Showing 105001 words to 108000 words out of 137760 words
Su Maina da Lami
ɗ
o sai gani suka yi
an cigaba da daurin aure. Kamar a mafarki, kamar kuma almara ya ji muryar mai sanarwa yana shela a lasifika yana fadin.
"An
ɗ
aura auren Ibraheem Tafida
ɗ
a ga Mai Martaba Sarkin Gombe da Sadiya Sa'ad Shagari akan sadaki naira na gugan naira har dubu
ɗ
a
ri biyar."
Sai wuri ya
ɗ
auki kabbara. Malam ya share hawayen tsantsar farin ciki da dadi.
Mutane aka hau kallon kallo, Maina kuwa ya yi
ɗ
if! Ya ji duniyarsa na juyawa, da gaggawa ya kai duba ga Mai Martaba sai dai tuni ya sadda kansa sakamakon ha
ɗ
a
idanun da suka wanda kwarjinin ya yi mishi yawa. Ƙirjinsa ke bugu da ƙarfi, shi kuma? Shi dai Maina ko kuwa akwai wani Ibraheem Tafida bayan shi?
'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Ya furta a ƙasan ransa.
Sadiya gaba
ɗ
aya ta yi wuri-wuri da ita
. Tana zaune ne kawai a
ɗ
akin nasu tare da su Zahra da Nudrat wacce tun safe ta taho nan don ta ce ita
ɓ
angaren aminiyarta take, sai faman kai kawo na ajiyewa ƙawayen Sadiya abinci suke yi.
A farko ma yaƙe take bin su da shi daga baya fuskarta kadai ka ka
lla za ka shaida cike take da tarin damuwa. Ta ƙara duban agogon wayarta, ƙarfe uku saura mintuna. Hayaniyar da ke falon na ƴanmatan da shewarsu bai sa hankalinta kasa kai wa ga babban dan Anti Hafsatu mai shekaru goma sha uku ba, Ameer. Yanayin yadda ya s
higo falon kamar wanda aka jefo ka san cewa da magana a bakinsa haka kuma ya juya da sauri ya fita, kamar ta miƙe ta ji me zai ce tunda ta san ya bi su Abba
ɗ
aurin aure amma kuma bakinta da ƙirji suka yi nauyi lokaci guda. Har ji ta yi fitsari ya cika mara
rta. Tuni ta ajiye ƴar ƙaramar fankar dake hannunta wanda ke taimakawa gurin sama mata wadatacciyar iskar da zai hana kwalliyarta lalacewa.
"Kai Ameer! Ameer!! An
ɗ
aura auren?!"
Ta
ɗ
aga kai ta kalli Zahra a gaggauce kafin ta bi hanya da kallo cike d
a fatan Ameer din ya dawo a ji amsarsa.
"Haba ke ma dai kin san ta zama ta Hammana yanzu. Uku fa ina ji ya kusa. Bari na leƙa ma."
Cewae Nudrat tana dariya daidai lokacin da take ficewa zuwa cikin gidan. Nan Zahra ta mara mata baya saboda ta gama ka
rantar Sadiya, ta san kuma tsoron da ta ke yi. Ita ma kuma ta ji nata hankalin ya ƙi kwanciya, so take ta samu labarin
ɗ
aura auren yadda za ta kawo wa Sadiya albishir mai da
ɗ
i.
Hayaniyar da ke tashi a tsakar gidan ya sa wasu dake zaune suna cin abinci
har ma ita kanta Sadiya miƙewa zuwa can.
Mutane sun yi yawan da ba ta iya hangen fuskokin su Anti Hafsatu da ma Husna da sauran dangi dake maganganu. Sai dai kunnuwanta tsaf suke zuƙo mata muryoyinsu suna buga salati. Can kuma ta ji muryar Antinta Safi
yya a hautsine tana fa
ɗ
in.
"Kai Ameer dagaske ka ke yi? Ango ya gudu? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ita ma sai ta ji bakinta ya hau ambaton Innalillahi da ta ji Anti Safiyya na fa
ɗ
i. Ta
ɗ
an yi taga-taga, wata ƴar makarantarsu ta yi saurin r
ungumota ta gefen kafa
ɗ
a.
"Kai! Maza
ɓ
ace min daga nan! Yara sai
ɗ
auko zance!"
Gaba
ɗ
aya suka maida hankali ga duban mai maganar, su Baba Habu ne. Nan ya dubi kowa.
"Ku kwantar da hankalinku, aure har ma an gama
ɗ
aura shi. Ba wani tashin hankali
ba ne."
Nan kuma ya ja hannun Sadiya wacce ta rasa wane yanayi take ciki, ciwon kai, zazza
ɓ
i da ma faduwar gaba fiye da na baya sosai suka tarar mata. Ganin haka su Anti Hafsatu da Hajara wacce ta ga sama ta ga rashi suka mara mishi baya har kuwa cikin
wasu a dangin Malam din da ma Inna.
Ta zauna kawai tana duban yayan nata. Falon dai babu wani bare. Kafin Baba Habu ya kai ga cewa wani abu sai ga Abba da Malam sun shigo gidan daga can gidan Baffa inda Mai Martaba ya buƙaci ganinsu aka yi magana sosa
i.
Hajara gumi ta ji ya fara tsastsafo mata musamman ganin fuskar Abba a sake.
"Habubakar, meke faruwa ne? An saka mu a duhu."
Wata dattijuwa a dangin su Malam wacce ke matsayin Uwa a wurinsa ta fadi tana duban Abba. Ya na murmushi ta ce.
"B
abu abin da ya faru sai alheri. Aure kuma an riga da an
ɗ
ora shi. Ku zauna a yi magana ta nutsuwa."
Nan kowa ya zauna. Hajara wacce dama tun kafin ya kai aya ta zube ƙasa sharaf babu ma wanda ya kula da ita. Gaba
ɗ
aya jikinta ya gama mutuwa ta yadda ƙaf
afunta suka kasa
ɗ
aukarta,
ɗ
azun tana tsakar gida ne ta ci uban ado tana tauna cingam a zaune saman kujera ta
ɗ
ora ƙafa
ɗ
aya kan
ɗ
aya tana ƙarewa masu shige da fice kallo zuciyarta wasai, ko a mafarki ba ta yi tunanin wannan baƙin cikin za ta riska a gaba
ba don har wata shewa take bugawa ita ce har da gayyatar jiga-jigan ƙawayenta kawai don a zo a taya ta dariyar rinca
ɓ
ewa da auren Sadiya zai yi. Sai dai me? Jin zantukan da Abba ya shiga yi ya sa ta ji ashe dai firgicin da ta shiga da zancen farko na Abba
mai sauƙi ne kan labarin da ya soma ba su bayan bude taro da addu'a da ma yin doguwar nasiha ga Sadiya har da nunawa kowa na falon muhimmancin yarda da ƙaddara. Kamar daga sama kuma ta ji yana fadin.
"To a ƙarshe da haka ta faru, auren a take bisa umar
nin Mai Martaba Sarkin Gombe, aka
ɗ
aura shi da
ɗ
ansa Ibraheem da suke kira Maina."
Nan falon ya
ɗ
auki kabbara sai kuma wata gu
ɗ
a da wata Gwaggonsu ta
ɓ
angaren Malam ta ranga
ɗ
a duk da hawayen da suka yi wa fuskarta kaca-kaca saboda ru
ɗ
anin da zuƙatansu s
uka shiga da farko.
Su Anti Hafsatu da Safiyya su kansu sai kukan ya koma dariya.
Inna dama ba ta falon tana can
ɗ
akinta amma kuma cike take da fargabar me ke gudana a falon Malam.
Sadiya har a lokacin kanta tana ƙasa, rawar sanyi sosai take yi.
Hawaye kuwa wani na bin wani, wai Hamma ne ya ce ba ya sonta? An
ɗ
aura masa aure da Fareeda? Meyasa duk wanda ta ƙaunata yake gudunta ne? Ko soyayyar ce ba ta kar
ɓ
e ta ba?
'Maina? Mai..."
Cikin daƙiƙa biyar ta tuno shi, shi ne tabbas. Ɗan uwa kuma
aboki ga Hamma
ɗ
an Sarki. Kawai sai ta ji ƙarfin kukanta ya ƙaru. Mutumin da ko ganin juna ba su ta
ɓ
a yi ba? Za ta iya rantsewa tun wayarsu ta farko kuma ta ƙarshe ta ji bai mata ba, ta tsane shi.
"SubhanAllah, ai zazza
ɓ
i ne a jikinta."
Ba ta ji ma
sadda Husna ta kai hannu saman goshinta ba, sai furucin da ta ji ya dakar mata kunne.
"Ki yi hakuri Sadiya, bari a kar
ɓ
o maki magani. Amma lallai ki sani gobe idan Allah ya kaimu jirgin safe za ku bi zuwa Gombe tare da mijinki."
Abin da Abba ya furt
a kenan. Nan kuma ya ba wa kowa umarnin tafiya yace a bar Sadiya a falon ta huta bayan ya ba Baba Habu umarnin siyo mata maganin zazza
ɓ
in. Bayan kowa ya watse a falon daga shi sai Malam sai Sadiya dake dunƙule a gefe tana kuka murya a shaƙe. Abba ya ƙara y
i mata doguwar nasiha ya kuma roƙe ta kar ta ba su kunya, kamar yadda shi AbdulMajid ya so su kunyata amma Allah ya rufamusu asiri, toh ta daure ta yi hakurin zama da mijin da Allah ya za
ɓ
ar mata.
Ta jinjina kai tana share majina da hankicif dake hannu
nta. Sai da ya kammala sannan Malam shi ma ya sanya mata albarka ya ƙara da ƴar guntuwar nasiha kafin su ce ta kwanta ta huta za su koma sallamar baƙin da suka zo daga nesa wa
ɗ
anda ke can babban gida. Bayan fitarsu ta haye saman doguwar kujerar mai cin mut
um uku ta kwanta, ba jimawa sai ga Zahra ta shigo. Ganinta yasa Sadiya miƙewa ta fada jikinta ta bu
ɗ
e sabon shafin kuka. Ita ma Zahra hawayen ta ji sun zubo mata, ta yi mata murna da wannan sauyi, sai dai kuma hakan bai hana jin tausayinta ba. Ta riga ta s
an irin zafafa so da ƙawarta ke yi idan ta tashi, komai na son ba ta iya shi ba. Ba ta tafiyar da kanta a duniyarsa a hankali, tana zurfafawa ne gaba
ɗ
ayanta ta shige. Toh irin wannan ranar ake tsoro. Can kuma ta share nata hawayen don bai kamata ita da za
ta lalla
ɓ
a ba, ta sanya ta wani kukan. Sadiya ta
ɗ
ago kai ta na dubanta.
"Ki na ganin hakan daidai ne? Ya rayuwata za ta kasance a Gombe? Zahra na ta
ɓ
a baki labarin Maina, ba kalana ba ne. Ya fi ni aji da ma dukkan wani abu da zan
ɗ
aga na yi tutiya d
a shi. Babu wanda ya hango shi ma kamar dole aka masa a kaina? Ta ya ya zai so macen da bai santa ba bai san halinta ba? Ni fa? An tabbatar idan muka rayu tare zan so shi? Kuma da suke batun tura ni Gombe shikenan na bar karatuna?"
Zahra ta yi murmushi
a kokarin danne nata damuwar.
"Sadiya godiya ya kamata ki yi wa Allah. Kar ki yi baƙin ciki bisa dukkan za
ɓ
in da ya yi maki. Ki duba iyayenki da ma manyan mutanen da suka hallara a taron
ɗ
aurin aurenki, idan har AbdulMajid bai ko duba su ba ya tsallake
ya je aka aura mishi Fareeda, toh ki sani girman sonta da yake yi ya wuce misalin da zan kwatanta maki. Idanunsa sun rufe ya za
ɓ
i ya kunyata iyayensa da namu da ke kanki a idanun jama'a ya bi son zuciyarsa. Dayake Allah ba azzalumin bawansa ba, sai ya yi
maki sakayya nan take. Ya ba ki wanda ya fi Abdul kyan nasaba da komai na rayuwa. Don Allah kada ki yi baƙin ciki, addu'a ki ke ta yi na nemawa kanki za
ɓ
in Allah ko? To ki saka a ranki Ibraheem Tafida shi ya za
ɓ
a maki. Kukanki kamar butulci ne
ga ni'imar d
a Allah ya maki. Ke ba za ki gane akwai masu jiran faruwar hakan ba sai idan kin ga yadda Anti Hajara ta fice daga gidan nan kamar kububuwa ta cika ta yi fam! A kan kunnena cikin harshen turanci na ji cikin ƙawayenta na fadin ta gama cika musu bakin yau ba
za a
ɗ
aura aurenki ba har tanadin liyafa ta yi a gidanta zasu je can ƙarfe hu
ɗ
u a yi shagali. Toh Sadiya wannan ka
ɗ
ai ba..."
Maganganun Zahra suka katse saboda sallamar da Anti Hafsatu ta yi ta shigo hannunta
ɗ
auke da leda mai tambarin wani babban kemi
s dake kusa da su. Sadiya wacce nasihar Zahra ya shige ta sosai gaba
ɗ
aya ta ji zuciyarta ta sanyaya, abu
ɗ
aya kuma da ta sani har ga Allah ba ta san ta ya za ta fara rayuwa da wanda ba ta ma san shi ba balle ta ji sonsa a zuciya. Ga kuma mamaki da tsoron
Hajara da ya ƙara
ɗ
arsuwa a ranta.
"Sannu Sadiya, amma da sauƙi yanzu ko?" Fa
ɗ
in Anti Hafsatu tana zana a gefenta. Zahra ta mike ta
ɗ
auko ruwan roba dake ajiye a gefe guda kusa da firij
ɗ
in Malam sai kofi. Nan ma Anti Hafsatu lalla
ɓ
a Sadiyar ta dinga y
i har tana fa
ɗ
amusu wai Maina zai shigo da daddare ya gaisa da iyaye. Ita dai ba ta ce uffan ba.
"Tsaya kin ci abinci?" Anti Hafsatu ta fa
ɗ
i tana dakatawa daga
ɓ
allo maganin da take shiri. Girgiza kai ta yi.
"Bari na
ɗ
ebo mata." Fa
ɗ
in Zahra tana mi
ƙ
ewa ta fita. Can kuma ta dawo, sai a sannan Sadiya ta dube ta.
"Ina Nudrat?" Ta furta a sanyaye. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke.
"Tun bayan da Ameer ya ce an fasa daurin aurenki ta
ɗ
auki gyalenta da mayafi ta fice tana hawaye. Na tabbata gidansu ta
nufa."
Jinjina kai kawai Sadiya ta yi ba ta ce uffan ba. Ta sani dole Nudrat ta ji ciwon abin da yayan nata ya aikata. Hawaye ta ji sun cicciko sai ta share su da sauri. Ba ta son jefa zuƙatan da suka damu da al'amarinta cikin damuwa da rashin sukuni.
***
A gidan su Nudrat kuwa, hankalinsu gaba
ɗ
aya ya tashi bayan labarin abinda ya faru da ya iso musu. Nudrat ma a hargitse ta shigo gidan sakamakon wayar da ta yi da ƴar Yafendonta, Khalisat wacce ta ba ta labarin ai Hamma dagaske ya gudu ya auri Fare
eda, kuma wai Mai Martaba sun iso gidan ana ta yi wa Maina busar sarewa da kirarin ya zama Ango wurin Sadiya. .
Kuka wurjanjan haka Nudrat ta shiga yi, ba ta ta
ɓ
a hasko ƙaddara za ta musu wannan juyin ba. Hamma ne ya yi musu wannan cin kashin? Sadiya da
Maina an musu aure?
Haka ta dinga tunane-tunane har ta ƙarasa gidan, wuri a cike daƙyar ta samu ta rufe fuskarta da mayafi ta wuce zuwa ciki kunnuwanta na dauko mata muryar Hasken Fadar Sarki yana ta zuba uban kirari ga Ibraheem Tafida Ango.
Tana ƙ
arasawa ta ga wuri a hargitse ana yi wa Nene firfita, da gudu ta ƙarasa. Ashe suma ta yi da ta ji tsiyar da
ɗ
anta ya shuka. Nudrat ta
rungume Nene ta cigaba da rera kukanta. Tausayin Nenen ta ji, a karan kanta kunyar Sadiya da ma danginta take ji, da wane
ido za ta ƙara kallonta? Ƙila ma Sadiyar ta yi zaton ta sani shiru kawai ta yi.
Daƙyar dai ƙura ta lafa a gidan su Nudrat. Bayan tafiyar Sarki da tawagarsa da ma baƙin da aka gayyato na cikin garin da suka zo biki, Baffa ya ke
ɓ
e da Nene ya taushe ta. Y
a kuma ƙara da fa
ɗ
in.
"AbdulMajid kansa ya yiwa. Ki taushi zuciyarki kar ta kai ki ga yi masa mummunan baki. Zuru ma ka
ɗ
ai ya ishe shi. Ya za
ɓ
i duniya a kan mu iyayensa. Ya tozarta mu a bainar jama'a, toh ina mai tabbatar maki ko ba ki ce komai ba, zai
ga ishara a rayuwarsa. Ki shirya idan an yi Isha'i ku je ku ƙara ba iyayen yarinyar nan haƙuri."
Nene daƙyar ta ha
ɗ
iyi miyau mai
ɗ
aci tana gya
ɗ
a kanta.
***
IBRAHEEM TAFIDA (MAINA)
Tun shigarsu falon ya yi zaune saman kujera gami da kwantar da
kai ba tare da ko cire alƙyabbar da ke sanya a jikinsa ba. Na'urar sanyin da ke ka
ɗ
awa a falon bai tafiyar masa da gumin da ke tsastsafowa a goshi da ma cikin gargarsar dake kwance luf a hannunsa ba.
Lami
ɗ
o ya dubi Gi
ɗ
a
ɗ
o kafin su maida duba ga Khamees
wanda shi kansa ya yi shiru. Cikin su hu
ɗ
un aka rasa wanda zai fara furta koda harafi ne. Can Khamees ya dube su, daga yanayin da ya musu inkiya ya sa su miƙewa su ba su wuri. Ya sani kaf
ɗ
insu babu mai iya tunkarar Maina da kowane irin zance bayan sa.
"Maina." Ya furta bayan ya yi ƴar gyaran murya. Ya
ɗ
ago idanunsa da suka yi mugun ka
ɗ
awa ya sauke a kansa ba tare da ya ce kanzil ba. Sai dai kallo
ɗ
aya Khamees ya fahimci ran maza ya
ɓ
aci.
Khamees ya
ɗ
an kauda kai yana ƙara shiga taitayinsa kafin ya
ce.
"Komai ya faru, ka
ɗ
auke shi matsayin ƙaddara."
"Na ji."
Khamees bai ƙara magana ba sanin hali, har ya fidda ran ma zai ji ta bakin Maina
ɗ
in sai ya ji ya ce.
"Hukuncin nan na Mai Martaba bai yi tsauri a kaina ba? Laifina bai yi girman da
za'a hukunta da aure ba. Aure irin wannan ma na huce haushin Abdul. Why me? Yes na yi laifi wurin amsa kira a fili har ya yi sanadin da Abdul ya yi zafafan kalamai ga
ɗ
iyarsu, toh a ba ni hukuncin da zuciyata za ta iya
ɗ
auka. But Khamees aka aura min ita?
Sa..Sadiya right? Yarinyar da ban ta
ɓ
a gani ba, ba ma ni ne a ranta ba. Ni ma kuma ka sani auren ma ba ya cikin abubuwan da na saka a gaba yanzu."
Ya na kai wa nan ya furzar da huci mai zafi kafin ya ƙara kwantar da kai jikin kujera ya lumshe idanu yan
a