Showing 12001 words to 15000 words out of 161911 words
mata gata dai ba wata babba ba Dan a lokacin bazata wuce 18 years ba Saidai abunda ya basu mamaki ta rik'e sunanta Zarah.
Saida Zarah ta s
hekara guda gidansu Malam batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad'i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure
.
ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k'aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen ungu
war sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta
aminiyarta d'aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d'aya Hauwa'u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata
ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna.
"ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka
samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi .
kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Jum
a a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce " .
a kira mata Malam "haka ko akayi shigowarshi d'akin tayi daidai
da haifo santaleliyar y'arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya.
Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d'iyar tayi cikin k'arfin ta ce " mik'omun naga kyautar da Allah yayi mun"
mik'a mata y'ar akayi
Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y'ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce "Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai
y'ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya mun
ke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki "
tari ne yaci karfinta Mik'awa Malam y'ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa " ga Amanar y'ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka za
me mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan "
a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid'imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce "me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace ha
ka haihuwar take kowa haka yakeji"
Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce "bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce "Ga Amanar y'ata nan A hannunku ku rik'emun ita amana sannan
ku bata tarbiya nasan zaku iya ".
" Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce "Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y'arki" .
Kallon y'ar kawai take tana tari cikin k'arfin ha
li ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik'awa Malam ta ce .
"idan y'ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da
zan maku Bayani ya K'ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k'ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika.
Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta
Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y'arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d'inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimpl
e dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta.
Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y'arta da taci suna Asma'u
ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad'a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah ".
kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma'u ta had'u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata j
injinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara
biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bak
anikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin akan baiyi Aure ba yaci yayi Aure yanzu.
Inda ya hadu da Wata zawara rabi'atu da yaranta biyu a lokacin kamar mutuniyar kirki haka ya a
ureta tare da yaranta duk yanda zaiyi saiya ciyar dasu Inda Ya maido da Zarah gidan Wanda a lokacin ta nuna Duk d'aya ne a gaban idonshi zata nuna tafi kowa son Zarah Inda Bayan idonshi irin azabar da take gana mata kare baici Malam bai tab'a ganewa ba sab
oda Zarah ta tashi da wani irin hakuri kome za a mata bata tab'a fada masa ba.
ta haifi yaranta Biyu da Malam Safiya sai kuma khairat Azaba sosai take ganawa Zarah kasancewar ta sameta yarinya mai hakuri Wanda Malam baisan da hakan ba saidaga baya ya fa
himta A unguwar ba Wanda baisan irin wahalar da rabi keba Zarah ba.
Malam ya tsayewa Zarah Karatun boko da na arabi Zarah yarinya ce mai baiwar kokari Dan kokarinta saidai a kirashi na baiwa saboda yanzu za a ayi yanzu za a kwashe duk karatun da tayi
tare sukayi da Asmy Dan sun zama kamar y'an biyu kuma maman asmy ta rik'e Amanar da aminiyarta ta bata danma Mama Rabi dake azabtar da ita Yaran Mama Rabi duk sun lalace saboda Rashin tarbiya da bata basu ba khairat ce cikinsu kawai ta fita zakka zarah tu
nda ta taso ta fara perioud take shan wahala dan duk wata saidai akaita ayi mata allura irin fita daga hayyacinta da take har suma take sannan tana da larurar tsananin sha'awa mai karfi wanda wani lokacin abun ya taso mata saidai a bata maganin bacci wanda
shawarar dr din da aka taba kaita wajenshi ne dan ya bata magani ya basu hakan .
wannan kenan.
*FCT ABUJA*
Manyan motoci ne na gani na fad'a Sunkai Sha biyar jere suke suna tafiya cikin gudu saboda bikin da za a gudanar na bud'e shahararren sabo
n shopping mall d'in da ya amsa sunansa.
Wajen shake yake da manyan mutane tun daga kan y'an kasuwa "shahararrun masu kudi da sauransu *MD SHOPPING MALL*naga an rubuta a saman ginin yanayin yanda akayi rubutunma kad'ai ya isa ya sanyaka Yin k'auyanci
.
Waje ne da ya tsaru da kyau saika rantse ba k'asa Nigeria kake ba saboda yanda zakayi mamakin irin dukiyar da aka zuba a ginin ma b'ata lokaci ne.
Nan aka fara gudanar da bikin bud'e Wajen Bayan jawabai daga bakin manya da shahararrun y'an kasuw
a Inda akazo ga jawabi wajen mai gayya mai aiki wato mamallakin wannan shahararren wajen watau Mustapha Dikko *MD* .
"hamshak'e ya ke a wajen banyi Tunanin yana jin hausa ba saboda kwata_kwata baiyi kama da hausawa ba Fari ne sosai kamar bature ko kum
a ba indiye Sanye yake cikin bak'ar coated wacce ta amshesa ta kara fito masa da kyau da kuma hasken fatar sa kallo d'aya zakayi masa kaga asalin ba india
sanye ya ke cikin siririn farin glass sumar kan nan nasa lufluf gwanin sha'awa da burgewa ga k
uma sajenshi Dake zagaye da kyakyawar fuskarsa daya kara kayatar da tsananin kyaun da Allah yayi mishi.
a gaskiya ni kaina saida na rude da ganin zubi da kyau irin na wannnan bawan Allah zan iya cewa tsawon rayuwa ta ko a film bantaba ga namiji da ky
au irin haka ba duk inda karshe da baiwar kyau take tofa Yakai a kirasa da komai Dan guy din ya had'u karshen had'uwa (lol).
Daga zaunen da yake batare da ya mik'e ba ya amshi abun maganar tare da Fara jawabi cikin zazzak'ar muryarsa Yanayin yanda yake.
maganar saika d'auka wani sautin wak'a ne mai ratsa zuciya ke tashi.
baiyi wata magana mai tsayi ba saboda shi daman Chan ba mutum bane mai fiya son magana da yawa ba Hasalima yanzu a k'agare yake A gama taron nan ya tafi dukda dalilinshi kowa yazo w
ajen amma ya k'agu saboda hayaniyar da ake a wajen dan shi ba mutum bane mai son hayaniya .
camera ce A kansa ta gidajen television da dama kowa so yake ya d'auka jawabin harya gama ana haskasa da camerori.
"Tsaki yaja yana kauda kai Dan ba abund
a ya tsana irin taron jama a "
jabir ne dake kusa dashi ya rad'a masa a kunne"Sorry bloody Dan Allah yau karkayi mana halin naga ka fara tsaki ka.daure har a gama bikin nan kasandai duk Wanda yazo wajen nan kai yazo tayawa farinciki".
Lumshe ido MD
yayi tare da bud'esu a hankali batare da yace uffan ba kamarma ba dashi jabir yake magana ba hakan bai damesaba saboda idan da sabo ya saba da halin aminin nasa Shidai burinshi Indai bazai kwafsa musu ba ya jira har agama falilllahil hamdu".
Ba aja
wani lokaci ba aka gama komai Inda MD ya Mike Security na take masa baya Sunkai su 30 yanda kasan wani president .
security gabansa haka bayansa ma sai kakkaresa ake nan fa y'an jaridu suka shiga d'aukar rahoto har ya isa motarsa Inda suma suka shiga mo
tocinsu A motar ma tunda ya shiga Danna waya ya ke
"Jabir ne dake gaban motar da juyo tare da tambayarsa ya ce " Ranka ya dad'e ina muka nufa"Kamar baya da shirin magana Ya ce "Airport" Ya fad'a
yana cigaba da latsa waya kamar bashi yayi maganar ba "Ji
n haka ya sanya jabir ganowa Kaduna Zasuje kenan ".
Ko a Airport d'inma saida nayi mamakin irin yanda mutane ke kallonsa y'an mata har Tuntube suke suna cewa.
" wlh shine MD ne "wata har tsuma take tare da Rungume y'ar uwarta ta ce " Alhmdllh Gaskiya
yau rakiyar nan munzo a sa'a ganin mutumin Dan ban tab'a tunanin tab'a gani ba a rayuwa yau nagansa karkiga yanda nake da muradin ganin guy d'innan cikin Sauri ta d'auko wayarta tare da shiga snap daga nesa ta dinga daukoshi Dan tasan ko giyar wake ta sha
bata isa ta tunkari wajenba yanda security d'inshi ke zagaye dashi.
Ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga Kaduna koda ya isa Kaduna Chan dinma haka ne Tsaki ya dinga ja shi d'aya saboda a Rayuwarshi ba abunda ya tsana sama da Kallo da kuma yanda y'an mat
a ke rudewa idan suka gansa Har suka isa Unguwarsu da ke G R A ya na Jan tsaki .
Horn biyu sukayi mai gadi ya Wangale musu Get d'in Aljannar duniya kenan gidane katoton gida mai girman gaske fad'ar kuma kyau da tsaruwar gidan ma b'ata baki ne Dan saim
u cinye page Ukku zaku iya kwatanta gidan da gidan indimi.(lol)
Motoci biyar Duka suka danno gidan kai tsaye Ta tsakiyar ita ce tashi A hankali yake fitowa daga motar bayan ya fara ziro kafufuwanshi dake shanye da hadadden cover shoes koda ganin takalmi
n kasan ba na kananan mutane bane a haka harya karasa fitowa daga motar.
kamar Wanda baison taka k'asa ya fara tafiya securities d'insa ne suka biyo shi da hannu ya musu nuni da su dakata Kai tsaye hanyar Part d'in mahaifiyarsa Ya nufa Kafin ya k'ara
sa shiga Yaga fitowar Chuchu da gudu Tare da rugowa ta fad'a Jikinshi Sosai nayi mamakin yanda Ya sakar mata murmushi Wanda Ya Kara fito masa da baiwar kyawun da Allah yayi mishi ashe daman idan yayi fara'a yafi kyau yake tamke fuska.
"Shima Rungumeta y
ayi Tare da shafa bayanta ya ce " I'm very glad to see you my Beloved sister "Cikin farinciki da muryarta Mai kama da ta masu iyayi ta ce " me too yaya nafi kowa farincikin ganinka tunda akace ka taho nake ta zumudi" Ta fad'a ta na kama hannunsa Tare da ja
nshi Dan su shiga ciki ta ce "Yaya muje kaga irin abubuwan da na shirya maka Dafota yayi kamar dafayya tun a hanya ta shiga fara zuba masa surutu Wanda har ya fara isarsa har suka isa tafkeken palourn ta na zuba masa surutu.......
β
πΏ
*07026166536*
*G
AWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE.
π―
ββ
οΈ
πππ
*
1, *MU GANI A ΖASA...*
π₯
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ΖWAI..*
π₯
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*
π₯
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
π
_Mrs Bukhari_
5, *A
UREN WATA TARA*
π©
ββ€
οΈ
β
π¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda hu
Ι
u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda
Ι
aya N300
*DOMIN TURA KUΖIN KAI TSAYE*
π
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya
π
0810 43
3 5144
Masu tura katin MTN
π
0814 179 9224
Ζ³
an Ζasar Niger zasu tura nasu anan.
π
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda hu
Ι
u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda
Ι
aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.*
π₯
π₯π₯ππ©
ββ€
οΈ
β
π¨
~share please ~
*_Miss Hajo ce_*
π€πΏ
[8/26, 16:46]
β€
οΈ
β€
οΈ
β€
οΈ
:
π
*AUREN WATA TARA*
π¨
ββ€
οΈ
β
π¨
MALLAKAR
*Hajara L Sadeq*
π
Ώ
οΈ
.........*11 & 12*
A palour ya tarar da mahaifiyarsa abar kaunarsa matashiyar mata da
bazata wuce 55 years ba Amma Hutu da gayu ya boye shekarun.
sanye take cikin shigarta ta alfarma ta manyan mutane Idanunta sanye cikin farin glass Saida na K'are mata kallo naga sak kamarsu d'aya da MD har farin wacce daga ka ganta kaga Ba India Cikin
farinciki ta tari Dan nata hug din juna sukayi suna farincikin ganin juna ta ce "Sannu da zuwa Baba na kazo lafiya"
"Alhmdllh Ammy na sameku lafiya" Alhmdllh ta fad'a ta na kama.hannunshi kamar wani yaro kan sopar da take suka zauna Kallonshi ta yi ta
re da kama hab'arsa ta na duban fuskansa ta ce "Baba na ya naga ka d'an rame".
kanshi ya d'ora bisa kan kafad'arta ya ce "Ammy idonki bai gane maki daidai ba ba wata rama fa da nayi"
Chuchu ce ta shigo da tilin kuloli a hannunta mai aikinsu na biy
e da ita da sauran Ajewa tayi gabanshi ta ce .
"Yaya na kazo kaga irin delisiou din da na shirya maka" Ammy ce ta ce "iyye to Auta bakin bari ya huta ba sai yazo ya ci"
Diddira kafa ta fara cikin muryar shagwaba da sangarta ta ce "umm umm ni dai wlh
yanzu nakeson yaci basaiya huta ba "
Kamo hannunta yayi tare da zaunar da ita gefenshi ya ce "Caml down chuchun yaya bud'e naga abubuwan da aka shiryamun"
Cikin murna ta mik'e tare da bude masa d'aya Bayan daya Abinciccika da snack Sunkai kala go
ma shi abunma saida ya so bashi Dariya "Ya ce.
" Auta yanzu duk ina zankai wannan ai saikuma cikin Yayan naki ya fashe"Cikin shagwaba ta ce "Nidai yaya saikaci Duka "
Yasan halin y'ar rigimar Autar tasu hakan ya sanyashi d'aukar spoon Duka abincin
yabi ya d'andana lumshe ido yayi Dan taji dad'i tare da jinjina mata good da hannu ya ce .
"Muje ki amshi tukuicinki Auta abinci yayi dadi" Tsalle ta daka tare da cewa "yeyeye yaya na muje Daman nasan zakaji dad'in abincin " .
Ammy Ce ta ce "Daman na
san ba banza ba wannan rid'in da kike "
Juyowa tayi tare da yiwa Ammy gwalo ta Ce "Aidai yaya ne " Dariya Ammy tayi tare da girgiza kai Had'in kan na yaran nata sosai yake yi mata dad'i A daki MD ya yiwa Chuchu kyautar had'ad'd'iyar Zoben gold mai matu
k'ar tsada tare da turarruka masu k'amshi da tsada daman ita ya sayowa Sannan ya bata Rafar y'an dubu dubu zo kuga murna wajen Chuchu sai sanyawa Yayan nata albarka ta ke ta na "tsallan murna "
dak'yal ta samu ta bar Yayan nata ya huta Bayan Ya fito d
aga wanka Wanda saida ya d'auki dogon lokaci jikin mirror yaje Wanda shake yake da mayuyyuka da turarruka kamar mace
"nan ya shiga shafa mayuyyuka yanda yake shafa man kamar mace "
K'ank'anin kaya ya sanya Tare da hayewa Gado Dan yana buk'atar huta
wa Tunda ya dawo daga America bai