Showing 15001 words to 18000 words out of 137760 words
zama dole idan da so da kauna. Marigayiya Asma'u tana daga cikin masu kwantar mata da hankali da nuna mata muhimmancin hakuri, ta sani sarai Asma
'u ba fa da kishi irin na jahilai. Matar ta san me take yi sosai. Kuma tana ji a ranta koda ace ma Malam ya dauko aure, Asma'u ba za ta tashi hankalinta ba, sai dai soyayyar da kowa ya shaida Malam na yi wa Asma'un ne yasa babu wanda ya taba kawo mata zama
da kishiyar. Ga shi kuwa sai bayan rasuwarta ne ya yi auren.
Lokacin da aka yi auren Abba da Amaryarsa Zulfa'u ne, Malam ya yi rashin matarsa Asma'u. Abba ya yi angwancinsa cike da jimamin mutuwar matar aminin nasa. Kar Haj Mariya ta ji labari, don za
fin mutuwar Asma'u da tashin hankalin da take ciki ya kara mantar da ita wani abu wai kishin Zulfa'u. Girkin ma gaba daya sakarmata ta yi har tsawon sati biyu saboda ba ta cikin nutsuwarta.
Hamza, Radeeya, Lubna, Huzaifa, Amir da Amira, Husna, Khalid d
a Affan. Su ne yaran Haj Mariya.
Amarya Zulfa'u wacce aka auro daga Maiduguri kuwa yaranta uku. Musaddik, Amina (Meenat) da autarta Zainab (Zee Mama).
Hamza ya yi aure yana zaune da iyalinsa a Kaduna inda yake a barikin soja, Radeeya da Lubna su na
zaune a nan Kano da mazajensu. Sai ko Huzaifa da ke ƙasar India inda yake karantar fannin medicine. Amir da Amira suna dab da yin candy, Husna da Musaddik kuwa suna aji na farko a babban sakandire, yayinda Meenat ke aji na biyu a firamare, tare suke tafiya
da Sadiya. Sai ko Zee Mama da suke tafiya aji guda da Husna.
Wadannan su ne zuri'ar Alhaji Abubakar B Shara
ɗ
a.
Tun daga sadda ya yi magana kuma, Sadiya da Husna suka koma lesson a gidansa a daki na musamman wanda ya ci sunan Study Room don babu ko
mai a ciki sai litattafai da sauran kayan karatu, nan inyamurar malamarsu ke koyar da su tare da Meenat da Zee Mama sai ko Husna da Musaddiƙ.
***
A lokacin ne samari suka dinga
ɓ
ullowa suna son Hajara, aikuwa duk wanda ya kawo kyauta to fa ita da Hus
na ke sanyawa a gaba su karar, idan na amfani ne na manya ta yi abin ta, idan kuwa kudi ne siyayyar akan Husna yake ƙarewa. Sadiya ko oho, sai ko idan Husna ta turje akan lallai sai an yiwa Sadiya ne saboda tana kaunarta sannan Hajarar ke yi tana kiranta d
a mayya kwadayayya.
Shekara na zagayowa ta sake maimaita jarrabawar Jamb. Sai dai wannan karon ma sakamakon bai kai yanda ake buƙata na medicine ba, ta sha kuka a karshe don kanta tace ta hakura za ta nemi nursing. Shi kuma cikin ikon Allah ta hannun A
lhaji Abubakar wanda tsabar aminta ne yasa Malam sanyawa dansa sunan suke ce masa Baba Habu, ya nema mata gurbin nursing din. Sadda aka yi jarrabawa ta yi nasarar tsallakewa. Murna kamar ta yi me. Shi kansa Alhaji Abubakar wanda suke kira da Abba ya yi far
in ciki kwarai da Hajara ba ta watsa mishi ƙasa a ido ba.
Aikuwa ana soma karatu ta maida hankali sosai, hakan ya sa ma ta rage shiga harkar Inna Mairamu, ita ma ta samu salama.
Sadiya ta taso yarinya marar son hayaniya a wasu lokutan kamar dai Inn
arta, amma fa ko a kafa ba ta kama Inna a bangaren hakuri ba, Inna takan ji za ta iya yafewa mutum, ita kuwa Sadiya abu daya ta rike a ranta, Hajara da Safiyya da ma sauran yayyunta idan an cire Yaya Zakari da Anti Hafsatu, babu wanda ke son su ita da Inna
rsu. Shiyasa ita ma ba ta son su, koda dai tana mugun tsoron Anti Hajara don ko muryarta ta ji sai gaba daya ta ru
ɗ
e, ko wasa take yi a
ɗ
aki za ta hanka
ɗ
e kayan wasan nata wani lokacin har tana bugewa haka za ta shige har bayan gadon Inna ta
ɓ
uya tana rawa
r jiki. Sai da Inna ta ha
ɗ
a da roƙon Allah da yawaita addu'a kafin wannan tsoron ya ragu da kashi talatin. Ko inda Malam yake Sadiya ba ta zuwa idan Hajara na wurin, wani lokacin abinci kasa ci take yi idan an yi zaman ci sai dai daga baya ne Inna ke zuwa
ta kai mata
ɗ
aki ta ci.
A hankali kuma tana girma tana ƙara wayo tsoron na
ɗ
an raguwa ba kamar a baya ba.
***
Tafiya ta yi nisa, Sadiya na ajin farko a sakandire, Hajara ta kammala karatunta na Nursing. Lokacin shekarunta goma sha biyu a duniya,
yayinda Husna ke da shekaru tara. Ita kuwa tana firamare aji hu
ɗ
u . A wannan shekarar dai Hajara ta fara aikinta a karamin asibitin dake kusa da su kafin a cewar Malam, ta samu aiki a babban asibitin gwamnati. Tun fara aikinta kuwa sai idanunta ya kara bu
ɗ
uwa. Ita dai ba ta da kyau na a zo a gani, sai dai akwai dirin jiki ga uwa uba iya daukar kwalliya. Da wannan take jan hankalin maza. Kanta yana ƙara rawa da yanda suke ru
ɗ
ewa su na sonta. Haduwarta da wata abokiyar aikinta mai suna Nusaiba, ya kara jefa
rayuwarta cikin ru
ɗ
in shai
ɗ
an. Sanadiyyar Nusaiba ta koyi sakin jiki ga duk wani likita ko abokin aikinsu da ya nemi ya latsa ta, farko takan biye musu ne kawai don son zuciya da kuma jin dadin abin, sai daga baya ta fara kar
ɓ
ar ku
ɗ
i. Sai ya kasance ba ruw
anta, hatta club takan bi Nusaiba su je ta dinga fakewa da tana da night duty, sau daya Malam ke kawo ta a motarsa da magriba asibitin ya yi tafiyarsa, yana barin wajen za ta hau abin hawa ta nufi gidansu Nusaiba idan a ranakun ita ma ba ta da aikin kwana.
Manyan mutane sosai Hajara ta sansu, inda ba ta ta
ɓ
a tunanin takawa ba ta taka, sai ta ji a duniya ba ta da burin da ya wuce ta auri wani shahararren mai ku
ɗ
in. Don a yanda take
ɗ
an
ɗ
ana rayuwar kwana ko wuni a cikin AC ba ta jin za ta iya auren talak
a.
Sanadin wannan yawace yawacen nata ne ta ja Malam da Inna suka yi fada kawai don Innar ta ce Malam din ya sanya idanu a kan Hajarar don tana tunanin da matsala. Aikuwa ya hau ta da fada sosai kan cewa tana zargin
ɗ
iyarsa. A karshe har yajin kwana a sh
imfida daya ya yi da ita. Ya bar cin abincinta, sai dakyar Inna Mairamu ta samu suka dawo daidai. Tun daga lokacin ta dauke idanu akan Hajara, ba dai ta cire ta cikin addu'o'inta ba da yi mata fatan shiriya.
Ta sanadiyyar wani babban Alhajin da take mu'
amala da shi kuma mai fa
ɗ
a a ji a gwamnatance, ta samu gurbin aikin jinya a asibitin gwamnati na Malam
Aminu Kano. Ta rufe Malam da cewa neman aurenta yake yi shi ne dalilin da yasa ya nemar mata. Malam sosai bakinsa ya ƙi rufuwa musamman da ya ga babban m
utum irin Alhaji Habibu Tofa ya tako har gidansa ya zo sun gaisa ya kuma yi masa bayanin cewa shi ya nema mata aikin saboda yana sonta da aure. Har da ba da hakurin rashin soma gabatar da kai kafin yin wannan karambanin, Malam ya nuna babu komai ya yi godi
ya sosai.
Koda suka fito daga wurin Malam sai da suka yi wata dariya da cafkewa ganin an shirga mahaifin mata. Har a ran Hajara za ta so ya kasance mamemin aurenta dagaske amma ya nunamata shi gaskiya ba zai iya ƙara aure yanzu ba tunda bai jima da yin
ta uku ba. A motarsa ma da sunan suna hira sai dai ya
ɗ
an yi wasa da ita sosai kafin su yi sallama.
***
Zakari wanda ya samu aiki a wani kamfani kuma daidai gwargwado ana biyan kirki, nan da nan ya gingimo aure, tarin lefensa sai ya kasance a wurin
Inna Mairamu yake yi. Hajara na kyallara idanu ta gani ai sai ta sanar da Safiyya da ma wasu a danginsu. Nan da nan abu ya nemi zama rigima wai don me sai a wurin Inna Zakarin zai yi tarin lefe. Malam bai dauki maganar wani abu mai zafi ba, ganin ma abin
kamar zai tashi hankalin gidansa ya tsawatar ya kuma hana kowace mace a dangi zuwa don yin maganar. Anan kam Inna Mairamu ta samu sa'ida, amma fa zagi takanas Safiyya ke zuwa ta yi mata har da su Allah ya isa. Ga kuma na Hajara. Mustafa da su Hashimu dai Z
akari suka yi wa caa wai don me ba zai yi shawara da su ba kafin ya kai mata. Har da cewa ba zasu ba shi komai na gudunmuwa ba.
Haka har biki ya zo aka yi shi cikin rufin asiri, Inna Mairamu wasu abubuwan ita ta yi mishi da kudin
ɗ
aya cikin tumakanta d
a ta siyar wanda take kiwo a wajen Kawu Jibo na gadonta. Ya ji dadi sosai da abinda ta yi hakanan Malam har godiya ya yi mata.
A Daura ya auro matarsa yar fulani da ita, har fulatanci tana ji hakan ya sa ta shiga ran Inna Mairamu sosai, sunanta Hameeda
. Iyakarta sakandire. Yarinyar na matukar girmama Inna, kuma tana kaunar Sadiya da Husna. Su kuwa su Hajara sai ta yi bakin jini a gurinsu tunda ita kadai ce a matan yayyun ke shiga lamarin Innar. Sauran duk basu wani damu da lamarinta ba.
***
Daga wa
nnan lokacin kuma sai tashin hankalin da ya biyo baya na fasa auren Hajara.
Mutum na farko sun ha
ɗ
u ne sanadin mahaifiyarsa da ya kai asibiti ba lafiya, yanda Hajara ta tsaya wajen nuna kulawa sosai gareta ne ya sa ya ji nan duniya ta burge shi kuma za
i iya aurenta, haka ma a
ɓ
angaren mahaifiyartasa ta yi na'am da Hajarar matsayin matar
ɗ
an nata. Saboda har suka bar asibitin Hajara kan je har gida ta gaishe ta. Ita kuwa Hajara ganin irin kudin da suke facaka da shi a asibitin da ma yanayin wayoyin da ya
ke amsawa yana batun ƙasashen waje, inda ya je da kuma dawowar da ya yi daga London saboda jikin Mahaifiyarsa da ya motsa duk su suka ru
ɗ
a ta, ta maida kanta wata salihar gaske a gabansu.
Ranar da Sunusi ya fara zuwa gidansu ya nemi iznin zance wurin M
alam kuwa, ai kwanan farin ciki ta yi. Har tana cewa Malam ita fa ta gaji ta
gani shi take son aure. A gaban Inna Mairamu ta cewa Malam kuma duk sadda ta yi aure da Husnarta za ta tafi. Malam dariya kawai ya yi, ya sani babu kunya ko kadan tsakaninsu da ya
ransa don yakan yi hira da su sosai. Ya sakar musu fuska hakan yasa wasu lokutan yake gane damuwarsu da ma wasu abubuwan. Sai dai duk irin ganiyarsa, yarda da ya yi da Hajara ya sanya bai ta
ɓ
a hasaso wai tana bibiyar maza a waje ba da sunan soyayyar shan m
inti. Ba dai ta ta
ɓ
a bari a kusanceta kusanta irin ta mata da miji, amma ban da hakan, komai ta aminta namiji ya yi da ita.
Watansu hudu tare da Sunusi, bayan sallah ƙarama ya turo aka sanya ranar aurensu har da ku
ɗ
i dubu dari mai matukar daraja a wanc
an lokacin. Kawayenta suka cika gida da yan uwa aka yi ta murna da farin ciki, Inna Mairamu ta sha habaici a wajen dangi inda wasu ke fadin ai fa Hajara ta yi goshi, kaf a yaran Malam ma babu wanda aka kawo kudin aurensa kamar nata, kuma an yi an gama ba z
a'a ƙara ba.
Abba ne ya dauki nauyin yi mata komai na kayan daki, Malam ya rasa kalmar da zai yi amfani da shi wajen godiya gareshi, ga kuma kayan abincin da za'a girka na gida yan uwansa maza sun ce basu yarda ya siya ko gishiri ba, su zasu yi. A cewa
rsu Hajiya Asma'u mutuniyar kirki ce ta mutane wacce ba ta da rowa sam, don haka burin da ta ci na bikin Hajara idan babu idanunta, to su za su bugi kirji su cikamata shi. Ga kuma uwa uba shi Malam din mai kokarin zumunci ne da kyautatawa yan uwa daidai gw
argwado. Watan tafiyar Alhazai na shiga aka kawo lefe na gani na fa
ɗ
a a lokacin, wanda sai
ɗ
an wane da wance.
Hajara kanta ya kara fasuwa, gyaran jiki na musamman ta je can makwafciyar Hafsatu ƴar Maiduguri take mata. Ga kayan ha
ɗ
e-ha
ɗ
en da ta samu na
wata daga Sokoto. Abin har daurewa Hafsatu kai ya yita kasa shiru tace.
"Wai Hajara ina kika san duk wadannan magungunan? Dama kin san ana yin su?"
Hajara dariya kawai ta yi ta basar yayinda mai mata gyaran jiki ke tarewa da fadin
"Ai ba za ta kas
a sani ba Malama, kar fa ki manta zamanin kullum sauyawa yake ƙara yi. Ba irin namu lokacin ba ne."
Da wannan Hafsatu ta ji mamakinta ya ragu.
***
Tashin hankalin da ya riski Inna Mairamu ana gobe daurin auren Hajara ne ya sa dole ta nemi iznin Ma
lam a daren ta fita zuwa asibiti don duba Kawunta Jibo da aka ce an kai shi bai san ma wanda ke kansa ba. Haka ta tsallake ta bar yan uwan Malam din da na maman Hajara sai ko yan bikin zuwa asibitin tare da Sadiya da ta dinga magiyar ta tafi da ita. Ita ma
ba ta musa ba ta ja
ɗ
iyarta suka bar gidan gudun zagi ko cin mutunci daga yan bikin.
Har hawaye ta yi ganin halin da Kawu Jibo ke ciki, wai hawan jini ne ya yi sanadiyar zubewarsa a dakinsa, Allah ya taimaka Dada da kusa. Da
taimakon makwafta da
ɗ
ansa
wanda bai fi sa'an Safiyyar Malam ba, Sharu, suka kai shi asibiti. Sharu ne ya kira a waya ya sanar da ita.
Jikin da sauki don likitan ya ce zai tashi da yardar Allah. Ta jima anan sai daga baya Dada ta saka Sharu ya tare mata abin hawa ta tafi gida d
a zummar gobe za ta yi sammakon dawowa kafin a fara hidimar biki.
Washegari kuwa da sassafe ta je asibitin da abin kari, Malam bai samu shiga na sai saƙon gaisuwa da ya bayar yace a yi ga Kawun zai shiga ya duba shi bayan daurin aure, ganin har Kawu na
magana hankalinta ya kwanta. Shi ya ba ta umarnin komawa ga hidimar bikin idan yaso daga baya ta dawo tare da mijinta. Da wannan Inna Mairamu ta koma gidan hankalinta kwance, sai dai na mutanen biki a tashe.
Ta yi saroro a tsakar gidan ganin Hajara da
Safiyya sun ha
ɗ
a kai suna runtuma ihun kuka, wasu a manyan ma sharce hawaye suke yi. A bakin Hafsatu take ji wai Sunusi ya fasa auren Hajara kuma ma wai ya bar mata komai na kayan da ya kawo. Salati Inna Mairamu ta saki don ba karamin razana abin ya sanya
ta shiga ba. Jin lamarin ta yi tamkar ga ƴar cikinta ya faru. Hawaye ta shiga matsewa. Ta karasa da zummar rarrashin Hajara aikuwa ta yo kanta.
"Munafuka algunguma! Ni dama na sani! Tun ganin da na yi maki ki na safa da marwar shige da fice a daren jiy
a da safiyar yau jikina ya ba ni wata baƙar muguntar ki ke shirya min. Me na yi maki Mairamu da za ki datse min igiyar farin cikina tun ban kai ga
ɗ
an
ɗ
ana ba? Allah ya isa tsakanina da ke! Ni dama na san tun da aka kawo kudina ki ke bakin ciki da hakan! Do
n ba Sadiyarki ce ta samu miji kamar nawa ba! Wayyo Allahna, mutuwa mai yankan kauna ta raba ni da uwata abar sona!"
"Ke Hajara yi min shiru haka, bana son hauka."
Cewar Haj Mariya a tsawance kafin ta ja ta su yi daki tare da wasu a yan uwa. Wasu kuw
a suka yi wa Inna Mairamu caa wacce ta yi tsaye tana
ɗ
igar da hawaye ta ma rasa kalma
ɗ
aya da za ta yi amfani da ita wajen kare kanta. Kai ka ce ba ta sanar da su halin da
ɗ
an uwan mahaifinta ke ciki ba har ma suka bi ta da addu'ar nema masa lafiya. Kowa
ya shiga zaginta daidai gwargwado sai kuwa su Mama Iyabo da wasu a yan uwa masu kare mata. Ranar tashin hankalin da Inna Mairamu ta shiga Allah ka
ɗ
ai ya sani.
Da zazzabi sosai ta kwana ban da kuka da ta ci ga Sadiya da Hafsatu masu taya ta da kuma ba t
a hakuri. Zakari ma shiga da fita ya dinga yi yana ba ta hakuri. Haj Mariya duk da ba wani shiga harkar Innar take yi ba, amma ba ta wani tsane ta, sai da ta shiga ta ba ta hakuri dangane da abin da Hajarar ta yi gami da nunamata ba ta cikin nutsuwarta ne.
Karshe ma gidan Abban ta wuce tare da ita bisa umarnin Abban da ya cewa Malam ya dace Hajara ta dan bar layin na
ɗ
an lokaci.
***
A ka yi wannan ta wuce, tsana mai tsanani na Inna Mairamu ya ninki a zuciyar Hajara. Ko