Showing 150001 words to 153000 words out of 161911 words

Chapter 51 - AUREN WATA TARA COMPLETE

18 Oct 2026

810

da ciwon Kai yake ya rame Sosai gashi yaki yaje asibiti Ammy ko i

tama duk hankalinta ya tashi ganin yanda beloved son din nata ya koma ita kanta batasan md Yana yiwa Zahra har irin wannan son ba sai yanzu lallashi ba irin Wanda batayi Masa ba Amma yakiji Baba tsoho ko Yana daya daga cikin gidajen Baki na md inda Ammy ta

saukesa kafin Shima su waiwayi jigawa wajen ahalinsa sun Bari dai a gama da matsalar Zahra Ranar da Zahra ta cika sati ukku da tafiya idan ka kallesa saikayi Masa kuka saboda yanda ya firgice kamar ba mr MD billonia ba matashi da kudi Ranar ji yayi baza

i iya jure rashin Zahra ba saboda yanda yakejin zuciyarsa kamar zata tarwatse a daddafe ya Kira chuchu a waya Koda tazo saida tayi hawaye ganin yanda Yayan nata ya zabge Address din garin da suka Kai Zahra ta basa tare da fada mashi drivern da ya kaisu bai

yi wata wata ba ya Kira drivern a tare da jabir suka tafi garinsu batsari Wanda tafiyar sirri sukayi Allah yasa Drivern ya gane Gidan Koda sukayi sallama da bappa ya fito ganin Baki ne ya sanyashi masu iso har cikin gida Md kanshi Kasa ya gaishesu Har baba

da yake zaune baba ya Gane jabir cikin girmamawa suka gaisa Yana tambayar jabir ya mutanen gidan sannan yayi mashi godiya akan Abunda yayi mashi Lura da shine baban Zahra ya sanya mD Kasa had'a ido biyu dashi dakyal jabir ya iya bude Baki ya ce "Baba Da

man magane ce tafe damu akan Zahra"Inajinku wace magana kenan"Baba ya fad'a"saida jabir yayi Jim kafin ya. Dago ya ce "Daman hakuri ne muka zo mu Kara Baku akan Abunda ya faru Dan Allah Baba kuyi Hakuri wannan abokina ne Kuma shine mijin Zahra baban yaran

shine mukazo mu Kara Baku hakuri "Kallon md baba da bappa sukayi kafin Bappa ya ce "Allahsrk shine yaron kenan To Ai komai ya wuce Hakuri an Riga anyi d'an Adam ai baya wuce rubutun Allah duka abunda ya faru ya faru ne a bisa kaddara da Kuma rabon yaran Na

n dan haka daga bangarenmu ya wuce yaro tunda dai ba Zina sukayi ba Aure sukayi har aka haifi yaran ta hanyar sunna kaga ai komai yazo da sauki "saida ya md ya sauke boyayyar ajiyar zuciya "Baba Shima cewa yayi "Ya wuce Allah yafe Mana Tare "Ameen baba mun

gode jabir ya fada shiru sukayi kafin Jabir ya ce "Sai magana ta gaba baba yace kuyi hakuri Dan Allah ku mayar Masa da Zahra saboda Yana sonta Kuma ba rabuwa sukayi ba "nannefa baba ya murje ido ya ce "baisan wannan Zancen ba "Magiya Jabir ya dingayi Shim

a md ji yake kamar zai fashewa baba da kuka cike da magiya ya ce"Dan Allah baba kuyi hakuri ku yafemun wlh tallahi in son matata Dan Allah baba kuyi hakuri ku maidomun ita karku rabamu "Saida MD ya bawa bappa tausayi Kallon baba bappa yayi ya ce "Meyasa z

akayi haka Yusufu kaida bansanka Da tsauri ba Kayi hakuri a barwa Allah lamarin Nan Karka shiga lamarin aure tunda kaga Allah shine ya hadasu tun farko dukda Bata shara'a a ba akayi abun to me zai Hana abar Masa sauran yayi ikonsa Dan Allah kayi hakuri ka

janye fushin Nan Karka shiga ka zak'e cikin lamarin tunda ba a asan Abunda Allah zaiyi gaba ba"Numfashi baba yaja kafin yayi shiru saikuma ya dago ya ce"Na janye fushi na ka nemu yarda a wajenta idan ta amince ba matsala saiku sasinta Allah ya zab'a Abunda

yafi Zama alkhairi"wata irin ajiyar zuciya mD ya sauke kafin ya dago ya dinga jerawa baba addu'oi Sosai ya shiga yiwa baba godiya yanda kasan yayi Masa albishir da gidan Aljanna"Jabir ne ya ce"Tana ciki ne bappa"a a a kanwar mahaifinta ta tafi da ita kat

sina yanzu Tana katsina ita da yaran"Cikin sauri MD ya dago ya ce "Bappa Dan Allah bamu address din gidan da take Dan Allah"Murmushi bappa yayi ya ce "Kai jikannan nawa ka cika azarbabi to bari Nak'i fad'a maka tunda dai Daman kwacen amaryace zakamun "Dan

Murmushi MD yayi Yana Kasa dakai Yana Sosa keya"Shidai baba shiru yayi Jabir ne yayi dariya ya ce "A a a bappa ai kayi mata tsufa"Saida suka danyi barkwanci kafin Baffa ya Basu address din gidan Ba yanda baiyi dasu ba Su tsaya ko fura a Dama musu Amma suka

kiya saboda saurin da MD yake su wuce katsina kudade bandir biyu md ya bawa su bappa Amma sukaki amsa ba irin yanda baiyi dasu ba Amma suka ki amsa suka kafe ba yanda ya iya sai maida su yayi a yammar driver ya wuce dasu katsina sai Bayan magrib suka Isa

garin katsina salla kawai sukayi suka wuce Unguwar su mama habi dake Bayan high court Basu wani Sha wahala ba Wajen gane gidan almajiri suka tura suka ce ana sallama'bayan fitowar Almajirin ya ce "ance wai wa ake nema"Mamy"MD ya fada jabir yayi sauri ya c

e "Kace Zahra ake nema"Kallon md yayi ya ce "waya santa da Mamy in Banda Abunka "Dukna riikicene shysa wlh jabir bakasan irin son da nakeyiwa yarinyar Nan ba shiyasa"Dariyar mugunta jabir yayi ya ce "Au Haba yaushe ka Fara son matar Wata tara Kuma tsaki md

yaja yace"Kaga matsalata dakai kenan to wannan dai matar ta Har Abada ce Babu rabuwa "Dariya Jabir yayi fitowa Almajirin yayi ya ce "Ancewai Bazata fito ba "OMG"MD ya fada"Jabir ne ya ce "zasuyi tunanin wasune ko samari kaga Tana da aure bazasu Bari ta fi

to ba fa"Eh Kuma hakane "MD ya fada kafin ya kalli yaron ya ce "ka ce "Baban su Y'an ukku ne yazo"To Almarin ya fada Yana komawa"Ajiyar zuciya mD ya sauke Dan yaji Dadi koba komai ana tsare Masa igiyar aurensa Fitowa Almajirin yayi ya ce "ance wai ku shiga

"Ajiyar zuciya mD ya sauke jabir ya bawa Almajirin 2k kafin su shiga Cikin gidan da a palourn Mai gidan aka saukesu Kafin mama habi ta shigo da hijab dinta dafara'a ta tarbesu suka gaisheta Cikin girmamawa Bayan ta zauna ta ce "Kuyi hakuri an tsaidaku waje

bamuganeku ba saidaga baya"Murmushi jabir yayi ya ce "Ba komai mama"Madalla Diyarta ce to shigo ta aje musu ruwa da lemo Bayan ta gaishesu ta juya mama habi ta ce "Ku Sha Mana"Jabir ne yasha MD baisha ba "Shiru sukayi kafin mama rabi ta ce "koba a fada ba

nasan ga Baban yaran nan ganin Kama karara Masha Allah"ta fada Tana Kallon md "Murmushi Jabir yayi ya ce "e shine mama. Daman zuwa mukayi mu Kara Baku hakuri"A Haba yaron Nan hakuri Kuma na me ai komai ya wuce anzama d'aya tunda harda zuri'a Allah dai ya

Raya Ameen MD ya fada Kasa Kasa kafin jabir ya ce "Mungode Daman daga Chan batsari muke munje mun karaba su Baba hakuri Kuma sun hakura harma sun amince da maganar Komawar Tata suma suka fada Mana Nan inda take.akan muzo Kuma mu nemu amincewarku. Da Tata s

hine mukazo Mama Dan Allah ayi hakuri ta koma dakinta wlh Yana sonta Kuma insha Allah zai riketa da Amana"shiru mama tayi kafin ta dago ta ce "Ai ba matsala tunda Sun amince muma mun amince Allah zaba Abunda yafi alkhairi saiku nemu yarda a wajenta Bari na

shiga na turo muku ita "ta fada Tana mikewa ta shige ciki"MD jinshi yayi Cikin wani irin farinciki Jin abun ya Fara zuwa dasauki Koda mama taje ta fadawa Zahra wadanda ke tafe Saida tayi mamaki mama ce ta ce "tashi ki Mike kuje da yaran ku gaisa ko"Zahra

kamar zatayi kuka ta ce "Dan Allah akai mashi yaran ni ba sainaje ba"Dukda Tana da bukatar ganin nasa"Tsaki mama habi taja ta ce "Da Allah tashi kibani waje bansan shiririta kije ku gaisa mutanen su taho tundaga kaduna saboda ke Dan iskanci Kiki zuwa ku ga

isa maxa tashi kije kafin ranki ya b'aci"ganin ran mama ya b'aci ya sanyata mikewa da Akhbar a hannunta Ta fito MD suna zaune Yar mama habi ta kawo mishi yaran su biyu Amar da Little Sosai ya yaba yaran sun Kara kyau da wayo har Dariya sunayi sunyi bul_bu

l gwanin ban sha'awa Duka biyun ya dauka Yana musu Dariya ya ce "oyoyo my kids I really miss you so much please karku sake nesa da daddynku zai shiga wani Hali"Daidai shigowar Zahra Cikin hijab sab'e da Alkhbar tunda ta shigo palourn MD ya kafeta da kallo

Bako kiftawa yanajin wata irin kauna da soyayyarta na Kara fusgarsa ji yake kamar yaje ya rungumeta Harta zauna Yana kallonta a sace Zahra ta kellesa idonsa suka sartse Cikin na juna sauri tayi ta kauda Kai gabanta na faduwa nauyayyar Ajiyar zuciya mD ya s

auke yanajin wani irin sanyi na ratsa sa shiru Zahra tayi Bata tanka ba jabir ne ya ce "Hajiyarmu ina yini Kodai har yanzu fushin ake damu nidai ina bada hakuri Kuma ina wanke laifi na "Dan Murmushi Zahra tayi ta ce "Ina yini Yaya jabir anzo lfy"lafiya qal

au ya triple dinmu "Alhmdulillahi"ta fada Kasa Kasa Tana wasa da zoben hannunta"MD bai daina kallonta ba kamar zai cinye ta Biyun ya aje kan sopa kafin ya koma kujerar da take kamar zai shige jikinta saurin matsawa tayi tare da satar kallonsa suna hada id

o ta Galla Masa harara"Mika hannu yayi ya amshi little dake Zillo a hannunta Ajiyar zuciya ya sauke tare da kissing din little ya ce "i Really miss you my All above I love you so much my beloved daughter ina sonki Sosai takwarar Ammy na Kuma Favorite wife

d'ina gaki Kuma daughter ta "ya fada Yana mata Dariya kamar tasan me yake cewa tahau Masa Dariya hada Zillo "Tabe Baki Zahra tayi Tana Shirin mikewa ya ruko hannunta juyowa tayi tare da tsatsaresa da Dara daran idanunta tare da juyasu ta ce "ka sakeni me

ye haka gaban mutane da Allah"ajiyar zuciya ya sauke Yana kallonta ya ce "Please ki dawo ki zauna Dan Allah muyi magana wajenki nazo"Kamar bazatace komai ba saikuma ta ce"Inajinka Amma ka.sakeni"Ai na sakeki nasan tafiya zakiyi Dan Allah ki dawo ki zauna"

to ka sakeni Mana ha a saikace wata yarinyar nace ba inda zanifa "sakinta MD yayi ganin Bata tafi ba ya sanyasa sauke ajiyar zuciya Bayan ta zauna Dan nesa dashi Tana wani hade fuska Cikin kakkausar murya ya Fara magana Cikin sigar lallashi da kwantar da K

ai ya ce"Dan Allah Dan girman Allah Mamy kiyi hakuri ki janye fushin da kike Dani wlh nayi regrade duk Abunda nayi maki bana daidai ba Ina sonki Mamy son da bazan iya kwatantashi da komai ba son da bantaba yiwa wani mahaluki irinshi ba Mamy shigowarki rayu

wata nasan abubuwa da Dama Wanda a chan da ban sanshiba Mamy shigowarki rayuwata nasan meye so inasonki son da ni kaina bazance ga adadinshi ba Ina sonki fiye da yanda nake son kaina Mamy Dan Allah kiyi hakuri ko bazaki Soni ba yanzu Ina neman alfarmar da

kidawo gareni mu shimfida sabuwar rayuwa irin ta kowasu ma'aurata mu gyara kuskuren da mukayi a baya mu tarbiyantar da yaranmu sannan mu Basu Kula irin wacce kowasu iyaye ke bawa yaransu Dan Allah Mamy Ina kaskantar da kaina akan kiyi hakuri ki dawo garen

i insha Allahu zan koya Miki Sona da kaunata Zan Kula dake Zan soki na kaunaceki na baki duk wace kulawa Dan Allah ki ceci rayuwata please Mamy"Sosai Zahra tayi mamakin Jin furuccin nashi a gareta wai yana sonta tunani tayi bafa ita yake so ba kawai saboda

yaranshine da yake mugun so shekara goma bai samu haihuwa ba shine zaiyi mata wayau yace Yana sonta ta koma gareshi Ya wulakantata shida matarshi karshema Kila ya saketa ya kwace Mata yaran tunanin wanannne ya dira tsam a cikin zuciyarta Sosai taji ranta

ya b'aci lokaci guda

،

mikewa tayi tare da kallonsa ta ce "zamana da Kai ya Kare babushi bazan koma gareka ba ka koma chan Wajen matarka Amma ni Nan da ka gani karka Kara tunanin wai zan koma maka inma mafarki kake. Ka farka kagama tafiyata"Tana game fadar

haka tabar palourn Cikin sauri tanajin wani daci da zafi a cikin zuciyarta Jin yaudarar da suka shirya Mata a cewarta"Tashi MD yayi Cikin tsananin tashin hankali ya bita, tuni tabar palourn dafe kanshi da yayi matukar Sara Masa yayi ya ce "Innalillahi wa

Inna ilahiraji'un "Ganin Yana Shirin faduwa ya sanya jabir yayi sauri ya tallabeshi ya zaunar dashi Shi

kanshi jabir baiji dadin Abunda Zahra tayi ba yarasa wata irin bakar zuciya ce da ita shi har yanzu baiga wani laifin zo a ganin da MD yayi Mata ba take

wahalar dashi Haka idan taimakonema ita MD ya Fara taimaka bataji laifin kawarta ba saishi mamakin MD yake Akan wani irin so ne wannan yake yiwa Zahra da har take Masa irin wanna wulakancin Yana shanyewa Wanda tunda yake bai Tana tunanin akwai macen da

MD zaizo tayi Masa haka ba matanda rububinshi sure Amma ya like yarinyar karama na Shirin nakasashi "MD. Wani irin zafi yakeji a cikin zuciyarsa kamar zai fashe da kuka ya kalli jabir ya ce...........

✍

️

*Domin magana da marubuciyar 07026166536*

🇳

🇬

*Happy Independence day*

🇳🇬

_*Miss Hajo ce*_

🤙

[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy:

👩

‍❤

️

‍

👨

*AUREN WATA TARA*

👩

‍❤

️

‍

👨

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*

( Miss Hajo)

*Ga Mai Bukatar sayan complete doc na book dinnan a t

untubeni akan wannan number 07026166536*

*FINALLY THE END

الحمدلله*

💃🏾

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

_BONUS PAGE_

😝

🅿

️

................*99 & 100*

Ta Ce "Bani da bakin da Zan yi amfani dashi Wajen gode make mijina kayimun komai a rayuwa ka bani fa

rinciki Nagode Nagode Allah ya saka alkhairi Allah ya faranta maka fiye da yanda ka farantamun "Ta karasa fada cikin kukan farinciki "murmushi kawai MD yayi nayajin kauna da soyayyar matar tasa na fusgarsa ya Ce "Ameeeeeen my beloved wife ke Kika Fara bani

farincikin da bantaba tsammaniba farincikin da dukiya ta suka kasa sayamun kome nayi maki ban Isa na biyaki tukuicin abunda kikayimun na alkhairai"Sosai Zahra tayi dokin motar murna da fainciki ba irin Wanda Bata nunawa mijin Nata ba addua ko ya sashi Kam

ar me Daren ranar Zahra ta bashi hadin kan da Bata taba bashi irinshi ba ta jiyar dashi dadi Sosai..satinsu biyu da tarewa Wanda irin love din da suke zubawa mutum yaji Saiya girgiza a satinne aka shirya tafiya jigawa gabaki daya suka tafi baba,ammy,Zahra,

MD,sai triple kasancewar ta fly sukabi basuyi wata tafiya ba suka Isa Sosai baba yayi mamakin cigaba da sauyin da aka samu a garin ya habaka Sosai Kamar ba garin ba dakyal ya iya gane Unguwarsu Kai tsaye Gidan k'aninshi mai biya mishi suka nufa Ai Ganin ba

ba Saida Alhaji tukur ya tsorata shida matarshi acewarsu fatalwace dakyal suka yarda shidinne Rungume juna sukayi Sosai alh tukur ya Sanya kuka ya Ce "Yaya Kaine Daman Ashe da raban xamu sake ganawa kenan karyace akayi Mana akace an kasheka "Baba na hawaye

ya ce"nine da kaina tukur"kafin Kace me Yan uwan baba sun cika Gidan kowa yazo sai yayi kukan farinciki mutumin da daukarsu ya mutu kasa da shekara ashirin da biyar su ganshi yanzu dole suka girgiza Kuma cikin ikon Allah y'an uwan baba duka suna Nan da ra

nsu Basu mutu ba"nanfa Kuma aka Fara yiwa Zahra kallon Mamanta Saida baba yace musu ba ita bace zaiyi musu bayani"A katoton parlourn Gidan aka saukesu Dan ba laifi k'annan baba dukansu a da chanma da halin su bare yanzu da cigaba yazo Shima babban gidane N

an mutane akayi ta kawo gaisuwa mutane duk sun cika Gidan Bayan ankawo musu Abun tarbar Baki daya daga cikin K'annan baba alh Habu ya ce"Yaya muna jinka kayi Mana bayanin Ina ka shige kaida Zahra tsawon Shekaru"Nan baba ya kwashe labarin komai ya Basu ciki

har da haduwarshi dajikarshi da Kuma rasuwar y'arsa da irin taimakon da MD yayi masa "Salati kowa keyi masu kuka nayimasu tsinewa mudan nayi Ya"Yan Yan uwa ko Mata da iyaye sai rungumar Zahra suke Sosai kowa yayi mamakin Jin mudan shine ya kashe Hajiya s

aratu(kakar zaha?)Sannan yayi kokarin kashe Dan uwansa godiya Sosai aka shiga yiwa Ammy da MD Alh tukur ne ya Ce "Haba biri yayi Kama da mutum Amma Abun Nan yazo da mamaki mudan fa dashi akayi suturar Hajiya saratu ya dinga kukan munafurci a fuska yafi kow

a shiga tashin hankalin ance Mana y'an fashin da suka kasheka Suka tafi da gawarka da Zahra har adduar ukku da sadakar bakwai data arba'in Saida Akayi muku Ashe dai da sauran kwananku a gaba gaskiya mudan bazai gama da duniya lafiya ba Haba kenan shiyasa d

a aka tambayesa dukiyarka ya Ce Babu abunda naka Dake hannunshi duka ka amsa sannan barayin sunkwashe komai haka kawai muka kyalesa saboda mu Kai ka fiye Mana komai bamu kuma waiwayarsa Akan dukiyarka ba saboda a ganinmu Fatima maringanyiya itace magajiyar

ka fiye damu to Bata Nan da Tana Raye ne ma a lokacin zamuce saimun kwatar Mata hakkinta ba ayi shekara biyu da faruwar Haka ba Mudan ya kwashe komai nasa Dake Nan har Gidan daka saya Masa ya sayar tare da matarsa da y'arsa sadiya da tun kana Nan aka haife

ta suka tashi ya Ce wai ya samu wani babban aiki a kaduna Babu Wanda ya kawo komai akai mukayi mishi fatan alkhairi Tunda ya komai kaduna mudan mudashi ko a waya Sosai hankalinmu ya tashi kasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login