jiki mana sai d'ari_d'ari Kike Ni ba mutum bane mai tsanani ina da saukin kai daman Kiranki ne nayi Dan na fad'a maki sirrin dake zuciya ta a Gaskiya Zarah tun sanda kika shigo makarantar nan Naji kin kwantamun arai nake so

nki soyayya ta Aure bata yaudara ba Tun kina aji daya naso Na fad'a maki amma kwarjinin da kikemun yasanya na kasa Sai yau Allah yayi na fallasar da sirrin zuciya ta fatan za'a amshi tayina hannu bibbiyu" sosai Zarah tayi mamakin jin maganar da ta fito dag

a bakinshi da mamaki take binshi da Kallo tama rasa abun cewa sai k'asa da kanta da tayi gabanta na fad'uwa Suleman ya ce "Yadai kinyi shiru Zarah ko baki amshi tayin da nayi maki bane" Batasan lokacin da ta furta Kalmar "zanyi tunani tukun" ta na gama fa

d'ar haka tabar office d'in gabanta na fad'uwa "kawayenta ne hibba Da Jamcy da suka rakota suna ganinta sukayi kanta hibba ta ce " Lafiya me ya ce maki naga kin fito a rikice kinsan mutumin nan ba mutuncin kirki ya isheshi ba"Ajiyar zuciya Zarah ta sauke t

are da cewa "Kudai kawai muje wlh abun yaban mamaki wai mutumin nan zaice ya na sona" wara idanu sukayi a tare suka ce "so " Sai Kuma hibba tayi Dariya ta ce "chab Wlh ki amince masa idan ba haka ba Zai Kadake a last paper baida mutunci wlh kuma d'an iska

ne na Bugawa a jarida haka sukayi Da wata budurwa yayata ta na bani labari daga tak'i amince masa wlh Ya kada ita a last paper kuma da gangan Dan Ance kokari gareta" wara idanu Zarah tayi ta ce "Na shiga ukku kuma shine kike cewa Na amince masa Bayan kinsa

n d'an iska ne " jamcy ce ta dafa ta ta ce "Karki damu ai ba kowa ake Kalla ayima zancen iskanci ba yanzu dai fad'a mana yanda kukayi dashi...nan ta basu labarin yanda sukayi hibba ta ce " To wlh tunda kikaji ya ce Aurenki zaiyi ki rabu dashi bazai maki za

ncen banza ba sannan kuma yana ganinki amerar makaranta kinsan ance d'an iska baya

Auren y'ar uwarta y'ar iska Shima tagari yake nema wlh da gaske yake Dan tun sanda ake lecture na lura da irin kallon k'urullar da yake maki nasan sonki yake ki rabu dashi k

awai kuyi soyayya "tab'e baki Zarah tayi ta ce"Bama sai Inda ya k'ara gani na ba.....Koda Tabawa su Asmy labari suma irin yanda Su hibba suka fad'a mata haka asmy ta bata shawara ita dai jinsu kawai take Amma batajin zata iya soyayya da wannan Bayan akwai

baikon Aurenta da Hafiz (Nikam nace again kuma ga auran md akanki)Chuchu kuwa cewa tayi"Karki biyeshi momcy bazai kada ke ba Inma ya kada ke ai akwai Allah Duk mutumin da Akace Dan iska ne kaji tsoransa kinganninan bana k'aunar Dan iska shiyasa ko huld'a

banayi dasu tunda nazo makarantar nan ba kowa nake abota dashi ba Saboda tsaro ku kadaine zance aminai na kuma Dan na yarda daku 100% na tabbatar kudin mutanen kirki ne kuma tare na daku na k'aru da abubuwa Dan haka Ina baki shawarar kawai kice masa an san

ya miki Aure a wuce wajen"Zarah ta ce "Daman Chuchu duk jinsu nake wlh shawararki ita ce shawarar kirki sai sannan Asmy ta ce " Kuma fa hakane "a zuciyarta Asmy ta ce " Astagfurillah to ya matsayin Auren nan na Zarah yake a musulunce laifi ne tayi mu'amula

da maza"wata zuciyar ta ce "Mata ai Aure duk Aure ne ko wayar da take Da hafiz haramun ne" Sosai taji gabanta ya bada daram Zarah ko bata tab'a kawo wani Aure a kanta ba harkar gabanta kawai take Dan mancewa ma take da wani Aure a kanta Dan bata d'auki Au

ren Aure ba dukda ta na da ilimi....Yau Zarah ta shirya tayi kyau sosai Cikin doguwar rigarta Abaya Black mai shegen kyau hijab ta d'auko zata sanya Chuchu ta rik'e hijab tare da cewa "Haba Momcy kici gayun nan ki sanya hijab Allah ban yarda ba gyale zakis

a ai ba matsatsun kaya bane sannan Ko larabawa ai sanyawa suke har suyi salla ma dashi please ki yafa gyalen wlh sai kinfi kyau" Badan Zarah taso ba dole ta yafa gyalen nanko Chuchu ta shiga koda da tana cewa "Wow Momcy wlh kin hadu yanda kikasan wata firs

t Lady taho muyi hoto ta fad'a tana shiga snap" Murmushi kawai Zarah tayi nan ta shiga kashe musu hotuna masu kyau chuchu ce ta ce "Wlh momcy karkiga yanda kikayi kyau aikedin Matar manya ce wlh ba yara ba da yaya na kika dace bada kowaba" Harararta Zarah

tayi ta ce "ba nace ki daina had'ani da Yayan naki ba ni ta Hafiz ce ta fad'a tana mata far da ido" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ki dai bar cika baki kika sani ma ked'in ko rabon Yayan nawa ce Saikiga Hafiz dinma ya mutu" Wara idanu Zarah tayi tare da Kai mat

a Dukan Wasa a baya ta ce "Ta Allah ba taki ba muguwa Ya Hafiz dina bazai mutuba sai yaga ma Auren jikokinmu" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ah su jikoki manya sai mu gani Har na hangoki gidan yayana " Sanin Zarah ta biyewa Chuchu sai ta fasa fitar ya sanyata g

irgiza kai kawai ta fita ta ce "Dan yanzu Sauri nake ai zan dawo tare da fita daman Asmy ta fita yi musu chefane kai tsaye napep ta Tara Inda ta fad'a masa sunan unguwar da zai kaita kamar yanda Dr Halima ta turo mata sunan unguwa ta na isa Ta kirata ta ce

" Aunty na iso nan tayi mata kwatancen Inda take"Dr Halima ta ce "okay ga yarinyata nan zata zo ta taho dake" Zarah na nan tsaye taga wata yarinya da bazata wuce sa'ar khairat din gidansu ba Ta na ganinta ta gane y'ar Dr Halima ce saboda kamar da suke Yar

inyar ta gaishe da Zarah ta amsa mata da murmushi Tare da kama hannunta har suka Isa gidan Cikin mutuntawa Dr Halima ta tari Zarah tare da cewa"oyoyoyo Amarya Yau dai Allah yayi Gaki a gidana "Murmushi Zarah tayi tana zama ta ce " ina yini Aunty munsameku

lfy"Alhmdllh Zarah ya kwana da yawa kin bace ko ya amarci"Murmushi kawai Zarah tayi ta na kasa da kanta kafin kace me an cika mata gabanta da abubuwa har mamaki tayi irin tarbar da aka mata Inda Dr Halima ta tsareta saida ta cicci wasu sosai Zarah ta yaba

da kirkin Matar wajen magriba Zarah ta ce mata zata tafi sosai Dr Halima ta cikata Da abubuwan Arziki

su turarruka masu kamshi sai Godiya take mata akan ziyarar da ta kawo mata ita dai murmushi take har waje ta rakota tare da cewa"A dai cigaba da hakuri Za

rah zaman Aure d'an hakuri ne Sannan ki dinga yiwa mijinki biyayya Allah babu ruwansa da bakyason Auren zai kamaki da laifin hakkin mijinki muddin kina tauye masa"da mamaki Zarah ta d'ago ta na kallon Dr Halima gabanta na fad'uwa ta ce "Dr kina nufin kinsa

n komai " Ganin yanda ta rikice lokaci guda ya bawa Dr Dariya ta dafa ta ta ce "Baki d'auke ni y'ar uwa ba kenan ina son ki daukeni yar uwa a garin Nan kamar yanda dr aliyu ya fadamun bakisan kowa nan garin ba Aure ne ya kawoki sannan shima mijin aiki ne y

a kawoshi garin Zarah Ai Dr ya fad'amun komai ya ce " Auren ne bakiso shysa ma ranar Har hakan ta faru kiyi hakuri ki zauna da mijinki lfy kinji kanwata "Boyayyar Ajiyar zuciya Zarah ta sauke a zuciyarta ta ce " Dr d'innan Allah ya hore masa iya tsara kary

a Munafiki da Aikin lawyer ko jarida ya dace bada Asibiti ba a fili kuwa murmushi tayi ta ce "Insha Allahu Aunty ki koma zan samu abun hawa" To nagode a gaida mai Gidan nima saina shigo gidan naki insha Allah"sannan ta mik'a mata 500 tace gashi kiyi abun h

awa"Kin amsa Zarah tayi ba yanda batayi da itaba amma taki amsa Cikin unguwar taci gaba da tafiya Dan bataga Alamun samun abun hawa nan kusa ba ga kiraye kirayen magriba da Aka fara tana cikin tafiya Taji parking d'in mota bayanta bata waigaba saboda a mat

uk'ar firgice ta ke "keeeee" Ta ji anfada Wanda ya tabbatar mata da ita ake da wata zazzak'ar murya Saurin Juyawa tayi Ganin fuskar da bazata tab'a mantawaba da ita ba a rayuwarta ya sanya gabanta fad'uwa tare kara

wa saurinta volume Binta yayi yana kiran

keeeee amma bata waigo ba Zarah batayi aune ba saiji tayi anyi charab an d'auketa wutsil wutsiltu ta fara tana yagushinshi tuni hawaye harsun wanke mata fuska ta ce "Meye haka Malam ka ajeni " Baimasan tanayiba bai direta ko ina ba sai Gaban mota tare da

rufewa ya zagaya tashiga driver sit ya tada motar a guje yabar wajen.....

✍

🏿

_Ki saya da zuciya daya y'ar uwa Dan girman Allah kar a fitarmun da Littafi kud'in karantawa kuka biya ba na mallaka ba_

*07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN

CE.

πŸ‘―

‍♀

️

πŸ‘ŽπŸ‘‡πŸ‘‡

*

1, *MU GANI A ƘASA...*

πŸ”₯

_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*

πŸ₯š

_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*

πŸ’₯

_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*

🌎

_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*

πŸ‘©

‍❀

️

‍

πŸ‘¨

_Miss H

ajo_

Guda biyar 1k

Guda hu

Ι—

u N700

Guda uku N600

Guda biyu N500

Guda

Ι—

aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

πŸ‘‡

0037219728

Fatima Rabiu Sunusi

StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

πŸ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

πŸ‘‡

08

14 179 9224

Ζ³

an Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

πŸ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f

Guda hu

Ι—

u 700f

Guda uku 600f

Guda biyu 500f

Guda

Ι—

aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.*

πŸ”₯πŸ₯šπŸ’₯πŸŒŽπŸ‘©

‍❀

️

‍

πŸ‘¨

_*Miss Hajo

ce*_

πŸ€™πŸΏ

[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy:

πŸ…Ώ

️

.........*33 & 34*

"Kana nufin Dr Had'in baki kukayi batare da izini na ba kuka dauramun Aure ?daman lokacin da Asmy tayimun maganar nan kunrigama kun gama komai sannan ta fashe da kuka ta ce " Wlh Dr banyarda

ba Saidai a farke.Auren "Lallashinta sosai suka shigayi cikin magana mai dadi da kwantar da hankali har Dr ya samu Zarah ta tsagaita kukan Dagowa tayi da rinannun idanunta da sukayi mata ja ta ce " ya na Ina Dr ku sa ya rubuta takardar saki ya bani kamar

yanda kuka k'ulla Auren haka zaku since Dan wlh bazan iya kai tsawon wata Tara da Auren mugun azzalumi macucin mutumin nan ba"numfashi Dr ya ja ya ce "Karki damu Zarah zai sakeki Ai ba Aure bane kamar ko wanne Aure ne akayi a bisa larura insha Allahu karki

damu baza akai wata Tara ba sannan ya d'ora da cewa Dan Allah karki kullaci y'ar uwarki batayi hakan Dan komai ba saidan k'aunar da take maki ki nutsu kiyi tunani Zarah Asmy bata chanchanci haka daga gareki ba" Zarah batace

uffan ba Dan har yanzu Abun nan

ciwo yake mata sai Mikewa da tayi Dr ya bita da Kallo ya ce "Ina zaki kuma" Hostel "ta fad'a ta na kauda kai" d'an murmushi yayi ya ce "to Malama Zarah kin Sallami kanki Da kanki kenan" Turo baki tayi batace uffan ba "Jaber ne yayi murmushi ya ce " Muje n

a saukeki "wani banzan kallo ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce" bana buk'ata "Saida ya kumshe dariyarsa Dr ne ya ce " To ni na kaiki ko nima fushin ake dani"Ta na kauda kai ta ce "Zan tari napep naje ba sai an kaini ba " da kyal Dr ya samu ya shawo kan

ta ta yarda shi ya kaita amma jaber firr kiyawa tayi a lokacin da Aka sallameta Dr Halima bata kan Aiki Taso suyi bankwana amma kuma bakomai ai tunda suna da number wayar juna sun dinga gaisawa.

Har suka isa makaranta Zarah bata magana shine de sai zuba

yake ya na bata kamalai masu kwantar da hankali akan wannan din ba wani Abu bane Tayi hakuri ta dauki hakan ba komai ba ita dai jinshi kawai take ya na sauketa Ya ce "To Malama Zarah sai ankawo mana ziyara k,o?,Wani kallo tayi mata tare da kauda kai tayi g

aba batace uffan ba Dan Shima mugun haushinsa takeji shikam murmushi yayi harga Allah yarinyar na burgesa sai yanzu yake Danasanin k'in Aurenta shi da kanshi da yayi (Nikam nace Gaskiya Dr da jaber kun rainawa zarah wayau )

Zarah na isa hostel bata iske k

owaba hakan ya tabbatar mata da Suna lectures Cire hijab d'inta tayi Tare da hayewa Gado Bayan ta jona wayarta chaji da tayi kwana hud'u rufe Ta na nan Kwance ba bacci take ba tunanin rayuwarta take tun daga farko tanajin zafi a cikin zuciyarta Ji take ina

ma tana da wanda zata fadawa sirrinta taji sanyi Goge hawayenta tayi ta ce " Allah ya jikan ki Mamana ke kad'aice sirrina kuma a halin yanzu bakya raye dukda ban sanki ban san wani naki ba ko da danginki na gani da zanji sanyi a raina"

Around 2pm Chuchu d

a Asmy suka shigo Bayan dawowansu daga lectures sosai suka yi murnar ganin Zarah da farinciki Chuchu ta ce "Kindawo kenan momcy Sannu da dawowa ya mai jikin" Dagowa tayi ta Kalleta tunani tayi wane ba lfy Hakanan dai tayi mata murmushi ta ce "Da sauki" All

ah ya k'ara sauki Ai Asmy ke Cemun Matar babanki ce ba lfy "jinjina mata kai kawai Zarah tayi Asmy ce ta ce " kindawo lfy Zarah"banza zarah tayi mata tare da Juyawa ta lumshe ido kamar mai bacci sosai hakan ya bawa Chuchu mamaki Dan tsawon rayuwarta bata t

ab'a ganin haka tsakanin wannan y'an uwanba Dan ita duk daukarta cousin sisters ne badai tayi magana ba.

Tunda zarah ta dawo bata da wata walwala sanyinta ya karu fiye da Wanda take dashi Batayiwa Asmy magana Wanda hakan sosai yake damun Asmy Chuchu ma ha

rta fahimta koda ta tambayi Asmy me ya had'asu cewa tayi sundanyi fadane zasu shirya.... yau Zarah Bayan fitowarsu daga lectures zaune tayi bakin wani block book ne hannunta amma kwata_kwata Hankalinta baya ga littafin ta Lula duniyar tunani har abokinta Y

usuf yazo ya zauna bata sani ba saida yayi mata tabi tukwana ta dawo hayyacinta kirkirar murmushi tayi ta ce "yaushe kazo" Zaunawa yayi ya ce"tund'azu naga kina ta tunani wai Me ya faru ne daughter naga kina yawan tunani kwanannan baki da walwala"Murmushi

kawai tayi ta ce "Bakomai wai muna da lectures Anjima kuwa?Girgiza kai yayi ya ce " a a a malamin ya d'agata ya maida gobe da Yamma kuma ya ce C a zaiyi"okay to daman nazata za ayi shiyasa na zauna bari na wuce hostel Dan na gaji "tare suka Mike suna tafe

ya na mata hira harsuka isa hostel bata iske su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login