Showing 57001 words to 60000 words out of 137760 words
musu albarka don shi a nasa zaton har Husna aka yi aikin.
Washegari kuwa sai ga Inna da tsakar rana sun dawo, sosai Sadiya ta shiga murna, ko babu komai ka
ɗ
aicin da ya yi wa zuciyarta yawa dangane da Huzaif zai ragu.
"Me ya ramar d
a ke haka?" Tambayar da Inna ta soma jifanta da shi kenan. Ta yi dariyar yaƙe.
"Inna rama dai? To sai dai yanayin jarrabawa."
Inna ta bi ta da hakane kawai, ta sani wataƙila gidan Hajarar ce ta yi rayuwa a ƙuntace tunda babu shaƙuwa ko na sakanni tsa
kaninsu.
***
Tun tana ƙirgen kwanaki, har suka soma zana jarrabawarsu ta Neco babu wani yunƙurin kira ko magana daga Huzaif. Zuwa sannan duk dauriyarts ta kasa, ta yi mishi magana har da kiran whatsapp amma bai ko bi ta kai ba.
"Kin takura min Sad
iya, don Allah ki bar ni ina fama da karatu ne. Ke ba ki san ki nemi mutum a gaisa ba sai kin gama wulaƙanta shi ko? To ni ma ai ina da abin yi. Ba a kanki zan zauna na ƙare rayuwata ba. Ki taimaka ki ba ni lokaci kar ki yi sanadin da zan
ɗ
auki matakin da
ba zai mana da
ɗ
i ba Hajjaju."
Wannan shi ne amsar da ta samu sadda ta takura mishi da magana a whatsapp. Kalmar Hajjaju ta yi mugun baƙanta ranta, ta ji ciwon kalamansa. Ta sha kuka sosai. Haka ta daurewa zuciyarta ta kashe wayar gaba
ɗ
aya ta cilla ciki
n sif ta cigaba da harkokinta da karfin hali.
Zahra ke zaune tana kwa
ɓ
in lalle za ta yiwa wata Amarya, ita kuwa Sadiya ta yi shiru kawai ta zubawa lallen idanu amma sam hankalinta na ga tunanin Huzaif. Duk yadda ta so tattara komai ta watsat hakan ya fa
skara, sau da dama murmushinsa, da
ɗ
a
ɗ
an kalamansa kai har ma da yanayi na
ɗ
aukar gayunsa sukan hana ta sakat, ta sani tana kaunarsa ba na wasa ba. Sauyin da ya ke zuwar mata da shi, sauyi ne irin wanda ba za ta iya jurewa ba. Satinsu
ɗ
aya da soma jarrabawa
r Neco amma gaba
ɗ
aya ta kasa saita kanta ta maido walwalarta yadda ya kamata. A gaban Inna kawai dauriya take yi duk da ta sani daga yanayin kulawar da Inna ke ƙara ba ta, ta fahimci tana da wata damuwar da ba ta fito ta bayyana mata shi ba.
"Sadiya!
Ke!"
Muryar Zahra ta tsinta kamar daga sama ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zaman hijabinta gami da kauda kai daga kallon Zahrar da take sakamakon hawayen da suka cicciko mata sai ta waske da fa
ɗ
in.
"Ke bari na ko
ma gida kafin Inna ta ji shirun ya yi yawa."
Zahra ta riƙo gefen hijabinta wanda ya sa dole ta fasa miƙewar amma kuma hawayen sun zubo.
"Meyasa Sadiya? Meyasa za ki takurawa rayuwarki ki hana kanki sukuni a dalilin
ɗ
a namiji? Wallahi na tsani na ga k
ina zubar da hawayenki akan Huzaif. Ban ce bai cancanta ba, amma kuma duk wanda ya nuna kai ba ka da muhimmanci a rayuwarsa, kai ma ka fita hanyarsa gaba
ɗ
aya ka hutarwa ranka. Don Allah Sadiya, ina ha
ɗ
a ki da girman Allah ki yi ƙoƙarin rage damuwarnan. Ku
ma na yi alƙawarin zan ji ta bakin Huzaif, zan mishi magana. Da yardar Allah komai zai wuce."
Sadiya ta share fuskarta tana murmushin da bai kai zuci ba.
"Kin san ban ta
ɓ
a son wani
ɗ
a namiji ba Zahra, ban iya soyayyar ba, akan Yaya Huzaif na koya. Am
ma kuma yanzu ya ke wulaƙanta ni. Hum. Kar ma ki
ɓ
ata bakinki wajen yi mishi magana. To me za'a ce masa?"
"Mu ke da abin cewa kuwa Sadiya. Bari na gama yi wa yarinyarnan ƙunshi zan shigo gidan ki ban lambarsa. In sha Allahu yau ba za ki kwana da damuwar
sa ba."
"Uhum." Shi ne kawai furucin da Sadiya ta yi sannan ta miƙe tana mata sallama. Ta gifta ƴanmatan biyu dake zaman jiran a yi musu ƙunshi ta fice.
Tana shiga gidansu ta tarar Inna na sallar Azahar sai kawai ta fa
ɗ
a
ɗ
akinsu da sallama. Husna ta
iske riƙe da waya tana ƙyaƙyata dariya ga dukkan alamu chatting take yi. Tana ganinta ta miƙe zaune fuskarta
ɗ
auke da ƴar damuwa har Sadiya ta cire hijabinta tana ƙoƙarin ninkewa.
"Sis, anya kuwa? Wai kodai na ƙara yi wa Yaya Huzaif magana ne? Ni na t
sani ganinki cikin damuwarnan."
Sadiya ta dube ta, tuni Husna ta fara hawaye. Sai ta ji haushin kanta ya kama ta ma. Don me za ta dinga sanya masoyanta kuka har haka?
"Ba fa damuwarsa ba ne, kawai raina ne babu da
ɗ
i yau."
Husna ta share hawayenta
ta sauke ajiyar zuciya.
"Har na ji sanyi. Dama za ki ban dama ai da na sami Abba na mishi..."
"A'a, bana so. Mu bar zancen kafin ma Inna ta tsinkaya."
Daga haka ta mike ta fice a
ɗ
akin, Husna kuwa ta bi ta da kallo tana mata gwalo kafin ta toshe
bakinta sakamakon dariyar da ta kama ta. Hauka take yi za ta bari sulhu ya shiga tsakanin Huzaif da Sadiya? Ko na farkon ma da ta ce mata ta yi masa zancen yace baya son maganar ƙarya ce kawai ta mata don kada ta yi tunanin ba ta yi ba. Yanzun ma da shi su
ke hira, koyaushe cikin ba ta labarin ƙasar Indiya yake yi. Ita ma haka za ta yi ta labarin gida da abin da ke faruwa amma koda wasa ba ta ta
ɓ
a sanyo mishi batun Sadiya ba, shi ma kuma haka. Wannan ne yake ƙara yi mata da
ɗ
i.
***
Bayan Watanni Biyar.
..
Abubuwa da yawa sun fara masu da
ɗ
i da akasinsa, marasa da
ɗ
in kusan gaba
ɗ
aya kan Sadiya ya ƙare a gidan, kamar dai abin arziƙi, Huzaif ya dawo da kula ta bayan sulhun da Anti Hafsatu ta yi musu. Ita
ɗ
in ma a zuwan da Sadiya ta yi ne gidanta hutu baya
n ta yi Candy ya sa ta fahimci akwai matsala tsakaninsu. Da kanta ta yi kiransa a waya ta whatsapp suka yi doguwar magana. Ta kula dai kamar kame-kame ne zantukansa marasa dalili, ƙarshe ta saka Sadiya ba shi haƙuri, shi ma ya ba ta.
Rayuwar ta
ɗ
an koma
musu daidai amma fa ba ta bar fuskantar matsala daga wurinsa ba. Sai ta yi magana ya ƙi kula ta, kuma a gefe sai ta ji Husna na fa
ɗ
in ai ba su jima da yin magana da shi ba. Wannan kan yi mata ciwo matuƙar gaske. Ba don tana ji a jikinta cewa Husna ba za ta
ta
ɓ
a ba da fuskar su yi soyayya da Huzaif ba da ta ce kodai soyayyar suke yi.
A haka har suka ci wa
ɗ
annan watannin, lokacin yaye Huzaif ya yi, Abba da Mami suka shirya suka tafi. A bakin Meenat take ji ai tuni Yayyunsa mata Radeeya da Lubna sun soma ha
ɗ
a lefe don a lokacin da aka saka na biki ya kasance Huzaif na dawowa za'a
ɗ
aura aure.
Sosai Anti Hafsatu ke zuwa gidan tana kawo wa Sadiya kayayyaki na gyara hakanan Safiyya ita ma tana nata kokarin. Inna dai kallonsu kawai take yi abin na burge ta ya
dda yan uwan ke ji da Sadiya a yanzun. Husna gaba
ɗ
aya zaman gidan ya fice mata a rai, damuwa sosai take shiga. Ranar da Yaya Lubna da Radeeya suka zo gidan har suka dauki awon undies
ɗ
in Sadiya wuni ta yi kuka wannan ne dalilin da ya jawo ta tattara ta ko
ma gidan Hajara bayan Hajarar ta kira Malam ta yi ƙaryar rashin lafiya.
"Anti don Allah kada ki bari na rasa Yaya Huzaif. Na rantse mutuwa zan yi. Yanzu fa sosai muka shaƙu da shi, ya ce min ba ya kaunar Yaya Sadiya, ya dauke ni abokiyar shawararsa."
Husna ke zancen a mugun firgice sa'ilin da ta ke zaune gefen Hajara tana kuka tamkar ranta zai fice. Hajara ta shiga rarrashinta gami kafin ta ce.
"Kar ki sake ki sanya damuwa a ranki. Na fa
ɗ
a maki Huzaif ba zai ta
ɓ
a auren Sadiya ba. Ke ce matarsa. Y
anzu dai ki zuba idanu ki bari ya dawo. Komai da zai faru za ki ganewa kanki. Za kuma ki sha mamaki kin ji ko? Ke ko biki kika ga an soma kar ki sake ki tashi hankalinki. Ni na san me na taka."
Husna dai ta ji ne kawai ba don ta gasƙata ta ba, ta yaya z
a ta fasa damuwa alhalin ga shi nan komai na ta tafiya cikin tsari?
Ita kuwa Hajara hankalinta kwance kasancewar ta yi imani kwarai da abin da Bokanta ya ce. Aiki ne ba na wasa ba zai soma tasiri a kan Huzaif duk ranar da ya sa ƙafafunsa a ƙasar nan. K
omai zai juye masa ya ji nan duniya babu wacce yake so da aure kamar Husnarta. Wannan ne ya sa ta ji nutsuwa sosai.
***
Ana gobe za'a kawo lefe su Abba suka dawo amma babu Huzaif wanda ya tsaya ƙarasa wasu abubuwa da ya shafi makarantarsu. A bakin Ma
lam ne Sadiya ta ji cikin satin bikin nasu ne zai iso wato ana gobe
ɗ
aurin aure. Ita dai gabanta kawai faduwa yake yi, Abba na dawowa gari da kwana uku aka kawo lefe na gani na fa
ɗ
a can babban gida kamar yanda Malam ya tsara. Jerin akwatuna har saiti biyu
ɗ
auke da tsadaddun kayayyaki. Husna kasa zuwa wurin ta yi, Hajara kuwa duk da ta san da shirinta sai da ta ji kamar ta yi hauka ganin tarin dukiyar da aka zuba da sunan mallakin Sadiya. Ta ƙara cin alwashi a rai ko za ta yi yawo tsirara auren Sadiya ba zai
ta
ɓ
a faruwa ba a duniyar nan dai.
Sadiya kuwa duk da ramar da ta yi amma fa ta yi kyau sosai irin na gyaran Amare. Fatarta har wani sheƙi yake yi. Ɓangaren su Inna ma haka suke ta yi mata shirin da ya dace. Zahra wacce tuni ta riga Sadiya aure amma ko
mai ake yi da ita don Mijinta ya san irin shaƙuwarta da Sadiya wannan ne dalilin da bai hana ta taka nata rawar ba.
Babbar damuwar Sadiya lokacin bai wuce na shafe sati uku da ta yi babu wata magana tsakaninta da Huzaif ba, koda ta yi ba ya amsawa. A b
aya yakan amsa da ok, yes, no da sauransu, amma ban da yanzu. Tunaninta wane irin aure za ta yi babu kulawar miji?
Ranar Litinin ma ƙunshi Zahra ke ranga
ɗ
a mata na bikin da za'a fara ran Laraba amma kuma hawaye take fitarwa. Fa
ɗ
i take yi
"Ta ya ya
Zahra? Ta ya ya za'a ce zamu yi aure haka kamar irin na dolen nan? Meyasa Yaya Huzaif zai aure ni idan ya bar sona? Meke faruwa ne wai?"
Zahra ta dakata da ƙulle ledar da ta saka a ƙafar da ta zanawa lalle ta yi tana jin ita ma nata idanuwan na ciccikow
a da hawaye, don haka a raunane ta ce.
"Ya zan maki Sadiya? Ya ki ke so a yi? Na ce maki mu sanar da manya don su san halin da ake ciki kin ce kina gudun fa
ɗ
an Malam kar ya ga kamar ke ce bakya so. To don Allah idan ba su ji ba ta yaya za'a magance wan
nan matsala?"
Sadiya ta ha
ɗ
iyi miyau tana sanya bayan hannunta ta share hawayen dake saman fuskarta dalilin tafukan hannun rufe suke da leda wanda Zahra ta
ɗ
aure bayan ta kammala zanen ƙunshi.
"Ba zan iya ba, dagaske laifina za'a gani tunda shi bai
fito ya nuna ba ya son auren ba, zan
ɓ
ata zumunci. Shirun ya fi alheri."
Zahra ita ma ta share nata hawayen.
"Ba ki fasa addu'ar da na ba ki ba ko?"
Sadiya jinjina kai tana jan majina. Zahra ta ce.
"To ki sa a ranki da yardar Allah komai zai da
idaita. Allah zai maki za
ɓ
i. Sadiya ba za ki ta
ɓ
a auren wanda zai wulaƙantaki ba. In sha Allahu komai zai wuce ya daidaita tsakaninku. Kin ji? Ki bar kukan nan kada Husna ta dawo ta ganki itama ta rikice."
Sadiya ta ƙara gya
ɗ
a kai tana share fuskarta so
sai.
Husna dake la
ɓ
e a zauren gidan Zahra tana jin su ta yi murmushi da ƙwafa.
'Ai ba za ki ta
ɓ
a auren Yaya Huzaif ba Anti Sadiya. Za kuma ki gani.'
Ta furta a ƙasan ranta tana gyara zaman ledar lemo mai sanyi da ta kar
ɓ
o musu a shago. Daga nan
ta yi sallama ta shiga ciki. Ba ta nuna musu ta ji komai ba. Ana kammala yi wa Sadiya ƙunshi ita ma ta miƙa nata hannun.
"Ni dai a yi min irin na Anti don Allah." Abin da ta ce kenan. Zahra ta harare ta.
"Ba ki da wayo amma, ta ya ya za'a yi maki ƙ
unshi irin na Amarya? Sannu kin ji ko."
Husna ta
ɗ
aure fuska ta dubi Sadiya.
"Sis don Allah a yi min irin naki. Mene ne a ciki?"
Sadiya ta yi murmushi. Ita ta taya Husna roƙon Zahra akan ta yi mata babu komai. Zahra ta rantse ba za ta yi ba, wann
an ya sa Husna
ɗ
aukar zafi ta ce ta fasa ƙunshin za ta je a yi mata a wani wurin. Zahra kuwa tace sai dai a yi hakan. Ƙarshe ma tana gama cin abincinta ta fice a gidan ta bar su da zummar za ta neman gidan ƙunshi.
"Ai kuturu da ku
ɗ
insa alkaki sai na ƙa
san kwano." Shi ne abin da ta ce a ƙarshe sannan ta sa kai ta tafi. Sadiya cikin takaici ta dubi Zahra.
"Ke dai akwai rigima wani zubin, mene ne ciki don ta yi irin ƙunshina?"
Zahra ta ja tsaki.
"Bana son hauka fa, kin ta
ɓ
a ganin inda aka yi wa w
ata irin ƙunshin Amarya kuma ƴan gida
ɗ
aya? To na rantse ba zai yiwu ba. Idan har ni zan yi mata ta jima ba ta yi fushin ba. Mahaukaciya kawai, sai ta je can ta ƙarata."
Ita dai Sadiya girgiza kai ta yi kawai, Zahra da Husna ai sun saba tamkar wasu saƙo
da saƙo. Kamar dai jininsu ne bai ha
ɗ
u ba sam.
Sai Magriba ta bar gidan Zahra don har baƙin ƙunshi ta zana mata mai
ɗ
an karen kyau. Ita ka
ɗ
ai ta koma gida madadin farko da suka fita tare da Husna. Har aka yi isha'i Husna ba ta dawo ba sai wuraren takw
as na dare. Lallen da ta yi har ya fi na Sadiya kyau, kowa ya gani sai ya yaba kuma ace inama a ƙafar Sadiya yake tunda ita ce Amaryar. Ita kuwa Sadiya ko a jikinta don ba wannan ne matsalarta ba. Lamarin Huzaif ya shafe komai.
Ranar kamu take jin batu
n dawowar Huzaif a daren. Meenat da ta zo gidan kwana ta yi ta zolayarta wai sai ta bar ƙunci tunda dai Angon ya iso gari. Madadin ma hakan ya yi mata da
ɗ
i, ba ta ji komai ba face fa
ɗ
uwar gaba.
"Ki tashi ki je falon Abba wai Yaya Huzaif ke son ganinki.
"
Abin da Husna ta ce kenan kafin ta juya ta fice a
ɗ
akin ta bar ƴanmatan dake ciki da yin gu
ɗ
a a kunnuwan Sadiya. Ita kuwa sai ta ji ƙirjinta na cigaba da lugude tamkar an ce ta je ga ajalinta. Daƙyar ta mike bayan Zahra ta yi mata ido, har lokacin ata
mfar da ta sanya na kamu ne a jikinta, fuskarta fayau don ta ce ita sam ba za ta yi kwalliya ba. Ta yafa gyalenta ta fito. Ba ta kula zolayar su Adda Ruƙayya da wasu a ƴan uwan Malam dake soye-soye da yanke-yanke duk na shirin yinin gobe ba, ta yi hanyar f
alon Malam da sallama
ɗ
auke a saman harshenta sannan ta sa kai ta shiga. Tana kuma ji a ranta ta shirya kar
ɓ
ar dukkan wani abu da zai zo da shi a wannan dare.
"Wannan ma ai zancen banza da wofi ne. Shi wani abu yake sha a can Indiyan da zai kawo mana
wannan wasan kwaikwayon? Ina aka ta
ɓ
a haka? Daga
kan Yaya ka koma kan ƙanwarta? Ba zai yiwu ba, bari na je na sami shi Alhajin, sai na dawo."
Malam ke maganar cike da tsantsar
ɓ
acin rai da mamaki don abin akwai
ɗ
aure kai kafin ya sa kai ya fice daga fal
on. Inna dake zaune ta kasa ce mishi uffan har ya fita balle kuma wata Yayar Malam
ɗ
in Inna Asabe da Ƙanwarsa da suke zaune a falon cike da jimami. Husna dake gefe kuka take yi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
Sadiya kuwa kallo kawai take bin kow
annensu da shi. Babu baka sai kunni, ji take idan ta dage akan sai ta ce wani abu, wannan karon kukan ba zai yiwu ba wataƙila ta shiga kwarara amai tsabar yanda zuciyarta ke tashi sanadin kukan da ta sha. Idanun sun