Showing 114001 words to 117000 words out of 137760 words

Chapter 39 - KAZAR KWANCI COMPLETE

23 Oct 2026

323

ta huta ko za ta nutsu ga

ɓɓ

anta su bar rawar da suke yi. Tana fitowa ta tarar har Antinta ta f

iddo mata wata sabuwar atamfarta glitters irin manyan ƴan dubu talatin da

ɗ

oriya wanda Malam a aljihunsa ya dauka ya  bayar aka siya mata don fitar biki sai dai kuskuren da tela ya yi yasa ba ta sanya ba sai yanzun.

"Su Safiyya sun taho fa. Husna wai H

ajara ta ce ta bari su taho gobe ta jirgi."

Ambaton Hajara da Antin ta yi sai da Sadiya ta ji ƙirjinta ya

ɗ

an fa

ɗ

i, ta tuna maganar da Zahra ta fa

ɗ

amata da sunan ƙawayen Hajara ke fa

ɗ

i. A fili kuma ta yi musu fatan isowa lafiya daga nan ta hau shiri. It

a ma Anti Hafsatu wankan ta fa

ɗ

a ta yi. Cakarewa ta yi cikin nata Voyel din mai tsada don kaf kayanta ba ta

ɗ

auko wanda ta ke da tabbaci za'a raina ajinsu ba. Hakan yasa da kanta ta yi wa Sadiya za

ɓ

in kayayyakin da ya kamata ta

ɗ

auko.

"Kin ga abin da n

a kula wannan ita ce Uwargidan Mai Martaba daga yanayin kirarin da ake mata da ma sunan da ake kiranta da shi, Mai Babban Ɗaki. Kuma kamar dai ba ta da matsala.  Sadiya dole sai kin nutsu kin karanci dabi'ar kowa a gidan nan kafin ki saki jikinki da su. Wa

su zasu ra

ɓ

e ki ba don Allah ba, wasu kuwa zuciya

ɗ

aya za su so su mu'amalance ki. Ke dai ki girmama duk wand ya girmeki musamman idan ya riƙe girmansa. Dama ban sanki da rashin kunya ba, in sha Allahu ki ka riƙi addu'a komai zai zo maki da sauƙi. Don Alla

h Sadiya ki rufe idanu ki ba masu jiran ƙiris a auren nan kunya. Ki wanke zuciyarki ki rungumi za

ɓ

in da Allah ya yi maki.

Baiwa ce ba ka

ɗ

an ba a daidai sadda wani bai aureki ba, Allah ya kawo maki madadi da ya fi wancan komai na rayuwa. Gina sonki a zuciya

rsa ba abu ne mai wahala ba a gurinki mace. Ke dai ki zama mai biyayya da kyautata tsakaninku. Wataran za ki

ɗ

aga hannu ki godewa Allah da ni'imar da ya yi maki na auren Maina. Ina jin wannan a jikina."

Anti Hafsatu ta ƙarashe tana mai murmushi, ita ma

Sadiyar ta

ɗ

an murmusa. Ba ta san irin adadin ƙaunarta da Antin ba, mace mai sonta da Innarta. Takan mance ma ba Uba suka ha

ɗ

a ba, ji ta ke kamar ciki guda suka fito da ita.

"Nagode Anti. Allah ya bar mu tare."

Ta amsa da amin. Daga haka suka fito f

alon kamar kuwa jiran fitowarsu ake sai ga sallama bayan an kwankwasa ƙofar. Amsawa suka yi, Hindu ce tare da wasu bayi

ɗ

auke da manyan fulas na abinci, haka aka dinga jera musu, bayan sun kwashi gaisuwa. Hatta da lemuka da ruwa sai da aka ajiye. Bayan fit

arsu ne kuma suka ci ka

ɗ

an a cikin wanda za su iya don wani ma ko ta

ɓ

awa ba su yi ba. Ba jimawa kuwa sai ga Hindu da

ɗ

aya a cikinsu riƙe da wani ƙaton bowl da aka yayyanka kayan marmari. Ganin sun kammala ya sa ta ba da umarnin a fara kwashe kayan, sai da

aka kammala ita ma ta musu sallama ta fita Anti Hafsatu na ƙara furta godiya.

Can kuma suna nan aka ƙara sallama, wannan karon ba muryar Hindu ba ce, suka amsa, wata mace ce da za ta girmi Anti Hafsatu tare da wata baiwa wacce kalar kayan da ke jikinta

ne irin na bayin da suka zo

ɗ

azun ya sa su fahintar

ɗ

aya ce a cikinsu, ita kuma riƙe take da ƴar jaka.

Matar doguwa ce mai jiki ka

ɗ

an. Ta ci ado kamar mai zuwa gidan biki. Fuskarta

ɗ

auke da murmushi ta ƙaraso ta zaune tana kallon Sadiya. Ganin haka Sad

iya ta yi gaggawar saukowa tana kokarin russunaws ta gaishe ta duk da ba ta san ta ba amma suna tsantsar kamanni da Maina.

Da sauri ta riƙo ta miƙar gami da zaunar da ita gefenta a lokacin da ta ke amsa gaisuwar Anti Hafsatu tana ƙara wa da tambayar ya

gajiyar hanya.

"Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya."

"Masha Allah. Suna na Saudatu,

ɗ

aya daga cikin Yayyun Maina."

Dama ko ba ta fa

ɗ

a ba sun

ɗ

auki haske, kamannin sak kawai dai ita

ɗ

in  tana da

ɗ

an duhun fata.  Daga haka Gimbiya ta waiga ta dubi

Baiwar da ke durƙushe kanta a ƙasa ta ce.

"Fauziyya."

Sunanta kawai ta kira yarinyar ta fahimta don haka a ladabce cike da ladabi ta matso ta bu

ɗ

e jakar ta fiddo gidan wata sarƙa ta ajiye, ta ƙara fiddo wata alkyabba fara ƙal mai adon zare kalar go

lden ita ma. Gidan sarƙar ta fara miƙawa Gimbiya Saudatu. Ita kuwa ta taimakawa Sadiya da cire fashion mai tsada da ta sanya sannan ta taimaka mata da saka wani arnen gwal mai daukar idanu. Anti Hafsatu sai ta rasa ma me za ta ce, ƙasan ranta wani irin far

in ciki da hamdala kawai take ga Allah na wannan sauyin da Sadiya ta samu. Daga zuwansu ko awa

ɗ

aya ba su kai ga cikewa a garin ba har rayuwar Sadiya ya fara sauyawa?

Gimbiya Saudatu kuwa ta ƙara kallon Sadiya wacce har a ƙasan ranta ta ji dadi da ta gan

ta a haka, tabbas idan an cire nasabar da mahaifiyarsu ke ta fa

ɗ

an wai ba a duba jinin sarauta an aura wa autan nata ba sai bare, toh kuwa ba ta ga makusa a tattare da ita ba. Ita kam ta yi mata kuma tana fatan halayyarta ma ya kasance irin fuskarta. Wato

mai kyau. Sosai ta ga sarƙar ta kar

ɓ

e ta sannan ta miƙe tsaye riƙe da hannun Sadiyar, da sauri Fauziyya ta

ɗ

auki alkyabbar ta da ke wani irin ƙamshi mai da

ɗ

i ta miƙa mata. Nan ma mayafin da ta yi Sadiya ta lullu

ɓ

a ta cire ta ajiye ta sanya mata alkyabbar.



'Allahu Akbar! Masha Allahu la kuwwata illa billah.' Fa

ɗ

in Anti Hafsatu a zuciya har da wasu ƙwalla ta ji sun cicciko mata a idanu ganin wani irin kwarjini da haiba a fuskar Sadiya wacce ita kanta jikinta ya yi sanyi ga kuma nauyin da bakinta ya yi ta

ma rasa me za ta ce.

"Kin yi kyau sosai ƙanwata. Allah ya sa kin shigo gidan nan a sa'a. Ki saki jikinki, a hankali za ki san mu don ba laifi yawa ne da mu. Komai a sannu za ki fahimta kin ji ko?"

Ta gya

ɗ

a kai a

ɗ

an kunyace, Anti Hafsatu ta amsa ad

du'ar da amin.

"Ku na iya biyo ni muje, Mai babban

ɗ

aki tana jira."

Suka amsa da toh suna masu bin bayanta. Ita kuwa Sadiya ta ji duk ta takura, daga zuwa an ƙaƙaba mata alƙyabba? Allah dai ya sa ba haka za ta dinga yawo a gidan ba. Ƙila ma iyakar n

a yau ne. Haka ta dinga saƙe-saƙenta, can wani

ɓ

angare na zuciyarta na tunanin ko ina Angon nata ya shige? Amma kuma tana ta kokarin basarwa don a ganinta me ma zai dame ta da tunaninsa?

Haj Saratu ta amsa gaisuwar Sadiya ita ma ta yaba yanda ta yi kya

u. Nan kuma ta umarci Gimbiya Saudatu da yi musu jagora zuwa sassan Fulani Kausar da ma sauran matan Sarki Abdallah Tafida don ta gaishe su.

Falon na Haj Saratu a cike da mata, haka aka dinga bin Sadiya da kallo ga gefe ta

ɗ

azun ba cigaba da zuba mata

kirari. Ita dai tana rungume jikin Gimbiya Saudatu jefa ƙafafunta kawai ta ke. Haka har suka iso wani

ɓ

angare jama'a na biye da su a baya. Falon shi ma yana da girma kamar na Haj Saratu, ga kuma

ɗ

akuna a can ciki. Iya tsari ya tsaru don ba ma za ka iya tan

tance wanda ya fi kayan alatu da na Fulani Kausar da na Haj Saratu ba.

Tana hakimce a saman kujera ta yi wani irin zama na ƙasaita. A gefenta zaune can

ɓ

ari na daban wasu ƴanmata ne su biyu sai ko wata babbar mace ita ma dake bin su da kallo. Anti Haf

satu ta kalle Fulani Kausar dakyau, ko ka

ɗ

an ba ta ga kamarta da Maina ba, ta dai gane uta ce mahaifiyarsa a kirarin mai zuba kirari dake ta yi babu ko gajiyawa. Fuskarta kawai ya fallasa sirrin zuciyarta don babu ko

ɗ

igon walwala a samansa.

Gimbiya Sa

udatu duk ba ta ji dadin yanayin dake saman fuskar Umman tasu ba, ai ko don masu

ɗ

aukar bidiyo ta daure ta yi murmushi koda kuwa bai kai zuci ba amma ta kasa. A wulaƙance ta amsa gaisuwar Sadiya tana cin magani. Daƙyar ta iya fa

ɗ

in.

"Allah ya yi albarka

." Mutane aka hau amsawa da amin.

Haka aka zagaya da Sadiya har sauran

ɗ

akuna biyu na matan Mai Martaba. Daga nan kuma bisa jagorancin Jakadiya da aka kai ta wajen Mai Martaba. Babu wanda ya shiga, hatta da Gimbiya Saudatu duka tsayawa suka yi. Ita

ɗ

in

yake son yin magana da ita sai ko Maina da ke zaune tun ma kafin ta shigo. A ladabce Sadiya ta miƙa gaisuwa, ya amsa mata.

"Alhamdulillah. Muna maki murna da shigowa wannan masarauta mai albarka. Ba ma yi maki kallon suruka, ke

ɗ

iya ce a wurinmu. Za

kuma mu riƙe amanarki, dukkan wani abu da kile buƙata, ki sanar da mu za mu yi ƙoƙarin ganin an maki matuƙar bai sa

ɓ

awa addini da al'adunmu ba."

Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha da kuma yin alƙawari ga Sadiya zai

ɗ

auki mataki mai tsauri a kan

ɗ

ansa m

uddin ya kama shi da zaluntarta ko yaya. Haka nan ya jaddadawa Maina ya ji tsoron Allah, ya kuma kiyaye yin abin da zai

ɓ

ata ransu. A ƙarshe ya sanya musu albarka ya kuma yi musu addu'a.

Nan ta miƙe fuskarta da hawaye ta fito ta bar shi da Maina. Ji ta

ke kamar ba ita ba, wai ita ce da wannan matsayin da muƙami. Ita ake ta girmamawa, ta shiga roƙon Allah a rai kada hakan ya haifar mata da girman kai, ya sa ta zama mai tausayin na ƙasa da ita kamar yadda ta ke tun farko.

***

"Za ki zauna a nan ne ha

r zuwa nan da kwanaki uku da za'a kammala gyaran sashenki a kuma yi bikin miƙa ki zuwa can."

Ta tuno kalaman Haj Saratu sadda ta ke ninke alƙyabbar, ita kuwa Anti Hafsatu na faman kallon sarƙar da take mayarwa cikin gidansa.

"Anti."

Sadiya ta fur

ta, ta

ɗ

ago ta kalle ta tana murmushi.

"Na'am Gimbiyar Maina."

Sadiya ta nanata sunan a ƙasan rai, wai Gimbiyar Maina. Sai ta girgiza jai ta zauna gefen gadon.

"Anti zan iya rayuwa a gidan nan?"

'Yar dariya Anti Hafsatu ta yi.

"Za ki iya,

babu abin da zai cinye ki. Kar fa ki manta kina da Allah, toh akwai wani abu da ya gagare sa?"

"A'a. Amma ba ki kula kamar wacce aka ce mahaifiyarsa ba ce..nufina kallon da na ga ta yi min. Ban sani ba ko don a fakaice na kalle ta, ko ban gani da kyau b

a ne."

Ajiyar zuciya Anti Hafsatu ta yi.

"Wannan kar ya dame ki, ki kyautata mata zato. Ba za ki samu matsala da ita ba. Yanzu duk ba mu isa yankewa kowa hukunci ba sai zama ya yi zama. Ki fidda komai a ranki."

Sadiya ta yi

ɗ

an murmushi sannan ta

jinjina kai ba ta ƙara cewa komai ba, amma tabbas jikinta na ba ta cewa ba ta samu kar

ɓ

uwa a wurin surukarta ba yadda ta samu a wajen sauran matan Mai Martaba musamman Haj Saratu da suke

ɗ

akinta.

Su Safiyya ba su ne suka iso ba sai dab da sallar Magri

ba. Su ma nan suka sauka amma

ɗ

akinsu daban shi ma babba, su kansu sun jinjina irin tarbar arziƙi da aka yi musu. Zahra kamar ta shi

ɗ

e don farin cikin wannan daular da Allah ya jefo ƙawarta a ciki. Ranar dai kusan raba dare aka yi hira ya yin da tuni Zahra

ta shiga IG tana kallon bidiyon da tuni ya ya

ɗ

u na Sadiya a cikin alkyabba. Wannan ba ƙaramin

ɓ

ata mata rai ya yi ba. Kamar jira ake yi har an

ɗ

ora ta? Kuma ma har da fuskarta a waje? Toh amma ya za ta yi tunda ba ta ma san ko aikin waye ba, kuma koda ta

sani ina ta ga ƙarfin cewa wani abu?

***

Misalin ƙarfe tara da mintuna na washegari Litinin, Hajara da Husna suka iso. Anti Hafsatu wacce suka yi waya da Khamees ta sanar mishi da zuwan nasu, tuni ya aika mota can a yi jiransu. Suna kuma zuwa, aka sha

idawa direban, ta hanyar waya ya gane su ya

ɗ

auko su. Tun daga motar Hajara ta san an zo wajen. Sadiya ta samu duniya yadda ya kamata. Husna kuwa bakinta ya ƙi rufuwa tana rungume da Sadik da ke bacci tana bin hanya da kallo kamar ta yi fiffike ta gan ta c

ikin masarautar a gefen yar uwarta.

A fakaice Hajara ta watsa mata harara gami da jan tsaki a zuciya.

'Banza marar zuciya. Maimakon ta yi bakin ciki ba ita ce a wannan matsayin ba, sai faman rawar jiki ta ke yi.'

Ta ayyana a ranta. Babban dalili

nta na zuwa bai wuce abu biyu ba. Ta wanke kanta a wurin dangi daga zargin tana yi wa Sadiya hassadar da aka fara mata saboda lura da yanayin ficewarta a gidan ba a hayyaci ba ranar da aka

ɗ

aura auren. Sai ko ganewa kanta muhallin Sadiya, har yanzu ganin k

omai take kamar a mafarki, za kuma ta so ta ganewa idanunta. Ta san Inna na can ta a farin cikin ta aurar da duka yaranta da ƙuruciyarsu. Ta kuma sani Sadiya ta taka sa'ar da Husna ba ta kama ko ƙafarsa ba. Wannan baƙin ciki da shi za ta mutu. Sai dai ta y

i rantsuwar gallazawa Inna, ta ci alwashin sai ta zama abar tausayi. Gwara su biyun duka ta yi maganinsu ta ha

ɗ

a musu zafi ta ko'ina. Zai fi kyau da ta zo Gomben da kanta don gane ta inda za ta fara ƙulla zaren makircinta.

Wani irin gumi ne ya shiga tsast

safowa Hajara tun daga irin yadda bayi suka shiga zubewa a sashen Haj Saratu su na gaishe su. Ga uwa uba daular da aka narka a falon.

"A yi musu jagora zuwa Gimbiya  Sadiya."

Wannan laƙabi na girma da aka jingina sunan Sadiya da shi ya ƙara tayar da

hankalinta. Dama ta san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. To amma ai ta gama ayyana dukkan hakan a rai bai kyautu ace ya mata zafi kamar haka ba. Abu ne da ta kwana da sanin jin fiye da shi idan sun zo. Haka ta

daure da yaƙe saman fuskarta suka bi ba

yan baiwar don dama akwatinsu na kaya ya riga su yin gaba.

Su Anti Hafsatu duka suna falon, Sadiya na zaune cikin wani leshi

ɗ

an ubansu kalar purple an bi patterns dinsa da adon stones har ƙasa daga gaba. Ta yi

ɗ

aurinta tsaf haka ma fuskarta ta sha kwa

lliyar da Zahra ta tursasa mata yi acewarta ko don masu shige da fice suna zuwa ganinta, su gan ta tsaf.

Baiwar nan ta zube ta fara da yi wa Sadiya gaisuwar ban girma. Sadiya ta amsa hankalinta na ga Husna suna yiwa juna murmushi. Hajara kafafunta daƙy

ar suka ƙarasa da ita ga kujera ta zauna tana yaƙen dole. Nan kuma hira ta ƙara

ɓ

arkewa har sadda aka kawo wa Husna da Hajara abin kari. Nan ma kayyakin abinci ne iri iri. Daƙyar Hajara ta iya cusawa a cikinta, ƙarshe ma ta ce amai take ji tana buƙatar kum

a ta huta. Zahra ce ta yi mata rakiya

ɗ

akin da babu wanda ya sauka a ciki wanda a nan aka ajiye kayanta ita da Husna.

Tana shiga ta rufe kofar ta zauna gefen gadon ta shiga fidda hawayen baƙin ciki.

"Wannan gidan bai dace da Sadiya ba!  Na rantse k

o zan yi yawo tsirara sai na fisge Sadiya daga gidan nan don uwarta!"

Ta firta a fili tana share fuskarta. Ta rasa meyasa take shakkar Boka ta yadda ta kasa fushi da shi. Wuyarta ya

ɗ

auki waya ya kira ta akan ta zo, ban hankalinta ke tashi ta rasa nutsu

wa jiki na rawa take amsa mishi za ta zo din. Idan ta zauna kamar irin na yanzu, sai ta dinga mamakin abin, amma kuma a karshe dole take watsarwa tunda ta rasa mafita, wuyarta dai ya kira. Ga kuma alƙawarin da ya ƙara yi mata da ta tsinci kanta da amsa mis

hi da toh, wai zai yi iyakar yin sa ya raba Sadiya da gidan. Ita kam dama a inda ya fadi a nan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login