Showing 66001 words to 69000 words out of 143803 words

Chapter 23 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4743

magana kuma ni ban ce ki yi min kuka ba."
Ya faWa ganin ta yi rau-rau idanunta sun kawo ruwa.

Kamar umurni ya ba ta sai ta yi ?o?arin mayarwa ta na son kallon sa.

A.m ya saka hannun sa ya shammace ta kawai ya cire mata hijabin jikinta ya na faWin.

"Ni fa yanzu ban ga abin Soye-Soye a tsakaninmu ba bayan kin san ke Win matata ce,wanda aure ya ba ni damar mallakarki a gurin makwaWaicin ?anin mahaifinki."

Ta kauda kanta ba ta ce komai ba sai kuma ta saka kuka.
Dun?ule hijabin ya yi ya jefar ya ci gaba da faWin."Anyway yanzu dai ni maigida na ba da umurnin in dai daga ni sai ke ne a gidan,to amaryar wucin gadi ?ar ta ?ara saka hijabi ki bari sai in wanda kike jin kunya ta dawo sai ki saka abinki,amma ni da ke ai ba kunya tsakaninmu ko."

Ya gama maganar ya na tambayarta ya na wani irin murmushi mai kama da na mugunta ko ya na son shirya wani ?eta.

Juwairiya ta ji wani irin sanyi a ranta karan farko haWuwara da A.m yau ne rana ta farko da ya yi mata murmushi,duk da murmushin na sa da wata manufa ya yi amma hakan ya ba ta matu?ar citta a ranta.

Ta matsa daga kusa da shi ganin irin ?are ma jikinta kallo da yake ta fara tafiya a hankali.
"Juwairaah."
Ta tsaya cak daga tafiyar da take yi amma ba ta jiyo ba,shi ya taho har in da take ya matsa kuda da kunninta ya ce " Ina zaki matar wucin gadi ai ban gama magana ba,kin san ya kamata a Wora daga in da aka tsaya ko."

Banza da shi ta yi tana mamakin wai haka yake mai ya sa yau ya ?ara zuwa da salo ne?

" To shikenan tun da kin ?i magana da ma zan yi godiya ne na ranar nan gaskiya na ya ba sosai,wannan daren momerable and remarkable ne a gurina,Allah shi zai saka miki saboda ai ba ta ki da ?anin mahaifin ki ya yi."

Ya faWa ba tare da kunya ba kuma ya na kallon ?wayar idanunta.

Juwairiya ta Wago ta kalle shi ba tare da ta shirya ba ta ji ta sakar mishi wani lalausar murmushin,har dimple Winta suka losa ta ruga da gudu ta shige Waki tare da rufo ?ofar.

A.m ya saki dariya don kunyarta ta na matu?ar burge shi matu?ar gaske,saboda ya na son mace mai kunya juyawa ya yi zuwa waje jin shigowar motar Zainab,ya saki duk wani wula?anci da yake son yi mata da tsanar ta da yake ji zai more abin sa kafin zuwa ranar rabuwar su,saboda tsakani da Allah ya ji wani girmanta a ranshi tun ranar da ya mallake ta,tsananin talaucin da take ciki bai saka ta zubar da mutuncin kanta ba.
?a ?an'uwana mata don Allah mu kama darajarmu domin shine mutuncinki, don Allah ?an mata ka da son abin duniya ko jinkirin aure ya sa ki zubar da mutunci,don ki na tunanin kin daWe ba ki yi aure ba ba zaki yi ba,ki tuna lokacin ki ne bai yi ba,kuma duk daren daWewa in da kina raye za ki yi,yayin da ki ka yi aure wula?anci shi ne abin da za ki girba har ?arshen rayuwarki.

Kuma ?ar'uwa da ki yi saurin aure ki fito gara ki daWe ba ki yi ba,ki daure har ki samu wanda zai kula da ke emotionally,phisically financially,and mentally.Shawara ce.

Juwairiya gado ta faWa tare da Waukar filo ta rufe fuskarta da shi.
" Mai ya sa yake min irin waWannan kalamai ne wai dama ba shi da kunya haka?Kai na rasa gane wa wallahi gabaki Waya ya canza dariya fa ya yi min."

Sai ta saki murmushi ta mirgina wani gefen ta na jin wani irin nishaWi a cikin zuciyarta.

" To ko ya fara sona ne?"

Da sauri ta kori wannan tunanin a cikin zuciyar ta amma kuma ta na fatan haka ta kasance,da sai ta ce tafi kowace mace sa'ar miji duniya,don A.m wuta ne gurin kyau da tsari.


Washegari Juwairiya ta na kicin abinci take haWawa hankalinta kwance cikin jin daWin abin da ya faru,jiya tsakaninta da shi jiya saboda kwana ta yi muryar sa na maimaita godiyar da ya yi mata.

A hankali ya shigo ba tare da ta sani ba don ta zage ta na haWa mishi abincin da zai ?ayatar da shi.

Ji ta yi an rungume ta ta baya ba tare da ta lura ya shigo ba.Wani irin ihu ta saki tare da matsawa gefe,sai kuma da ta lura shi ne ta Wan saki murmushi.

" Kai ki na da matsala Juwairaah!Yanzu da matar gidan na nan mai kike tunanin zai faru?Ke akan komai sai an ga gazawar ki?"

Ta yi shiru kawai ta na murmushi ba tare da ta ce komai ba,don ita ba ta san Zainab Win ta fita ba.

"Kawo min abinci yunwa nake ji."

Ya faWa tare da saka hannun shi a daidai gurin dimple Winta ya fita.

Bin sa da kallo ta yi har ya Sacewa ganinta ta yi ajiyar zuciya sannan ta shirya masa abinci.

Bayan ta ije masa abinci ya na zaune da remote a hannunsa ya ce ba tare da ya yi duba gareta ba."Amaryar wucin gadi zo mu yi hira tunda matar so ba ta nan,na lura kamar kina da ciwon rashin magana."

Sai ta tsaya ta na kallon shi da ya yi fuska kamar ba shi ya yi maganar ba.
" Ki zauna mana kika yi min tsaye haba sai kace wata soja."

Namma zama ta yi ba ta ce masa ?ala ba don ta lura so yake ta tanka.
A.m da ya kasa controling Win kan sa ya matsa kuda da ita ya na mata wasu irin abubuwa.

" Don Allah ina ro?on ka bu Waya.".
Ta ce yayin da idanunta suka fara zubar hawaye tsayawa ya yi ya na kallonta zuwa can ya nisa ya ce da ita."Ina jin ki Juwairaah."

A hankali ta yi ?o?arin saita muryar ta ta fara magana cikin sanyi.
"Ka ce kar na saka soyayyar ka a zuciyata ni ma ina ro?on ka da ka dai na ?o?arin kusanta kan ka da ni mu tsaya daga iya sharaWinmu,saboda ina tsoron kar zuciyata ta kamu da sonka duk da na san kai Win ba sa'ar soyayya da ni ba ne,kaddara ta haWa mu ina jin tsoron ranar da zan tsinci kai na cikin soyayyar ka don na san ka yi min nisa na har abada,amma soyayya ba ?arya ba ne kuma zuciya ba ta da ?ashi,A.m babu wata mace da za ta yi tozali da kai ba tare da ta faWa cikin kogin son ka ba.

Jikinsa ya yi sanyi matu?a ganin maganar da take yi daga cikin zuciyarta ta fito.

"Juwairaah kin taSa ganin an yi zaman aure ba tare da haka ba?Duk auren da kika ga ya ginu to hakan ya gina shi.Bani da nufin na cutar dake ki yadda da ni ki yi ?o?arin ya?ar zuciyarki daga son jefa ki cikin wahala da take son ta yi,kafin na aureki sai da muka yi sharaWi babu so a cikin tsarinmu don ba zan taSa zama dake na har abada ba ,amatsayin matata.Kuma karki manta uban ma?udan kuWi na sa na auro ki".

Ya numfasa ya na kallonta ganin kukan da take yi hannunsa ya saka tare da tarar hawayen da yake zuba kamar an buWe famfo.

" Ki adana sauran hawayen ki a kwai ranar da zaki bu?ace su kar fa su ?are,na tabbata ranar da kika haifa min baby in na baki abin da na yi ninya Juwairiya zaki nemi hawayen ki ki rasa bayan kin ?arar da su akan banza,don ni banga abin kuka a nan ba.Ki tuna mahaifiyarki na cikin kwanciyar hankali da jin daWi shin hakan bai saka ki saka ni a cikin farin ciki ba?"

Ya tambaye ta idanunsa a kanta hawaye suka ci gaba da zuba ganin ta?i magana sai sai ya mi?e ya fice daga gidan.

"Humh ba na tunanin a kwai abin da za ka ba ni na yi farin ciki fiye da ka sani a cikin zuciyarka.Am ka ?i ka gane abu ne na zuciya Allah ya jarabce ni da sonka tun kafin ka bijiro da manufar ka a kaina,na yi burin kar mu haWu tun ranar da na yi tozali da kai a kundin rayuwata."

Kuka take kamar wata zararriya ta na maganganu sosai daga baya mi?ewa ta yi,bayan ta fahimci ya fice daga gidan ta ci gaba da aikinta.

A haka rayuwa take wucewa A.m ya na more amaryar wucin gadi duk da ya ?osa su rabu,amma ya na girmama lamarin Juwairiya a zuciyar sa.

Tun ta na Wari-Wari da shi har ta saki sosai da shi domin ya bada duk wata ?ofa da zai saka ta saba da shi,har ta kai ga A.m ya na waya da Juwairiya a Soye su sha hira ya na tambayarta ko ya jefa ?wallon a raga.
Duk sadda ya yi mata wannan maganar hankalinta ya kan tashi matu?a ita gani take irin abubuwan da yake mata son ta yake.

Juwairiya ta saba da A.m ta na jin sa a ran sa kullum sai sun haWu da juna ranar da Zainab take gida kuwa,dole sai ya kira ta a waya sun yi hira wannan ya ?ara saka ma Juwairiya son shi na mutuwa ta na jin duk ranar da ya rabu da ita mutuwa za ta yi.

Amma idan Zainab ta na nan ko kallon Juwairiya ba ya yi,har yau in zai yi maganar ta ko Zainab ta yi mishi nuna yake bai ri?e sunan ta ba,sai dai ya ce wancan ko wa ta ke da suna.
Tun Zainab na mata ?orafin ta rin?a cire hijabinta har ta gaji,ta dai na don ta fuskanci ko mai za ta yi mata ba za ta dai na ba,kuma ina ruwanta tun da ta fahimci Juwairiya a kwai tsafta da kula da kai.

Juwairiya ta goge ta waye ta ?ara wani irin kyau jikinta ya ciko ko ina,ita kanta mamakin yadda ta goge take yi,sai dai ko hoda ba ta saka wa bayan kwalli duk da Zainab ba ta hana ta ba.

To ina ma take da lokacin kanta daga aiki sai chert,don in dai ba ta gurin aiki ta na ri?e da wayarta,ko magana take hankalinta na kan wayarta.
Duk lokacin da Juwairiya ta samu tsarki sai ta samu lemun tsami da ruwan gishiri ta sha,ita burinta ko a matsayin mai aiki za ta zauna in dai ya na nuna mata irin wannan soyayyar za ta rayu da shi na har abada.

Kimanin tsawon wata bakwai A.m ya na jiran ya ji ta ce mishi ta na da ciki,amma shiru kake ji malam ya ci shirwa,har ya fara tunanin to ko shi ma baya haihuwa.

Hankalin sa ya fara tashi sosai gashi A.m har ya kasa daurewa ya tambayi Juwairiya shi fa ya ?osa,lallaSasa take yi ta na faWa mishi Allah ne bai kawo ba,amma a ranta ta san abin da take yi.

Ya na zaune a falo zuciyar sa na tafarfasa da ya tabbatar Zainab ta ?ara tafiya ba tare da ta sanar mishi ba,ya ji a ran shi tunna ya na da Juwairiya zai ci gaba da ha?uri har zuwa sadda za su rabu,amma duk da hakan dole ta Wauki mataki saboda ya kamata ta sanar mishi ko da bai amince ba,ba wai ta kashe wayarta tafi ba.


Wayar A.k ya katse masa tunanin da yake yi sai dai bai Wauka ba wayar ta katse ya bi,amma ba network sai a ka ce wayar a kashe.

Wani irin bugu ya ji ana yi mishi wanda ya tada hankalin sa da sauri ya fita don shi a zaton shi Sarayi ne suke so su shigo mishi,duk da ce wa ?arfe huWu da rabi ne na yamma.

Ya na isa get Win maigadi ya she?o da gudu ya na faWin." Ka yi ha?uri ina bayi na zaga.Wannan wa ne mahaukaci ne yake ?wan?wasa ?ofa Allah ya sa lafiya."

A.m bai kalle shi ba ya buWe kofar sai kuma ya ?ame cikin tsananin mamaki ganin Baba Sani a tsaye ya na ta mazurai.

NI MA NA YI MAMAKIN GANIN SA SABODA NA SAN BA ALKHAIRI YA KAWO SHI BA NA IJE BIRONA DON NA HUTA.

KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN KAR KU GAJI BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN LINTAFIN.

SAKACINA KO HALIN MAZA

TAKU



JAMLA LAWAL ZANGO





TUNATARWA

DON ALLAH ?AN'UWANA MATA KADA KARATUN LINTAFI YA ?AUKE HANKULANMU MU MANTA DA BAUTAR UBANGIJI,KU TUNA ALLAH YA HALICCE MU DON MU BAUTA MASA NE.

YAU TAKE JUMA'A KAR A MANTA KARATUN SURATUL KAHAFI ALLAH YA BA MU ALKAIRUN DA KE CIKINTA AMIN








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha shidda.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.







*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 21*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM



A.m ya tsaya cikin tsananin mamaki ya na kallon Baba Sani da ya ci magani fuskar sa babu walwala ko kaWan, alamun da rashin mutunci ya zo koma fiye da haka don a wula?ance yake kallon A.m da yake jin kamar ya kai mishi bugu.

" Uban me ya kawo wannan mara mutuncin gidana ya akai har ya san gidana."

Irin tarin tambayoyin da A.m yake yi ma kan sa wanda ya kasa amsa ko da guda Waya ne.
" Kai Malam na ga ka na kallona kamar ba ka gane ni ba."
Baba Sani ya ce cikin Waurewar fuska ya na ?arasowa gurin A.m da ya harWe hannun sa a ?irji ya na kallon sa a wula?ance burin sa ya ji mai yake tafe da shi.

"Ba zan kalle ka ba ka san halina ba ni da mutunci mai ya sa ka zo gidana,bayan ka san duk abin da muka yi sirri ne a tsakaninmu,shi ne za ka biyo ni har gida saboda kai tantiri ne."

A.m ya faWa fuskar sa babu sauran fara'a ji yake kamar ya sha?e sa,domin ba?in cikin dake cikin zuciyar sa.

"Ban sani ba na ce ban sani ba wallahi kamar yadda kake faWin ba ka da mutunci na fika,don ni yawo nake a tasha da gidan karuwai kai ko ina tunanin iskancin na ka haye ka yi,in ban da iskanci ?ar Wan uwana a gidan ka kake tambayata abin da ya kawo ni gidan ka.Ai tushiya mafarin dawa."
A.m ya zare idanun sa ya na kallon shi ganin yadda yake Waga murya ya na son kowa ya ji,duk da unguwar ta su ta manya ce kowa ya na cikin gidan sa,amma A.m hankalin sa ya tashi ?warai sai ya shiga waige-waige ba yan ya galla ma maigadi harara dake tsaye ya na kallon su.

Sum sum ya wuce sannnan A.m ya taso ma Baba Sani cikin hargowa zai make shi,don yadda yake jin zuciyar sa na tafasa kai dukan shi ne samun sau?i.

Ganin da gaske dukan shi zai yi sai ya masa da sauri,amma ya?i wucewa a gurin faWa yake ya na hargowa tare da nuna A.m,da yake jin zuciyar sa kamar za ta yi bindiga.

A.m ya ?ara kai ma Baba Sani duka daidai lokacin da motar A.k ta sawo kai,da sauri ya yi parking tare da fitowa ya ri?e A.m da yake hargowar dukan Baba Sani.

" Ba ka da hankali ne A.m ka san me kake shirin yi ?anin mahaifin Juwairiya za ka daka karka manta shi ya ba ka aurenta?"

A.k ya faWa don ya kwantar ma A.m hankali ganin yadda ya zuciya.
"Allah ya sa mahaifinta ne yazo ba shi ba,tunna ya?i kama kan sa wallahi zan kulle shi igiya ta yi rara."

A.m ya ce cikin zafi yayin da yake jin kamar ya sha?e shi,shi ba?in cikin sa yadda akai har ya gane gidan sa.
" Bar shi A.k ka bar shi ya yi min rashin mutunci dama na lura ba shi da mutunci,amma tsoratar war sa ba za ta yi tasiri a cikin zuciyata ba.

"Ka gaya mishi in ya na son lafiyar sa, to ya bar nan kar kuma ya ?ara gangancin wucewa ta hanyar gidan,nan ballantana ya yi tunanin ?wan?wasa min gida,ka san ba shi da mutunci da ba ni ya samu ba haka zai fasa ?wan kowa ya ji."
A.m ya ce ya na kallon sa da yake ta karkaWa jikin sa alamun irin da rashin mutunci na zo ko fiye da haka.

" Ka kwantar da hankalin ka bai kyauta ba duba ga irin halaccin da muka yi masa,amma ka tsaya mu ji mai yake tafe da shi."

Ya ce da A.m sannan ya juya ya kalli Baba Sani ya ce."Mai ya sa ka yi haka ba yan mun yi waya da kai na ce maka zan zo."

Baba Sani ya kalle shi tare da kaWa kan sa ya na ce wa."To dussa ne ni da za ka shanya ni kwana biyu na jira ka ba ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login