Showing 102001 words to 105000 words out of 143803 words

Chapter 35 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4733

ruwan rashin mutuncin da yake kwankwaWa daga gurin Zainab da iyayenta.

A mota suna tafiya shiru A.m ya yi ?uta ya kalli A.k da hankalin sa ya na kan tu?i ya ce." Ka na jin wannan yar rainin wayon ko,wai wata ?asa za ta!Zainab ta raina ni matu?a ban san yadda zan yi da ita ba,amma in dai ta yi gigin fita waje Allah sai na hukuntata."

Shiru A.k ya yi ba tare da ya tanka mishi ba yana tu?in sa a ran sa cewa ya yi." Kamar da gaske zai iya."

?aramin tsaki ya yi ganin haka sai A.m ya kama bakin sa ya yi shiru bai ?ara cewa komai ba,don maganar da yake masa kame-kame ne lamarin Zainab yana ba shi haushi sosai.

" Har yanzu ban ji kayi maganar Juwairiya ba."A.k ya faWa ba tare da ya kalle shi ba.

" Shiru ya yi ba tare da ya tanka ba duk da ya Wan daina jin zafin ta amma har yanzu yana jin haushin asarar da ta yi mishi.

" Ka rabu da ni da wannan shiriritacciyar ina maganar matar so wake ta matar shige,sai ka bari na gama da wanda zuciyata take muradi ba wata can ba."

Tuki A.k ya ci gaba da yi ba tare da ya tanka a bin da ya ce ba a ran sa shika Wai ya san me yake tunani.

Juwairiya ri?e da waya a hannunta suna kokuwa da Hauwa da ta rantse ba za ta kira shi ba.

" Hauwa ki taimake ni don Allah kada ki sa zuciyata ta fashe! Na san har yanzu A.m yana fushi da ni ne ha?urin zan ba shi."

Wani mugun kallo ta sakin mata ta ce." Wai ke ba ki da aji ne? Shi ya sa ya raina ki ya ke wula?antaki,Allah ya halicci mace da daraja mai girma a gurin Wa namiji in kika ba shi lokaci da kan sa zai kira ki,don haka ba zan ba da wayata ba."

" Wayata tana gidan sa babu ta in da zai kira shi kuma na san cewa ba zai taSa kirana ba,ko sau Waya ki bani na kira shi don Allah."

Ta faWa tare da marairaice fuska hawaye a kan ?uncinta.
" Bari na tura masa da tsa?on ha?uri daga gareki in har yana bu?atar ya kira ki zai neme ki,amma ba zan bari ki kira shi ba nuna son da kike masa ya yi yawa shi yasa yake gasa miki gyaWa a hannu.

Sai ta koma ta zauna ta zabga tagumi da kalar tausayi har hanzu hawaye na turereniya a fuskarata.

Yanayin da ta yi sai ya ba Hauwa dariya da takaici.

Wayar ta Wauka ganin ta?i cin abincin da ta ije musu ta faWa kogon tunani.

Tsa?on ha?uri ta tura masa da basu wuce kalmomi biyar ba ta ije wayar.

A.m dake kwance a kan makeken gadon sa da yake jin faWin sa ya kai faWin duniya.Filo ya jawo ya rungume da tare da jan tsaki.

Tsananin Sacin rai yake Wauke da shi saboda ya ya je gidan su Zainab ta bar ?asar.

Da ?yar ya iya dawowa gida ya kwanta yana jin wani irin zafi a ran sa.Tun ranar da tsa?on ban ha?uri ya shigo daga Juwairiya wanda yau kwana biyar da shigowa, bai ko karanta da kyau ba balle ya tura reply wani irin haushinta yake ji da yanzu ya fara irga ranakun da zai zama Daddy.


Wayar sa ta yi ringing har sau uku sai a na huWun ya Wauka a kasalance ba tare da ya tanka ba.
" Ban yi tunanin za ka amsa kirana ba balle ka Wauka."Muryar Baba Sani ta daki kunnin sa.
Da hargowa ya ja tsaki da takaicin ?in duba wayar da bai yi ba ya Wauka,wanda hakan ya kasance ne saboda baya son ya kalli wayar lokacin da kiran ya shigo.

" Ban san kai ba ne da babu abin da zai saka na amsa wayar,mara mutunci mai ya sa ka kira wayata?"

" Na kan yi mamaki in ka yi min wannan tambayar Juwairiya da take gidan ka irin mangwaro ce ka samo ka shuka ta fito,da kake tambaya ta dalilin kiran ka."

Shiru A m ya yi masa a yanayin da yake baya bu?atar tashin hankalin Baba Sani don yana shakkun shi sosai.
" Na so na zo da kaina amma dana tuna baka da mutunci,kuma ka yi min gargaWi sai na dana tsufana,gudun kar na mutu da ?afa Waya sanin baka da mutunci,kuma sam baka girmama na gaba da kai.

"Fine gara da ka yi ma kanka ?iyamullaini ?a?i zuwa in da nake da sai ka raina kan ka wallahi."A.m ya ce ran shi a Sace.
" ?ar Wan'uwana na biyo naji ba'asi A k ya zo nemanta jiya."Gabansa ne ya faWi ya yi shiru bai tanka ba,amma tsoro fal a zuciyar sa ya manta Mama ba ta gari,kwata-kwata bai yi tunanin in da za ta je ba,saboda haushin da ta ba shi ko tunanin halin da take ciki bai yi ba.

" Na ji ka yi shiru ne ko ka Satar mini da ita ka san fa ita Win dukiya ta ce,so ka kiyaye don wallahi zan iya shuka rashin mutuncin da baka taSa tunanin in da shi ba."

" Har a kwai wani rashin mutuncin da za ka yi min da zai firgita ni bayan san baka da mutunci gabaki Waya rayuwarka,a tsiya za ka ?are don baka gaji arzikiba garyar matsiyata."

Dariya Baba Sani ya saki jin abin da ya faWa sai ya ba shi amsa da.

" Ashe masu arziki zasu zama matsiyata don in ka yi gigin Satar da ita saina zaman maka ?adangaren ba?in tulu,don haka ka kula ba ni da mutunci kai ma sheda ne."

A.m da ran shi ya ?ara Saci matuka kaWa kan sa ya yi sannan ya ba shi amsa" Kama ta ya yi na zo na kamaka in ji dalilin da ya sa take zubar min da ciki,don na san wata?ila kai kake saka ta kuma wallahi in har na gane da saka hannun ka sai na saka kaf zuriyarku an Waure ku."Ya ce da shi ciin Waga murya .

" To shikenan Wan ?aruna ina jiran ka amma ?ila ni zan fara Waure ka,matu?ar ka salwantar min da ?ar Wan'uwa kuma jarina,wai yaushe kuWin da ka ba ni zai gama aiki?"Ya canza maganar da sigar tambaya.

Da takaici ya kama shi jifa fa wayar ya yi ba tare da ya kashe ba,yana jin dariyar Baba Sani can kuma ya kashe wayar.

" Ina ga Juwairiya da tsinannen Babanta Sani su za su yi ajalina."

Ko me ya tuna da sauri ya Wauko wayar da ya yi jifa da ita.

Numbar da ta turo masa da tsa?on ha?uri ya fara bincika duk da bai wani karanta tsa?on sosai ba.

Wayar na ringing tana ?ara tayar masa da zafin dake cikin zuciyar sa.

Sau uku ya kira amma ba'a Waga ba har ya yanke shawarar ba zai ?ara kira ba,sai kuma ya ji muryar wata mace ta yi sallama.

" Ina Juwairiya take."

Ya faWa a gundure da takaicin kiran da ya yi." Ban sani ba kuma in ga wrong number ka yi saboda ban san mai wannan sunnan ba "

Ta faWa da Wan daga murya dama abin da ta yi ninyar ta yi masa kenan,saboda yanzu matu?ar haushi yake ba ta yana can yana wahalar da kan shi,ga in da ake masa son mutuwa.

" Ko da ban san ke wace ce ba kar ki raina min wayo kin san dai abin da ke tsakaninmu ,ba kiran ta na yi don ina so ba,a'a saboda ta Sata mini kuma sai na nuna mata kuren ta."Ya ce da Hauwa ran sa a Sace.

" Ok kai da ka santa kake wannan maganar amma na yi maka bayanin ban san ta ba balle na sa abin da ya haWa ku."

Hauwa haushi yake ba ta ji take kamar ta kama shi ta yi masa shegen duka saboda irin mutanen nan masu gatsali.

Ta buWe baki za ta yi magana ji ta yi an fisge wayar Juwairiya ce daga bayan ta wacce ta shiga bayi a she ba ta san ta fito ba.

Jikinta har rawa yake lokacin da ta kanga wayar a kunninta tare da fashewa da kuka.

" Hello don Allah ka yi ha?uri ka yafe min wallahi ba zan ?ara ba zuciyata za ta fashe na rashin ka a kusa da ita k..."Wata uwar tsawa ya daka mata.

" Ban kira ki don ki gaya min tsoki buruku ba kin ji na rantse kar ki bari mu haWe dake don sai kin raina kanki.Gidan uban wa kike Baba Sani ya kira ni ya ce min ba ki a gidan sa?Da auren kike gantali ni dama na san ?an iskan ?awaye kika yi da su suke zuga ki,to makarantar ma na da?ile tun da baki san mutunci ba kuma na rantse miki za ki fuskanci fushina mai tsanani."

" Don Allah ka yi ha?uri ka yafe min na yi kuskure ba zan ?ara ba."

Hauwa ce ta fara kiciniyar fisge wayar da ta yi mata kyakykyawar ri?o.
"Dole A.m ya din ga wula?anta ki haba kamar ba mace ba duk kin zubar da ajin ki ya raina ki an faWa miki so hauka ne haka ake nuna ma masoyi ?"

Duk yadda ta so ta karSe wayar ta ?i bata,har du?awa ta yi tana ba shi ha?uri yayin da idanunta ke zubar da hawaye.


" Gidan ?awata Hauwa Tukur."

Ta bashi amsa har tana in ina garin saurin ta faWa masa." Minti goma na baki ki dawo gida in ba haka ba za ki fuskanci hushina."

A wannan lokacin Hauwa ta ?arSe wayar."A.m duk abin da kake yi Allah yana kallon ka,don Allah ya jarabce ka da ?aunarka sai ka din ga wahalar da ita?Ina jiye maka ranar da Allah zai kama ka a kanta...."

" Ke karki kawo min maganar banza matata ce fa kin san irin ma?udan kuWin da na saka na aure ta?In har na gane ke kike zugata saina Waure ki igiya tai rara.Maza ta dawo cikin mitinan da na bata."

" Juwairiya ba za ta dawo ba saboda ba ta da lafiya sosai in har ka matsu da ta dawo to ka zo ka Wauke ta."

?if ta kashe wayar cikin Sacin rai saboda tunanin da take mishi ya wuce wannan.

" Haba Hauwa kina gani har sallar dare nake yi don ya kira ni shine za ki ce ba zan koma ba,kin san wannan batsa kika yi don tafiya zan yi."Ta ce cikin murna.

"Ki ce dabbe za'a yi a gidan nan na ga wanda zai kada wani ko da ganina kin san ba za ki ibi komai a jikina.Wallahi mugun haushin sa nake ji ya faye son kan da da yawa na, yi ba?in cikin Wauke Mama da ya yi ita ce kawai za ta iya ?watar miki ?ancin ki,don ke baki maida kanki mace ba shi yasa yake gara ki ya na amfani da son da kike masa.


A.m da yake jin haushin kiran da ya yi mata yana ta zagaye kamar mai Wawafi.

Ya fi kusan minti talatin yana jiran ta dawo ko ba komai ya rage damuwar abinci da kullum yake fama da yunwa,don ko gidan su ya je babu wanda yake masa tayin abinci,ya san ana yin hakan ne don a hora shi.

Wayarsa ya Wauka yana tsaki ya tura tsa?o kamar haka.

" Turo min da adireshin gidan."

A lokacin da tsa?on ya shigo Hauwa na tsaye ta ri?e Juwairiya ?am da take son ta fice daga gidan.

" Ina tausaya miki Juwairiya ko wani namijin kika aura ba A.m ba za ki sha wahala sosai,na lura baki iya Soye so ba in dai kina son mutum su maza ba'a musu haka yayin da suka fahimci mace ma son su wula?anci yake biyo wa baya."

Hawaye ta share ta kalle ta ta ce." Wata?ila ba ki taSa soyayya ba ne shi ya sa kike daWin haka amma son da nake ma A.m irin na in ban same shi ba sai rijiya."
" Ina na taSa so ai kin san auren ?iyayya na yi da mijina.Ta yi mata gatse sannan ta Wora da cewa "Ai ko kina ruwa wallahi don ina tausaya miki."

Kama hannun Hauwa ta yi ta ri?e sai hawaye shar!"Ki bar ni don Allah na tafi."

Kallon ta ta yi tana dariya ta ?ara cewa." To mara aji matar mahaukaci, ya ce na tura masa da adireshin gidan, sai ki kwantar da hankali don na fiki murnar tafiyar ki ko banza yau zan yi bacci lafiya, ba tare da na yi rarrashin kukan da ake min duk dare ba.In kun so sai ku kashe kanku munafukai kawai."Wani irin daWi ya lulluSe jin zai zo duk da tana tsoron haWuwar su amma idanuwanta suna ?ai?ayin son ganin sa.Yana isowa hon ya shiga yi ba ?a??autawa.

Da gudu ta ruga har tana bige ?afa da ?ofa amma bata kula ba,ko sallama ba ta yi mata ba sai hannun da ta Waga mata.

Duk da bugun da zuciyarta take mata amma gaka nan ta yi shahada ta shiga suka zuba ma junan su ido.
A.m da yazo da fushi duk sai ya nemi fushin ya rasa musamman da ya ga ta rame kamar wacce ta yi ciwon shekara.

Kau da kan sa ya yi ga barin kallon ta ya Wauki biro ya saka a tsakanin yan yatsun ta ya matse da ?arfi har sai da ta yi ?ar ?ara saboda zaba.

" Kin san irin girman laifin da kima yi mini?Kin Sata mini rai ?warai kuma saina miki horo mai tsanani,na rantse kika ?ara gigin ?ara zubar min da ciki saina illata ki sannan jikina ba zai yi wahala ba sai kin mayar da abinnda kika zubar.
?aryar iskanci kike ba ki san waye ni ba muje gidan za ki ga abin da zai faru dake."

Tsananin tsoro ya cika mata zuciya ganin irin muguntar da ya yi masa,sai ta ji tsoron kar yazo ba kowa a gidan ya kashe ta a banza,saboda har yau tana tuna irin sha?ar da ya yi mata.

Ganin fuskar sa babu fara'a hankalinta ya ?ara tashi.
" Ka yi ha?uri na gane kuskure na insha Allahu ba zan ?ara ba kuma na yi hakan ne..."

" Ban tambaye ki dogon surutu ba in har kina son na yi ha?uri to ki ?o?arta ki mayar da abin da kika yi mini asarar shi a yau."

Ya faWa ba tare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tu?in da yake yi.

Yanayin yadda ya ya nuna mata hankalinta ya Wan kwanta,domin ta yi tunanin fuskantar haka daga gare sa,ta Wauka dukan mutuwa zai yi mata kuma ya kore ta.

Tun da ya faWi wannan maganar bai ?ara cewa uffan fa har suka iso gida lokacin a na kiran sallar isha'i,don haka parking kawai ya yi ya fice masallaci.
Ajiyar zuciya ta saki mai ?arfi tana ?are ma gidan kallo wanda rabon ta da wata biyu kenan

Da ta tuna Zainab sai da gabanta ya faWi ras! Duk da ta san ba ta gidan shi ya sa ya je ya Wauko ta,a ranta take tunanin ko ta yi tafiya zuwa waje.

Bayan ya shigo tana zaune a falon gidan sai ?are wa falon kallo take saboda ganin ya canza,kallonta ya yi sai kuma ya Wauke kan sa zai haye sama.

Da sauri ta ri?e hannun shi." Don Allah ka yi ha?uri ka yafe min wallahi na tuba kuma na yi nadama."

Hararar ta ya yi tare da galla mata tsaki ya janye hannun sa sai kawai ta faWa jikinsa tana kuka sosai.

" Ke fa matsala ce ta ko ina bayan asarar da kika yi min kukan banza za ki rarrashe ni da shi ko?Kawai zan ha?ura ne in har kin yi al?awarin yau za ki mayar min da asarar da kika yi min."Ya faWa cikin wata irin murya.

?ago kanta ta yi tana share hawaye ta kalle shi sai kuma kunyar abin da ya faWi ya sa ta sunne kanta tana murmushi.

" Yunwa nake ji ?warai kin korar min matar so,sai ki maye makwafin ta kafin ta gama hutun ta dawo,sai ki yi ?o?arin mai da asarar da kika yi mini don ba zan wahalar da kaina ba.

Da sauri ta tashi ta ?walalo masa ido tana dariya sai kuma ta nufi kicin,wanda dama kafin ta yi alwala sai da ta Wora masa abu mai sau?i wanda zai ci,don ita yau murna ba zai barta ta ci komai ba.

Mamaki ta yi da ta ga ya biyota kicin Win duk da ?orafin abin da ta yi masa yake yi,da kuma yi mata gargaWin kar ta ?ara sai ta ji sanyi sosai a ranta ,saboda yana da saurin fushi zai kuma iya yanke komai ba tare da tunani ba,amma kuma yana da saurin sauka.

Ba ?aramin mamaki ta yi ba da ya nuna mata shifa da gaske ita za ta mai da asarar da ta yi masa

Hakan ya sa ta dage sosai don ta faranta masa saboda ya manta komai.Daga ?arshe da kan sa ya karSi jagoranci komai,saboda bai san ya yi missing Winta alot haka,a haka bacci ya yi ya kasheta da ?aunar sa da take sakata hauka a kan sa,sai ya fake da duk a cikin horo yake mata wanda so yake ya maida asarar da ta yi masa.

Sai da suka makara sallar asuba ita ce ta farka ta zare jikinta sannan ta tashe ki,kan dole a gida ya yi sallah,ya kuma sawa suka koma bacci.

Ba su tashi ba sai misalin sha biyu na rana kiran wayar da A.k yake yi ya tashe shi.

Tsaki ya saki zai kashe wayar sai dai da sauri ya mi?e ganin kira rututu a wayarsa,da ya kalli agogo salati ya fara yana Wan buga bayanta ganin sha biyu har ta gota.

Mi?e wa ta yi ita dama tuni ta farka ba ta so ta farkar da shi ne,ya sa ta ci gaba da kwanciya amma yunwa take ji matu?a.

" Hello hala yau mutuwa ka yi ne ana ta kiran waya ka san muna da ba?i sai ka zo ka buWe mini falon ka ina waje ba?i na ta jira.

Da sauri A.m ya sauka ?asa shaf ya manta da client din sa da za su zo yau yana faWin." Ki sauko ki bani abinci mai sau?i fita zan yi."

A.k ya dogare a bakin ?ofa yana kallon sa ganin sa da kayan bacci." Wai hala rashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login