Showing 3001 words to 6000 words out of 137760 words

Chapter 2 - KAZAR KWANCI COMPLETE

23 Oct 2026

301

zargin jama'a.

Tana nan zaune tana

ɗ

an jan carbi tana tunane-tunane har Malam ya dawo daga masallaci. Ta sanar da shi alfarmar da Hafsatu ta roƙa ya amsa da toh.

Washegari da safe bayan Malam ya kamma

la kari ya fita babu jimawa wurin ƙarfe sha

ɗ

aya Inna Mairamu na maida kayan wanke-wanken da ta yi kicin sai ga sallamar su. Sadiya ce a gaba, ta karasa da sauri ta rungume uwarta gami da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, ita ka

ɗ

ai ta san a kwanakin nan irin

musgunawar da Hajara ta yiwa rayuwarta a gidan Anti Hafsatu kai kace ita ce silar da aka fasa auren nan. Ba don ma Anti Hafsatun na kwa

ɓ

ar Hajara ba da ba ta san ina abin zai tsaya ba. Koda za su taho daga ta taka ƙafar Husna ba tare da ta kula ba Hajara t

a kwashe ta da wani wawan mari a fuska har sai da suka kusan fa

ɗ

a da Anti Hafsatu. Haka suka shiga motar kowanne ransa babu dadi har suka ƙaraso gidan.

Inna Mairamu ta

ɗ

ago Sadiya daga jikinta tana

ɗ

an murmushin yaƙe duk kuwa da shatin yatsun da ta gan

i kwance gefen fuskarta. Abinka da farar fata har wurin ya yi ja ga idanunta su ma kana yin kallo

ɗ

aya za ka fahimci ta ci kuka.

"Ke kuma sai ka ce wacce ta shekara ba ta nan? Ni matsa can ki bani wuri."

Kafin ta yi magana sai ga Husna ta shigo babu

ko sallama tana turo baki, hannunta riƙe da jakar kayanta.

"Ke Sadiya wa kika mayar ƴar aikinki? Wallahi ki koma ki shigo da jakar ki don ni ba baiwarki bace."

Sadiya itama ta juyo ranta a

ɓ

ace, wannan raini da Husna ta yi mata yana baƙanta ranta ai

nun. Ta sani dai ba laifin kowa ba ne face Hajara, ita ce ta jaza mata. Ta dubi Inna, Inna ta yi mata alamar kar ta ce komai wannan yasa ta yin ƙwafa kawai, sanadin Husnar ta sha mari wajen Hajara. Matar da take tsananin shakka tun tana ƙarama sai dai zuwa

yanzu ta rage jin tsoron ba kamar a baya ba. Kawai dai ba ta iya maida mata martanin zantukan da take yi musamman ga mahaifiyarta. Tana wannan tunanin sai ga Hajara ta shigo wannan ya sa ta ha

ɗ

iye abin da ta yi niyyar fa

ɗ

i.

"Momina, wuce ki ajiye jakar

mana. Ke kar

ɓ

i ki miƙa mata ciki."

Ta furta tana maida duba ga Sadiya dake tsaye gefen Innarta, kamar ba za ta yi ba sai kuma ta tuno marin da ta sha ta ƙarasa ta kar

ɓ

i jakar hannun Husna ta shige dakinsu idanunta cike taf da kwalla, ban da gidansu, in

a ne gidan da ƙarami ya raina babba ya mayar da shi tamkar bawansa. Ɗaki ne wanda ba ta da makwanci sai ƙasa a katifa yayinda Hajara ta maida gadon nata ita da Husna. A farko ma a ƙasa Sadiyar ke kwana sai da Inna ta yi magana ne sannan Malam ya siyo katif

a maidaidaiciya ya ce Sadiyar ta dinga kwanciya a ƙasa acewarsa ai gaskiya Hajarar ta fa

ɗ

i, gadon ya yi musu ka

ɗ

an su uku duk kuwa da girmansa.

A tsakar gidan kuwa Hajara ba ta ko gaida Inna ba ta yi

ɗ

akin, Sadiya ta fito da sauri gudun kada ta yi mata w

ani laifin. Inna ta bi ta da kallo sannan ta maida ga Anti Hafsatu dake sallama riƙe da jaka ganin haka Sadiya ta kar

ɓ

a ta kai

ɗ

akin ta ajiye. Falon Inna suka shiga gaba daya aka zauna ana gaisawa. Husna da har lokacin ba ta bar yiwa Inna kallon mai laifi

ba da ta tauye rayuwar Yayarta ta hana ta aure saboda ba ita ta haife ta ba, zama kawai ta yi amma fuskarta gaba

ɗ

aya babu wani annuri.

"Ku

ɗ

an bamu wuri toh, zamu yi magana." Cewar Anti Hafsatu tana dubansu, Husna

ɗ

an ta

ɓ

e baki tayi sannan ta miƙe, In

na ta bi shigar ta da kallo. Wani leshi ne wanda ko ba a fa

ɗ

a ba a ido an san mai tsada ne an mata

ɗ

inkin riga da siket da ya kama jikinta don ma dai babu wani abin a zo a gani a surar domin duka duka shekarunta goma sha biyu a sannan amma sai ka dauka ta

gurmi Sadiya saboda girman jiki. Wannan leshi yana

ɗ

aya daga cikin irin

ɗ

inkunan da Hajara ke mata. Ko kusa Inna ba ta kaunarta da ire-iren

ɗ

inkunan masu kama jiki sai dai ba ta isa ta yi magana ba Malam zai hayayyako mata ya goyi bayan ƴar gaban goshinsa

Hajara.

Bayan ficewarsu Anti Hafsatu ta soma magana fuska dauke da damuwa.

"Inna na sani dole za ki fuskanci matsaloli game da fasa auren nan na Hajara da ake yi. Amma don Allah ina roƙon ki ƙara hakuri kuma ki toshe kunnuwanki daga dukkan wani abu

da zai je ya zo ko a

ɓ

angaren ƴan uwana ko danginmu. Mutane ne a yanzu sam ba su da tawakkali, gutsiri tsoma ya yi musu yawa. Ki yi hakuri da dukkan abin da su Gwaggo suka ce maki."

Inna Mairamu ta

ɗ

an yi murmushi, hankali da nutsuwa irin ta Hafsatu da

Zakari yana matuƙar burgeta ainun. Tun faruwar al'amarin idan ka cire

ɗ

ai

ɗ

aiku daga danginsu, babu wani ko wata acikin yaran mijinta da ya tare ta da irin wannan kalaman masu sanya nutsuwa da kwantar da hankali sai Zakari sai kuwa Hafsatun don ita Safiyya

ma har iskokan ƙarya ta tayi ta zage ta tas.

https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a

*Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.*

***

*Kazar Kwanci...*

*Free page*

*05*

"Kar ki damu Hafsatu, da ace zan dinga damuwa da abin da mutane ke fa

ɗ

i a kaina game da lamarin nan ai da yanzu na ƙare a kwance. Allah shi ne shaida ina zaune da ku da zuciya daya, kaf dinku ina muku kallo tamkar na yaran da na raina da hannuna. Komai zai

wuce da yardar Allah. Itama Hajara in sha Allahu mijinta zai zo, Allah ya bata ikon yarda da ƙaddara."

Anti Hafsatu ta share kwalla na tausayin Inna Mairamu, mace mai nunamusu kauna da zuciya

ɗ

aya, ga hakuri da kawar da kai da kuma maida lamarinta gaba



ɗ

aya ga Ubangiji. Kafin Anti Hafsatu ta kai ga cewa wani abu sai ga Hajara ta shigo ta musu tsaye a kai. Wani kallo take watsawa Inna kamar ta ga kashi fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye tun bayan Husna ta fesa mata cewa Anti Hafsatu ta fito da su wai za

ta yi magana da Innar ta yi saurin fitowa ta la

ɓ

e. Komai a cikin kunnenta suka fa

ɗ

i.

"Ke Hajara wane irin rashin ladabi ne wannan? Mu kika tsayawa a kai haka tamkar wasu sa'anninki?"

Hajara ba ta ko bi ta kan Anti Hafsatu mai wadannan zantukan ba t

a

ɗ

ora nata zancen.

"Duk abin da ka yiwa

ɗ

an wani a rubuce yake sai an yiwa

ɗ

iyarka. Abin da kike fatan ya kasance a kaina, Mairamu (kamar yanda take kiranta tun farko wanda har ta koyawa Husna) ki sa a ranki har abada ba zai tabbata ba sai dai ki gani

akan Sadiya. Zama ba aure, karuwanci, cikin shege duk za ki gani a jikin wannan

ɗ

iyar taki mai kama da zabiya. Aure kuma ko ana ha maza ha mata zan yi shi, ki zuba idanu ki ga ikon Allah. Ƙaryar mutum wallahi!"

"Ke Hajara!" Anti Hafsatu ta mike lokaci g

uda tana kiranta murya a

ɗ

age, hannu ta

ɗ

aga da niyyar marinta ko me ta tuna sai ta dunƙule ta fasa ta

ɓ

ige da nuna ta da yatsa idanunta na fitar da hawayen baƙin ciki. Ita ko Inna Mairamu kanta a ƙasa ta runtse idanu tana ambaton sunan Allah, zafin kalama

n da Hajara a yau ke jifan

ɗ

iyarta da shi da mummunan bakin da take yi gareta ya sanya ta kasa jure yin shiru wannan karon ta

ɗ

ago kai tana kallonta.

"Hajara kar ki bari Allah ya kama ki da laifin ƙazafi da kuma ƙage. Sadiyar dai da kike aibatawa kin f

i ni kusanci da ita don ko yau rabuwar aure zai iya zama dalilin da zan nisanta da ku gaba

ɗ

aya, ita

ɗ

in kuwa babu yanda za ki yi da ita saboda dolenki ce kuna tsatsonki."

"Hajara ba ki da hankali, kin manta wace ce ita kike a wajen mahaifinki? Wallahi

ki kiyaye harshenki domin nan gaba zai iya haifarmaki da dana sani marar iyaka. Yau ace Mama na raye an fadamaki za ta ji dadin irin wannan abu da kike aikatawa? Ko kuwa an fa

ɗ

amaki Husna za ta so ki dinga yiwa Mahaifiyarta irin wannan cin kashin?"

Idan

un Hajara har ƙanƙancewa ya yi tsabar bala'i ta dubi yayarta murya a sama ta ce.

"Ki bar kiran Mamana a wannan sha'anin, tana can kwance cikin kabarinta. Alhamdulillah ta rabu da mutane lafiya, uwa uba ta rabu da mijinta lafiya yana mai addu'a da nema m

ata gafarar Ubangiji. Sannan Alhamdulillah uwata ba ta cutar da rayuwar kowa ba. Husna kuma ita kanta ta fahimci wace ce Babarta Mairamu, ta soma gane ita ke haddasa rashin yiwuwar aurena. A hankali za ta gane komai."

Inna Mairamu zuwa lokacin ma ta kas

a ƙara uffan, Anti Hafsatu kuwa zagin Hajara take yi kawai tsabar takaici, abin da ya hana ta kai mata duka bai bwuce dokar da Malam ya sanya musu akan Hajara ba, har Allah ya isa ya yi ga duk wanda ya sa hannu ya ta

ɓ

a masa ita. Koda dai ba akan Hajara ba

kawai, shi tun fil'azal mutum ne da babu wanda ya isa ya dokar masa yara.

"Lallai yau na ƙara yarda ba za ki ta

ɓ

a sauya hali ba. Wannan rashin hankalin da kike yiwa Inna wallahi muddin ba ki bar yinsa ba sai kin ga sakamakonki a rayuwa. Shashashar banz

a da wofi wacce ba ta san girma da mutunci Dan Adam ba."

Ita dai Hajara guntun tsaki ta ja ta fice tana banko labulen, Sadiya dake kicin tana ganin ta shige

ɗ

akinsu ta fito a guje ta yi wajen Innarta tana kuka sosai a duniya ta tsani Hajara ba don komai

ba sai saboda cin zarafin Innarta wanda nata ya ninka na sauran yan uwan, sukan ma nuna halin ko in kula irin na ƴan boko ga Inna, amma ita kuwa idanunta take murjewa ta ci mutuncinta son rai.  Itama Innar nata hawayen ba su bar zuba ba. Anti Hafsatu kuwa

hakuri take ta ba Inna kamar harshenta zai tsinke. Har sai da Innar ta dakatar da ita da nuna nata kar ta damu babu wani abu.

  A can

ɗ

akin kuwa, Husna ta ji komai da ya wakana zuciyarta ta

ɗ

an yi babu dadi, babu wanda zai so a dinga cin zarafin mahai

fiyarsa haka, amma kuma ai a ganinta gaskiya Antinta ta fa

ɗ

i, duk abin da ka yiwa wani za'a yi wa naka. Har Hajara ta shigo ba ta motsa daga inda take zaune rike da

babbar wayarta ƙirar Infinix da Antin ta siyamata wai ta dinga kallo. Akan wayar ma sai da

Malam da Inna suka yi fa

ɗ

a, ba ta ga dalilin da za'a ba Husna waya ba, duka-duka a ganinta yarinyar shekarunta nawa a duniya? Karshe dai da Malam ya yi mata kaca-kaca dole ta zuba idanu, takan yiwa Husna nasiha da nunamata irin hakan da ake mata sam ba gat

a bane, amma yarinyar sai take ganin kawai Innar ta takura mata ne.

"Anti Hajara."

Cewar Husna fuskarta dauke da tsantsar damuwa, ita har ta rasa ma bayan wa za ta bi, takan ji ciwo idan aka yiwa Inna, kuma takan ji zafin asirin hana aure da aka ce

Inna ta yiwa Antinta.

Hajara ta dube ta sai ta ƙara fashewa da kuka ta janyo hannunta cikin nata.

"Momina, meyasa Mairamu ba ta kaunar ta ga nayi aure? Me nayi mata da take fatan na dauwama a gida? Shikenan don uwata ta mutu sai na zama marar gata?

Kinga don nace abinda ta yimin za ta gani a kan Sadiya shi ne Anti Hafsatu har kusan dauke ni da mari ta yi. Wato ba ta son a yiwa Sadiya amma idan da ace ke nace a yiwa babu abin da zai dame ta ko? Na fadamaki, saboda kina kaunata shiyasa Mairamu ta fi nu

nawa Sadiya so sama da ke, hum, ai shikenan. Ki yi addu'a na samu miji na yi aure, wallahi gidana za ki koma."

Husna itama kukan take yi, bilhakki tausayin Antinta take ji, tana kuma jin zafi idan ta tuna wai Mairamu ta fi kaunar Sadiya saboda ita. Ta k

uma soma yarda da hakan, kuma Hajara ta ce ba don komai ba ne sai ganin Sadiya kyakkyawa ce za ta yi amfani da ita domin ta zame mata tamkar jari, ita kuwa tunda ba ta da kyawun fuskar Sadiyar, kuma wai Sadiyar sunan mahaifiyar Innar ta ci, ita kuma saboda

sunan maman su Hajara ce kuma matar da Babansu ya fi kauna shi ne dalilin da yasa komai ta aikata sai ta ce bai yi ba ta daina.

"Kiyi hakuri Anti, kinji? Nima na fi so kiyi aure na bi ki gidanki. Na gaji da zama tare da Mairamu tunda ba ta kaunata."

Hajara ta murmusa ba tare da ta ce komai ba sai aikin kallon lallen da aka zana mata a hannu don bikin aurenta har ma ya soma gogewa.

©Rufaida Umar.

https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a

*Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka

a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.*

***

*Kazar Kwanci...*

*Free page*



06

Anti Hafsatu ba ta kuma bi ta kan Hajara ba, abin da ya faru kuma bai sa ta iya zaman jira har Malam ya dawo su gaisa ba, tana yin sallar azahar

ta ci abinci ta tattara ta bar gidan. Sadiya kuwa kamar yanda ta saba haka ta zauna tana taya Inna da wanke-wanken kwanukan da suka

ɓ

ata na abincin rana, Hajara da Husna ko ta kan abincin ba su bi ba, tana nan tana gyara wurin da ta kammala aikin Husna ta

fito yafe da siririn gyale ta shuri takalmanta ta fice daga gidan. Da idanu kawai Sadiya ta bita, can kuma sai ta dawo hannunta riƙe da leda babba sai

ɗ

aya dauke da lemo da ruwa ta shige

ɗ

akin. Ita kuwa Sadiya tana kammalawa ta nufi dakin Innarta, kamar y

anda ta bar ta haka ta tarar da ita. Ta zauna fuska dauke da damuwa.

"Haba Inna, don Allah ki bar damun kanki da tunanin abin da ba za ki iya gyara shi ba."

Inna ta sauke ajiyar zuciya ta dube ta.

"Kar ki damu Mamana, ba wannan ke damuna ba, rayuw

ar Husna nake tausayawa, an

ɗ

auki turbar lalata min tarbiyyarta amma ina ji ina gani ban isa na yi magana ba. Wannan shi ne damuwata."

Sadiya ta sauke ajiyar zuciya.

"Ki cigaba da addu'a Inna. In sha Allahu komai zai yi daidai."

Ta gyadamata kai.

"Allah ya dafamana."

"Amin inna."

***

WAIWAYE...

Malam Sa'ad Shagari ya dubi Mairamu cike da nutsuwa. Ita kuwa kanta na ƙasa tana

ɗ

an murmushi. Shima sai ya tsinci kansa da murmusawar kafin ya soma magana.

"Sai kika yi mamakin gani na k

o Mairamu? Ban ji kin tambayi abin da ya kawo ni ba?"

Ba tare da ta dube shi ba ta amsa.

"Ba komai, nasan ko da me ka zo alheri ne ai Malam, ya gida ya kuma ƙarin hakuri? Naji a wurin Malama Fauziyya cewa uwar gidanka Allah ya yi mata rasuwa, Allah y

a gafarta mata na so shiga da na dawo na yi maka gaisuwa duk da ya dauki lokaci amma Allah bai nufa, kuma sadda aka yi rasuwar sai nima abin ya zo kan ga

ɓ

a, an yi min wata rasuwar a can gida na tafi, yayata da muke uwa daya uba daya, shi ne ma dalilin jima

wata ban dawo ba."

"Allahu Akbar, Allah ya gafarta mata."

Mairamu ta amsa da amin, shiru ya

ɗ

an biyo baya kafin ya

ɗ

ora.

"Mairamu, koda ban fa

ɗ

a ba, nasan Malama Fauziyya ba za ta rasa sanar da ke ka

ɗ

an daga dalilin da yasa na zo wajenki ba. Amma

zuwa da kai ya fi saƙo. Kamar yanda kika sani, Marigayiya matata Hajiya Asma'u, da mahaifina da mahaifinta uwa daya uba daya, hakanan iyayenmu mata su ma auren dangi na zumunci ne ya faru tsakaninsu har suka haife mu. Wanda cikin iko na Allah soyayya ta ƙu

llu tsakanina da Asma'u tun tana matsayin

ɗ

alibata har Allah ya nufa ita za ta zamo uwa ga ƴaƴana bakwai. Ba zan

ɓ

oyemaki ba, ta kasance mace mafi soyuwa a gareni, bana jin a duniyata na ta

ɓ

a son wata

ɗ

iya mace irin son da na yiwa Asma'u. Mace mai hakuri d

a kuma kauda kai, a tsawon shekarun da muka rayu da juna da ita, sa

ɓ

anin da za ki ga ya ha

ɗ

a mu sai dai ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login