Showing 93001 words to 96000 words out of 143803 words

Chapter 32 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4751

da take ciki ba ya ce." Ki kwantar da hankalin ki ni kaina na yi al?warin saina raba auren ku,in har na bu?aci kuWi bai ba ni ba,wallahi saina tona asiri komai ya wargatse saboda na tsani ganin ki a cikin wannan daular,in kuma baya haihuwa ne sai ya sake ki don ba za ki zauna da shi ba."

Ba ta ce masa uffan ba har ya gama magana ya fice.

Juwairiya sai ta ji ba za ta iya zama a cikin gidan ba,domin duhun da ya yi mata yafi duhun ?abari.

Ta yi kuka har ta ba uku lada tana ji wani irin kunyar Mama matu?a tun kafin ta haWa ido da ita.Take nadama ta shige ta har ta fara tunanin ba za ta taSa yadda ta ?ara haWa ido da Mama ba,matu?ar A.m bai aminta da ita ba a matsayin matar sa,wacce zai yi rayuwa da ita na har a bada.

Duk kiran da yake mata ?in Wagawa ta yi tana cikin haWa kayanta,sai ta ji hucin mutum a bayanta,wanda ta gane A.m ne domin in dai ya zo guri turaren sa yake fara bayyana kan sa.

Kuka ta saka masa sosai tana dukan sa a?irjin sa,ba tare da ya hana ta ba ya ?yaleta don ya san dole ta yi,ita da take da hawayen banza ba'a taSa ta ba ta yi kuka ina ga an rabata da Mama.

Ganin tana ta dukan sa amma ya ?i ko motsi sai ta ?ara fashewa da kuka tare da faWawa jikin sa.

" Mai ya sa zaka rabani da Mama anya ka yi min adalci kuwa,da wane ido kake son na kalle ta?Bayan ta san cewa na yi aure ba tare da sanin ta ba! Ni na san Mama ba za ta taSa yafe mini ba,domin ita ba irin Baba Sani ba ne."

?ara rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya na jin gangar jikinsa ya yi kewarta matu?a.

" Ki gane ba ni da nufin na cutar da ita sai dai na yi hakanne don kar ta hanani samun farin cikina.Ina cikin damuwa sosai aurenki da na yi na yi ne don na samu cikon burina,amma kullum damuwa yake ?ara min ga Baba Sani da ya maida ni bankin sa, ga Mama sannan Zainab ta fara zargina dake jiya na shiga tashin hankali domin a kwai wanda yake bibiyarmu.Anya Juwairiya ke alkhairi ce a gareni?"

Ya faWa yayin da idanuwansa suka canza launi saboda tsananin damuwar da yake ciki.

Da sauri ta janye jikinta gare shi tana jin wani iri zafi sosai jin abin da ya faWa.

" Wayyo Allah na! Na ro?e ka ka cire min son sa a cikin zuciyata mutumin da nake so fiye da rayuwata,yake ganin ni ba alkhairi ba ce a rayuwarsa."

Ta faWa a fili sai hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Tasowa ya yi zai ri?e ta ya buWe baki ya ce." Sam b......"

" Don Allah ka fita daga gidan nan ba na son ganin ka! Ka fita kafin kasa zuciyata ta buga."Ta katse shi tana nuna masa hanyar fita.

Cikin zafi ya kalle ta." Ok na ji zan fita amma ki gaggauta dawowa gidana domin ki haifa min babyna mu rabu tun kafin Zainab ta fahimci komai,sannan Zainab ta sha alwashin cusgunawa rayuwarki domin ta gano gaskiyar lamarin dake tsakaninmu,don haka ki shirya duk wani cin kashi da za ki gani a gidan,sannan ba zan yi koma baya ga lamarin ba domin mu samu mu fita daga zarginta."

Sai Juwairiya ta fara kallon sa kamar wani mahaukaci yayin da take ji tabbas A.m ba ya sonta kamar yadda ya sha faWa mata.

Wani irin ba?in ciki ya tokareta wanda y saka ta ji a ranta za ta iya bijire musu duka tare da tona asirin komai,don a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya Waukar cin kashin da Zainab za ta yi mata ba.

Tabbas za ta tona komai ta fito ta nuna ma duniya ita ma matar shi ce,in yaso sai sama da ?asa ta haWe,haka kawai ya din ga ?wallo da rayuwarta don kawai ya ga tana son sa.

Ri?e rigar A.m da ya juya zai fita ganin ta ?i cewa komai da nufin ta gaya masa ba?a?en maganganu,amma yayin da ya zuba mata idanun sa masu kama da an zuba zaiba a ciki,sai ta ji wata irin narkakkiyar dalma na son sa ya zagaye duk ilahirin jikinta,kuma ba ta taSa ganin Mama ta yi sa in sa da mahaifinta ba.

Juwa ta yi da sauri ta yi ta shige Waki tare da sakin kuka mai ?arfi.

A.m ya daWe a ?ofar gidan ya du?ar da kansa a kan sitiyarin motar sa,sosai ya jima a gurin ya na jin damuwa a ran sa.

Wayar sa ya zaro ya nemo numbar ta da ya yi saving da suna damuwata,domin haka yake kiran ta tun da ta shigo cikin rayuwar sa ta saka mi shi damuwa.

Da ya yi nufin ya kirata akan su tafi sai kuma ya tuna bai san wanda yake musu shishshigi ba,da sauri ya figi motar sa a guje ya bar ?ofar gidan,a ran sa ya na addu'ar Allah ya sa ta dawo yau saboda ya yi missing Win girta.

A ranar ta shirya ta koma gidan A.m saboda gidan ya yi mata babu daWi.

Suna zaune a falo Zainab ta kwanta gaba ki Waya a jikin shi tana zuba mishi shagwaba,yayin da shi kuma sai biye mata yake yana ?ara saka ta cikin lambun son sa.

Hankalin sa na kan ?ofa ganin yamma ta yi ba ta shigo ba,wayar sa ya zaro ya ?ara tura mata da tsa?on da ya tura yafi sau ba adadi kamar haka.

"Aslm mai kike yi har yanzu ba ki dawo ba,na gaya miki kar ki ?ara mintuna a gidan na maza ki dawo.Da fatan za ki bi umurnina a matsayina na mijin ki n wucin gadi."

Tun da ta ?aranta sau Waya ba ta ?ara gigin ?ara karanta wa ba,duk da tsa?on yana shigowa duk bayan mintuna.


Da siririyar sallama ta shigo wanda idanun A.m yana kallon ?ofar shigowa.Karab suka haWa ido ya yi sauri ya Wauke kan sa,sai ya Wan ture jikin Zainab ya mi?e da sauri zai haye sama.

Zainab da sauri ta kalli bakin ?ofa ta kuma mai da idanunta kan A.m da ya mi?e yana danna waya zai haye sama.

" Honey ina za ka je."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Ba shopping kika ce zan kai ki ba?Ina son na watsa ruwa zafi nake ji."Ya faWa ba tare da ya kalle ya ba.

Hannun sa ta kama ta ri?e tana sakin mi shi lallausar murmushi. Tare nake son mu yi jirani just one minute."

Ta juya kan Juwairiya dake tsaye kamar sanda tana kallon su."Sannu mara mutunci Mamar ta ki mutuwa ta yi da kika je kika zauna?"

Juwairiya da take jin gabaki Waya ranta babu daWi ,ba ta tanka mata ba sai ajiyar zuciya da ta sauke,na alamun wacce ta ci kuka ta ?oshi.

" Ke ni za ki kawo wa rashin mutunci banza yar matsiyata ki kula in kika ce hauka za ki yi mini,wallahi sai in kashe ki in kashe banza,na ga uban da zai tsaya miki.Ai ni duk wanda ya shiga gonata saina raba sa da rayuwarsa,kuma mu zuba mu gani shege ka fasa."

Ka sa ce mata komai ta yi ta saci kallon A.m da ya jingina jikinsa da kujerar dinning har yanzu,danne-danne yake a wayarsa ba tare ya tanka ko kallon Waya daga cikin su ba.

" Ni fa zafi nake ji so zan shiga ciki sai kin shigo."Ya faWa babu ko Wigon damuwa a ran sa.

" Yarinyar nan ta ba ni haushi fa tana sane da kuWi nake biyan ta,amma ta je gida ta zauna Allah saina cire kuWina don ba zan yi asara ba."Ta ce tana kallon A.m ko zai ce wani abu.

Watsa mata mugun kallo ya yi tare da jan tsuka." Duk abin da za ki yi mata ki ba ?ar aikin ki ba ce,ina ruwana wannan ya rage naki."
Yana gama faWin haka ya haye matakalan bene ba tare da ya kalle ta ba.

" Ki yi ha?uri jikin ta ne ya yi tsanani har sai da muka kwanta asibiti k..."

"Rufe min baki shashasha." Ta katse ta cikin tsawa.

" Da ga yau duk wani aikin gida ya koma kan ki Lantana ba za ta ?ara komai a gidan nan ba,maza ki wuce underwears Wina sun yi datti ki haWa da na A.m ki wanke.Ta faWa tare da kama kunninta sai kuma ta saki ta haye sama.

Tun daga wannan ranar take wahalar da ita duk wani aikin gidan ita take yi,dalilin haka ko makaranta ba ta zuwa wani lokaci,domin ?awayen ta take kwasowa ta saka ta girki,har in za su tafi ta ba su abincin ba sai sun yi girki ba.

Wani lokacin sai ta kira ?awarta ta ce ga za ta turo Juwairiya ta yi kwana biyu ta taya ta aiki.Ga zagi da cin mutunci komai aka yi ita ce.

Juwairiya ta yi shiru ne sakamakon tsorata ta da A.m ya yi kan in ta yi gigin tona asiri,zai cutar da Mama sannan ba zai gaya mata in da take ba.Hakan ya sa take jure duk wani cin kashi da take mata.

Kusan tsawon lokaci ta yi tana saka ido a tsakanin su haka Lantana ko tari ta yi idanunta na kanta.

A.m ya kauda duk wani abu da na zargi da shiga tsakanin su,har faWa yake ma Juwairiya kamar bai santa ba,kuma kullum cikin sata aiki yake in dai yana gida.

Duk wani saka ido ta yi ta gaji daga bisani ta ci gaba da harkokinta dama ta san A.m ba zai taSa iya kalon ta ba,balle yanzu da duk ta zube ta lalace saboda wahalar aiki da ?uncin son maso wani da take yi,sai hanci da ta yi gashi kullum sai ta yi mafarkin Mama da Ibrahim.

Tafiya ta kama Zainab ba tare da wani shakku ba ta bar ?asar bayan ta saka Lantana,ta din ga kwana a gidan har ta dawo hakan bai wani WaWa A.m da ?asa ba ya amince.

Cikin dare bayan sun yi bacci A.m yake sha?a mata Lantana maganin bacci,wanda in ta kwanta sai safiya take farkawa.
Sai safiya ta yi ta din ga ?orafi tana mamakin baccin da take yi ita dai Juwairiya dariya take mata sosai.
Juwairiya ta gasganta A.m ?arshe ne gurin wayo da basira,ita kanta mamakin sa take ga wayo da iya kalami ga mace wanda hakn yake sa ta mutu ?aunar sa.


Zaune suke a cikin makaranta ita da Hauwa Juwairiya ce ta siyo su agwaluma da yalon Bello,tana ta ci tana lumshe idanun ta domin su take son ta ci.

Hauwa ta kalle ta ganin yadda take ci kamar wata mayunwaciya.
Ganin yadda ta kafe ta da ido sai ta Salli agwalumar ta cige baki,saboda tsami amma haka take son sha.

" Humh ke ma ka yi mamaki kamar wata mayya haka na tashi ina son na sha agwaluma,bayan ni ba mutuniyata bace saboda tsaminta."Ta ?ara Salla tare da lumshe idanunta saboda daWi.

Dariya Hauwa ta saki ta ce."Anya lafiyarki ?alau kuwa ko dai ciki kika samu?Ni fa ina ganin kamar ciki ne da ke?"

Da sauri ta mi?e tare da yar da agwalumar cikin tashin hankali ta zare ido ta ce."Na shiga uku ciki fa da kika ce gaske ne?"

" Ina zan sani tunanin haka nake gani a jikinki yau kuma kin zo da ba?on lamari abin da ban taSa ganin kin sha ba kike sha.To ke ya kamata ki gane yaushe rabon ki da yin Satan wata?"

Ta tambaye ta ganin yadda ta diririce har hawaye sun fara sintiri a fuskarta.

" Umh umh wallahi na manta tashin hankali ba zai barni na tuna ba,amma ina ganin kamar tun ina gidan Mama wayyo Allah na bani!"

"Mene ne na banuwa Juwairiya fata za ki yi Allah ya sa wannan cikin ya dasa so tsakanin ki da mahaifinsa."
" Tab!Ai wallahi in Zainab za ta iya haihuwa to ni ma zan bar wannan cikin a jikina zubar da shi zan yi ko da zan rasa rayuwata ne,nufin ki na fara irga watannin rabuwa da A.m na koma gurin Mama? Ba zan iya ba domin ban san da wani idon zan iya kallon ta ba."Ta ce cikin kuka.

" Haba wai ke mai yasa ba ?ya fahimtar magana da Waukar shawara ne! Ki bar cikin jikin ki na tabbata shine makamin da zai jawo kusanci tsakanin sa da mahaifin sa."

Hauwa ta faWa cikin zafi domin zuwa yanzu ta fara ba ta haushi ganin ta cika kafiya da taurin kai.

" Na lura ba kya sona so kawai kike na rabu da farin cikina.To sai na zubar da cikin nan kuma babu wanda ya isa ya hana."

A zafafe ta furta cikin Sacin rai tana gani n kamar ba ta son zaman ta da A.m.

" Ni ban ce ba ina ba?in cikin yadda kika Wauki so kika ba ma namiji wai shin shine kaWai namiji a duniya,na tabbata ko rabuwa kuka yi za ki samu namiji mai kyau ki aura,ke ma ki na da kyau."

Mi?ewa ta yi tare da Waukar takaddun ta."In har za ki taimakamin na zubar ki zo ki raka ni asibiti,in kuma ba za ki ba ai na san hanya."

Ta nufi hanyar fita da sauri Hauwa ta biyo bayan ta duk da ba ta farin ciki da zubda cikin amma babu yadda za ta yi.

Likita ya kalle ta cikin mamaki sam ba ta yi kama da mutuniyar banza ba,amma mai ya sa take son ta zubda ciki? Da kuma ya tuna mugu ba shi da kama.

" Don Allah likita ka taimaka ka zubda cikin nan ko nawa ne za mu baka."

Juwairiya ta faWa jikinta na rawa ta kwaso duk kuWin da ke jakanta ta ije a teburin sa.

Duk tsoron da take ji na allura haka ta bari ya zumbuWa mata tana cige baki,sannan ya Wauko wani magani ya ba ta kan in ta ji ciwo ta sha guda biyu.

Tun kafin ta dawo gida take jin wani irin jiri kamar za ta faWi! Ko da ta dawo gida kwantawa ta yi saboda ciwon da mararta take yi,yayin da ciwon yake ci gaba kamar ana tsira mata allura.

A haka ta kwana kamar za ta ba?unci lahira, duk yadda ta so ta Wauki waya ta kira Hauwa ta gaya mata za ta mutu,saboda Zainab na nan A.m ko kallonta ba zai yi ba,amma ta kasa saboda ciwon mutuwa da take ji.

Washegari ko Waga Wan yatsarta ba ta iya wa sunan Allah kawai take faWi a bakinta da yake motsawa,tana kukan rabuwa da Mama ba tare da sun yi bankwana ba.

Jinin dake zuba kamar an buWe famfo ya sa ta gane mutuwa za ta yi,sai ta fara maimaita kalmar shahada numfashinta na Waukewa.

Zainab da duku-duku ta fice asibiti saboda a kwai wani bawon Allah da za ta yi mata aiki da misalin biyar da rabi na safe,tun jiya aka so ayi aikin sai dai an kawo shi ta riga tabar asibitin,kuma ?a'ida ne in har ta koma gida ba ta dawowa.
A.m dake zaune a falo ya na kallon news mamaki ya kama shi ganin har wannan lokacin ba ta fito ba ta Waura abin karya.

Mi?ewa ya yi tare da saka takalmi ya nufi Wakinta.

Halin da ya ganta ya yi masifar Waga mishi hankali,ba tare da wani tunani ba ya taitayeta ya saka a mota ya nufi asibiti da ita.

Da ?yar aka samu aka tsaida jinin bayan cikin ya fita.Hankalin A.m ya tashi gani yake kamar mutuwa za ta yi wani irin tausayin ta ya kama shi,ya na jin bai yi mata adalci zai barta ta mutu a Waki.

Zura mata ido ya yi cikin tausayi ya na shafa kanta.Da sauri ya kamata ya ri?e tare da tallabota ganin ta buWe ido.

Juwairiya zuciyarta ta buga ganin likita ya shigo ri?e da fayal a hannun sa,tsananin tsoro ya cika mata zuciya don ta san yau a sirinta zai tonu.

A hankali A.m ya maida hankalin shi kan likitan da ya mi?a masa fayal,ya ba masa bayani da harshen turanci duk da cewar Bahaushe ne shi.

" Ina baka ha?uri na zubewar baby don madam ta yi Sari ne,har sai da muka yi mata wankin ciki.Ga waWannan maganin za ka siya an sallame ta."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ri?e likitan ya yi tare da jijjiga shi." Mai ya sa ka bari cikina ya zuba ka san shekara nawa na yi ina son na haihu?Wallahi sai kun dawo min da cikina don ba zai yiwu ba!"

A.m ya faWa ya na naWe hannun riga zai yi dabbe gani yake kamar gazawar su ya sa cikin ya fita.

" Am sorry wallahi bamu da hannu a cikin zubewar cikin na nan! Amma na yi mamakin yadda kake son kaga ka haihu matar ka ta iya zubda cikin dake jikinta,don bincike ya nuna mana magani tasha mai ?arfi har cikin ya fita."

Sai A.m ya kalle shi kamar mahaukaci ko bai fahimci mai yake nufi ba,ya kuma juya ya kalli Juwairiya wacce ta bayyana gaskiyar zargin da yake mata,saboda yadda ta yi tsuru-tsuru na rashin gaskiya.Wani irin sha?a ya kai mata cikin tashin hankali.

Zainab da ke tafe a cikin motar ta tana tu?i cikin tsananin nishaWi,sakamakon ta yi aiki cikin nasara wanda hakan yake saka ta tsananin farin ciki a duk lokacin da ta yi aiki.
Wayarta ta Wauka ta kira layin A.m amma har ta yi masa kira biyar bai Wauka ba.
Ko da ta iso haka kawai sai ta ji gabanta ya faWi.

Maigadi ya wangame mata get ta shiga ta yi parking da sauri ta shige ciki,saboda yunwa take ji matu?a.Da fari ta so ta fara cin abinci amma sai ta ga rashin dacewar hakan ta shige wanka.

Bayan ta fito tana Wan dube-dube a cikin dirowar gadonta sai ta ga wani magani an Soye shi a cikin dirowar.

Da sauri ta buWe gabanta ne ya buga dam! Sa'ilin da ta ga sunan dake manne a kwalin maganin.

" Maganin Waukar ciki da wuri."Ta maimaita sunan maganin da Hausa.
" Me A.m yake yi da shi bayan ni ba na haihuwa?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ba ta da amsarta.
Wayarsa ta gani duka uku a gida bai Wauki ko Waya ba sannan ba shi a gidan.
Juwairiya sunan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login