Showing 15001 words to 18000 words out of 143803 words

Chapter 6 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4731

kunya ya lulluSeta.
Ganin yadda ta diririce sai ya shige Wakin sa akan ya Wauko abin da ya saka shi ya dawo saboda mantuwa da ya yi,wato wasu fayal da ya ije da nufin ya tafi dasu sai gashi ya manta da su kuma ana bu?atar su.Ashe da rabon ya yi gam da katar!Don shi ya ga matar aure dama tuni ya yaba da hankalinta.

Ko da ya shiga cikin Wakin wani irin kasala ya ji y rufe shi ya faWa kan gadon shi ya na jin wani irin shauki na ta ya na zagaye ilahirin jikin shi.Ko da ya shiga Wakin faWa kan gadon sa ya daWe ya na jin wani girmar lamari har na tsawon lokaci,sannan daga bisani ya mi?e ya Wauki fayal Win ya fito.

Kawai sai ya tsinci kansa da bin hanyar kicin Win ya Wan tsaya nesa da kicin Win zuciyar sa na bugu da ?arfi,take yake jin lamura suna sauya mishi har ya fara dana sanin dawowar sa gida gashi komai na son ya canza musamman akan yarinyar da take ba shi girma

"Abnaj fito na gyara muku tibin ku barta ta yi aikin ta,kun dame ta da surutu."Yace da yaransa da suke kicin Win suna ta zuba da Anty Juwairiya kaza,ita kuma ta na ta yi musu dariya ba yan ta basu kwan da ta soya musu.

Yaran suka bi shi suna murnar zai gyara musu tibi,bayan tafiyar sa ziciyar Juwairiya ya buga dam!Da ta kalli ?wayar idanunsa cikin rashin sani ganin yadda ya kafa mata idanu lokaci guda,abin da ta hango ya matu?ar tsorata ta wanda bai yi kama da so ba sai tsantsar sha'a warta da ta hango.In ko haka ne abincin ta ya ?are a gidan.

Bayan fitar sa ta Waga labule ta na kallon farfajiyar harabar gidan,sai kawai ta ji hawaye ya na sauka a kan ?uncinta bai yi kama da mutumim banza ba saboda ya na da dattako.To me ?wayar idanunsa suke nuna mata?Ita kuma irin na ta jarrabawar kenan?




Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na takwai.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TAKWAS*


Tun daga wannan ranar Juwairiya ta ga canji a tattare da shi,ya sakin mata sosai kuma ya na matu?ar kyautata mata,ko hira yake da matar shi sai kiji ya tsoma ta ciki yace"Wai haka aka yi Juwairiya ita za ta faWi gaskiya."

Ranar da ya fara mata hakan ta yi matu?ar razana ta kalli Anty Naja ta ga ko me za tace amma sai taga sai dariya take ta na jin daWi har ta na ?ara tambayar Juwairiya,wani tsabar takaici kaWa kanta kawai ta yi ta shige kicin Win wanda dama shi ya ?wala mata kira don kawai ya tambaye ta.

Bayan sati Waya sai gashi ya dawo gidan da wuri da yake a ranar matar sa na gurin akin ta na night duty acan za ta kwana.Bayan ya yi sallar magariba ya kulle ko ina na gidan ya shigo,tun da taga ya dawo da motar sa ya wuce masallacin kofar gidan sa gabanta ya faWi hankalinta ya tashi,domin ita canjin da ta gani a gurin sa ya na tsorata.

Bai fito ba ya na karatun kur'ani har kiran sallar isha ya tafi masallaci,sannan bayan ya yi sallah ya dawo ya zauna a falo shi da yaransa suna kallo shi kuma ya na aiki a laptop Win sa.
"Abnaj je ka kira min Antyn ka Juwairiya kace ta zo ta bani abinci."Yace mishi ba tare da ya kalle shi ba,burin sa ya ganta ya san ta Soye kanta a Waki don kar ya ganta.

Yaron ya ruga da gudu zuwa can ya dawo yace."Ga ta nan zuwa."Ya ci gaba da kallon sa bata jima ba ta fito da dogon hijabin ta har ?asa.Ita sai yanzu dake matu?ar dana sanin gadin mijin wata da yaran ta da take,don a a kwai haramcin haka a cikin addini mace baliga da namiji ba muharramai ba dama na ukun su sheWan ne.

Nesa da shi ta tsaya kamar za ta yi mishi magana sai kuma ta juya ta shige kicin ta Wauko abincin shi ta ije mishi za ta juya."Ba kiji ba Juwairiya."Yace da ita ganin za ta shige Wakin da take kwana har ta na haWawa da gudu-dugu.

Tsayawa ta yi bata re da ta juyo ba ta na watsa da yatsun hannunta gani take kamar zai hai?e mata kamar yadda ?anin mahaifinta ya yi mata,amma sai ta ga ya ?araso ya tsaya Wan nesa da ita ya mi?a mata sabuwar waya mai kyau a kwali ya Wan daure fuska."Ga shi na ji Antynki tace Abnaj ya saka miki waya a ruwa ta lalace shine na hutar da kuWin ta,amma fa ki kiyaye ki dai na basu don nan gaba in kika bari suka lalata sai na haWa da bulala kafin na canza miki wata."Yace ya na kashe mata ido.
Zare ido ta yi ganin wayar da ya siya mata irin wanda take gani a hannun su masu kyau da tsada,ina ita ina wannan wayar ta na ?ar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja."

Kamar ya san me take tunani sai ya kaWa kansa yace."Karki damu na san me kike tunani zan yi mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki karSa kin san babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace maraya.

"Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ?ar aiki bai kama ta na ri?e irin wayar nan ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa.

Shi ma ya Wan razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya Wan sosa ya kafe ta da idanunsa yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana."

"Ka yi ha?uri don Allah ba na son kyakykyawar ala?ar mu da matarka ya Sace,kai sheda ne mace ce na ?warai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.
Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya Wan yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki zamo uwar ?a?ana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya.

Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan Win ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ?ila in Anty Naja ta gane ba lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake ri?e a hannunta da ya bata take kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta Wauka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron sani ta bata da kanta.

Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na Waga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida.

Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi ?warai ta yi shuru kawai ta na jinjina abin a ranta,ta Wauki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa tace."Ina ga ko ha?ura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci."
"Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi ?warai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane."
"To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na ri?e irin wayar nan don Allah kaWai ya san abin da Baba Sani zai faWawa jama'a."
"Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da mi?ewa don Wauro alwalar kiran sallar magariba da ke ta kwaWawa masallacin kusa dasu.
Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda ?an kwanakin yake mata,ta na ganin shi ta ?ara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta.
Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta ga ita yake kallo kamar bai taSa ganin ta ba.Mi?a masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty Naja ba."
"Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika ?i Waukar wayata jiya da daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama ma?iyi Juwairiya?"Ya ?arashe maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu daWi,ganin namiji mai natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi.

Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai ta?i auren shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin ta?i kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai ma hawaye da ta soma ganin haka ya Wauki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta.

Kwana biyu haka suke wasar ?ar Suya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta.
Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na damina garin ya fara haWa hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma ba?in hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai.
Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma ganin har an fara iskar hadari ya sa ta buWe gidan baya ta shige,tare da haWe girar sama da ?asa don karya tambayeta dalili

Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da ya fara tafiya.
"Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba.
"Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar.
Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar ?an mata kenan da kun ga namiji ya na ?aunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin ?wayar idanunki."
Ta Wan saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da Wawainiya da yake musu ta ja numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake tsa?anina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace ba."

"Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya faWa a raunane kuma a ta?aice.Babu amma Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya saSa ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya buga da ?arfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata magana can,kawai na gane bakya sona ki ce na ha?ura kina da wani hakan zai sa na bawa zuciyata ha?uri duk da na san za ta shiga wani hali."

Yanayin da ya yi maganar sai ya bata tausayi amma ta san abin da yake so ba mai yiwuwa ba ne.Murfin motar ta Salle za ta fita ganin sun ?araso gida ya yi parking,sunan ta ya ?ira da wata irin murya.Ta waigo ba tare da tace ?ala ba,sai ?asa da kanta da ta yi wato alamun ta na sauraren sa.
"Ki yi tunani zuwa ?arshen sati nan nake so na turo magabata na,ina ganin za ki dakata da akin nan kafin kizo a matsayin ?anwa kin ga sai ki Wora daga in da kika tsaya ki na samun lada rututu!

?alle motar ta yi ta fice dai-dai lokacin da ya mi?a mata ?an rafar Wari biyar kusan kimanin dubu ishirin ba tare da ta karSa ba ta fice,musamman da ta ga Baba Sani tsaye a ?ofar gida shi da wani mutum ya zura mata ido.

Ganin jikinta ya soma rawa ya kalli in da take kallo,sai hakan ya yi mishi daWi domin faWuwa tazo dai-dai da zama,ya buWe murfin motar ya fito ya nufi su Baba Sani dake kallon Juwairiya kamar ya sha?e ta.

Da sauri ta matsa za ta bi ta bayansa ta shige cikin gidan da ya bake ?ofar,amma sai ya daka mata tsawa tare da jan hijabinta."Ina zaki ?ar iska maza dawo,iskancin naki ya kai har a kawo ki gida a mota.Kawai sai ya saka salati da ?arfin sa ya ci gaba da cewa."Inna lillahi gara da ka mutu Yaya Ahmed in da ka na raye Juwairiya ita za ta ?ashe ka.Karuwa kika zama fa ke ko kunya duniya ba za ki jiba tunna baki ji na Allah ba."
"Ashsha!Subuhanallahi haba Malam ya za ka dinga jifan ta da waWannan muggan kalamai?Iya sani na Juwairiya yarinyar kirki ne ta WaWe ta na tare damu ta na mana aiki.Yanzu haka mun daidaita ne nake son ka bani auren ta,ma'ana na yaba da hankalinta ina sonta."

Wayyo Allah faWin haka da ya yi wato ya na son Juwairiya ji Baba Sani ya yi kamar ya watsa mishi fetur ya kyasta ashana domin ba?in cikin sa biyu ne a kan maganar.Na farko ta ya ya za 'ai mutum me hannu da shuni yace ya na sonta,sannan kuma ba?in kishinta ya taso ya lulluSe mishi zuciyarsa kawai sai ya ?ara kuka ya na faWin ma abokin da suke hira cewar."Kaji ko wai na ba shi aurenta bayan ya gama iskanci da ita ni nasan ya na naWe tabarmar kunya ne.Amma ta ya ya zai auri mazinaciya!Ba Juwairiya dake tsaye ta na kuka ba har ta Daddyn Abnaj sai da yaji wani irin abu ya soke shi ya rintse idanunsa ya na jin kamar ya sha?o wuyar Baba Sani,take ya fahimci wani abu wato na zaman ?unci da suke yi iya zaman su da ita bata taSa basu labari ba,duk da ya san cewa ba lai-lai bane ta gaya musu kasancewar ta na da zurfin ciki.

Ya kalli Juwairiya da ta ?ara sautin kukan ta ganin mutane sun fara taruwa Baba Sani yaci gaba da magana da ?arfi ya na nanatawa,sai ta ruga da gudu dai-dai lokacin da Baba Sani ya kai mata bugu a bayanta.

Ba ta san ya suka ?are ba ya dai shigo gida ya na ta faWa tare da ja mata jifa'i kala-kala, Juwairiya ta so ta tanka saboda abin da ya yi mata a gaban mutumim da yake girmama lamarin ta,amma Mama ta hana duk san da ya gaya mata ba?a ta buWe baki za ta yi magana Mama za ta hana ta,har ya gaji da rashin mutuncinsa ya fice.

A ranar Juwairiya ta ci kuka sosai ta ji ta ?ara mugun tsanar shi a ranta.
Washegari ganin ta?i shiryawa taje aiki Mama ta shigo Wakin ta tsaya ta na kallonta tace."Juwairiya ba zaki je aiki bane naga rana ta yi."
"Na ha?ura da aikin Mama gara na zauna a gida dama kin san mun yanke shawarar na daina zuwa,sai ga abin da Baba Sani ya yi min a gaban shi Allah kunya nake ji matu?a.Karuwa ya kira ni."Sai kawai ta saka kuka ta na jin zafin kalmar da ya danganta ta da ita."
Mama a ranta har tafi Juwairiya damuwa amma sai ta Wan gyara murya tace."Ki yi ha?uri komai lokaci ne watarana sai ya yi dana sani,amma da kin daure kije kila ma ya shafa miki lafiya don na tabbata ba zai ?ara miki maganar soyayya ba,ganin yadda ya tozar taki."
"To Mama shikenan a haka rayuwata za ta ?are duk wanda ya fito neman aurena sai Baba Sani ya Sata lamarin gaskiya na gaji."Tace cikin hawaye yayin da ta tuna katoSarar da ta yi na faWin hakan,kamar ta nuna ta na son auren kenan sai ta zari hijabinta da sauri ta fice zuwa aiki.

Ko da ta isa bata sami Anty Naja ba duk da ta san dama abu ne me wuya ta same ta,abin mamaki ta yi sallama ta shiga fuskarta babu walwala,sai ta same shi zaune akan one siter ya zuba tagumi ya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login