Showing 21001 words to 24000 words out of 137760 words
rayuwarta, sai dai meyasa sai Innata? Meyasa ita mafi yawa ke zargi da wannan
ɗ
anyen aiki? Ashe ba su yarda cewa Allah ya isa ya gudanar da mulkinsa yanda ya so ba? Allah da kansa ya ce zai jarraba wa
ɗ
anda suka yi imani, ta ya ya idanun jama'a ke rufewa ba sa ganin gaskiya? Son zuciya ko kuwa dai tsantsar rashin tawakkali ne?"
"S
on zuciyar ce Sadiya, sai kuma tsanar Inna da ya riga ya dasu a ransu har ta yi girma kuma ta yi rassai. Ki ma bar tunanin nan, babu abin da za ka yi ka burge wasu mutanen, maida hankali kawai ga rayuwarku, shiyasa Inna ke burge ni. Tana iyakar kokarinta w
ajen kulawa da su da zuciya daya, abin da ta ga ya fi ƙarfinta kuma ba ta matsawa kanta, sai ta maida komai ga Allah."
Sadiya ta share hawayen da ba ta san sun fara zubo mata ba. Girgiza kai ta
ɗ
an yi.
"Inna tana da karfin zuciya ba irin tawa ba. Ni
na san yanda nake ji a kirjina duk lokacin da Anti Hajara ko Anti Safiyya suka ya
ɓ
a wa Inna magana a cikin gidan nan. Ba zan iya maida musu martani ba na sani Zahra, amma kuma hakan ba ya hana zuciyata jin wani irin zafi."
"Ki yi hakuri Sadiya, ki ƙara
hakuri da addu'a. Komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba."
Ta yi wata ƴar dariya marar sauti ko hayaniya.
"Ki ka ce kamar ba'a yi ba? An yi da yawa, abubuwa sun faru ba ka
ɗ
an ba wanda koda ace sun manta, ba zan iya mancewa ba."
Zahra ta share hawa
yenta, tana da saurin kuka da raunin zuciya musamman akan abin da ya shafi rayuwar Inna da Sadiya. Ba ta son ta ƙara mata damuwa sai kawai ta wayance da miƙewa tsaye.
"Ni zo ki raka ni, mu bar wannan maganar. Ba zamu iya gyaran komai da baki ba, duk abi
n da ya fi ƙarfinmu bai fi ƙarfin Allahu ba. Don haka mu cigaba da addu'a. Haba ta Isma'il,
ɗ
an murmusa mu gani. Yace yana son fara ko mayya ce, da ya tashi sai ya ha
ɗ
u da ke." Ta ƙarashe da dariya. Sadiya ta ja tsaki tana kai mata duka ta goce.
"Allah
ya yi min tsari, ai ko maza sun ƙare ba zan auri wannan mayen matan ba. Gwara ma ya tattara komatsansa ya koma ƙauyensu ya cigaba da noma."
Ta ƙarashe tana kokarin warware hijabinta da ke ninke a hannun kujera, sadda ta idar da sallar la'asar ne ta bar
shi a nan.
Zahra wacce har a sannan dariya take yi ta amsa.
"Ke fa ƴar rainin wayo ce, Jigawar ce ƙauye?"
Ta
ɓ
e baki Sadiya ta
ɗ
an yi tana mai kokarin fita daga falon ta ce.
"Ni dai muje ki gaida Malam sai ki tafi. Kar ya ga na fita da yamman
nan."
Suka ƙarasa kuwa da sallama falon Malam din, yana zaune har ya watsa ruwa ya sanya ƴar tshirt mai gajeran hannu da dogon wando marar nauyi, Zahra a ranta tace gidan ƴan boko kenan. Ita a gidansu babansu ai ba ta jin ta ta
ɓ
a ganinsa da kananan kay
a da girmanta dai. Shi kuwa Malam babu ruwansa, sam ba ya son abin da zai takura jikinsa. Wasu lokutan ma idan bokon ya motsa, shigar riga da wando irin na ma'aikata banki yake yi ya wuce kasuwa abin sa musamman a yanayin sanyi.
Malam ya amsa gaisuwart
a fuska a sake yana tambayar baban nata. Ta amsa da lafiyarsa kalau. Nan ta yi sallama da Inna suka fice tare da Sadiya.
A hanya ma hirar makarantarsu suka dinga yi da sauran ƴan ajinsu har sai da Sadiya ta saki ranta sosai. Ba su yi wani nisa ba suka
rabu don ta rantse ba yau za ta shiga gidan su Zahrar ba. Sun saba dama irin wannan rakiyar tunda layinsu daya amma akwai tazarar sosai a tsakanin gidajensu. Su na farkon shigowa layi, ita kuwa Zahra suna can ƙasa ka
ɗ
an. Idan Sadiya ta je gidansu ana hira
a hanya har sai ta rako ta ƙofar gida zasu ankara, hakanan ita ma idan ta tashi yi wa Zahrar rakiya. Wannan karon ba ta bari sun yi hakan ba ta ja tunga jin an fara kiraye-kirayen sallar Magriba, haka suka rabu da zummar sai goben idan an ha
ɗ
u a islamiyya
don ba bokonsu
ɗ
aya ba kuma ana cikin hutu ma sauyin aji za'a yi idan sun koma. Ita Zahra ta gwamnati ma take yi yayinda Sadiya ta ku
ɗ
i ce.
***
Da sallama Haj Mariya ta shiga falon Abba wanda ke amsa waya, ta ƙarasa ta nemi wuri ta zauna ganin yanda
yake ta fara'a ta ji kamar ta canki da wanda yake wayar. Ba ta tabbatar da zatonta ba sai da ta ji ya ce.
"Toh ni dai wannan maganar ba ni ya dace na yiwa Mamin taka ba, kai ya kyautu ka sanar da ita. Ga ta nan."
Nan da nan fuskarta ta cika da annur
i, ta kar
ɓ
i wayar tana mai duba sunan. "Huzaif Abubakar." Haka dama Abban ke adana lambobin yaran nasa a waya. Cike da zumu
ɗ
i ta amsa wayar da sallama. Bayan gaisuwa ta tsinci muryarsa mai taushi yana fadin.
"Mamina, na yi kewarki sosai."
Murmushi ta
yi mai sautin da ta san zai shiga kunnuwansa.
"Kai fa da
ɗ
ina da kai kenan, idan ka yi abu sai ka ce Affan ko Zee Mama. Ina ce jiya ma mun gaisa da kai."
Ta na jin sautin nasa murmushin kafin ya ce.
"Na fi shekaru uku rabona da gida kinga kuwa ai
ba ni da maraba da su, sun ma fi ni gata tunda koyaushe kuma tare da su. Ni ma toh albishir zan maki cewa ina dab da zuwa na ganku na koma. Amma fa ba zan ce ga lokaci ba, sai dai kawai ku gan ni. Watakila nan da kwanaki, ko sati, ko watanni."
Ta
ɗ
an
ɓ
a
ta rai.
"A'a Huzaifa, fa
ɗ
amin rana
ɗ
aya don a shirya maka tarbar da ta dace."
"No Mamina, ke dai ku zama cikin shiri. Watakila ke ma jikinki ya ba ki isowata ƙasar irin yanda ya faru a film din Kabhi Kushi Kabhi Gam."
Ta yi dariya.
"Sannu ba'i
ndiye, zama cikinsu ya sa ka fara daukar
ɗ
abi'unsu ko? Toh ni ban koyar da kai wannan hali ba. Allah ya kaimu, ya dawo da kai lafiya."
Ya na dariya ya amsa da amin.
Nan ta miƙawa Abban nasa suka yi sallama kafin kuma ta dube shi.
"Wai dagaske yake y
i? Kuma bai tsayar da ranar zuwa ba?"
Abban ya yi dariyar zancenta. Ya na taunar dabinon da ya siyo mai taushi irin na Saudiya ya ce.
"Huzaif ne fa, ko kusa bai ba ni rana ba. Ya dai ce a yi maki albishir ya kusa zuwa gareki, shigowarki ta sanya na b
a ki wayar. Kin san shi ya maida mu kamar kakanni a wasu lokutan."
Ta
ɗ
an
ɗ
aure fuska don ita dagaske ta matsu yaron nata ya dawo kusa ta gan shi duk kuwa da cewa sukan yi video call wasu lokutan.
"Shikenan ai, Allah ya kawo shi lafiya."
Abba ya a
msa da amin ba tare da ya ce komai bisa sauyin fuskarta ba. Idan da sabo dama ta saba mitar rashin dawowar Huzaif din, balle kuma yau din da ya yi mata
ɗ
an
ɗ
ani haukaci, gaba
ɗ
aya za ta dinga zuba idanu ne ta ga ta inda zai
ɓ
ullo kuma yaushe.
Dakyar ya
samu ta saki fuska ta mance da batun Huzaif a
ɗ
an taƙin.
***
"Wai Hajara dagaske fitar za ki yi? Ba za ki yiwa kanki fa
ɗ
a da biyewa su Waleeda ba a wannan asibitin?"
Nudrat ke zancen tana dubanta cike da mamakin ganin yanda ta yi shiri tsaf cikin
wani arnen leshinta ruwan madara wanda ta samu tun a lefen da Sunusi ya yi mata. Gaba daya kirjinta a bu
ɗ
e sai ko ƙugunta wanda tsabar matsa da siket
ɗ
in ya yi mata kamar zai yage. Mamakin Nudrat bai wuce yanda Hajara ta ƙi karatun ta nutsu a rayuwarta ba
, ta ya ya za'a ce neman aurenki na tarwatsewa amma har ki kasa barin munanan ayyukan da ki ke aikatawa? Kuma babban abin da ya tsorata ta bai wuce ganin yau har allurar hana
ɗ
aukar ciki ta yi ba, kenan hakan na nufin za ta soma bada kai bori ya hau?
"P
lease Sister Nudrat ki fita a rayuwata! Wai mene ne dalilinki na yi min kutse haka? Duk cikinmu ni ka
ɗ
ai ki ka takurawa! Sauran da suke fitar me ya hana ki sanyamusu idanu haka?"
Murmushin takaici Nudrat ta yi sa'ilin da Hajara ta dauki zundumeman hijab
inta har yana sharar ƙasa ta zura.
"Allah ya baki haƙuri, ina yawan yi maki maganar ne saboda na damu da ke ne. Ina tausayin yanda ake fasa aurenki. Kuma ina maki kallo kamar wata ƙanwata ku..."
"Ya ishe ki, kar ki fama min tabon da har gobe ina jin
ra
ɗ
a
ɗ
insa. Ki bar yi min kallon ƙanwartaki tunda dai babu abin da ya ha
ɗ
a mu sai aiki. Ba na son sa ido da shiga sharo ba shanu. Mtsw."
Wayarta dake ƙara ta cire a chaji don tsabar
ɓ
acin ran da Nudrat ta jefa ta ciki har tana kokarin mantawa da ita. Ga
nin sunan Dakta Sani na yawo saman wayar ya sanya ta ƙin
ɗ
agawa tana mai jan guntun tsaki. Ita fa ba ta son takura, mutum ba wani abin kyautar arziki ya ke yi wa mace ba amma sai jarabar tsiya. Gaba daya ta saka wayar da chajar a cikin jaka ta zuge zif kaf
in ta fice ta yiwa sauran ma'aikatan sallama da zummar ta tafi gida alhalin wasu a ciki sun san dawan garin. Wasu kuwa har gobe sun kasa yarda da abin da ake fa
ɗ
i a kanta, suna yi wa hakan kallon ƙarya da kuma ƙage.
Sai da ta fice daga asibitin gaba da
ya kafin ta tari abin hawa zuwa Zoo road inda anan me su Waleeda ke jiranta domin ziyartar gidan wani babba kuma hamshaƙin
ɗ
an siyasa dake gidan hutunsa tare da wasu abokan ashararancinsa suna jiransu. Saurin da take yi don ta je bai wuce jin cewa wannan
karon akwai wani babban aiki da zasu ba su ba wanda hakan zai ba su damar mallakar ku
ɗ
a
ɗ
e masu nauyin gaske da ba su ta
ɓ
a zato ba. Ana sauke ta daidai gaban wani katafaren Mall dake wajen ta dubi Waleeda,
Blessing da Azeema abokan aikinta da halinsu ya y
i mugun zuwa
ɗ
aya don wata ƙazantar ma da suke shukawa ita ba ta ko rabinsa ta ce.
"Sorry, na
ɓ
ata maku lokaci."
Blessing wacce ta ji hausa kamar jakar Kano ta ce.
"Ai mun dauka wancan mayen Daktan ne ya tsaida ki."
Ta yamutse fuska, ba wanda
bai san nacin da Dakta Sani yake yi ga nurses mata ba a asibitin babu ma kamar sabbin zuwa. Wacce halinsu ya zo daya su daidaita, wadanda kuwa ba halinsu kenan ba su nemi tona musu asiri sai ya ja jikinsa.
"Rabu da dan duniya, na ga yana ta kirana har
a hanya da nake tafe, banza na yi na rabu da shi. Ana harka da manyan ƙwari wa yake ta shi? Ai yau da shirina na fito ko me zai faru ya faru."
Suka yi dariya gami da shewa. Daidai lokacin da Waleeda ta shiga amsa waya tana yiwa direba kwatancen inda su
ke. Ba jimawa sai ga wata lafiyayyar mota baƙa wuluk mai bakaken gilasai ta faka a gabansu, suka bu
ɗ
e suka shiga. Anan ne Hajara ta cire hijabinta ta shiga kwalliya a fuskarta. Ko mayafi ba ta yafa ba. Koda ta kammala shirinta, shiru ta yi tana duban waje,
tana ji ƙirjinta na faduwa don yau ta rantse koda ace budurcinta zai tafi, to fa ta shiryawa hakan, a ganinta tunda aure ya gagare ta, ai komai ma yanzun za ta iya aikata shi. Tsanar Inna na ƙara ninkuwa a zuciyarta, ta sani ita ce silar jefa ta wannan mu
mmunan tafarkin, da ace ta bar ta ta yi aure da hakan duk bai faru ba. Watakila da yaranta biyu. Mace da namijin da zasu ci sunan iyayenta mafi soyuwa a ranta. Ta tuno da Sadiya, ƙwafa ta yi. Ta rantse sai ta tarwatsa rayuwar Sadiya ko ta wace hanya ce yan
da Innarta ta tarwatsa nata. Sai da Azeema ta ta
ɓ
a ta tana magana kafin ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ita da Blessing da Waleeda kadai ne masu aikin jinya a asibiti, Azeema kawar Waleeda ce mai zaman kanta. Asalinta ma ƴar Kaduna ce ta zo ta kama haya
a Kano saboda iyayenta sun yafe ta adalilin barikin da take yi na gaske iyakar karfinta da jiki. Wannan ta sanya suka hade kawunansu suna cin karensu babu babbaka. Nusaiba kuwa wacce ta samu aiki a babban asibitin gwamnatin da ke can wajen garin Kano ya y
i sanadin ja baya da alaƙarsu sai ko ta waya. Kusan koyaushe sai Nusaiba ta kira ko ta ta
ɓ
o ta a chat su yi hirar rayuwa. Ita ma har lokacin ba ta yi aure ba, abin da ta ga dama take yi.
Dama kullum hu
ɗ
ubarsu ga Hajara bai wuce ta saki jiki ta bada kai bo
ri ya hau ba. Ita da ta san dukkan wata hanya ta tsarin iyali ai ba za ta ta
ɓ
a daukar ciki ba. Kuma koda aure ne ya tashi sun ci alwashin yi mata
ɗ
inkin da babu wani
ɗ
a namiji da zai gane ta ta
ɓ
a bariki.
Ba ta taba ji a ranta za ta dauki hu
ɗ
ubarsu ba s
ai a yanzun da ta ke jin haushin auren ma tunda ba a yarda ta yi sa ba. Har suka isa jefi-jefi take tsoma musu bakinta a hirarsu.
***
"Ba wani aiki ne mai wahala ba a wajenku ma'aikatan abin, muna buƙatar mabiyar jariri, wato mahaifar da ke tahowa t
are da jarirai har guda biyar. Idan har ku ka yi mana wannan ƙoƙarin muka samu, muka kuma yi
nasara kwalliya ta biya ku
ɗ
in sabulu har muka hau wannan kujerar mulkin, toh muna rantse muku sai kun za
ɓ
i nawa ku ke da buƙata a wajenmu."
Gaba
ɗ
aya kusan a gi
gice suke kallon kallo tsakaninsu, babu kamar Hajara wacce ta ji kamar ta saki fitsari a wando. Aikin tsafi da asiri? Kuma wai ita ake buƙatar saka hannunta ciki?
Ta dubi Alhazan su uku, Alhaji Nasiru, Garzali da Nuhu. Miƙewa ta yi tana girgiza kanta
da ja baya har tana tuntu
ɓ
e da
ɗ
an kamfen Waleedah da ke yashe a tsakar falon.
"A'a, a'a, babu ni a cikin wannan tafiyar. Ba zan yi ba. Zan sadaukar muku da jikina ku cigaba da yanda ku ka so, ba kuma zan tona asirinku ba. Sai dai na rantse ba za'a yi
wannan harkar tsafin da ni Hajara ba!"
Daga haka ta shiga tattara kayayyakinta ta shirya tsaf, kallonta kawai suke yi babu kamar Alh Nuhu wamda ya ji hankalinsa ya yi mugun tashi, shi ne ya fara saninta a
ɗ
iya mace, kuma shi yanda yake ji ma a ƙoƙon ran
sa aurenta zai yi ba zai bari ta ku
ɓ
uce masa ba don ta yi masa
ɗ
ari bisa
ɗ
ari. Miƙewa ya yi ya riko hannunta dake faman rawa, kai duka jikinta ma rawar yake yi, ta tsaya tana dubansa.
"Kar ki yi mana haka Hajara. Mun ji, mun ji ba za ki tsoma hannunki a
cikin harkar nan ba. Amma ina za ki je yanzu a daren nan? Don Allah ki yi hakuri ki zauna mu kwana a nan, gobe sai ki tafi."
Hankali a tashe ta dinga girgiza kai, gaba daya ta ru
ɗ
e ta fisge hannunta, daƙyar ta yarda da batun Alh Nuhun wanda ya tsawatar
wa su Alh Nasiru masu yi mata bambamin cewa ba ta isa ta fita ba tare da ta aminta da batunsu ba ko kuma su dauki mataki a kanta. Ɗaki ya ja ta ya rufe daga shi sai ita, nan ya dinga yi mata alƙawarin ba zai bari a cutar da ita ta ko'ina ba. Ita kuwa ban d
a uban kuma babu abin da take yi. Anan ne fa ya rantse mata shi da aure ma yake sonta. Ta dakatar da shi ta ce sam ba ta son batu na aure. Ya dai ji ta, ya kuma yi shiru amma ba don ya kyale batun auren ba. Haka ya lalla
ɓ
a har ya maimaita abin da ya yi
ɗ
in
a farkon zuwansu masaukin nasu, a karshe ya cikamata asusun banki da zunzurutun kudade har miliyan biyu, wannan ba karamin gigita Hajara suka yi ba.
"Wallahi aurenki nake son yi Hajjo. Ki yi tunani ki ban damar da zan gabatar da kaina. Na rantse maki
za ki ji dadi fiye da tunaninki a zamantakewarmu. Sai kin zama cikin mata abin kwatance. Na ji labarin yanda ake fasa aurenki a bakin Waleeda, kuma hakan bai karyan zuciya ba. Ni zan aureki mu sha sha'aninmu son rai. Wancan maganar kuma da aka yi,