Showing 129001 words to 132000 words out of 161911 words
ce "Lafiya ammy" Da sauki Zahra ce Zata haihu muka kawota sunce bazata iya haihuwa ba sai anyi mata cs shine muke buk'atar sa hannunka"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ammy yanzu tana ina Ina ne za
a sa hannun"Sosai MD ya rikice ya rude Shi ya sanya hannu kuma shi ya bada jininsa kasancewar group o garesa suna gani aka shiga Theater room da zahra sosai Chuchu ta fashe da kuka Ganin kamar zata rasa kawartata Ammy ma hawaye take tana addu'ar Allah sa
ayi aikin lafiya MD ma addua kawai yake hankalinshi a matuk'ar tashe yake "Ba ayi 30 mminutes ba sukaga fitowar dr D'auke da jariri a hannu fuskarshi d'auke da Fara'a suna ganin haka suka Kallesa Ammy ta ce " An sauka"Alhmdllh Dr ya fad'a yana mik'a mata j
aririn"Amsar jaririn Ammy tayi "Allahu akhbar Allahu akhbar" kawai Ammy ke fad'a ganin yau ita ce rik'e da jinin MD a hannunta shiko gogon har yanzu gaba d'aya hankalinshi yana kan ga wani hali zahra ke ciki Nurse biyu suka ga sun Kara fitowa rik'e da wasu
jariran a hannu"sai sannan MD ya kusa daskarewa ganin sun nufo su da Yaran Daya daga cikin nurse ta mik'awa MD.jaririyar ta ce "Congratulation Sir Allah ya raya" d'ayar kuma ta mik'awa Chuchu da itama ta daskare a wajen Kallon y'ar MD Yayi ya kalli saura
n yaran dake hannun Chuchu da Ammy kamar Wanda bakinshi yayi masa nauyi ya ce "Kuna nufin Duka yaran nan aka ciro kuma Duka nawa ne" Murmush
i nurse din tayi ta ce "Triple ta haifa gasunan Allah raya "farincikin da MD ya shiga fadarsa bata baki ne ji yake t
amkar a mafarki wai yau shine Allah yaba yara har Ukku baisan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zubo masa ba ya goge ya ce " Alhmdll.......
β
*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE.
π―
ββ
οΈ
π
π
π
*
1, *MU GANI A ΖASA...*
π₯
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ΖWAI..*
π₯
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*
π₯
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
π
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*
π©
ββ€
οΈ
β
π¨
_Miss Hajo_
Gud
a biyar 1k
Guda hu
Ι
u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda
Ι
aya N300
*DOMIN TURA KUΖIN KAI TSAYE*
π
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya
π
0810 433 5144
Masu tura katin MTN
π
0814 179 9224
Ζ³
an Ζasar Niger zasu tura nasu anan.
π
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda hu
Ι
u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda
Ι
aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.*
π₯π₯π₯ππ©
ββ€
οΈ
β
π¨
_*Miss Hajo ce*_
π€
[10/3, 7:
17 PM] Mother Mamy:
π
Ώ
οΈ
.........*85 & 86*
Amera koda isarta jikin dadynta ta fad'a ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah dad ku fad'amun me yake faruwa bansan abunda ya faru ba hankali na bai kwanta ba " Lallashinta ya dingayi akan ta nutsu ba komai ban
e ta Bari ayi bincikike tukwana washegari dak'yal ta Bari gari ya waye ba yanda Mamanta batayi.da ita ba akan ta Bari a bincika aji gaskiyar Lamarin ta kiya ta ce "saitaje gidan Ammy tunda shi tayi ta kiransa kusan 1 week baya dagawa abunda baitab'a yi mat
a ba " girgiza kai mamanta tayi ta ce 'Ai daman Amera na fad'a maki tun ba yanzu ba akan ki tsaya kiyi zaman Aure kwata kwata rayuwar da kika zab'awa kanki ba rayuwar y'a mace mai mutunci bace"da Allah mom Ni kibarni Naji da abunda ke damu na fisabilillahi
"ta fad'a tana yin gaba tana gunguni "Girgiza kai Hajiya Farida tayi ta ce "Allah ya kyauta"Dadynta ko zirga zirga kawai yake...k'arfe 7:am zaune suke a palourn Dagashi sai Ammy Bayan kiran gaggawa da tayi masa shiru yayi ya maida hankalinshi ga sauraron a
bunda take son fad'a masa fuska ba wasa Ammy ta ce " d'ago ka.kalleni babana"ba shiri ya d'ago yana fuskantar mahaifiyar tasa "Hannu Ammy ta mik'a masa ta ce " bani takardar Saki ukkun zahra "Lokaci guda MD yaji wani irin tashin hankali ya ziyarce sa a mat
uk'ar rude ya ce"Ammy saki kuma" Eh saki ko kana da wata maganar ne daman ba Dan ka saketa ka aureta ba,ba Dan ta Haifa maka d'a ko y'a ka aureta ba to ai burinka ya cika ta Haifa maka yara har Ukku kaga ko amfaninta a wajenka ya k'are dan haka ka saketa t
a kama gabanta itama taje tayi Aurenta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa "Cikin tsananin tashin hankali ya ce "Ammy kiyi hakuri kibar maganar nan please ni har yanzu Mamy matsayin mata ta take kuma haka zataci gaba da zama insha Allah please Ammy kiyi hak
uri kawai ki barmun matata kodan yaran nan Ammy kinsan d'an sai uwa please Ammy ina begging d'inki kidaina maganar sakin nan ba Ni Gaskiya bazan iya sakin Uwar y'ay'a na ba" ya fad'a kai tsaye "Sakato Ammy tayi tana kallon ikon Allah kafin ta tab'a hannu t
a ce " ikon Allah daman Kasan da ruk'on d'a sai uwa ka shirya rabata da Y'ay'anta ka kaiwa Matarka Matar so da.kafi sonta da kowa inbanda asirinku ya tonu to wlh baka isa ba saika saketa"Hankali tashe ya d'ago ya ce "Ammy Dan girman Allah ki daina maganar
sakin nan nifa bazan saketa ba period magana Zan zauna da ita na bata kulawa kodan yaranta Dan Allah Ammy naci darajan yaran nan"baka isa ba wlh watau nufinka Zama ka zauna da ita zaman Y'ay'anta lallai Babana kai harka isa ka zauna da zahra zaman Y'ay'a
nta zahra harta isa tayi zaman ,y'ay'a to bazata zauna dakai ba sannan zata baka Y'ay'anka kaje ka kaiwa duk ubanda zaka kaiwa ka kaiwa Amera uwarka ko iyayenta su rik'e maka y'ay'an amma.koni bazan rik'e maka su ba Tunda baka da mutunci sannan zahrar ma b
azata rik'e maka su ba bari naje na D'auko maka su sannan na k'ara ganin k'afarka a gidannan Zakaga mamakin irin Rashin mutuncin dazan maka tunda Haihuwarka nayi bakai ka haifeni ba " ta fad'a a fusace tana Mikewa"Cikin sauri ya yi Sauri ya riko k'afar zan
en Ammy Ya ce "Baki fahimce ni bane.Ammy Dan...bai k'arasa abunda yake son fad'a ba ta fusge zanenta cikin Sauri ta haura sama " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ya fad'a yana dafe goshinshi Daidai shigowar Amera d'akin a matuk'ar rikice "kallonta yayi ya
nda tashigo da itama d'in shi take kallo kafin ta karaso palourn cikin tsananin tashin hankali ta fashe da kuka tare da kama.hannunshi ta ce " Ka fad'amun Gaskiya MD me yake.faruwa Wasu Yara ne ake zancen an Haifa maka Bayan Banida masaniya ka fad'amun gas
kiyar cewar bakai bane wasune kawai suke.karya da yaranka ne"Ba karya bace Yaransa ne halak malak Shiya haifesu da Matarsa da ya aura kina Chan kina yawon tambadewa a jirgi harta haihu baki saniba ta Haifa masa Yara Ukku reras lokaci guda ko kina da abun c
ewa ne zakizo kiwa mutane hauka da ba abunda kika iya sai bakin kishin jaraba to alkadarinki dai ya karye Duka Asirin da kika masa ya sakesa yayi aurensa ya rabu dake saiki koma Chan k'asar tambadewar taki kici gaba da tambadewa a sararin samaniya "Hajiya
kaka ta fad'a tana shigowa palour" a matuk'ar rude Amera ta juya ta Kalleta kafin ta saki Hannun MD tanajin zuciyarta tamkar zata tarwatse ta ce "What sai kuma ta fashe da kuka ta ce " wlh Allah karya ne bazaiyu ba ,bazaiyu ba MD yayi Aure ya haihu da wata
,karyane ,ihu ta k'walla iya karfinta tana girgiza kai kamar zata hau bori "tab'a hannu Hajiya tayi ta ce " ikon Allah to ko aljanu zata tada kihau bori Kece bishiyar kuka karewar iskokai mahaukaciya y'ar mahaukata Kaikuma Solon hofi tsayawa ma kayi kana k
allonta"MD Yama rasa Inda zai tsoma ransa fitowa Ammy tayi tare da little zahra a hannunta Chuchu na biye da ita tare da biyun tana hawaye ta ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri karki basa yaran nan Momcy zata shiga wani hali Kinga koda kika amsosu kuka take Da
n Allah Ammy kar fushi yasa kiyi aikin Dana sani" Daidai shigowarsu palourn Duk Kallon Amera suka tsayayi dake kwala ihu kafin ta chukumi MD iya karfinta ta shakesa ta ce "Daman kai Bakin Munafuki ne bansaniba,Mayaudari ne kai daman ,ashe duk kalaman da ka
ke fad'amun na bazaka iyamun kishiya ba na karya ne to wallahi tallahi ka sani Mustapha baka isa ba kayi Kad'an ka yaudareni kaci bulus wlh baka isa ba ka hada matsayi na Dana wata ba karya ne Wlh zan kasheka zan kasheta zan kashe kaina Bayan na kashe shag
gun yaran Dan wlh badai aure ba Saidai in y'an zina ne kuka haifa.Marin da taji an wanka mata ne ya sanyata Had'iye maganar da ta fito daga bakinta Dagowa tayi da kalli wacce ta maretar Ammy ta gani tsaye kanta tana huci rike da baby cikin b'acin rai Ammy
ta ce " Duk iskancin da zakiyi ki tsaya iya mijinki shine Wanda zakiwa kici bulus amma ba zahra da yaranta da sukafiki matsayi da daraja a wajena ba baki isa ki shegantar mata yara ba sannan anfada Yayi Aure matarsa ta Haifa masa Yara ba karya akayi ba ko
haramun ne Dan yayi Aure tunda ke kin kasa basa farincikin da kowace mata take bawa mijinta hakan yasa yayi Aure kuma da masaniyarmu yayi kece baki sani ba yanzu kuma ai kinsani"Wani irin kallo Amera Kebin Ammy dashi tana rik'e da kumcinta ta ce "Ni kika m
ara " An mareki Dan Ubanki ko ramawa zakiyi" "Kutumar uban nan to Inma na rama din ke uwata ce ko haihuwa ta kikayi munafukai ke mijinki har ya mutu ya taba miki kishiya ne da zaki sanya nawa mijin yayimun kishiya daman Nasan ba kaunata kuke ba shine har K
uka sanya yayi mun kishiya to wlh kusani ni Amera nafi k'arfin kishiya nafi k'arfin hada miji....d'auke da Mari har sau Ukku da taji anyi ne ya sanya ta kasa fadar abunda tayi niyyar fad'a cikin huci MD ya ce" baki da hankali ne Amera mahaifiyar tawa kike
fad'awa hakan Dan iskanci ko ubanki ya isa ya fad'awa mahaifiyata haka bareke kodan Kinga Duk abunda kike ina kyaleki kina cin Darajar Abu biyu ne Inbanda haka da baki isa kiyi wani abun na kyaleki ba"kuka sosai Amera ta fashe dashi tare da k'walla Ihu duk
saida suka toshe kunnuwansu Kafin ta bud'e ido Jaririyar dake hannun Ammy idonta yakai kukan kura tayi tare da nufar Ammy ta amshe Jaririyar Tana shirin timata da K'asa Zahra ta rugo A guje batasan sanda wani k'arfi yazo mata ba ta amshe y'ar daga fad'uwa
r da Amira taso kadata Huci kawai zahra take tana kuka Dan yau ita kadai tasan tashin hankalin data shiga da Amera ta kada mata yarnan da batasan yanda zatayi ba jijjiga yarinyar ta fad'a data fara tsala wani irin kuka kowa Ajiyar zuciya ya sauke ganin iri
n kokarin da zahra tayi saboda ba k'aramar shammatarsu amira tayi ba Cikin Hargagi Hajiya ta ce "Ka fitar mana da mahaukaciya Matar nan gidan nan Dan ubanka tunda ta shanyeka Ibanda sakarai ta zagi uwarka Ka tsaya kana kallonta baka sauke mata saki Ukku ba
" cikin ihu Amera ta ce " da Allah iwa mutane shiru ke asuwa Ke ki sakeni d'in tsohuwar banza kawai" Ai MD baisan sanda ya k'ara d'auke Amera da wani Marin ba ya ce "Dan baki da hankali iyayen nawa da kakata kika zaga?Anzagesu din kaima wuce a zageka kayi
banza d'an iska Mayaudari tana kallon zahra dake jijjiga y'arta tana kuka ta ce " Daman Y'ar Iskar karuwarka ka aura Macuci Mayaudari"waige waige ta fara tana neman mabugi Chan ta Hango Fankar K'asa cikin Sauri ta nufi wajen iya karfinta ta Karya Fankar
ta d'auko K'asar da gudu ta nufi wajen zahra zata maka mata MD yayi Sauri Yarike cikin tsananin b'acin rai ya ce "Wannan wani irin hauka ne kike Amira" Kallon Chuchu da zahra Ammy tayi ta ce "Ku wuce ciki" Zahra hada gudu_gudu suka wuce Dan sosai ta tsorat
a da Amira Dan bata mance karansu na farko ba Cikin b'acin rai Hajiya ta ce "Bazaka saketa ba Sai kallonmu ka tsayayi ta zageni ta zageka,ta zagi uwarka ta shirya kashe maka y'ar da ka shekara goma Kana fatan samu ka tsaya kana kallonta Dan Kana Asararre"M
D rasa Inda zai tsoma ransa yayi cikin bacin rai Ammy ta ce " ku barmun gida daga kai har ita inba so kake na yi muku abunda bakuyi tsammani ba "Cikin tashin hankali ya ce " Dan Allah Ammy kiyi hakuri idan sakinta kike so nayi sainayi"Daga masa hannu Ammy
tayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba ya rage ruwanku amma Abunda nakeso ta barmun palour sannan a maida mun duk abunda ta lalatamun na palour " tana gama fad'ar haka ta haye sama da Kallo Hajiya ta bita kafin taja tsaki ta ce "Kaji d'ayar mahaukaciyar a tu
nani na zakice ya saketa ne ko ki tsine masa amma ke ta kayan Da aka lalata miki ma.kike Allah mai iko zaman gidannan ko kayan takaici Aiko zuwa zanyi na tattara kayana na bar garin haihuwa yau har tajamun Zagi" Hajiya ta fad'a tana goge hawayen takaici k
afin tayi fuuuu itama tabar palour "Cikin b'acin rai MD.ya kalli Amira ya ce " Hakan da kikayi burgewa ce to hankalinki ya kwanta kin had'ani da iyayena sannan zakisan iyayena Suna da martaba da daraja sunfi k'arfin zagi a wajenki ki biyo ni"ya fad'a yana
fita sai sannan tsoro da fargaba suka kama Amira ta tuno da abunda tayiwa Ammy da Hajiya kaka sai sannan hankalinta ya fara dawowa jikinta tasan karya take ta zagi mahaifiyarshi da kakarshi ta kwana Lafiya karfa ya saketa "Cikin tashin hankali ta bishi Ind
a ta sameshi cikin mota ya had'e kai da sitiyarin mota Cikin tashin hankali ta fashe da kuka ta ce " Dan Girman Allah MD.karka sakeni wlh tallahi bansan na zagesu ba zuciya ce kasan bata da kashi"Wani irin kallo ha dinga binta dashi cikin Tsawa ya ce "shig
o nace" Cikin Sauri ta shiga da Sauri ya figi motar bai tsaya ko ina ba sai gidansu suna isa bakin get ya tsaya ya ce "Fita ki tafi gidanku " Kuka ta fashe dashi ta ce "Dan Allah honey karkace ka sakeni" Cikin Tsawa ya ce "Bakiji abunda nace ba " Ba shirin
ta fita tana fita Ya rufe motarsa ya jata da gudu da gudu Amira ta shiga gidansu tana wani irin kuka ta fad'a jikin dad d'inta ta ce "Na shiga Ukku Dad shikenan md ya rabu dani daddy yayi Aure bansaniba Matar harta haihu naje gidansu na zagi mamansa da ka
karsa yayi fushi ya maidoni gida shikenan dad nasan sakina zaiyi na shiga ukku wlh dad inason mijina ina kaunarsa bazan iya rabuwa dashi ba wata bata isa ta rabani dashi ba Dady zuciyata ji nake kamar zata tarwatse dad tana cikin wannan sai ganinta sukayi
ta sulale a wajen summammiya hankalin iyayenta idan yayi dubu ya tashi a guje aka wuce Asibiti da ita hankali tashi Kafin likitoci su fara kokarin ceto rayuwarta.....MD ya rasa yanda zaiyi da ransa yasan Ammy ba k'aramun fushi ta k'ara dashi ba nakin sakin
Amera Jabir ya kira a waya ya sanar masa halin da ake cikin hankali tashe Jabir ya ce " Innalillahi Abu dai baiyi dadi ba bloody me yasa kak'i sakinta Ammy fa da Hajiya ta zaga kishi hauka ne "Jabir bazaka gane bane ni kadai nasan yanda Naji zafin hakan a
cikin raina Nafi su Ammy jin zafi naki sakinta ne saboda Duniya zata zageni babu Wanda zai duba abunda tayi za ace na saketa ne saboda Na auri wata harta haifamun yara nayiwa Matar data zauna dani tsawon shekaru goma ko shad'aya butulci" numfashi Jabir ya
ja yace "Tabbas hakane kayi tunani bloody amma dai abunda yafi kamata kaje kaba Ammy hakuri yanzu kayi mata bayanin nan zata fahimce ka" Kamar yanda Jabir ya fad'a masa haka yaje ya samu Ammy da dare ko gaisuwar da yayi mata kin amsawa tayi cike da damuwa
ya ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri wlh bawai Dan banji ciwon abunda Amera tayi ba yasa ban saketa ba nayi hakan ne saboda gujewa surutun mutane za ace na saketa ne kawai saboda wata Matar ta haifamun yara na rabu da ita tsawon shekararmu goma ban rabu da it
a ba sai yanzu za aga Rashin kyautawata Wanda kome tayi baza a ga nata ba Amma Ammy kiyi hakuri indai zaki janye fushin nan naki wlh zan saketa yanzu daman na Turata gidansu Saina aika mata takardarta indai hakan zaisa hankalinki ya kwanta" Tunani Ammy tay
i tace tabbas hakane dagowa tayi ta Kallesa har saida yaso bata tausayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba Inama umartarka da kaje ka D'auketa ku koma gidanku Kamar yanda bazanso a saki nawa y'ay'an ba haka bazanso a saki nawasu ba ka mayar da Matarka gidanku
sannan Ka lallasheta harka samu ka shawo kanta Tabbas kishiya da ciwo musamman baka San da ita ba har sai da y'ay'a dukda dai batasan dalilin Auren ba saboda soyayyarta ne ni na yafe maka ba abunda kayimun amma dai ka sani ina kan bakana saika saki zahra
"cikin wani sabon tashin hankalin ya d'ago ya ce " Dan Allah Ammy kidaina maganar sakin Mamy na yarda zan saki Amira