Showing 99001 words to 102000 words out of 143803 words

Chapter 34 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4722

ya Wora akan Zainab don ita ta bada ?ofa har ta shigo rayuwar su.

Maigadi ya wangale ?ofa da alamun wani zai fita daga cikin gidan don ko hon ba su yi ba,Daddy Zainab ya fito da shiri makullin mota ri?e a hannun sa zai fita,ganin su ya sa ya tsaya yana musu wani irin wula?antaccen kallo.

Ya rantse da ace A.m ba Wan amininsa ba ne yau kotu za ta raba su da shi,tun da har ya iya dukan masa ?a guda tsoka Waya a miya.

" Mara mutunci uban mai ya kawo ka gidana ko ka zo ka ?ara dukanta a gabana ne? Ashe dama ba ka da mutunci na Wauki abu mafi soyuwa na ba ka?"

Masifa yake musu bai bari sun shiga daga ciki ba ya shiga zagin su har da A.k da ya yi rakiyan,sai da ya samu na shi kason saboda mahaifin Zainab ya yi fushi,bakinsa har kumfa yake saboda an bugi shalele.

A.k ha?uri yake badawa har da du?awa ya kuma janyo hannun A.m,don ya du?a da ya yi ?ikam ya na tsaye,zuciyar sa na tafarfasa jin rashin mutuncin da yake musu,a gaban ?an aikin gidan.

Da ?yar ya basu izinin shiga cikin falon ba?i suka zauna kusan awa babu wanda ya bi ta kan su.

Tsalam mahaifiyar Zainab ta shigo cikin falon tana kallon A.m a wula?ance.

" Sannu isashshe da za ka kama min ?ata da duka,an ce maka jaka na aura maka? Na rantse Zainab ba za ta dawo gidan ka ba,tun da ba ka da mutunci.
Mai take amfana da shi da auren ka sai tsiya da ha?uri na rashin haihuwa da ba ka yi,shine saboda kai mara mutunci ne za ka kama min ita da duka akan wata banza ?ar aiki,to wallahi ba ka isa ba don ba za ta dawo gidan ka ba.
Shekarar ku nawa da aure ko Satan wata ba ta taSa yi ba,dole ka sakin mini ?ata ko kutu ta raba mu."Ta faWi tana harare-harare.

Duk irin rarrashin da A.k ya yi musu amma sun kafe kan ba za ta koma gidan sa ba,sai nanata maganar ha?urin da take yi saboda rashi haihuwar da baya yi.

Cikin fushi A.m ya mi?e yayin da idanun sa suka kaWa suka yi jajur.
Ya buWe baki zai yi magana da sauri A.m ya kama shi suka fice waje.Hannun sa ya ja zuwa mota ba tare da ya ce komai ba,ya shiga motar suka fara tafiya.Ganin yadda yake huci sai ya kunna ?ira'ar alkur'ani.

Suna tafe babu wanda ya yi magana sai zuwa can A.k ya kalli A.m ya ci gaba da tu?i.Jingina kan shi da kujera tare da lumshe idanun sa.

A lokacin da A.k ya shigo cikin falon A.m ri?e baki ya yi cikin tashin hankali yana kallon yadda falon ya hargitse babu mamora a falon

" TaS sai ka tanadar mata wasu ka ije saboda duk ranar da ta san da igiyar auren ka da Juwairiya,wallahi in babu kayan da za ta fasa sai dai wani Abdurrahman ba kai ba,lallai Zainab na da zafin kishi."Ya faWa cikin tsigar mamaki da tsokana.

A.m da ran sa a Sace ya kalle sa da takaici ya ce." Fata ma kake min ko so kake na rasa wani shashin na jikina,ni kaina yau na ?ara tsorata da lamarin ta,dole na Wauki mataki kafin ta san da wannan zancan in dai ba so kake na koma tafiya da ?afa Waya ba."

Dariya A.k ya yi sosai ya ce." Wannan ya rage naka ni dai babu ruwana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka,kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho."

A.m ya matsa kusa da shi ya gallah masa harara."Ni ba wannan ba yanzu ya zamu yi da waWannan marasa mutuncin gaskiya bazan iya zama ni kaWai a cikin gidan nan ba,ni da nake da zu?a zu?an ?an mata biyu yanzu na koma babu ko Waya.Gashi yaunwa make ji wunin yau ko ruwa ban saka a bakina,saboda matsalar da damuwata ta saka ni."

" Ya rage naka sai ka san in da zaka je kaci abinci amma ba'a gidana ba,don matata ba kukun ka ba ne,ko da ka ga ada ina baka abinci saboda babu wanda zai baka ne,amma yanzu tun da a kwai Juwairiya sai ka je ka yi biko."Tsaki ya saki take fuskar sa ta canza.

" Na rantse har yanzu ina kan bakana sai na hukunta ta za ta san da wane irin namiji take zama,da na je na kirata gara na kwana banci abinci ba."Ya ce da A.k da ya Wauki makullin motar sa.

" Ok fine ya rage naka da na yi tunanin za ka yi bikon matar wucin gadi,ka huta kafin matar so ta dawo,saboda iyayenta sun yi fushi sosai kuma dole sai ka danne zuciyar ka akan duk abin da iyayenta za su yi maka,?ar su kake aure kuma kai ka dakar musu ?a."

" Na ji don Alkah ka tafi babu abin da kake yi sai ?ara tafarfasa min zuciya,da na so na gaya ma mahaifiyarta magana amma kuma na gode da ka hana ni da na yi katoSara."

" Ok bari na tafi tun da ba za ka dawo da matar wucin gadi ba,sai ka ci gaba da cin abincin Lantana,sannan kar ka yi gigin zuwan min gida mai mata biyu ya zama gwauro."

Ya ce yayin da A.m ya fito don ya raka shi ba tare da ya bashi amsar sha?iyancin da yake mishi ba.

Ya shiga cikin mota ya zauna tare da ri?e sitiyarin ya kalli A.m da yake ri?e da murfin motar yana jiran ya shiga,ya rufe mishi ?ofar motan.

" Ya kamata ka yi tunani A.m lokaci yana wucewa lamura canzawa,suke yi ka sanar da iyayen Zainab komai ka bayyana Juwairiya a matsayin matar k,tun kafin lamura su kwaSe maka.Na tabbata da kai ne ba ka haihuwa Zainab ba za ta zauna da kai ba."

Rufe mishi motar ya yi ganin ya shigar da ?afafunsa ciki,saboda fahimta da ya yi maganar da yake masa ba ta tasiri a zuciyar sa.

" Na riga na yi wa Zainab al?awari ina sonta ba zan iya haWata da wata ?a mace ba.Na san cewa Juwairiya na sona sai dai ba ta san irin namijin da ya kamata ta so ba,duba ga ni ba ajin aurenta ba ne kuma babban goro ai sai magogin ?arfe!Don haka ina kan baka na."

A.k ya ja motar sa ya fice ba tare da ya ?ara ce masa komai ba.

Zainab zaune a Waki ita da ?awarta Nabila suna hira,wacce ta yi takakkiya ta taho Zariya tun daga Abuja,saboda kiranta da ta yi tana kuka ta gaya mata abin da ya faru.

Nabila da ta gaji ta Wauko gajiyar hanya tana zaune akan gadon Zainab abinci take ci.

Wayar Zainab ta yi ?ara kusan sau goma na kiran ta,amma sai ta?i Waga wayar daga ?arshe kashe wayar ta yi ta wurgata can gefe a fili ta furta.
" Maye kawai mazinaci."

Ko da ba ta gaya mata ba ta san wanda yake kiranta.

" Yanzu kin tabbata abin da na ke gaya miki ko kin yadda namiji buhun ?aya ne? Wai ki gaya min ta ya akai kika gane suna cin amanarki?"

Zainab ta saki tsaki ta kalle ta da Sacin rai ta ce." Ni ba wannan ba ina acid Win da nace ki taho min da shi?"

" Karki damu tsa?on ki yana ije a jakata amma don Allah ki gaya mini,ya akai kika gane bayan duk kin Wana musu tarko sun tsallake?"

"Wani magani na tsinta a cikin drower ta A.m ya na sha na Waukar ciki da wuri."

Ta ce cikin damuwa yayin da idanunta suka kawo ruwa.

" In yana shan maganin haihuwa to meye hujjarki ko kina tunanin,A.m zai so ya haifi Wansa ta zina bayan ga matar sa ta sunna?Sannan ni ban ga abin da kika faWa a matsayin shedar suna cin amanar ki ba."

Ta faWa da tana kallon Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta manta cewar,ba ta taSa gaya ma kowa ba cewar ita ce ba ta haihuwa,sai ta shiga in da in da daga ?arshe hannunta ta kama tare da fashewa da kuka cikin kuka ta ce

" Yau zan gaya miki wani sirri amma don Allah ko sauran ?awayen, ba na son ki gaya musu cewar na gaya miki ni ce bana haihuwa ba A.m ba,domin ya yi min al?awarin ba zai faWa wa kowa ba kuma ba zai ?ara aure ba."

Gwalalo idanu ta yi cikin mamaki jin abin da ta faWi da gaske ita ce ba ta haihuwa ba A.m ba.

Sai tsananin mamaki ya kamata ta shiga kaWa kai kamar wata ?adangaruwa zuwa can ta nisa ta ce." Har yanzu wannan ba hujja ba ce Zainab saboda wata?ila A.m ya na shan ?wayoyin ne don yana tunanin ?ila ?wayoyin Zai taimaka miki."

"Haba akan me za ki ce haka bayan na gaya miki cewar mahaifata aka yi min aiki aka cire.Kuma idan haka ne mai yasa ka bai gaya min ba"Ta faWa cikin ?osawa jin bin da ta ce.

" Wannan ma ba hujja ba ce har yanzu ba ki da hujja Zainab.Kina abu kamar ba likita ba bayan kin manta mahaifa takan ti?o a jikin mace ko da an cire ta,mata nawa ne suka haihu bayan a n cire musu mahaifa?.Musamman ke da baki taSa haihuwa ba."

" Wayyo Allah kin sani a ruWu in kin ce duk wannan ba hujja ba ce,to numbar A.m da na gani a wayarta shi kuma mene ne?"Ta ce da ita tana kuka sosai.
" Ba zan Sata bakina gurin faWa miki irin son da nake masa ba.Na ro?e ki kamar yadda kika yi min al?awarin za ki watsa mata acid ki taimake ni ki yi yadda muka shirya,ga bayanin in da take gidan kawunta wanda na samu labarin mahaifiyarta ta Sata."

"Ok tun da haka kike so zan yi amma na so a ce mun Wan ?ara lokaci,mu samu ?wararan sheda, yau Win nan zan cika aikin ki na koma Abuja bari na gama cin abincin.Ni?abi zan saka na watsa ma shegiya ki huta.

BARI NA YI NAN DON YAU BANI DA TACE WA LAMARIN YAFI ?ARFINA.


KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 28*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Zainab dake shatatan hawaye ta karSi acid Win da ta mi?a mata,tana jin wani irin tsanar Juwairiya a ranta kamar ta je ta watsa mata da kanta.

Ganin Momy suka yi ta shigo tana murmushi a fuskarata ta zauna a gefen su.

" Humh ta yaro kyau take yi ba ta ?arko."


Ta ce tare da dafa kafaWar Zainab da har yanzu take Wigar hawaye,saboda gani take kamar a mafarki yake faruwa,ba ta taSa tunanin fuskantar haka da ga gare shi ba.

Ajiyar zuciya mai ?arfi ta saka tare da rungume Momy sai ta ?ara fashewa da kuka.

" Momy har yau na kasa yadda cewa A.m zai iya kula wata mace bayan ni,mace mara aji wanda ba ta da daraja a duniya duk cewar zargi nake yi amma in na tuna,sai na ji kamar na sha?e kaina na mutu."

Cikin kuka ta faWa da shagwaba gaba ki Waya ta haye jikin Momy tana shagwaba,sannan ta Wora da cewa.
" Ke sheda ce irin wahalar da na sha kafin ya amince da soyayyata! Yanzu sai wata aba wacce ban Wauke ta da ?ima ba ta shiga tsakanimu.Abin da ya yi min na ji na ha?ura da shi amma fa babu macen da za ta raSe shi,face na zama ajalin ta."

"Na sani ba sai kin Sata bakinki ba amm ni bana goyon baya akan acid Win da zaku watsa mata,saboda in har da gaske yake son ta zai iya yin komai don ta samu lafiya daga ?arshe kin ga ke kika rasa,amma da za ki bar komai a hannuna da sannu za ta gane kuskuren shigowa rayuwarki da ta yi sa..."

" Momy yanzu kina nufin na fasa watsa mata acid Win?"
Ta katse ta da tambaya tana magana da muryar kuka.

" Abin da nake so kenan in har zai yiwu kar ki manta ke ce ?ata Waya tilo da na mallaka, ta ya ya za ai na bar rayuwarki ta ?untata ki bar min komai a hannuna,mijinki kuwa sai ya gane bashi da hankali don wahalar da shi za muyi ki ?yale shi,zai gane ba irin ki ake wula?anta wa ba."

" Ai ni da nace ba zan kona gidan sa ba kawai ya sakeni na ha?ura da shi."Ta ce cikin shagwaba tare da ri?e hannunta.

" Ba ki da hankali mijinki za ki bar ma wata banza ?ar aiki? Ashe kishinki na banza ne tun da har za ki hau dokin zuciya ki kyale ma wata mijinki."


" Wannan karon Nabila ce ta karSe maganar da cewa." Momy ya kamata ta fahimci waye mijinta sannan kin san Zainab da ba?in kishi,ni har yanzu na kasa gane gaskiyar lamarin dake faruwa,amma ya kamata ta gwara A.m ta nisan ta kanta da shi har sai ya gane kuransa.

Zainab cikin zumSura baki ta ce." Ki bar shi da ni yake yi ba Anty Safna za ta tafi ingila ita da mijinta ba,bin ta zan yi na huta acan ba zan dawo ba sai na huta."

Nabila da mamaki ta kalle ta ta ce." Ki bar shi da ?ar aikin na ki Zey?"

" A''a na san cewa tun ranar da abin ya faru zai kore ta, so nake na gwara shi kin san yana masifar sona dole hankalin sa ya tashi."

Dariya ta yi ta ce." Haka ne ai bai kyauta ba amma yanzu Momy zuwana bai da amfani an fasa watsa mata acid Win?"

" ?warai kuwa Nabila ku bar min komai a hannuna ita Zainab ta fita waje ta huta kafin muga abin da zai faru."

Haka kuwa aka yi washegari Nabila ta koma Abuja.

A ranar da su A.m suka yi nasara Zainab ta fito musu sun ga rashin mutunci,don tun A k na saka baki yana ba ta ha?uri ta dawo,har ya gaji ya koma gefe yana kallon A.m da ya yi kalar tausayi,kamar zai yi kuka yana ro?onta.

Cikin muryar sanyi ya ce." Ki fahimce ni tun lokacin da muka je ?asar waje aka yi miki aiki,na tambayi likita ya ba ni wannan maganin tunanina ko za ki iya haihuwa."

Kallon mayaudari ta yi masa ba tare da ta tanka masa ba,domin gani take ya ci uwar rainin wayo.

" Allah ki yadda da ni don Allah ki dawo Wakina zuciya da gangar jiki sun yi kewarki."
Ya faWa a raunane kamar zai yi kuka tare da kama hannunta.

Fisge hannunta ta yi ta harare shi tare da yatsina fuska." Ai ka gama tsarani wallahi gara ma ka fita harkata,domin zuwa gobe in sha Allahu na bar ?asar nan ba zan dawo ba saina huta iya son raina."Ta ce da shi tana kallon sa a yatsine

Wannan karon murya a Wage ya fara magana." Kar ki sake ki fita wata ?asa don ba da izinina ba,kuma in kika sake kika je Allah saina Sata miki rai"

" Ai kin banza kawai a suwa ai ni yanzu duk abin da ka zaSa a aurenmu daidai ne in ba rabuwa za mu yi na fi son haka,da na zauna da fasi?i wanda ba shi da aji ya rasa macen da zai kula sai ?ar aiki.."

" Ya ishe ki Zainab sau nawa zan gaya miki babu wani abu da ya shiga tsa?aninmu da ita kin ?i bani dama na yi miki bayani,ban taSa kallonta da nufin wani abu ba don ni ban ga abin da zan nema ajikinta ba,kar ki manta yawo take a cikin hijabi kamar wata ?onanniya.Yarinyar da ba ta da waye wa mai zan yi da ita...."

Zainab tsaki ta yi ta wuce kawai gani zai tsarata ya bita kamar zai shige cikin Wakin ya na faWin." Na gaya miki kar ki bar ?asar nan ba tare da izinina ba."

Garam ta kulle ?ofar saura kaWan ta haWa da hannun shi da ya kai da nufin ya kamo ta ganin za ta shige.

Bango ya kaima duka tare da kama kan sa ya ri?e.
A.k da ke zaune hankalin sa na kan waya amma a zahirin gaskiya yana jin bada?alar da suke yi ne,mamakin aminin na sa yake yi saboda ya saki da yawa Zainab ta raina shi sama ba ta ganin darajar shi balle ta girmama auren su.

Ganin ya nufi hanyar fita ya mi?e cikin ?osawa shi kansa ya gaji da zuwa biko,yana ji a ran sa ba zai ?ara rako shi ba don ya gaji da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login