Showing 156001 words to 159000 words out of 161911 words

Chapter 53 - AUREN WATA TARA COMPLETE

18 Oct 2026

949

ya Amera tayi shegiyar Ashe duk Takama da gadara da take Akan kudi da duniya ita ta tashi cikin arziki kaza_kaza Ashe ma kudin dukiyar Kakanki ce kai gaskiya dai Baban amirar Nan yaji kuny

a wlh "Girgiza Kai kawai Zahra tayi ta Ce"Allah shiryeki chuchu Daman akan wannan ne har Kika tasheni bacci yaudai naji gulma kikeji nikuma bacci nakeji wlh"Dariya chuchu tayi ta Ce "Kamarko kin sani Allah yau y'an gulmar ne a Kai"washegari Zahra ta Kira b

aba a layinta bayan Asmy taturo Mata number Sosai suka Sha waya da mahaifin Nata sai Dadi takeji sunjima suna waya kafin suyi bankwana cike da kewar juna a cikin satin Nan aka yankewa Abban Amera hukuncin kiss ta hanyar rataya bisa ga rashin gardama da bai

yi a Court ba yasanya shari'ar tasu tayi sauki Sai sannan hankalinta MD ya Fara dawowa jikinshi Koda yaje ya labartawa ammy Sosai taji Dadi Kuma tayi hamdala koba komai Shima zaije ya girbi abunda ya shuka a ranar suka koma gidansu shida Zahra tare da yara

nsa ranar dai Zahra taga yadan warware Wanda da taimakonta hakan ya faru da girki ta shimfida Masa Mai dadin gaske bayan ta dau gayu Kuma ta faranta Masa a shimfida washegari Zahra na kwance jikin MD kan kujera Tana zuba Masa shagwaba Yana biyeta Yaran ko

suna tsakar polourn suna wasa da wutsil wutsiltu wayar MD tayi ringing yayi mamaki Ganin bakuwar number ta kirasa da special numbersa da makusantata ne kadai ke kiransa da ita kin dauka yayi Saida aka sake Kira Zahra ce ta Ce "Ka Dauka Mana Hubby ana kiran

ka fa"Dan kar Zahra ta zargi wani Abu ya sanyashi dagawa daga Bangaren Maman Amera ta na kuka ta Ce 'Ga Amira Nan mustapha zata mutu ba sunan da take ambata idan ba naka ba ka daure kazo ko bankwanar karshe ce kuyi Dan Allah"a zabure MD ya Mike ya ce "Subh

anallah mama Kuna wani asibitin "BIBA HOSPITAL"ta fada Masa "Cikin sauri ya katse wayar ya ce "gani Nan"Mikewa yayi hankalinta tashe binshi Zahra tayi ta ce"Lafiya dai?Da sauki Amira ce ba lfy ki koma zanje na gano"ya fada Yana fita waje ba shiri komawa Za

hra tayi ta zauna Tana tagumin kome ya samun amirar saikuma ta Tabe Baki ta koma wajen yaranta ta dinga yi musu wasa kafin ta Kara kimtsa Gidan da turarruka kamshi saikuma ta shiga kitchen Dan Dora sabon girki"Soaai MD hankalinshi ya tashi ganin halin da A

mira ke ciki numfashima dakyal takeyi "hankalinsa tashe ya kalli Mamanta ya ce "mama tun yaushe ta Fara ciwon"Tun ranar da tashin hankalin Nan ya faru take kwance Daman dai duk zaman da tayi gida ba lafiya ta fiya ba yanzu dai yau batama gane wadanda ke zu

wa da dawowa sunanka kawai take iya fada kafin Dr yayi Mata allurar bacci"innalillahi wa inna ilaihiraji'un"MD ya dinga maimaitawa kafin ya rike hannun Amira Yana kallonta yanda numdashinta ke fits dakyal Sosai yaji tausayinta Ganin irin ramar da tayi Yana

rike da hannunta Yana ta kallonta Yanajin rashin kyautawarshi na kin. Waiwayarta Wanda a nashi salon Dan ya hora ta ne su zauna lafiya Shi yasan idan yace baya kaunar amera yayi karya kodan sabon zaman shekara goma ai ba wasa ba saidai kawai yaji a ranshi

yafison Zahra fiye da soyayyar da yakeyi Mata a Cikin ranshi duk abunda mahaifinta yayi baijin Zai rabu da ita saboda Laifin mahaifinta daban ko a lahira Nata daban Laifin wani baya shafar wani ita kanta Mamanta tayi mamakin yanda MD bai nuna komai ba duk

wani abunda za a bukata Saida MD ya bada kudi koda amira ta farka da sunanshi a bakinta Yana kusa da ita ya ce"Bude idonki ki ganni honey nine mijinki a tare dake "A hankali amera take kallonsa kafin ta Fara hawaye ta garkame hannunsa ta Ce "Ka yafemun ho

ney duk Laifin da nayi maka Dan Allah honey inajin a jikina mutuwa zanyi honey zuciyata ji nake kamar zata fashe ka yafemun Kace ammy da su Hajiya su yafemun da duk Wanda nayiwa laifi.."ta karasa fada Tana hawaye"Sosai hankalinmu MD ya tashi rukota yayi So

sai ya ce"Kidaina fadar irin maganar Nan My Merah bazaki mutu ba Zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu muma zafin ciwo ne Dan Allah kidaina fadar Haka Kina tayar mun da hankalinna"Murmushi yake kawai Amera tayi "Mamanta ce ta karaso ta Ce "Ki daina fadar Haka

Amira kinsan ke daya Kika ragemun a fadin duniyar Nan ke daya gareni ba uwa ba uba ba miji bazan rasaki ba amera zamu rayu"Hawaye kawai Amera take Tana kallon maman Tata ta Ce "ki yafemun Dan Allah mama"kuka Sosai Mamanta ta ke tace bakiyimun komai ba ame

ra Baki da hakkina a tare Dake inma akwaishi na jima da yafe Miki banason kina kalama. Nan kina tayar mun da hankalin"MD ji yake kamar Shima yayi kukan mikewa yayi yaje wajen Dr din domin chuku_chukun a fidda ita waje cewa Dr yayi ba matsala sai a shirya f

itar da ita din zuwa jibi "yinin ranar mD Shi yayi jinyar Amira Yana rungume da ita duk abunda take so Shi yake Bata Daren ranar shine baikoma gida ba Saida yaga ta samu bacci sai wajen karfe Sha biyu ya koma gida Koda yaje bai samu Zahra a parlour ba Yana

shiga bedroom Amma ganta kwance ita da Yaran su duka suna bacci Banda ita daya same ta Tana kallon gefe Tana tunannika Wanda Saida yakira sunanta tukwana tasan da zuwanshi kallo daya tayi Masa da har bazata Masa magana ba saidai ta danne kishin da takeji

Tunda yayi Daren Nan tasan Yana tare da matarsa ta Ce "Ya Mai jiki"Numfashi yaja kafin ya ce "Da sauki dai za ace Amma waje Zan fitar da ita gaskiya ban yarda da kwarewar asibitin ba Tana Shan jiki Sosai ciwon Nata ya dagamun hankalinta"ya fad'a fuska ba w

alwalar"Allah ya bada sauki"ta fada Tana juya baya tare da rumtse Ido tanajin kishin amera Sosai a ranta "Tana jinshi ya dauke Yaran ya mayar dasu gadonsu na iri Wanda ake turawa kowanne Mai net dinsu kafin ya kwanta ya janyota jikinsa Zahra Najin haka ta

marairaice Cikin shagwaba ta Ce "nasan ka shawo gajiya kanason ka yi bacci please ka kwanta yanzu danka tashi da wuri Abbansu Amar"d'an murmushi MD yayi Yana jinjina hikima da wayewa irin ta Zahra Bata iya cemasa ita ta gajine bazata iya ba shiyasa ta sauy

a. Maganar cikin hikima baiyi Mata komai ba sai janyota jikinsa da ya karayi ya ce"Mu kwanta....washegari tun asuba MD ya wuce Asibitin ba yanda Zahra batayi dashi ba Akan Yama tsaya yayi breakfast Amma yakiya Bayan fitarsa Tagumi tayi tana Jin yanda zuciy

arta ke nukurkusa akan kishi wata zuciyar tace Mata matarsa ce fa tun kafin ya sanki suke tare shekara goma Sha ,Bata da lafiya dole yayi fiye da Haka ma '"Saurin mikewa tayi ta Ce "Au'zubillah"Kafin ta cire duk wani kishi da tasa a ranta ta aje gefe saima

.adduar samun lafiya da tayiwa Amira Bayan sun kimtsa Gidan tare da taimakon Yan aikinta Nanny din yaran Suma sun shiryasu kitchen ta shiga tayi girki Mai d'an yawa Bayan ta gama komai ta Sanya a warmers a lokacin 1:pm Cikin sauri tayi Wanka ta shirya Ciki

n kayanta masu kyau Bayan ta Sanya katuwar hijab dinta irin ta larabawan Nan har kasa wayarta ta dauka tare da Kiran number MD Bayan ya dauka ta Ce "ya sunan asibitin na shirya ne Ina son nazo na duba ta "Ki Dan jira minti biyar ga driver Nan zanturo ,zaiz

o ya kawoki Asibitin"ya fada a sanyaye"Okay"ba ayi 10 minute ba Saida driver yazo ya dauketa ita da yaranta sai nannynsu daya data rike Mata biyu koda suka isa har dakin da Amira take Sosai Zahra taji wata irin faduwar gaba Ganin yanda MD ya rungumo Amera

jikinsa Yana bare Mata ayaba dakyal ta iya control din zuciyarta da take Jin kamar zata rabe gida biyu ta gaishe da maman Amera ta amsa Mata Cikin mutunci Dan ta gane ta tare da tambayar ya Yan Gidan ta ce "Alhmdllh"Dagowa MD yayi ya kalli Zahra dayaga ta

Dan sauya zamewa yasoyi tun dazu Amma amera ta garkamesa Yana Jin nauyin mamantama Dake wajen Amma tun safe da yazo taki barinshi tashi a sanyaye Zahra ta kalli Amera Dake Numfashi dakyal ta ce "Ina yini ya jikin"Kallonta Amera take da idanunta da suka Far

a sauyawa tsabar wahala ta gyada Mata Kai ta ce "Alhmdllh"Kallon MD amera tayi ta Ce"Ce ta mikomun yaran na gansu"Ta fada Tana hawaye kallon Zahra MD yayi ya ce "Mamy d'an Miko Mata su "Zahra ji tayi kamar ta ce "a a a Dan Bata mance lokacin da Amira taso

halaka yaran ba dakyal tayi shahada ta Mike da little Dake haannunta ta nufi gadon Mika hannunta Amira tayi tana daga kwancen ta amshe ta "Zaki iya daukarta kuwa"Kirkirarren murmushi Amira tayi ta ce"Eh Zan iya yau jikin yafi koyaushe mun sauki"Alhmdllh Da

man haka nake sonji Insha Allahu Zaki warke gobe ne tafiyar da za ayi Dake Egypt"Girgiza Kai kawai Amira tayi Zahra ji tayi kamar zuciyarta ta fashe juyawa tayi zata koma amera ta ruko Hannunta juyawar da Zahra tayi sai gani tayi tana hawaye ta ce "Dan All

ah y'ar uwata ki yafemun duk rin abunda nayi maki ki yafemun banason na tafi da hakkin kowa ina Neman yafiya a gareki Dan girman Allah"zuciyar Zahra Sosai ta karye batasan lokacin data Fara hawaye ba. Ta ce "Ba abunda kikayimun Aunty Amira idanma kinyimun

na yafe Miki Nima kiyafemun insha Zaki warke ki tashi kamar kowa"Suna Jin Amira ta sauke ajiyar zuciya har lokacin Bata saki hannun Zahra ba saikuma ta hada Dana MD ta ce "Honey ga Amanarta Yar uwata Nan ka riketa da Amana kamar yanda ka rikeni Amana nasan

kaid'in Adalin mutum ne Kayimun halaccin da ba Wanda yayimun a rayuwa MD ka zauna Dani tsakani da Allah ka kyautatamun dukda irin rashin kyautawar da na dinga maka ka kula Dani ka Soni a lokacin da idan wanine xai gujeni Babu abunda zance a zama na dakai

saidai godiya Allah ya hada fuskokinmu a aljanna fiddausi Kema Zahra ki rikesa da Amana Karki Bari MD ya kubuce maki samun irinsa a Cikin maza Abu ne Mai wahala Ina tayaki murnar samun miji na kwarai na gari nagartaccen sannan inayi muku murnar samun zuri'

ar da kukayi Allah ya Raya su naso Ganin jini na a duniyar nan Ashe banida rabon Zan gani ,Dan Allah Ina Neman alfarmar da idan Kun haifi wata y'ar ku Sanya Mata suna na MD karka Manta Dani ko bayan Raina ka sani Ni amera na mutu ne da soyayyarka a Raina K

uma da ita zantashi Koda ranar gobe kiyayya Ina sonka mijina ina tsananin kaunarka Kuma Ina alfahari dakai Allah ya hadamu a darussalam"Kuka ne yaci karfinta Sosai Itama Zahra kuka take Sosai taji wani irin tausayin Amera Ganin irin yanda numfashinta ya sa

uya da tarin da take ya sanya Zahra dauke little Dake kanta MD ko a matukar rude ya Fara girgizata Yana Amira Amira Mamanta ko wani irin kuka ne Mai karaji ta fashe dashi gaba daya hankalinsu ya tashi ganin irin yanda numfashinta ke Neman daukewa suna Gani

n yanda bakinta yake motsi Amma Basu San me take cewaba a matukar rude hankalinta tashe MD ya fita ya Kira doctors likita hudu suka shigo bayan sun bada umarnin kowa ya fita MD kin fita yayi Zahra ko wake sukayi suna kuka Duk iya yanda likitoci suka so cet

o rayuwar Amera abun ya gagara ba ayi 20 minutes ba komai na jikinta ya daina aiki Ganin likitocin na cire oxygen din da suka da Mata da kayan aikinsu ya sanya MD rikicewa a matukar tashin hankalin ya ce "Me kuke nufi Dr kardai kucemun ta mutu"Daya daga Ci

kin Dr din ya dafasa ya ce "Am so sorry Allah yayi Mata cikawa dukkan Mai Rai mamaci ne kowa jiran tashi ranar yake ta rigamu Gidan gaskiya saidai muyi addu'ar Allah ya jikanta ya rahamce ta mu Kuma ya bamu guzirin taddasu"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un

MD ya fada kafin yaje ya rungumeta ya ce "Karkiyimun Haka amera me yasa Zaki tafi ki barni Amera kin mutu innalillahi wa Inna ilaihiraji'un yanzufa kike cewa jikin naki da sauki Dan Allah ki tashi saikuma ya fashe da kuka kamar mace Yana kan gawar Sosai l

ikitocin suka tausaya Masa sunsan ba karamun shigarsa mutuwar tayiba maman Amira ko da aka fada Mata mutuwar Suma tayi Zahra ko Tasha kuka dakyal ta iya daukar waya ta sanar dasu ammy mutuwar Amera Sosai Suma hankalinsu yayi tsananin tashi MD ba karamun ta

shin hankalin ya shiga ba a mutuwar Amira yayi kukan da bai taba yin irinsa ba tunda yazo duniya A Haka dai aka Kai amera gidanta na aure Wanda Anan akayi Mata. Sutura Sosai wajen jana'izar Tata ta cika da mutane a makabartama MD Saida yasha kuka dashi aka

sanyata ya jima Yana Mata addua da Neman Mata rahamar ubangiji Kira yake na yafe Miki Amira Baki mutu da hakkina ba komai kikamun a zamana Dake na yafe Mik

i Allah Miki rahama Allah yasa mutuwarki ta kasance hutu a gareki Allah yafe Miki mala'ikun rahama s

u amshi bakuncinki ya Allah Ka jikan Matata ka yafe Mata Sosai MD ya Sanya wasu daga Cikin Yan makabartama kuka kafin dakyal aka samu ya tashi dagakan kabarinta kafin kowa ya watse aka barta daga itasai halinta (

😭😭

Allahsarki Amera Allah jikanki) Koda Suk

a koma gida aka Fara zaman makoki MD baya iya cin komai kallo daya zakayi Masa kasan ba karamun shigarsa mutuwar tayi ba ko mahaifiyar Amira Bata Kai MD shiga wani hali ba Zahra ko itama Sosai ta damu idan Tana tuno da maganganun nasu da Amira na karshe du

kda ba wani sabo sukayi da itaba Amma mutuwar ta shige ta Kuma ta karyar Mata da zuciya a Nan inda Amira ta yi rayuwar aurenta akayi zaman makoki su ammy da Yan uwa da kowa dasu Zahra da mahaifiyar Amira duk Nan suke kwana Yan uwan Zahra ma na wajen babant

a sunzo motarsu guda sunyiwa MD gaisuwa sannan Bangaren Mamanta ma daga jigawa Suma da yawansu sunzo sunyi mashi gaisuwa Saida Akayi sati guda ana zaman makoki kafin ayi sadakar sati taro ya ragu ya rage Saina gida mahaifiyartama ta hakura tayi tawakkali M

D ne dai abincima saidai idan ammy ta kirasa Tana Masa wa azi da nasiha Harta samu ya danci Kowa yazo sai yayi Masa nasiha Akan yayi hakuri ya bita da addua Wanda ya tafi baya dawowa a sati na biyu suka koma gidansu saboda Yan gaisuwa yanzu sai daidai tund

a suka koma Zahra Bata gane kan MD hira ma basa zaunawa suyi kullum Saidai yayi shiru Yana tunani hirarta dashi saidai ta gaishesa ya amsa ko yanason wani abun tayi Masa yaransama idan ya daukesu baya musu wasa kamar da Sosai Zahra ta shiga damuwar da wann

an halin da MD ke nuna Mata hankalinta duk ya tashi yau sati biyu kenan da dawowarsu gida Amma basa Zama suyi wata hira Kullum Cikin tunani yake ga abinci ma idan ta girka ba Ci yake Sosai ba baifi yayi spoon ukku ba ya tashi wani Karin ma bayaci "Zahra sa

idai taje daki Tasha kukanta Yauma ta na Cikin Shan kukanta taji wayarta tayi ringing Tana Ganin chuchu ce ta Dauka yanda ta amsa Mata sallamar ne ya Sanya chuchu ta gane akwai matsala cewa tayi "Lafiya Momcy naji kamar muryarki kinsha kuka"Kukan da take b

oyewa ne Zahra ya kubce Mata ta fashe dashi Saida ta tsagaita kukan kafin chuchu Cikin damuwa ta ce "Subhanallah Aunty me yake faruwa ne Wai"Cikin kuka ,Zahra ta Ce "Chuchu bansan me nayi Masa ba tunda akayi mutuwar Nan bayamun magana bayacin abincina Sosa

i gaba daya na rasa abuna ke mun Dadi zaman Gidan duk ya isheni kwata_kwata bani da walwala bansan me nayi Masa ba"Ta karasa fada Cikin kuka "Ammy Dake Jin Abunda Zahra ta fada kasancewar handsfree aka Sanya wayar Kuma suna kusa da juna amsar wayar tayi a

hannun chuchu ta Kara a kunnanta ta ce Hello Zahra"Zahra Najin muryar Ammy gabanta ya fadi Allah yasa bataji ba saboda kartayi tunanin ko kararsa ne takawo saurin katse wayar tayi tare da yin Tagumi ta fashe da sabon kuka MD daga kofa zaishigo dakin yaji k

omai da irin yanda take kukan take fadawa chuchu batasan me tayi Masa ba Sosai yaji tausayinta ya kamasa Shi kanshi bayama sanin yamata Haka saboda kwata_kwata tunaninshi baya jikinshi Babban tashin hankalinshi da mutuwar Nan irin yanda ya banzatar da ita

wata ukku bai taka inda take ba kota kirasa baya Dauka Shi yafi komai tsaye Masa arai na Ganin rashin kyautawar da yayi Mata karasowa dakin yayi tare Kama hannun Zahra ya tallabo fuskarta Dake kuka ya Ce "Kiyi hakuri Mamy bakiyimun komai ba Baki taba yimun

laifi ba Dan Allah dalilin mutuwar Nan ne da Bata sakeni ba ya Sanya banason yin magana ko cin abinci Amma ba Wai Dan na musguna Miki ba Dan Allah kiyi hakuri ki yafemun"Lokacin guda Zahra ta dago saikuma ta sadda kanta kasa Tana hawaye rungumota yayi jik

insa ya ce "Baki hakura ba kenan"Girgiza Masa Kai tayi tana goge hawayenta ta ce "Dan Allah kayi hakuri Ka rage damuwar Nan a ranka Tana sakani Cikin wani Hali sainaga kamar ni nayi maka wani Laifin ne ita Kuma Aunty amera addu'ar ka take bukata a halin ya

nzu fiye da komai Allah ya jikanta"Yana goge Mata hawaye ya ce "Ameen my Mamy Insha Allahu Zan rage daga yau"wayarsa ce tayi ringing Yana Dauka daga Bangaren ammy ta ce "Babana lafiya meya hadaka da Zahra kake Mata gaba"Sorry ammy wlh ba abunda ya hadamu k

awai fahimtata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login