Showing 78001 words to 81000 words out of 137760 words

Chapter 27 - KAZAR KWANCI COMPLETE

23 Oct 2026

319



ɗ

akin. Ƙarfe biyu da mintuna arba'in. Suna da sauran awa

ɗ

aya da mintoci kenan. Ruwa ta dauka ta sha tana shirin ajiyewa sai ga Nudrat ta fa

ɗ

o

ɗ

akin da gudu-gudunta.

"Triple, taso muje ku gaisa da Hamma. Ya ce shi ma yau sai ya gan ki."

Sadiya ta

ɗ

an

fiddo idanu amma ba ta ce uffan ba dalilin magiyar Nudrat, a dole ta miƙe ta yafa mayafin da ta zo da shi saman doguwar rigar atamfar jikinta suka fito. Yana magana da Nene amma shigowarsu ya sanya shi maida hankali gare su. Da ido ya bi matashiyar da aka

kira da Sadiya wato Triple S

ɗ

in Nudrat. Ba laifi akwai dai kyau ga kuma alamu na nutsuwa tattare da ita. Ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa fuska a sake. Ita ma sai ta ga a fili ya fi kyau sosai fiye da hotuna, don kamar ma rage kyawunsa wayar ta yi.

"Kin ƙwace min Nudrat, ba ta da aiki sai hirarki. Yadda ta damu da ke ma yanzu ba ta wani damu da ni ba."

Sadiya ta yi murmushi.

"Ba haka ba ne."

Shi ma murmusawar ya yi, yana jin hatta da murmushinsa na

ɗ

an burge shi.

"Ai shikenan. Ya ka

ratu? Allah ya baku sa'a. Sai a ƙara mayar da hankali."

"In sha Allah. Amin. Mun gode Hamma."

Fadin Sadiya cikin girmamawa. Ya ƙara dubanta sai kuma ya kauda kai. Ɗakin suka koma suka bar shi da Mahaifiyarsa.

Tun shigar su

ɗ

akin Nudrat ke ba ta l

abarin Hamma, wai shi ne na biyu a

ɗ

akinsu bayan babbar yayarsu da ta rasu wato Yaya Maryam. Bai yi aure ba amma a cewarta a na dab da kai ku

ɗ

in aurensa. Sadiya ta yi masa fatan alheri. Nudrat tace sosai ya shaƙu da Yaya Maryam don ya fi su kusanci da ita

sosaima, kuma akwai tazarar haihuwa tsakaninsu don sai da Nene ta haihu har sau biyu suna rasuwa sannan ta haifi Qassim, Muneeb, Nudrat sai Jafar. Yanzun Nudrat ka

ɗ

ai ce mace a cikinsu wannan yasa suke ji da ita sosai.

Ƙ

arfe uku da rabi suka yi shirin

komawa makaranta bayan sun duba karatunsu, Nene ta dakatar da su ta ce su fita tare da Hamma wanda zai yi Zoo road sai ya sauke su kafin ya wuce.

Nudrat hakan ya yi mata dadi idan ka cire Sadiya wacce har ƙirjinta ke bugu. Na farko ta biyo Nudrat ba da

sanin Innarta ba, ga laifi na biyu

kuma za ta shiga motar Yayanta. Tsoronta kar a je wani a gidansu ya gan ta, abinka da wacce irin hakan ba ta ta

ɓ

a aikata shi ba. Idanunta ya yi ƙwal, ta ji kamar ta cewa Nene ta bar su su tafi amma kuma ba za ta iya ba.

Haka ta zauna jiki a sanyaye har Hamma ya shigo Nene ta ce ya sauke su. Ya amsa da ok ya yi gaba ya ce su taho.

Ledar da Nene ta ba ta wanda ta kar

ɓ

a daƙyar don har sai da Nene ta nuna ranta ya

ɓ

aci sannan, ita take riƙe da shi a saman cinyarta sai ko jak

arta na zuwa makaranta, tana son bu

ɗ

ewa ta sanya a cikin jakar amma kuma kunya take ji daga kar

ɓ

ar abu da zama a mota a ga tana cusa shi a jaka kamar me jira. Tana ji Hamma da Nudrat dake zaune a gefensa a mazaunin gaba suna ta kwasar hirarsu tana mitar it

a ba ta so ya tafi Gombe saboda jimawar da yake yi a can. Ta ƙara da fa

ɗ

in.

"Haka kawai don yana wani taƙama shi wai Prince ne sai ya dinga wani wahalarmin da Hammana. To ai mu

ɗ

in ma Prince ka ke a wajenmu." Ta ƙarashe tana

ɗ

an turo baki.

Hamma ya

yi ƴar dariya.

"Ke da

ɗ

ina da ke sai yawan rigima. Kamar ba ki san yadda muke da Maina ba. Kodayake zan

ɗ

auke ki mu je wataran. Triple, ba kya magana kin yi shiru."

Ya ƙarashe yana kallon Sadiya ta madubi kasancewar daga bayan kujerarsa take a zaune

. Ita ma aka ci sa'a ta

ɗ

ago ta kalle shi. Kauda kai ta yi tana

ɗ

an murmushi. Nudrat ita ma ta juyo ta kalle ta.

"Nan fa da kake ganinta kamar a ce mata arr ta gudu haka take ji. Hamma za ka yi mamaki idan na ce maka a ru

ɗ

e take."

Sadiya ta

ɗ

an fiddo

idanu ta kalli Nudrat, irin kallon ya aka yi ki ka gane? Nudrat ta

ɗ

an murgu

ɗ

a mata baki.

"Eh mana, ki ce min ba haka ba."

"Ru

ɗ

ewa kuma? Na me toh?" Ya ƙara fa

ɗ

i da Hausarsa wacce ba ta nuna ba sosai.

"Fa

ɗ

an Inna take tsoro tunda ta je gidan Do

danni mun cinye mata nama. Kuma Allah na sani sharrinta ne kawai, Inna ba za ta ta

ɓ

a cewa wani abu idan ta san gidanmu ta je ba. Ita ce dai farar kura kawai."

Sadiya ta ha

ɗ

e fuska tana hararar Nudrat dake dariya, a gefe guda kuma kunyar Hamma ta ji ya m

amaye ta.

"A'a Jerryn Muneeb, Triple fa ta fi ki gaskiya. Duk wata

ɗ

iya ta gari tana shakkar iyayenta, da kuma aikata abin da ta san zai zame musu abin magana. Wasu za ki ga daga irin wannan suke fa

ɗ

awa wata hanyar ta daban. Wani bin a kar

ɓ

i tayin saur

ayi zuwa shan ice-cream, ko kuma a raka ƙawaye, kinga mafarin

ɓ

arna ya samu. So ban ga laifinta ba, hakan ma yana da kyau. Daga yanzu ma kar a ƙara biye-biye wani wuri ba tare da an sani a gida ba. Har ke nake nufi."

Ya furta yana duban Nudrat, ta amsa

da toh sai dai a ganinta mene ne ciki don ita ko Sadiya sun je gidan

ɗ

ayansu? Ita ba ta ga wani abu ba.

Sadiya kuwa sosai ta ji Hamma ya burge ta yadda ya fahimce ta. Har cikin makarantar ya shigar da su ya nemi wuri ya tsaya.

"Toh yaran Nene, a ma

ida hankali ga karatu. Iyakar karatun please, ban da shirme da shiririta."

"In sha Allah. Mun gode." Sadiya ta amshe, Nudrat ma ta bi sahu. Ya bi Sadiya da kallo har ta fice a motar kafin ya kauda kai gami da sauke ajiyar zuciya. Ba ya son gasƙata abin

da zuciyarsa ke raya mishi game da ita. A iyakar saninsa so guda

ɗ

aya ne, kuma Najma yake yi wa shi.

'Ita tana maka son da ka ke mata?' Wani

ɓ

angare na zuciyarsa ya watsa mishi tambaya. Ya kawar da wannan tunanin ta hanyar jan guntun tsaki gami da daka

tar da Nudrat, a aljihu ya fiddo dubu uku yace ta ba Sadiya. Ta kuwa washe haƙora tana godiya kafin ya ja mota ya yi gaba.

Sadiya baki sake ta ke kallon sabbin dubu ukun da Nudrat ta saka a tafin hannunta, ta yi saurin kai hannu za ta jawo ta don ta ma

yar amma Nudrat ta matsa da sauri.

"Aa Nudrat, ba zan kar

ɓ

a ba."

Haka ta dinga magiya amma Nudrat ba ta ko kalleta ba. Ganin za ta

ɓ

ata mata lokaci kuma tana son gabatar da sallar la'asar kafin su shiga aji sai kawai ta zura a aljihun doguwar rigar

atamfarta da zummar idan sun fito lakca za ta mayar mata. Amma har suka rabu Nudrat ba ta kar

ɓ

a ba.

Inda Sadiya ta ji dadi yadda Inna ba ta mata fa

ɗ

a ba sai dai cewa da ta yi ta dinga kula kuma ta riƙe kanta, ba ta son zaƙalƙalewa mutane musamman masu

hannu da shuni haka. Malam ma ya abin da Nene ta bayar, ya kuma ji dadin yadda Sadiya da Innarta ba sa

ɓ

oyewa mishi komai, ko babu komai zai ƙara sanin

ɗ

iyarsa da mutanen da take mu'amalanta.

***

A kishingi

ɗ

e take a falonta, su uku ne zaune a cikinsa

. Waleedah, Azeema sai ko ita Hajara cikon ta ukun. Gasassun kaji suke ci suna korawa da lemo ita kuwa tana aikin latsa wayarta. Sallamar ƴar aikinta wato Atine ce ya sa ta

ɗ

ago kai, Azeema suka amsa.

"Lafiya?" Hajara ta fa

ɗ

i a zafafe tana kallonta don

ba ta ga dalilin da za ta zo ba a neme ta ba. Matar ta zube jiki na rawa ta ce.

"Ki yi hakuri ranki ya da

ɗ

e. Dama Gwaggo Atine ce ta zo ta nemi alfarmar na ce tana so ku yi magana mai muhimmanci. Ta ce don Allah ki ba ta damar nan."

Hajara ta ja do

gon tsaki. A fili ta ce.

"Wato matar nan na rufe ta daga kirana na kuma jaddada mata matuƙar ta sake sauya lambar wani ta kira ni sai na manta wace ce ita a wurina na zagi uwa da ubanta, shi ne ba ta daddara ba ta zo gidana?"

Ta yi ƙwafa mai ƙarfi sa

nnan ta dubi Atine.

"Je ki ki ce ta ƙaraso. Yau zan mata wankin babban bargo!"

'A zumuntarku.' Cewar Atine a kasan ranta, a fili kuwa toh kawai ta amsa kafin ta miƙe tana ficewa zuwa falon ƙasa.

Ta iske Gwaggo Atine a zaune ta sha wani uban lesh

inta mai shegen nauyi kalar na inyamurai, fuskarnan sai maiƙo take yi amma kuma bakin an shafe shi da jan jambaki. Dariya ce ma ta kusan su

ɓ

ucewa Atine sai ta danne ta ce.

"Yauwa ta ce ki hau."

"Ok." Gwaggo Atine ta furta don ita a wasu lokutan jin

ta take kamar wata baturiya. Ta dai yi karatunta har sakandire, tsalle-tsallen da iyayen suka kula tana yi ne yasa aka yi mata aure don kanta ya fiye rawa a lokacin.

Da rawar jiki ta haye saman ta shiga falon da sallama. Waleedah da Azeema suka dube ta k

afin su dubi junansu su fashe da dariya har da cafkewa. Gwaggo Atine kuwa ta kalle su a sheƙeƙe, ta san dai duk kusancinsu da Hajara ba su kai ya ita ba. Hajara dake ƙare mata kallo cikin takaici ta ja tsaki. Miƙewa ta yi ta na fadin.

"Biyo ni." Daga h

aka ta nufi hanyar

ɗ

akinta, Gwaggo Atine ta bi su Waleedah da harara sannan ta bi bayan Hajara.

Waleedah duk sai ta kasa sukuni, hankalinta gaba

ɗ

aya ya tafi a kansu, to me za su yi? Babu damar sani don haka kawai ta fiddo waya ta yi dogon rubutu ta tu

ra saƙo ta ajiye.

A

ɗ

akin kuwa suna shiga Hajara ta rufe cike da masifa ta ce.

"Wai ke ba na yi maki katanga da shigo min gida ba? Ko don ba ni da karnuka? Ko kuwa don kin ga ban nuna fuskarki ga Maigadina ba ta yadda ko kin tunkaro ƙyauren zai daka

tar da ke?"

Ta ƙarashe tana huci da jijjiga jiki tana watsawa Gwaggo Atine banzan kallo. Sai Gwaggo Atine ta zube gwuiwa a ƙasa.

"Na tuba Autar Mama, ki yafe ni. Na rantse maki wannan mutumin hatsabibin gaske ne, ya san aikinsa akasi kawai aka samu.

Amma ai ba a rasa nono a ruga, ga su nan da yawa kuma wa

ɗ

anda su ma sun san ta kan aiki? Ki ba ni wata damar na rantse maki ko so ki ke yi a haukata maki yarinyar can da uwarta sai an yi. Ai mantawa na yi da Zakanyar Daji."

Hajara ta yi shiru tana nana

ta sunan ƙarshe da Gwaggonta ta fadi. Zama ta yi gefen gadonta. Gwaggo kuwa sanyin na'urar yana ta ratsa ta amma fa ba ta bar gumi ba, ita babban burinta kar wannan gara

ɓ

asar na samun ku

ɗ

a

ɗ

e daga Hajara ya wuce ta.

"Wace ce ita kuma?"

Wannan tambay

ar ta sa Gwaggo jan numfashi ta furzar cike da samun nutsuwar zuciya, ko babu komai ai an zo wajen don haka ta gyara zamanta har da tanƙwashe ƙafafu ta soma magana.

"Wata hatsabibiyar bokanya ce, matar da idan ta yi maki aiki zai wahala ki isa gida aik

in bai riga ki kai wa ba. Ina tabbatar maki Autar Mama za ki sha mamakin yadda za ta kassara maki rayuwarsu. Ke ni ina ji a jikina ma kukanki ne ya zo ƙarshe. Ai da ma can na so kai ki tun farko, toh matsalar gaskiya ita ba nan take ba."

"A bangon duniy

ar ina zan je na same ta?"

Kai tsaye Hajara ta furta tana kallon Gwaggo, ji take dagaske ko a ina matar take za ta je gareta matukar kwalliya za ta biya ku

ɗ

in sabulu toh me zai dame ta? Ai buƙatar ma je Hajji sallah ne.

"A Mubi take."

Hajara kanta

ya ƙulle ta ma rasa ina ne Mubin? Kafin ta nemi ƙarin bayani Gwaggon ta

ɗ

ora.

"Can Adamawa."

"Kin kuma tabbatar da ba zan yi zuwan banza ba?"

Dariya Gwaggo Atine ta yi.

"Autar Mama kenan. Ai ba zan kawo maki gaibu ba. Saboda na ga zahiri loka

cin da na yi tashen rayuwa a gidan..."

"Ya isa, ban nemi ki

ɗ

auko min tsohon tarihinki ba marar cikakken tushe. Ki shirya, a goben nan zamu wuce."

Da girmamawa Gwaggo ta amsa tana washe baki.

"Yauwa yanzu na ji batu, ai da zafi-zafi daman ake bugu

n ƙarfe. Bari na koma gida na dauki abin da zai min amfani sai na dawo nan na kwana. Zai fi kyau ace sammako muka yi."

A wulaƙance Hajara ta dube ta.

"A wane gidan za ki kwana ki ke nufi?"

Jikinta ya yi sanyi.

"Wai da a nan, kin ga zai fi mana

sauƙi ko?"

"Babu wajen kwananki a nan ai Gwaggo, ki tashi ki kama hanya. Ke yanzu babu kunya go

ɗ

ai-go

ɗ

ai da ke ki wani zo ki tattare a gidan ƴarki? Auren ki ke son kashe min mu ha

ɗ

u mu durƙushe?"

Gwaggo ta kama baki, abin kuma ya fi ƙarfin ta mayar

da martani don haka ta miƙe kawai, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Tana son ta nemi na mota amma tana shakkar a ya

ɓ

a mata wata baƙar sai dai kuma ta

sani ba za ta iya jurar tafiya daga gidan nan ba tare da ta tatsi Hajara ba ko yaya. Don haka

ta juyo tana

ɗ

an gyara zaman

ɗ

aurin da ta yiwa zanin leshinta a saman riga ganin zai kunce.

"Toh, Allah ya huci zuciyarki dai. Amma a taimake ni da na mota. Kinga goben ma durof zan

ɗ

auko gudun kar su tsaya neman fasinja da Asubar fari mu je mu makara

."

Tsaki Hajara ta ja. A fili ta ce.

"Dama idan ba ki tambayi kudi ba ai ba kya ji dadi ba."

Gwaggo dai mamakin yadda raini ya gifta haka tsakaninta da

ɗ

iyar ƙanwarta take. Koda dai, ba a fushi da masu ku

ɗ

i wannan ne dalilinta na danne

ɗ

an zafi-z

afin da ta ji zuciyarta ta fara ta saka hannu ta kwashe ƴan

ɗ

ari biyar sabbi da Hajara ta wurga mata saman

ɗ

an teburin da ke ha

ɗ

e da gadonta. Godiya ta yi ta fito bayan ta musu wuri a jakarta.

Ko kallon su Waleedah ba ta yi ba ta fice, ita kuwa Waleeda

h da kallo ta bi ta don ta karanci yanayinta, ta gane kamar ma sun shirya komai ya wuce. Hakan ba ta gasƙata ba sai bayan da Hajara ta fito fuskarta dauke da walwala irin wanda tun zuwansu ba su gan shi a tattare da ita ba.

***

Tunani iri-iri babu wan

da bai zo mata ba a kwakwalwa. Idan ka ture wahalar doguwar tafiyar da ta biyewa Gwaggo Atine ta yi, da kuma taka tudu da gangare da ta dinga yi har ba don ma Allah ya kiyaye ba ta kusa fa

ɗ

awa wani tafkeken rami. Ga raunin da ta ji a ƙafarta dalilin fa

ɗ

uwa

r da ta yi dab da ramin. Duka wa

ɗ

annan ba su ne ke sanya Hajara ji kamar ta shaƙe wuyan Gwaggo Atine a tsakar daji ta kashe ta har lahira ba face saboda rashin nasarar da zuwanta ya haifar. Koda dai Bokanyar ta yi mata

ɗ

an albishir na cewa za ta yi komai d

on ta ga ta karya mugun sihirin da wancan la'anannen Bokan ya yi mata don ta tabbatarwa Hajara duk inda za ta shiga, aikinta zai matuƙar wahala ya cimma ruwa saboda da baƙaƙen aljanu ya yi wani haukataccen tsafi a kanta. Duk da haka ta dire wa matar kudade

da ta ba ta tabbacin shafawa Sadiya baƙin jini a wurin kowane

ɗ

a namiji.

Hajara ta ƙara furzar da huci tana mai duban saitin da Gwaggo Atine ta ke, baccinta take shara tamkar babu wani abu da ya faru. Ta ja dogon tsaki ta kauda kai ta maida ga kallon

dajin da suke ratsawa da ko sunan wurin ba ta sani ba.

Ranta a jagule haka ta shigo gidanta don dama ana shigowa cikin garin Kano ta sallami direban da ta

ɗ

auka haya da kuma Gwaggo Atine ta tuƙo motar da kanta.

Motar mijin nata da ta gani a farfaji

yar ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login