Showing 87001 words to 90000 words out of 143803 words

Chapter 30 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4729

dalilin aurenmu am sorry to say da Zainab ta na haihuwa babu abin da zai saka na aure ki.Kawai ni na san in muka rabu zan yi kewarki da kishin mijinki don ki na da baiwar da ba kowa ce mace take dashi ba."

Ta na son ta yi magana kuka ya ?wace mata amma hakan na ta daure ta ce."Mai yasa ka shigo da ni cikin rayuwarka ka san ba gurbina a cikin zuciyarka?"

"Saboda ki haifi yaro na bawa Zainab saboda ina son na ga ?waina ya sa na aure ki."Ya faWa muryar sa a Wage.

"To mai ya sa kake gaya min maganganun da suke yaudarar zuciyata?Ka tsaya iya kan abin da kake bu?ata a gareni."

Cikin kuka take mishi maganar sai ta juya za ta ruga da gudu da sauri ya janyo ta zai rungume ko mai ya tuna ya sake ta ta ruga da gudu ta na kuka.

Cikin motar shi ya faWa ya na wani irin huci kamar mesa ya daWe a gurin sannan ya figi motar a guje kamar zai tashi sama.

Lantana mai aikin Zainab da take laSe a bayan kango ta na kallon A.m da ya yi shirin rungume Juwairiya ta fito cikin tsananin mamaki ta na kallon in da motar shi tabi.

Zaro idanunta ta yi cikin tashin hankali ta na mamakin da ma cin amanar ta suke shi da ita?Allah Sarki baiwar Allah ta na can ta damu da ita gashi wayarta ba ta shiga,ashe ita ta na can suna cin amanarta.Haba!Biri ya yi kama da mutum ai ko yau dole Zainab ta ji abin da suke yi ita ta na can sai tsabar son kuWi ta Wauko mace zu?e?iya ta ije ma mijinta.

TO FA WAYYO ALLAH BA RI NA YI NAN DON GASKIYA BAN SHIRYA GANIN WANNAN TASHIN HANKALI BA.






KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.








*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 25*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM




Hajiya Zainab tana zaune a ?aton katafaren falonta ita da ?awarta mai suna Nabila wacce suka taso tun yarinta,amma ita tana aure a Abuja ta zo ganin gidane da kuma ta ya Zainab murnar asibitin da ta buWe.

Lantana ce ta shigo saboda tsabar gulma jikinta har kyarma yake yi.

Duk da ganin tana tare da ba?uwa amma sai ta kasa ha?uri har ba?uwar ta tafi, matsawa kusa da ita ta yi ta fara magana don tsabar gulma da yake cinta.

"Hajiya don Allah in ba za ki damu ba ina son na yi magana da ke kuma mai mahimmanci."

Zainab ta kalle ta she?e?e tare da jan tsaki ta na tauna jingam a bakinta.
"Ni fa Lantana na fara gajiya da halinki yadda kika san ke kika kawo babu duniya,na san yau ma bai wuce ki ce na baki kuWin aiki kafin wata ya ?are ba,kuma na rantse ko me za ki ce ba zan bayar ba."

Ta faWa hankalinta na kan waya ta na hira da matar da ta addabeta take ta tura mata da sallama kullum,ba ta daina ba har sai da ta yi nasara ta fara magana da ita suna gaisawa.

Lantana ta kalleta a ranta ta ce."Banza mara mutunci kawai ai wallahi don kawai iskanci suke yi da ita da na so ma ya aureta na ga ?aryar iya shege."

Amma a fili sai ta ce." Ba wannan ya kawo ni ba idanuwana sun yi mummunan gani kuma in kika ji,wallahi hankalinki zai tashi matu?a ba na son abin da zai cutar da ke ne kasancewar ki na taimaka min.

" Ke dakata karki dame ni da shegen surutunki."

Ta ce bayan ta ije wayarta sannan ta kalleta ta ci gaba da cewa." Za ki iya magana ba ni da matsala ?awata ce tun na yarinta."

Lantana ba haka ta so ba amma tun da ta faWi haka gashi gulma na iban ta sai ta kwashe abin da ta gani,harma da ?ara magi da gishiri don ya yi za?i cakwai ta fara gaya mata.


Ba ta kai ga ?arshen labarin ba in da take tunanin zai fi Waga hankalinta.

Zainab ta mi?e kamar wata mahaukaciya ta kai mata raruma.
Wani irin sha?a ta kai mata cikin ihu ta zare idanunta kamar mahaukaciya.

" Ke baki da hankali mijina kike maganar kin gan shi da wata in ma da wata kika gan shi,bai kamata ki haWa shi da wata ?azamiya kucaka yar matsiyata ba."

Sai kawai ta rufeta da duka da mari take kai mata.

Lantana ta hau ihu da ?arfi ganin dukan da take mata ta ?ara sakin ?ara ganin ta wawuro wani gilas za ta maka mata.

" Don Allah ki taimake ni wallahi abin da na faWa miki gaskiya ne,ba zan shirya irin wannan ?aryar na gaya miki kawai don na Sata miki."

Ta faWa yayin da ta ruga ta Soye a bayan Nabila da ta mi?e cikin tashin hankali ganin za ta yi kisa.

" Zainab be patient kar fa kishi ya sa ki aikata dana sani,ya kamata ki yi ma maganarta kyakykyawar fahimta,ita ba ?aramar yarinya ba ce da za ta yi miki gulma don son ranta."

" Ke Nabila dakata wallahi yanzu za ki fita da fashashshen kai mundin kika yadda da abin da take faWi,mijina mai aji da kyau za ta haWa shi da mai aikina.Na yadda da A.m ba zai taSa kula wata ?a mace ba,don ban taSa ganin ya kula mata masu aji ba bare ita ?azama mara gata da aji."

Ta ce da ita tare da ?ara rarumar abu ta yo kanta da shi.

Nabila ba ta damu da abin da ta ce ba ta tunkare ta tana ?o?arin ?wace makamin da ta Wauka.

Da ?yar ta samu ta zauna tare da dafe kanta ta ce."Na yi ba?in cikin da ki na nan ta kawo min wannan ba?in labari,da bakya nan sai na nuna mata haukana."

Sai kuma ta kai mata sha?a da ?arfi saboda gani take kamar ta raina ta ne ta kawo mata wannnan labari.

Lantana idanunta suka kaWa suka yi jajur ta na ?a?ari saboda ta sha?e ta sosai,sai zaro idanu take ta na dana sanin gaya mata gashi za ta ba?unci lahira ba ta shirya ba.

Lantana ta sada?ar mutuwa za ta yi ta tabbata da ita kaWai ne da Zainab a gidan, sai ta kasheta dama haka take da kishi akan mijinta take barin shi ya na garari.

Da ?yar Nabila ta ?waci Lantana da take fitar da numfashi sama-sama.

Ta samu ta tura ta cikin Waki tare da rufe ta a Wakin ta dawo gurin Lantana da take murza wuyanta.

" Kin tabbata abin da kika gani gaskiya ne?"
" Wallahi da gaske ne Hajiya da idona na gansu."Ta faWa cikin kalar tausayi.

" Ok ga wannan ki ri?e na gode da kika gaya mana ki ci gaba da saka ido a kansu."

Lantana da ta ga an mi?a mata farare gal da su sai ta washe baki,ta karSe ta soke sannan ta kalle ta ta ce.

" Hajiya na gode dama tuntuni nake lura da ita yadda take mishi kallo kamar mayya,zan ci gaba da bibiyar su amma fa sai dai ki bani numbar ki ba zan gaya ma Hajiya Zainab ba kashe ni za ta yi."

Bayan ta gama da Lantana ta buWe Wakin ta shiga ta na zaune akan gado,ko kaWan ba ta nuna damuwarta akan maganar ba,saboda ta saka a ranta A.m ba zai taSa dubi ga wata ?a mace ba.

Nabila ta zauna a gefen ta suna fuskan tar juna.
Zainab na yi matu?ar mamakin irin yadda kika yadda da mijnki duk da ba ina zargin sa ba ne, amma Lantana ba za ta taSa gaya miki ?arya ba musamman in kika dube ta za ki ga alamun gaskiya a fuskarta,na tabbata a kwai ?amshin gaskiya a maganarta ko da kuwa ba haka maganar take ba.

Duk da cewa A.m mutumin kirki ne wanda bai damu da irin wannan rayuwar ba,ni kai na ba na tunanin zan iya tarayya da mai aiki duba ga yadda ya tsani duk wani talaka,amma ki tsaya ki yi karatun ta natsu ki saka ido domin namiji ba shi da tabbas!"

Zainab ta kalli Nabila a wuka?ance tare da mi?ewa ranta a Sace ta ce.

" Ba na son wula?anci Nabila mijina za ki din ga haWa shi da wata.A kwai yadda a tsakaninmu da shi,muddin kika ce za ki faWi wani abu na rashin kirki a garesa wallahi yanzu za mu raba jaha da ke."

Ta buWe baki za ta ?ara magana ta Waga mata hannu tare da nuna mata ?ofa."Ki fitar min daga gida na yanke duk wata ala?ar da ke tsa?aninmu."

Mi?ewa ta yi ta Wauki jakarta ta na kallonta.
" Bazan yi fushi da ke ba ?awata zan yi miki uzuri har zuwa lokacin da za ki gane gaskiya,ni na san dole wata rana za ki neme ni bayan kin gane cin amanarki yake yi."

Har ta fara taku bayan ta gama magana sai kuma ta dawo,ta tsaya gaban Zainab tare da ri?e hannunta ta na hawaye ta ci gaba da magana.

" Ba wai ina son na tona miki rayuwar aurena ba ne a'a sai don na gaya miki don ki Wauki darasi a ciki.Kamar yadda kika ba wa A.m amana haka na Wauki yaddata na Wora akan Al'amin,ba ni da haufi akan sa na yadda da shi fiye da yadda na yadda da kaina.Kwasam na kama shi da kwandom a aljihun sa wanda hakan ya Waga hankalina matu?ar gaske har sai da na kwanta jinya.Na yi kuka sosai rikici sosai muka yi sai daga baya na ha?ura bayan duk mutuncin sa ya zube a idanuna."

Fara tafiya ta yi bayan ta gama gaya mata ta na kuka.

Jikinta ya yi sanyi da sauri ta kama hannunta ta ri?e tare da faWawa jikinta ta fashe da kuka sosai.

"Don Allah Nabila karki saka zuciyata ta gasganta abin da kike faWa min domin zuciyata ba za ta iya jure ganin A.m da wata mace ba!Kin ji na rantse miki duk ranar da A.m ya yi gigin kallon wata ?a mace to ni ce ajalinmu baki Waya,nufin sa zai iya ganin Wansa a duniya bayan ni na lalata rayuwata saboda shi?"

Ta ce ta na kuka tamkar wata wacce aka yi wa mutuwa sai kuma ta janye jikinta tare da share fuska.
" Kai ina! Zuciyata kasa karSar zargin da kike masa A.m ya yi min al?awarin ba zai kula ko wace ?a mace ba kuma na yadda da shi,in kuwa zargin da kike masa ya zamo gaskiya wallahi sai na canza kamannin ko wace ya mace da ta haWa jiki da shi, ke bama Juwairiya wula?antacciya ba ko yar gidan uban waye acid zan wasa ma shegiya ta mutu kowa ya huta."
Cikin matsancin kuka take magana gabaki Waya hankalinta ya tashi,sosai duk da ta yi ?o?arin ta saka zargin da take ma A.m,amma in ta tuna ko kallon fuskarta ba ya yi bare ya ri?e sunanta sai ta ji sanyi ta kauda zarginta.

" Haba Zainab kamar ba ki waye ba ina bokon na ki yaje? Ai yanzu karki nuna komai ki nuna tamkar ba ki san da wannan maganar ba,sannan ki saka matakan tsaro ki sa ido sosai a tsakanin su duk wata hanya da zai saka ki fahimci ko da wani abu ki kula da ita sa..."

" Kai."

Zainab ta ce sannan ta kalle ta taci gaba da magana." Ta ya ya za'ai na kauda kishina na saka ido don in gano abin da suke yi,ba zan iya ba ni kawai zan tambaye shi ne in ya gaya mini ?ona su duka zan yi,in ya so duk abin da zai faru ya faru!" Ta furta cikin tashin hankali yayin da take ji sam ba za ta iya ba.

"Na san ba zai iya auren ?ar aiki ba,amma yanzu sun cika Wora kwaWayin su ba sa iya Wauke idanun su.
Ki Wan danne kishinki ki gano wani abu in har kika gane ya na tare da ita, ni zan siyo miki acid ki watsa mata,ko ki bani kwangilar watsa mata babu uban da zai Waure ni yar manya ce ni mijina kuma canal."

Da ?yar Nabila ta yi nasarar kwantar mata da hankali,duk da har yanzu ta kasa amincewa,don haka ta saka a ranta ya na dawowa za ta tambaye shi dole ya gaya mata komai.

A tare suka fito daga Wakin suka nufi kicin in da Lantana take aiki,ganinZainab da gudu ta ruga ta na faWin.

"Wallahi Hajiya na gan...."

Da sauri Zainab ta Wora Wan yatsa a bakinta kan ta yi shiru,don ta na jin kamar ta ?ara mata wani dukan.KuWi ta ?ara ma Lantana da take ta murna sosai ga duka ga samun kuWi ita kam yau gulma ta yi riba.


Zainab na zaune a gaban madubi ta na tsantsara kwallliya zuciyarta cunkushe da tunani kala-kala.

Ji ta yi an rungume ta ta baya sannan ya Wora kan sa a bayanta,ba ta juya ba kasancewar tun kafin ya shigo ?amshin turaren sa ya bayyanar masa da shigowar sa.

Fuskarta a Waure ta juyo ta kalle shi sama da ?asa haka kawai sai ta ji wani mugun haushin sa da tsanar haWa jiki da shi.

Sakar mata murmushi ya yi tare da kamo hannunta.

" Gibbiyar mata sarauniyar mata a cikin birnin zuciyar Abdurrahman mai na yi ake fushi da ni? Ko don rashin dawowata da wuri ne am so so sorry babyna wallahi wani uzuri ya tsare ni na kira wayarki ba ta shiga."

Ya faWa da muryar sa mai sanyi da take kwantar mata da hankali ya kuma san ya na sace zuciyarta da ita.

Ganin ta ?i kula shi sai ya kamata suka faWa gado ya na sha?an kamshin turarenta ya na faWin.

" Wane irin turare kika sa yau kamar yafi wanda kike shafawa daWi,don ban taSa jin ?amshi mai kwantar da zuciya da saka nishaWi a rai ba..

Gaskiya kuma kwalliyar ta yi na kuma yaba bari kiga in siye ta koma nawa ne babu tayi."

?o?arin warware tawul Win dake jikinta yake yi ya na gaya mata kalamai masu daWi da kwantar da hankali.

Da sauri ta ?wace jikinta ta harare shi ta saki tsaki ta saka kayanta ta fice daga Wakin ba tare da ta kalli in da yake ba.

Tsayawa ya yi yana kallonta ran sa ya Sace saboda ya tsani tsaki ita ma ta san haka,don haka bai ?ara kula ta ba ya tuSe kayan sa ya watsa ruwa,bai nemi abincin ba saboda sai da ya tsaya gidan A.k ya ci abinci tun da ya san Juwairiya ba ta nan gashi ya kasa iya cin abincin Lantana.


Kwanciyar sa ya yi ba tare da ya ?ara kula ta ba,wanda hakan ya sa ta fara yadda da abin da Lantana ta faWa mata,tun da har zai iya ?yaleta ganin ta yi fushi ba tare da ya rarrashe ta ba ko ya tambayi ba'asi.

Tun tana saka ran zai zo ya rarrrasheta amma sai ta ji shiru,ta kalli agogon hannunta ?arfe Waya na dare sai ta sauka a chert ta shige Wakin sa tare da buga ?ofar da ?arfin gaske.

Tsayawa ta yi a kan sa ta na huci kamar wata mesa ganin bacci yake yi,filo ta Wauka tare da maka masa ya buWe ido cikin razana ganin ta tsaye a kan sa sai ran sa ya Sace,ya kalle ta bai ce mata komai ba amma idanun sa suna masa kallon gargaWi.

" Kaga Malam ka tashi magana nake son mu yi da kai."Ta ce dashi tana girgiza ?ugu idanunta a bushe kamar ba dare ba.

" Zainab."

A cikin wata irin murya ya yi magana sannan ya Wora da ce wa." Don Allah bacci nake ji ki bari sai da safe."
Ya rungume filo tare da mirginawa ya ci gaba da bacci,komai ya tuna sai ya juyo ya na kallonta ya mi?o mata hannu yana nufin ta zo su kwanta.

Wani irin kallo ta watsa mishi." Ka ga Malam wallahi sai ka tashi ba za ka barni da ba?in ciki na kasa bacci ba don ba zan iya bari gari ya waye ba."

Sai ta fara tsiya ta na mishi wasu irin maganganu da ya kasa gane mai take ce wa,sannan kuma ta hana shi bacci da ga ?arshe dole ya tashi saboda magana take da murya mai ?arfi,kuma abin da take faWi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login