Showing 27001 words to 30000 words out of 143803 words

Chapter 10 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4747

Mama ta samu ta daina kukan sannan ta yi mata bayani.Ran Mama ya Sace sosai ba ta san sanda ta ji jawaye ya na zuba a ?uncin ta ba." Na gaji da halin da yake min! Zuciyata ta fara gajiya amma ba komai Allah ya fi shi da ikon Allah sai ya yi nadama,akan halin da yake miki."

Sosai Juwairiya take kuka koda Mas'ud iyayensa suka koma gida suka sanar mishi a abin da ya faru,hankalinsa ya tashi matu?a duk ?o?arinsa na ya fahimtar da su,amma sun ?i ?arshe wan mahaifinsa ya gyara zama yace." Ko da a ce yarinyar ba halinta bane,to ?anin mahaifinta ba ya son ya baka ita ka kyale musu yarinya ga ?an'uwan ka nan sai ka zaSa a cikin su."

Ransa ya Sace matu?a da ma ya ba shi izinin ya turo dangin sa saboda ya faWa musu haka.
Motarsa ya Wauka sallama ya yi bai ko tsaya Mama ta amsa ba ya faWa gidan,a yadda ta gan shi ta san ba shi cikin hayyacin sa.

Da sauri Juwairiya ta ruga da gudu don ta saka hijabi ganin ya shigo." Mama ya Baba Sani zai yi haka? Juwairiya ya aiba ta a gaban iyayena. Wai me kuka yi mi shi ya tsane ku?"Ya faWa yayin da idanunsa suka kawo ruwa.

Cikin jimamin lamarin Mama ta share hawaye ta kalli Mas'ud da ya haWa kansa da gwiya hawaye na zuba a fuskarsa,sai ya ba ta matu?ar tausayi ta san yadda yake son Juawairiya duk da iyayensa suna da shi amma a haka yake son ta.

Ka yi ha?uri ka san matar mutum kabarin sa Allah be nufi Juwairiya matar ka bace,ka bi zaSin iyayen ka ni na san duk korar mata masoya da yake in har lokacin ta ya yi bai isa ya hana ba."

" Gaskiya Mama ba zan iya jure rashin Juwairiya ba zan je na sami Baba Sani duk abin da za'a yi sai dai ayi haka kawai ya din ga cusgunawa rayuwarku.Ya katse ta da faWin hakan ransa a Sace tare da mi?ewa.

" Zo Mas'ud don Allah karka je a yadda ranka yake a Sace za'ayi Satatta,ka san halin shi ba shi da ha?uri ni ce na haifi Juwairiya ina me baka ha?uri ka ha?ura da ita,shi kaWai ne wanda take gani a matsayin na ta in har aka Sata mishi wa za ta ri?e?Ka yi ha?uri Allah be nufa za ka aure ta ba."

Kawai sai gani ta yi ya saka kuka ya na kallon Juwairiya da ita ma take kuka na tausayin halin da suke ciki." Juwairiya zuciyata za ta shiga cikin wani hali na rashin ki.Ki yi min addu'a Allah ya ba ni mace me irin halin ki,ni na san ke wace ce ko idanunki mutum ya kalla ya san kina da tarbiya da natsuwa.Ina sonki zan ha?ura da auren ki saboda umurnin Mama."

Fita ya yi har da gudun sa ya na sharen hawaye Juwairiya ta mi?e da gudu ta shige Waki tare da saka kuka.Sam ita ba ta ga dalilin da Mama za ta hana shi ba,ba ta san me Baba Sani yake nufi da ita ba shi ya sa take girmama shi,abin da ya sa ta?i ga ya mata ta san duk ranar fa ta gaya mata ?udirin sa akan ta, ?ila zuciyarta za ta buga domin abin ya yi muni.

Tun daga wannan ranar ba ta ?ara gani Mas'ud ba ko wayar da ya siya mata Mama ?wacewa ta yi ta ije,don a yadda ta ga take-taken ta za ta iya kiran shi kuma shi ma haka.Tun ta na saka ran ze dawo har ta cire sai dai ta wahala kafin ta cire son shi a ran ta,sannan da ga baya taci gaba da al'amuranta.

Mariya ta sami miji za ta yi aure anan kusa da layin su za ta yi auren don haka su Juwairiya su ne ?an mata.Su Juwairiya an sha gayu da lalli an yi kyau sosa,ana ta hidimar biki don ba zama an saci Wan Sarawo.
Zaune suke ana hirar ?an mata Juwairiya ta kalli Mariya yadda ta sha kyau yace."Su amarsu kin ganki kuwa,dama komai munin amarya ranar bikinta sai ta haska."

Fari ta yi musu ta na dariya tace." Ku zauna kuna rungume filo ni dai Allah ya hutashshe ni na shige daga ciki,ku tsaya kuna ruwan ida kwayi kwantai."
Wani irin dundu Juwairiya ta duma mata ta nafaWin." Ji min ?ar ba?in fata wato fatan da kike mana kenan tunna kin shige daga ciki ko? To in sha Allah muna bayan ki."Sauran ?an matan suka taso mata ita dai Mariya dariya take musu,sannan tace." Ai ke Juwairiya Baba Sani ya hana ki aure da tuni kin haihu ma.Amma ba komai Allah ya na tare dake lokacin ki ne kawai ba yi ba."
Shiru ta yi sai hawaye yayin da mutanen Wakin suke ta ba ta baki.
A haka suka sha bikin Mariya aka kaita Wakin ganin Juwairiya za ta tafi ta kama ta tare da saka kuka.Sai kuma ta ba Juwairiya tausayi ta rungumeta ta na share mata hawaye.

Mariya ta share hawaye tace." Maganar da mukai dake akan aikin nan kije Allah za kiji daWi kin ga ni na yi aiki da su."Juwairiya tace." Ke ni raba ni da aikin nan don na yisu amma ban ji da daWi ba."
" Allah ki gwada wannan kin ga yanayin halin da kuke ciki,ga shan maganin Mama dole kina bu?atar kuWi."
" To zan shawarci Mama duk abin da tace sai na je."Da wannan Juwairiya ta tafi gida cike da kewar ?awarta wacce ta temaka mata.

Koda ta yi ma Mama magana shiru ta yi zuwa can tace." An ya zan barki kiyi aikin nan nifa tsoro nake yi kina ganin rashin mutuncin da Hajiya Binta ta yi miki,amma tuna kin ce Mariya tace ta na da mutunci sai ki je Allah ya tsare ki."

Numfashi ta saki tace." To bari na gwada mu gani."

Juwairiya ta fara aikin cikin jin daWi ga karatu da take samu ake yi wa yaran lesson da islamiya matar ma ba ruwanta.

Watan ta biyu a gidan ranar ta kammal aikin ta za ta tafi matar tace." Don Allah Juwairiya ki tsaya zamu je gidan biki ni da yarana,zuwa yamma zamu dawo sai ki tafi in kuma na yi dare zan kaiki a mota."

Duk a ranta ba ta so ba amma sai ta amsa da." To." Ta koma ta zauna yayin da ita kuma ta shirya da yaranta suka fita.

Tun da suka tafi har aka kira sallah ba ta dawo ba,ranta ya fara Saci don ba ta son ta yi dare kar Baba Sani ya dawo ya kuma ?ara mata wani sharrin.

Jin ?arar mota sai ta yi maza ta le?a ta windo ta na tunanin ita ce,sai dai cikin takaici ta koma ta zauna ganin mijinta ne ya dawo.
Ya shigo da sallama ya amsa ya na kallonta." Juwairiya har yanzu ba ki tafi ba?"Ya tambayeta ya na kallonta." Eh tunna ka dawo bari na tafi "
" No ki kira ta nima ?ara fita zan yi."
Don takaici ko amsa mishi ba ta yi ba to me ya dawo da shi koma wa ta yi ta zauna.

Ya shiga cikin Wakin sa mintina biyar ya fito sai kawai Juwairiya taga ya yi kanta gadan-gadan! Da sauri ta mi?e tare da saka salati dai-dai lokacin da ya fisgota ya haWa ta da jikin sa da ?arfi.

Kasancewar shi namiji me jiki da ?arfi ya yi nasarar kayar da ita ?asa tare da yi mata rumfa,yayin da dabbe ya kaure ko kaWan ba ta yi tsammanin ya na da wannan halin ba.Kuka ta saka ta na rokon shi,amma bai kula ta ba yaci gaba da ?o?arin ida nufin shi.

" Inna lillahi Faruk!Me zan gani dama amanata kuke ci?"Ta furta cikin ?araji! yayin da ta yo kan juwairiya ta hau ta da bugu.

Juwairiya ta yi kuka ta yi ihu ji take kamar numfashinta zai fita domin kanta ta hau ga ta da ?iba,da ?yar ya samu ya SamSare Juwairiya ta samu ta gudu.

Da ?yar ta samu ta isa gida ta na kuka a ranar ta rantse ba za ta ?ara yin aiki ba,ko da mutuwa za su yi yadda ta shigo Mama ta tsorata.

Bayan ta yi mata bayani tana kuka Mama sai da ta zubar mata da hawaye ganin halin da take ciki.A ?alla sai da ta yi sati ta na jinyar jikinta don har sai da ta kwanta ciwo.

Haka rayuwa take tafiya musu yau ba?i gobe tsummma ga ciwon Mama ya yi tsanani.Wani abin ?arin tashin hankali Ibrahim da dama can ba lafiyayye bane,saboda sikila ne shi jikin sa da ya yi sauki amma a cikin kwana biyun nan jikin ya tashi.

Ciwon shi sai yake son ya danne na Mama amma duk wanda ya ganta ya san ta na cikin tsananin ciwo.Ga kuma Baba Sani da ya sanar da Juwairiya ya yi mata miji wato Alhaji Tanimu.

A ranar da Baba Sani ya gaya mata sumewa ?au ta yi don ya tabbata Baba Sani ba ya ?aunarta,don ita da ya aura mata shi gara ta zauna ba aure ko ace mutuwa ta yi.

Waye a faWin garin be san Alhaji Tanimu ba wanda ya mai da mace tamkar rigar sawan shi.Mutum ne mara addini ga shi kamar wani hor.Kusan duk shekara yake sakin mace ya ?ara aure bayan ya tabbatar sun sami ciki,don baya son haihuwa a tunanin ta shi kan shi be san iya yawan yaran shi ba,duk da wasu ya na ba ma iyayensu mata kyauta wasu kuma ya kai su almajiranci.

Sannan an sha kama shi ?ara ?anana ya na musu ya lalata musu rayuwa irin mutumin da Baba Sani yake son ya zama mijinta kenan.Ai Juwairiya ?aramin hauka ta yi don gara yace ta shiga duniya.

Shiko Alhaji Tanimu se Winkirama Baba Sani kuWi yake yi hankalinsa kwance ganin zai mallaki wannnan zu?e?iyar,shi ya sa be damu ba ko sanda ya zo zance ta?i fitowa tallar ta fa aka kawo mishi har gida.

Rayuwa a wannan karan tafi yi wa su Juwairiya illah ga aba abinci sannan dukkanin su ba lafiya,ga Baba Sani da yake ta shirye-shiryen bikin ta don har an kawo kayan sa rana watan gobe biki.

Mama ta shiga tashin hankalin ciwonta ya ninku ga yunwa har takai sai su wuni ba su saka komai a bakin su ba.
Juwairiya ta tsara ma kanta ta gudu amma in ta ga halin da su Mama suke ciki sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta,ita kanta ba lafiya take da shi ba don ta na ganin har tafi su Mama jigatuwa saboda zuciyarta da take ji kamar za ta fashe.

Ganin yunwa zai kashe su sannan duk kuWin da Baba Sani yake karSa bai ta ba ba su koda na sabulu ba,ta je gurin Mariya ta ara mata naira dubu biyu ta fara jarin gyada.Da wannan suke samun abinci.

*******
Zaune yake cikin damuwa sai kuma ya mi?e don a yau jin sa yake duk shawarar da amininsa ya ba shi zai iya Wauka saboda halin da yake ciki.Makullin motar shi ya Wauka ya nufi gidan A.k.
Sai dai cikin rashin sa'a ba ya nan don haka bayan sun gaisa ya fice daga gidan ya samu wani guri mara hayaniya ya tsaya,tare da ciro waya ya kira A.k.

Ba'a fi minti goma ba sai ga A.k akan mashin ya sauka ya buWe gaban motar ya shiga ya na share zufa."Am sorry aboki motar da ka siya min na kai ta service ba'a gama ba kan dole na baro motar na hawo mashin.Are you under the weather?"Ya tambayi aminnin nasa ganin yanayin sa.

Yace ya na kallonsa bai tanka ba illa ajiyar zuciya da ya yi ya kauda kansa gefe guda,ganin yadda aminin na sa yake ya san yauma ba lafiya to ko dame yazo oho don ya san dai zancen.
Suka Wan yi shiru ba tare sun ce uffan ba na tsawon lokaci sannan A.k ya katse shirun da cewa." Lafiya na gan ka wani iri in ce ba mutuniyar bace ta haWa maka zafi."

"Akan maganar da na nemi shawarar ka yau ma na ?ara bijiro maka da ita.I really need your advise pleese help me out."A.k ya kalle shi yadda idanunsa suka kaWa suk yi ja ga mamakin sa sai ya ga hawaye ya na sauka da ga ?uncinsa.
Ya kama hannunsa ya haWa da nasa ya ri?e sosai ya na kallonsa ya ci ga ba da cewa."I know my wife she is a woman of raging jealousy.Bazan iya haWa ta da wata mace ba kuma ba yan haka na yi mata al?awari,amma ina jin zafin rashin yaro da ba ni da shi wanda hakan in ban Wauki mataki ba zai iya taSa lafiya ta,domin a yanzu ya kai matsayin da ba na iya bacci.

Tun da ya fara magana A.m ya yi shiru ya na kallon sa a ransa tunani yake to ko amininasa ya ci kai ne ko kuma rashin haihuwar ya taSa tunanin sa, kamar yadda yace shi dai ya san ta aure ake samun haihuwa ya ba, shi shawara ya?i bi saboda wani al?awari na shi na banza to amma bari ya ji me yake tafe da shi.

Ganin ya yi shiru ya dafa kafaWarsa ya na cewa."Try to be patient ka san zuriya kake bu?ata kuma dole a aure za ka same shi,ba zaka so ka sami Wanka ta zina ba wanda na san ba halinka bane,amma ni banga dalilin da zai sa ka?i ?ara aure ba bai ita ta Sata mahaifinta da kanta ba?"Ya Wan faWa da zafi kuma da tsigar tambaya.
" Haka ne." Ya ba shi amsa sannan ya ci gaba da cewa." Duk akai na ne ta samu wannan matsalar gaskiya i can't make up my mind ko zan iya cin amanarta."

?arin takaici maganganunsa suka ?ara ba shi gani yake ba shi da tsayuwa a gidan sa,amma shi bai ga yadda matar shi zai ta da hankalin shi ba,don kawai zai ?ara aure kuma duk laifin tane.
Ya kaWa kafaWunsa yace."It is up to you ni dai na gama baka shawara."Yace amma sai kuma ya ga hankalin aminin nasa ba shi a gurinsa wata?ila ma be san me yace ba.

A hankali ya bi gurin da yake kallo shima Juwairiya ce da tiren gyaWa a kanta da ga ganinta ka san ta na cikin wani hali, kusan ma ta na tafe ta na share hawaye saboda har Alhaji Tanimu ya kawo kayan auren ta na jin gara ta ha?ura ta aure shi,wata?ila shi Allah ya tsara ya zamo mijinta ta san bawa ba ya wuce abin da Allah ya tsara mata,sai dai yanayin halin da Mama da Ibrahim suke ciki ya sa ta zagaya wa da gyaWar da yau ba ciniki ta haWa da kuWin da Mariya ta ba ta ta kai su asibiti.

A.m da ya zuba mata ido ya na kallonta bai taSa ganin mace me sanyi da wani irin shauki a tare da ita ba sau,haka kawai ya ji ta kwanta mishi a rai ba wai son ya na son ta ba irin zai iya magana da ita har ya ba ta lokaci su yi wasa da dariya,kuma ya nemi shawarar ta kuma zai iya yin komai don ta yi farin ciki,zai iya cewa yau ne rana ta farko da ya ga wata mace bayan Zainab har ya na jin zai iya mata magana.

Wato in ya fahimci zuciyar shi ?awa yake son ya mai da ita ko ?anwa." To amma duk tsanar talaka da na yi sai ace na yi ?awa da ?ar talaka kuma ?as?antacciya ?ar talla kai an ya da wuya.".
Yace a zuciyar a cikin zuciyarsa ya na me ?o?arin kauda idanun sa daga gareta don jin hakan bai dace ba ace duk matsayin shi.Sai-dai idanunsa sun kasa Wauke kan su daga kallonta ya na ?ara za?ulo kyawunta.

Ta na tafe cike da damuwa har tazo ta gaban su za ta wuce." Me gyaWa." Kalmar da bakinsa ya furta ba tare da ya ba shi umurni ko tunanin hakan ba.

Juwairiya ta ji wani irin sansanyar murya mai kama da sarewa ta kira ta ta na son ta juya amma sai ta da?ile kanta da juyawar,don ?ila in ta ga mamallakin wannan muryar ba ta san halin da za ta shiga ba sai kawai ta ci gaba da tafiya yayin da aranta take addu'ar Allah ya sa karya ?ara kiranta, don ta san in ya ?ara kiran ta ba za ta iya tursasa zuciyar ta da ?in juyawa ba.
A.m ransa ya matu?ar Saci ?azama da ita ta na talaka zai kira ta ta?i waigowa ya so yaje ya yi watsi da kayan tallar,ya ga uban wa take ta?ama da shi ta?i amsa kiransa amma da ya yi tunanin ko kurma ce sai ?ara kiran ta a karo na biyu.
Cak! ta tsaya amma ba ta wai go ba ta na addu'a a cikin ranta yayin da idanuwanta suka za?u da suga wannan mamallakin muryar.A hankali ta tako ta iso gun motar su ta tsaya ta kasa magana kuma ta kasa Waga ido ta kalle shi.
Kusan minti goma ta na tsaye ba tare da ya kalleta ba me ya gani oho ganin ita ma ba ta da ninyar ta yi mishi magana kuma ba ta tafi ba A.k dai ya na zaune ya na kallon ikon Allah.

A.m ya buWe motar da nufin ya yi mata wula?anci dai-dai lokacin da idanuwan su suka tsar?e da na juna.
Kyansa yanayin jikinsa idanuwansa da yadda yake kallonta suka ruWa ta ta yi kamar za ta faWi, amma sai ta dafa jikin motar sa ta na kallon shi cikin wani irin shauki,lokaci guda ta ji abu me kama da guduma ya sauka akanta! Yayin da wani irin shokin na soyaryarsa suka dinga Wana mata son shi a cikin ranta,har ta ji za ta iya mutuwa in ba ta same shi ba.

Idanun su da suka tsar?e da juna sai ya tsinci kansa da kasa mata rashin mutuncin da ya yi ninya a yatsine yace."Nawa-nawa gyaWar."
Ta zuba mishi idanunta sai kuma ta janye ta lumshe su tare da kauda ganin ta gare shi ahankali da sanyaryar murya tace.Hamsin gwagwani Waya."
Ya Wan ?ura mata ido haka kawai kyawunta da muryarta yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login