Showing 48001 words to 51000 words out of 137760 words
ta ce a kawo. Ki karasa ladanki."
Tana kai wa nan ta miƙe da zummar tafiya. Huzaif mamaki ya kusan kashe shi, duk a kalamanta bai
ga inda ta tauna harshenta ba, ya yi mishi kama da kamar rashin kunya haka ko kuma wata manufa. Amma sai ya yi tunanin ƙila don saƙo da saƙo suke shi ya haddasa hakan.
"Ni da kaina zan zuba, ke za ki fara sha tunda ko babu komai dama nan gaba ci da sha
yarwarki ƙarƙashina za su dawo."
Karaf zancen na Huzaif ya dira a kunnen Husna da bai fi taki
ɗ
aya ta bar falon ba, ta juyo ta dube su. Sadiya na kallonsa ka
ɗ
an, yayinda shi kuwa ya sauko gami da
ɗ
an durƙuso ya bu
ɗ
e jug na kunun aya ya shiga tsiyayawa a
kofi. Babu wanda ya ƙara lura da wata halitta mai sunanta a wajen don haka a gaggauce ta karasa ficewa ta nufi
ɗ
akinsu.
Inda Allah ya taimaka ma Inna na
ɗ
akinta. Kuka ta fara ta jawo wayarta ta shiga neman layin Hajara. Tana
ɗ
agawa a ru
ɗ
e ta shiga tam
bayarta abin da ke faruwa. Murya a shaƙe ta amsa.
"Anti anya zan iya cigaba da jurewa? Wani abin kamar da gayya ake yi don zuciyata ta sosu."
Ta ji sadda Hajara ta sauke ajiyar zuciya.
"Za ki iya Momina. Ai jinin da ke yawo a jikina shi ke yawo a
jikinki. Ina da tabbacin ba za ki
ɓ
atan shirina ba. Ke dai ki cigaba da haƙuri kina nuna komai ba komai ba. Gudun ma wani abin ya faru a yi wani zargi can. Kinga ki kwantar da hankalinki, na san gobe ma ba za ki iya yinin gidan ba, zan tambayar maki Malam
ki shigo gidana kin ji ko?"
"Toh Anti."
"Yauwa Momina. Ki ƙara daurewa, ke za ki dara a gaba. Ke za ki zama Amaryar Huzaif kawai ki kwantar da hankalinki."
Duk da tana ji kawai Antinta ta fa
ɗ
i don ta rarrashe ta ne, amma sai ta ji murmushi ya su
ɓ
uce mata. Ba su jima tare ba suka yi sallama don Hajara ta ce ta maida hankali ga karatu tunda ta sanar da ita sun fara gwajin aji a makaranta (Test).
***
Washegari da safe Sadiya ta tashi zuciyarta wasai idan ta tuna yau iyaye za su shiga maganarta d
a Yaya Huzaif. Haka suka yi shirin makaranta ita da Husna bayan sun gama kari. Falon Malam suka fara shiga kamar yanda suka saba suka gaishe shi, ya amsa lokaci guda yana kar
ɓ
ar kofin kunun gya
ɗ
ar da Inna ke miƙo mishi.
"Ke Autar Mama ta ce za ki je gi
danta ko?"
Husna ta gya
ɗ
a kai tana
ɗ
an murmushin yaƙe tun bayan wayar soyayya da ta ji Sadiya sun yi da Huzaif a yau ta ji ranta ya sosu.
"Shikenan, idan kin dawo sai ko shirya ki wuce. Ta nemi alfarmar ki kwana biyu zuwa lahadi kya dawo don ba ta j
in da
ɗ
i ne."
Cikin jin da
ɗ
i ta amsa da toh. Ita dai Sadiya kamar ya da Inna ba ta ce uffan ba, ita ma ba ta ce komai ba. Suka yi musu sallama suka fice bayan Malam ya ba su ku
ɗ
in mota da na kashewa.
"Ina fatan babu matsala? Na yanke hukunci ban sanar
da ke ba."
Malam ya furta yana kallon Inna. Ta numfasa.
"Ko ka
ɗ
an, ai kana da ikon zartar da kowane irin hukunci kan yaranka, kai ne fa Babansu. Sai dai Hajara ba lafiya amma ba ka sanar da ni ba? Ai ko ban je dubiya ba zan kira a waya na ji ya jik
inta."
Girgiza kai Malam ya yi, sanyin zuciya irin na Inna na ba sa mamaki.
"Ita ya dace ta kiraki matsayinki na Uwa gareta ta sanar da ke. Na yi mata fa
ɗ
an hakan, sai na yi zaton ko ta kira ne. Amma ina mai baki hakuri."
Murmushi Inna ta yi.
"Shikenan, Allah ta ba ta lafiya ya sa kaffara."
"Amin. Anjima can babban gida za'a kar
ɓ
i baƙin da misalin ƙarfe uku na rana da yardar Allah."
"Toh, Allah ya nuna mana. Ya sa albarka." Amsar da ta ba shi kenan. Shi ma ya bi da amin.
***
Sadiya n
a zaune a
ɗ
akinsu da yammaci sai ga Zahra ta shigo tana mata gu
ɗ
a a kai. Harararta ta yi da murmushi
ɗ
auke saman fuskarta.
"Ka ga Amaryar Huzaif. Allah ya sanya alheri. Ai Mama ta cemin wai an saka nan da watanni goma. Kafin lokacin kuwa mun yi Candy a
binmu. Toh ko auren wa za'a riga yi tsakanin ni da ke?"
Zahra ta ƙarashe da dariyar mugunta, Sadiya ta kai mata duka don ta san dalilin dariyar, wato dai ta gama cin alwashin karatu da tutiyar babu namijin da za ta kula sai ta zama likita, amma kuma ga
shi so ya yi mata tarko ta fa
ɗ
a. Zahra idan tsokanar ta tashi haka za ta yi ta jan ta.
"Ina
ɗ
iyar tawa take?" Fa
ɗ
in Maman Zahra dake shigowa kafin kuma ta yi sallama. Sadiya ta yi ƙasa da kanta tana gaishe ta a kunyace. Ƴar gu
ɗ
a Maman Zahra ta yi wanda
ya sa gaba
ɗ
aya ta
ɓ
oye kanta a kafa
ɗ
ar Zahra tana murmushi. Fatan alheri ta yi mata ta fice. Haka ma wasu a cikin ƴan uwan Malam da suka zo yiwa Inna fatan alheri suka shigo dakin. Ranar kam Sadiya ta sha zolaya sosai.
***
Hajara ta fito daga
ɗ
akin
ta cikin shiri, Husna dake saman teburin cin abinci tana ba ƴar aikinta mai suna Atine umarni ya sa ta murmushi. Ba ta
ce komai na ta tsaya ta na kallon diramar da suke yi. Wai Atine ta dafa mata Indomie da gwangwanin kifi alhalin da sauran farfesun kayan
cikin da ta gani ta ce a dafamata. Atine kuwa sai haƙuri take ba ta. Husna ta ja tsaki.
"Ni ba zan ci ba, ki
ɗ
auke ki yi min yadda nake so."
Ta yi jifa da cokalin ta miƙe ta taho falon. Anan ne kuma ta ga Hajara, Atine da sauri ta yi kicin da faranti
n Indomie tana tsoron fa
ɗ
an Uwar
ɗ
akinta Hajara.
Kamo hannun Husna ta yi tana murmushi.
"Momina, ina fata da burin na ga kin samu rayuwar jin da
ɗ
i ta daula irin wannan ko fiye da hakan. Allah ya sa ki zama matar Huzaif."
Husna ta yi dariyar fari
n ciki gami a yin farr da idanu.
"Amin Antina. Fita za ki yi?"
"Eh, zan je wani wuri ba jimawa zan yi ba."
Ta gya
ɗ
a mata kai da fatan dawowa lafiya. Husna ta bi gidan da kallo sadda Antinta ta shiga mota direbanta ya ja. Hasko ta take yi a irin w
annan daular ita da Huzaif
ɗ
inta.
***
Hajara da ƙawarta Waleeda ce zaune a gaban wani ƙasurgumin boka.
"Yanzu me kike so a yi?" Tambayar kenan da ya watso mata. Ta sauke ajiyar zuciya.
"Ina son komai a bi shi daki-daki, ba na so a yi ƙwaf
ɗ
aya
ne. So nake a fara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu, ta yadda wasu lokutan zasu yi ta fa
ɗ
a da juna, soyayyar dai ta dinga tafiyar hawainiya. A ƙarshe kuma idan lokacin da za'a raba tsakaninsu gaba
ɗ
aya ya zo, zan yi magana."
Boka ya yi dariya.
"Ai
wannan ba abin tashin hankali ba ne. Aiki ne ƙarami, aljani kawai za'a tura musu, kowanne ya dinga jin haushin
ɗ
an uwansa.."
"A'a, so nake shi ya dinga jin haushinta, ba na son ita
ɗ
in komai ya sauya a tare da ita dangane da mu'amalarsu "
"Na fahimt
a, a kan shi yaron zamu yi aiki kenan."
Hajara ta jinjina kai tana murmushi.
"Akan sa ne. Huzaif sunansa."
"An gama. Kar ki samu damuwa. Ku ba ni nan da sati komai za'a yi shi a ƙare."
Hajara ta dubi Waleeda suka yi murmushi kafin ta
ɓ
alle baki
n jakarta ta fiddo maƙudan ku
ɗ
a
ɗ
en da ba ta san adadinsu ba ta ajiye a gabansa. Daga haka suka tashi suka fice.
***
Shirye-shiryen soma jarrabawa kawai Sadiya ke yi, sai ya kasance ƙarfe hu
ɗ
u take dawowa gidan domin koda an tashi sukan tsaya bitar da
ake musu a makarantar.
Kamar koyaushe, yau
ɗ
in ma tana falon Innarta tana karatun jarrabawa, wani al'amari ya faru tsakaninta da Huzaif da ya
ɗ
aure mata kai. Layinta ya kira a yammacin daidai lokacin da ta ba Inna waya suna magana mai muhimmanci da Ad
da Ruƙayya wacce take kusan sa'ar Innar amma kuma sunan na Adda Ruƙayya ya bi ta tun suna yara. Sun
ɗ
auki lokaci mai
ɗ
an tsawo suna tattaunawa duk dai akan abin da ya shafi zuwa Gombe da zasu yi biki a zuri'arsu.
Sun shafe kusan mintuna goma sha biyar
kafin daga bisani su yi sallama, Sadiya da ke a falon Inna ta baza litattafai tana karatu ta ji shigowar Inna da kuma wayar da ta ajiye mata ta fita. Ba ta ma ko dubi wayar ba don ita a yadda ta saka karatun a rai, gani take idan fa ba ta mayar da hankali
ba toh ba za ta samu ta haye darussan da za su taimaka mata kai wa ga gaci ba, abin nufi, watarana a wayi gari ta soma karantar fannin Likita da ta ke muradi. Daidai da Jamb da aka zana kwanakin baya, Malam sam bai bari ta zana ba don yana kan ra'ayinsa na
cewa matuƙar ba ta shiga
ɗ
akin aurenta ba to fa ba za ta soma karatu ba. Idan ta tuna sanadin Anti Hajara ne mahaifin nata ya sauya ra'ayi takan ji ƙarin tsanarta a zuciya, yanzun ma da tunanin ya fa
ɗ
omata sai ta tsinci kanta da jan guntun tsaki.
Wayar
ta da ta hau ƙara ya sa ta kai idanunta saman screen
ɗ
in, sunan Yaya Huzaif ne muraran ya bayyana, murmushi ta yi kafin ta kai hannunta jawo ta. Ta
ɗ
aga sannan ta soma magana.
"As..."
"Da wa ki ke waya Bebi?"
"Inna ce ke waya da Adda Ruƙayya, waya
rta batir ya ƙone shi ne na..."
"Ya isa please Bebi, ba na son ƙaryar banza da wofi. Na san wani ƙaton ki ka ba lambarki, idan ba haka ba ki rantse da Allah cewa Inna ke amfani da wayar sannan ki yi min screenshot lambar ki turo min ta whatsapp na gani.
"
Sai ta rasa me za ta ce, gaba
ɗ
aya kanta ya ƙulle tamau. Ganin komai take tamkar a mafarki, daƙyar ta ha
ɗ
iyi miyau cikin sanyin murya ta ce.
"Na rantse? Rantsuwa fa ka ce Yaya Huzaif? Meyasa zan ba wani lambata alhalin na san da sanya rana a kaina?
"
Tsaki ta ji ya ja.
"An fa
ɗ
amaki ni mahaukaci ne kenan Bebi, zan yarda ni ka
ɗ
ai ki ke kulawa ne alhalin ina da labarin duk sadda ki ka fita sai an samu mazan da suke biyo ki gida da sunan suna sonki? Ke na rantse ban yarda Inna ke amfani da wayarki
ba. Ƙarya ki ke yi Bebi tunda har kin kasa rantse min. Ni za ki ci amana?"
Tana jin alamar
ɓ
acin rai a muryarsa, sai ta ji ƙwalla sun cicciko mata.
"Wai Yaya Huzaif lafiya? Wane ya
ɓ
ata maka rai?"
"Haka ki ka ce ko? Laifi ne don na nuna kishi a k
anki? To ki je ko da waye ki ke magana Allah ya isa ban yafe ba. Da na san hakane wallahi ba zan siyamaki wayar ba idan ya so sai na ga ta hanyar da za ki ci amanar soyayyata. Amma bakomai, nagode."
Yana kai wa nan ta ji kit, ya kashe wayar. Ta fiddo wa
yar a kunne tana ƙura idanunta. Hawayenta tuni sun zubo saman kuncinta. Yaya Huzaif dai? Ƙaryatawa? Zargi? Ja mata Allah ya isa?
'Meke faruwa ne?' Ta tambayi zuciyarta, ba ta sani ba. Ta ji ranta ya
ɓ
aci sosai, ba ta kai ga tunanin komai ba ta ji ƙarar
shigowar saƙo a wayar, da hanzari ta duba. Shi ne ya rubuto.
"Dama an ce ka kiyayi mai kyau, babu abin da kuka iya sai yaudara. Za ku yi amfani da mutum ne don samun wani cikar burinku, a ƙarshe ku watsar da shi a kwandon shara. Babu yadda za'a yi Inn
a ta kar
ɓ
i wayarki ta yi wanda ya zarta mintuna biyar tunda ba cinikin fili za ta ƙulla ba ai. Ni ki ka maida
ɗ
an iska da bai san me yake ba. Shikenan, kar ki ƙara nemana a waya, ki rufe lambata kamar yadda ni ma zan rufe naki. Sai anjima."
'Innalillahi
wa inna ilaihir raaji'un!' Kalmar da Sadiya ta ambata kenan, hawayenta ya ƙaru, ya cigaba da zuba tamkar ruwan famfo. Sosai kalamansa sun yi mata zafi, ta ƙara karantawa, ta ji wani abu na taso mata na jin haushinsa don haka ta kashe wayar gaba
ɗ
aya. Rana
r karatun da ta kasa ƙarasawa kenan.
Inna ta bi ta da kallo sadda ta fito a falon rataye da jakar karatunta za ta shige zuwa
ɗ
akinsu.
"Ke, lafiya na ga fuskarki ta sauya?"
Ta
ɗ
an rike kanta.
"Bakomai, kaina ke ciwo sosai."
Ta fa
ɗ
a ne don k
are damuwarta, amma kuma dagasken kukan da ta ci a dalilin wannan kalaman marasa da
ɗ
in ji da Huzaif ya fesa mata, su ne babban dalilin da ya ha
ɗ
u da rashin cin abincin da ba ta yi ba na rana ya haifar mata da azababben ciwon kan.
"To ai dole kanki ya y
i ciwo Mamana, kin zauna za ki kashe kanki da boko alhalin ko abinci ba ki ci ba. Je ki ki ajiye jakar ki zo ki
ɗ
ebi abinci."
Kamar ta ce ta ƙoshi, amma kuma ta san idan har ba ta bi umarnin Innar ba, to hakan zai sa ta fahimci ba lafiya ba don haka sai
kawai ta amsa da toh ta shige
ɗ
akin. Husna dake amsa waya ganin ta shigo ta koma amsa wayar da uhm da kuma uhm uhm. Ita sam hankalinta ma ba a kanta yake ba, abin da ke cin ranta ya ishe ta wannan ya sa koda ta ajiye jakar ta fita don
ɗ
ebo abinci.
Hus
na ta
ɗ
an leƙa ganin ta shiga kicin ne yasa cikin ra
ɗ
a-ra
ɗ
a ta ce.
"Antina, na rantse fuskarta gaba
ɗ
aya ta yi ja kamar kuka ta yi ma. Kinsan ita haka fuskar ke komawa idan ta ci kuka."
"Eh Anti, ai ni ya kira sadda Inna ke wayar sai nace masa ni in
a
ɗ
akina, wataƙila Sadiyar ita ke yin waya."
Husna ta yi dariya ta ƙara da fa
ɗ
in.
"To shikenan Anti, zan ƙara takatsantsan. Sai mun yi magana."
Daga haka suka yi sallama ta katse kiran tana ƴar dariya. Tana kallon Sadiya ta shige falon Innar, kwan
ciyarta ta yi iskar fankar da ke ka
ɗ
awa yana mata da
ɗ
i. Zuciyarta kuwa wani irin sanyi ta ji yana yi. Hu
ɗ
ubar da Antinta Hajara ta yi mata ne ya shiga dawomata.
"Zan taimaka maki, amma ke ma sai kin ha
ɗ
a da irin namu makircin na mata. Kin ga dai na ce m
aki ki kula da duk wani taku naki da zai sa a zarge ki ta kowace fuska, yauwa, to kuma ina son duk sadda wani abun ya tashi wanda ki ka san zai iya haddasa hayaniya ko rikici tsakanin Sadiya da Huzaif, ki yi iyakar yin ki don ganin kin ƙara kunna wutar rik
icin madadin ki kashe shi. Kuma ki dinga bi ta sigar da ba wanda zai maki kallon zargi. Idan har aka tafi a haka ina mai tabbatar maki komai zai zo mana da sauƙi. Za mu yi nasara kan ƙudurinmu."
Tana kai wa nan a tunaninta ta bu
ɗ
e idanun da ta lumshe su
a farko, ajiyar zuciya ta saki. Kaunar Yayarta da ba ta da kamarta wato Hajara yana ratsa ta. Ta tabbata daga yanayin fuskar Sadiya akwai magana sosai. Wani tunani ne ya fa
ɗ
omata a rai don haka ta yi saurin jawo wayar Sadiya da ta ajiye a gefen gadon ta d
uba, ganin a kashe sai ta mayar, murmushi sosai ta shiga yi, wayarta ta
ɗ
auka gami da shiga cikin whatsapp. Kai tsaye saman lambar Huzaif ta tafi, ta ci sa'ar ganinsa a online kuwa. Don haka ta shiga rubutu.
"Hi, Yayana akwai wata damuwar ne?"
Kamar
jira yake yi ta ga ya soma rubutu, can sai ga saƙon ya shigo.
"Hum, babu komai ƙanwata, kawai yayarki ke neman
ɓ
atan rai ne. Amma shikenan."
Husna ta riƙe dariyar dake cin zuciyarta ta ba aikamasa da
ɗ
an dodon da ya zaro ido na waya. Ta
ɗ
ora da fa
ɗ
in.
"Ya Salam, meke faruwa? Na ga Sadiya ta na ta cika da batsewa ta kashe wayarta. Wa ya
ɓ
ata wa wani tsakanin kai da ita."
Ta ga sadda ya bu
ɗ
e amma kuma an
ɗ
auki mintuna kusan uku kafin ya tura mata martanin zancen.