Showing 78001 words to 81000 words out of 143803 words

Chapter 27 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4745

tabar gidan domin ba za ta zauna ba ya kashe ta.

Ta shiga cikin tsananin mamaki da ya ce Juwairiya matar shi ce,to mai hakan yake nufi bayan Anty Zainab ta gaya mata yar aiki ne.

Sam ba ta kawo cewar zai iya ije matar shi a gidan ta zama ?ar aiki ba,shi ya sa ta Wauka kawai ya gaya mata hakan ne don ya kawar da tunaninta aka suna zina.

HaWa kayanta ta shiga yi domin dole in Anty Zainab ta dawo za ta bar gidan ba yan ta tsegun ta mata.

Juwairiya kuwa kuka ta saki ta ?ara faWawa jikin sa." A.m ka na cutar da zuciyata mai kake tunanin zai faru in har ta faWa ma Anty Zainab abin da yake faruwa,kawai gidan nan zan bari ayau in ya so duk abin da zai faru ya faru,amm na gaji da wahalar da rayuwata da kake yi.

Da ?arfi ya janyo ta jikin shi ya na huci.
"Juwairaah ki saurare ni ba ni da nufin na cutar dake kawai ki fahimci abin Waya.."

Juwairiya ta katse shi ta na faWin cikin kuka da murya mai ?arfi.
" A.m ya ishe ka ba ka sona ka tsane ni wannan dalilin ya sa kake wahalar da zuciyata da gangar jikina,kullum sai dai ka yi min maganar ka na son jikina halina da kyawuna shin ni bani da zuciyar da za.."
"Juwairiya."

Ya faWa da ?arfi tare da girgizata ya na zare idanunsa.
"Karki kawo min maganar banza kin san dalilin aurenki so ban ga dadilin da za ki kawo min maganar banza ba."

Fisge hannunta ta yi ta na kallon sa ta na ja da baya har ta kai bakin ?ofa da gudu ta fice.

Ko da ta shiga Waki halin da ta ga Binta sai ta ba ta tausayi karSar tsummar da ta ga yaga cikin kayanta ta na ?o?arin Waure gurin yankar.

Hannu ta saka ta karSi tsummar ta Waure mata hannun yayin da hawaye yake kwaranya a fuskokin su duka.

" Ki yi ha?uri haka rayuwa take tafiya a ko da yaushe talaka shi ne a ?asa ko da shi yake da haskiya."

Ta faWa ta na kallonta idanunta na ?ara zubar hawaye.
Binta ba ta ce komai ba sai share hawaye da yake gangarowa a ?uncinta da ta yi.

A ranta ta saka ba za ta ?ara kallon kowa daga cikin su ba balle ta yi magana ta tono ma kanta tsuliyar dodo,ganin abin da ya yi mata ya sa ta fara tunanin ko bashi da imani ne amma har yanzu ba ta amince da faWin cewar Juwairiya matar shi ce,sai dai in za su yi mata badda kama don kar ta gaya wa Zainab.

Kallonta ta ?ara yi ta na jin tausayinta matu?a ganin yankan da ya yi mata ya shiga ciki sosai.

"Anya A.m ya na da hankali?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ta rasa amsa sai ta Wago ta ?ara kallon Binta a karo na biyu.
"Wannan dalilin ya sa na ce miki ba za ki fahimci komai ba."

Ta faWa tare da juya mata baya sai dai ta ji a jikinta kamar babu kowa a Wakin ko da ta juyo wayam ba Binta ta fice daga Wakin.

Duk yadda ta so ta yi magana amma Binta ta?i tanka mata sai in ta ga za ta takura mata ta saka mata kuka,hankalinta ya tashi matu?a ta yi zuru ta na kallonta.

Binta ta saka a ranta ba za ta ?ara mata magana ba balle ta tanka a kan cin amanar da suke yi ita da shi,Allah Allah ta ke gobe ya yi Zainab ta dawo ta saka mata kukan ta kaita gida.

A.m bai shigo gidan ba sai misalin bakwai bayan ya dawo daga masallaci kamar yadda bai neme ta ba,haka ita ma domin ko kiranta ba ta son ya yi saboda hankalinta ya tashi jin ya faWi za a yi mata dashen ?wan haihuwa.

Sai ta fara nadama matu?a ta na ji kamar ta gudu daga gidan don ta san mundin ta faWa mishi to ita ma yanka ta zai yi ko ya kasheta,saboda ya gaya mata duk abin da ke tsakanin su ba da wata manufa yake yi ba burin sa ya samu baby shi ya sa yake mata haka don haka ta saka a ranta abin da ya fi na Binta zai yi mata.

Kwanciya ta yi ba wani karsashi a tare da ita saboda duk yadda ta so ta zo su kwanta amma ta?i sai ta samu guri a Wakin da Baba take zama ta kwanta.

A.m da ya gama shirin baccin sa shiru ba ta zo ba dama bai saka ran za ta zo ba kuma shima ransa babu daWi don sun yi Wan tanka-tanka da A.k akan nemar shawarar sa da ya yi na dashen da yake so ayi mata,amama sai ya nuna rashin amincewar sa akan ya ?ara ha?uri har Allah ya kawo.

A.m ya ji ba daWi don ya gaji da jiran gawon shanu don haka ya nuna ma A.k rashin amincewar shi in da har ya ji zafi ya gaya masa magana,yayin da ya saka a ranshi kawai za su tafi ai shi ba uban shi ba ne da duk a bin da zai yi sai ya nemi shawarar sa.

?akin da take kwance ya nufa tare da saka cocilar wayarsa ya haska fuskarta,ba bacci take ba amma ta yi maza ta rufe idanunta jin shigowarsa.

Ta yi mamakin da bai tashe ta ba ya juya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya fita.

Hankalin shi ya Wan tashi ya shiga tunannin ko ta gudu ne don bai ganta ba,sai kuma ya duba Wakin da ya san Baba ta na zama ilai kuwa ta na Wakin ta takure a guri taya ta na baccin wahala, don ko numfashi ba ta saukar wa ta daWi ganin yadda ta takure kanta.

Sai dai ya yi mamaki ?warai ko da ya matsa kusa da ita sai ya ga ta mi?e zubbur ta na salati,wanda ya saka a ranshi mafarkin shi take yi.

"Inna lillahi na bani don Allah karka cutar da ni mahaifiyata ba ta da rai."

Ta faWa da muryar kuka ta na ro?onsa amma bai kula ta ba sai ya saka hannu a aljihun wandon sa ya zaro bindiga ya Wora mata a goshinta.

Ta buWe baki za ta yi ihu amma sai ya saita daidai bakinta ya ce da murya mai sanyi."In kika yi ihu sai na kashe ki.".
Ya faWa da wata irin murya da ta ?ara tsorata ta wanda ya sa ta yi sauri ta rufe baki ta tare da mai da kukan.

Ganin ta yi shuru ta na kallon sa har fitsari ta yi a wando.

A.m ya kalleta tare da watsa mata harara ya fara magana da ce wa."Gobe Zainab za ta dawo Allah ya sa ki faWi wani abu a tsakanina da Juwairiya kashe ki zan yi."

Wani irin kartawa cikinta ya yi ta ?ara toshe bakinta ta na tunanin yau Allah ya kawo ta gurin jidali gashi mai gida na son ya kasheta.
"Wallahi ba zan ce komai ba babu ruwana ka taimake ni karka kashe ni."

Ganin ta tsorata ya sauke bindigar ya na shafawa ya ce."Good in kunni ya ji gangar jiki ya tsira ina fatan kin gane."
Da da sauri ta Waga masa kai sannan ya fara taku zai fita wanda Binta ta fara addu'a Allah ya raba ta da shi lafiya.

Ganin ya kuma jiyo sai hankalinta ya ?unduma ya tashi ta ?ara firgicewa ta na tunanin mai ya saka ya dawo."
"In Zainab ta dawo ina son ki yi ?aryar aljanu a mai dake in da ka Wauko ki in kuma ba haka ba wannan zan saka na kashe ki."

Ya faWa ya na nuna ta da bakin bindiga sannan ya juya ya fice daga Wakin.
A ranar kasa bacci ta yi ta na ta kuka daga ?arshe dole ta koma Wakin da suke kwana don gani take kamar zai dawo ya kasheta.

Washegari gidan ya kacame sai gyara ake yi kasancewa da misalin sha Waya Zainab za ta iso shi kan shi gogan bai je ko ina ba ya na zaune a falo ta iso.

Tun da suka shiga Waki ba'a ?ara jin Wuriyar suba sai da aka kira sallar azahar sannan A.m ya yi wanka ya fito yayin da Zainab take biye a bayan sa don ta fito ta ba ma cikinta ha??in sa.

Binta da take jiran fito ba ta jima da jin fitowarta ba lokacin ta na waya ta fito da gudu ta ruga zuwa waje sai ta dawo ta kalli Zainab ta ?ara rugawa waje,tun Zainab ba ta damu ba sai ta Wan firgita tare da daka mata tsawa amma ba ta dai na ba ?arshe fashewa da kuka ta yi ta kama suratai.

Zainab da ta matsa ne sa da ita ta na faWin."Na shiga uku ke Juwairiya fito ki ga abin da take yi dama Anty Fati ta san ba ta da hankali ta kawo min ita?"

Ko da ta fito ta ga halin da take ciki sai hankalinta ya tashi matu?a yayin da tsoro ya shigeta gani take kamar ta yi hakan ne don ta tona asirin su.

"Gida za ni amai da ni gida a kwai dokin da nake hawa ni Sarkin ljanu a can in kuma yau ba hau ba duk saina yi maganin ku."

Ta faWa da tsamin murya ta na girgiza jikinta kamar ta na da aljanun da gaske.
" Na shiga uku kin ji mai take ce wa?"
Ta ce da Juwairiya da ta tsaya ta na mamakinta yayin da tausayinta ya cika ranta don ta san ta yi hakan ne don ta koma gida ita ba ta san A.m ya tsoratar da ita bayan wannan.

Kama ta yi ganin ta na jijjiga sai hawaye ya wanke mata fuska.

Zainab da ba ta taSa ganin wai mai aljanu ba sai ta tsorata ainun take ta kira Anty Fati jikinta na Sari ta sanar mata halin da Binta take ciki nan take ta ce bari ta turo direba da mai aikinta su taho da ita don sam iyayen ta ba su yi mata bayani ba.

Zainab ta tsorata sosai a ranta Allah Allah take direban Anty fati ya iso,abincin da take ci kasa ci ta yi ta tsaya ta na kallon ikon Allah yayin da jikinta ke Sari.

Suna cikin wannan halin ya shigo da sauri ta ?arasa gun shi ta yi masa bayani.

Ya kalli Binta da take kaWa kai kamar wata ?adangaruwa ta na zare ido,sai hakan ya so ya bashi dariya amma ya cije.

Wata uwar tsawa ya daka mata ganin ta gan shi sai ta razana kamar za ta gudu don Allah ya saka mata matu?ar tsoron shi.
?an natsuwa ta yi amma ba ta daina zare ido ba ita a dole ga mai aljanu.

A.m ya kalleta sai ya kauda kansa tare da taSe baki ya ce da Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta na kallon Binta.

" Maganin ki kenan da shegen kwashe-kwashen ki ta yi maza ya bar gidan nan ai ga yi nan kin je kin jawo ma kan ki mai almatsutsai."

Ya yi maza ya haye sama ya na dariyar yadda Binta take yi sai ka ce wata ?adangaruwa,saboda in ya tsaya dariya zai kubce masa.

Direba na zuwa Zainab ta saka aka kwashe kayanta tare da yi mata ihisani aka wuce da ita.

Ta na shiga Waki kuka ta fashe da shi na tausayin Binta haka kawai ya yi mata sanadin rabuwa da aikin ta bayan ya san ita marainiyace an ya ya kyauta kuwa.

Ta na kallon shi akan mutum wanda ya fiye son kan sa bai damu ba in dai zai faranta ma kansa da masoyiyar sa bai damu don ya cutar da kowa ba.

Don haka ko wayar da yake yi da ita in ya fita duk lokacin da Zainab take nan ta ?i daga ?arshe kashe wayar ta yi saboda haushin sa da take ji matu?ar gaske,don ya faye son kan sa akan komai.

Zainab ba ta ha?ura da neman mai aiki ba don har ta yi maganar a kawo mata wata.

Makarantar da ta fara sai hakan ya yi maata daWi sosai ikon Allah kenan duk da ta cire rai sai gashi Allah ya saka ta na da rabon yi.Abin da iyayen gidan ta suka zaSa mata ya sa ta ?ara yadda da cewar nufin su rayuwarta ba ta da wani amfani sai dai don ta yi musu hidima saboda girki suka zaSa mata,ita ta na ganin wani kalar girki ne ba ta iya ba,amma kuma da ta fara karatu sai ta raina kanta don gani ta yi kamar da can ba ta iya komai ba.

Ganin hakan sai ya dage damtse burinta ta iya girki ta yadda za ta siye zuciyar A.m,da take jin kamar ana mata wahayin son shi.

Duk da cewa makarantar sau uku take fita a sati amma ta na jin daWin karatun,sosai fiye da komai ba kamar da da ita kaWai take rayuwarta in dai matar gidan ta na nan.

Juwairiya ta yi ?awa Waya a makaranta wacce suka sha?u sosai duk da ba su daWe ba,sai dai ita matar aure ce har da yaranta biyu.

Suna matu?ar shiri sosai komai ma su tare suke yi ga halin su ya zo Waya ba ruwan su da hayaniya,musamman ita da take kullum cikin bege da ?aunar masoyin ta.

Kimanini wata uku da fara karatun Juwairiya wanda Zainab ta Wauko ?an aiki har guda uku sai A.m ya yi tsalle ya kawo ?auli da ba'adi.

Ganin haka sai ta kori Baba in da aka kawo mata mai jini a jika ta na koya mata girkin amma ba ta kwana don ta na da miji sai dai tun safe in ta zo sai magariba take komawa gida.

Ranar wata Juma'a Juwairiya ta tashi da ciwon kai mai zafi da zazzaSi ko tashi ta yi sallah ta kasa ga wani irin sanyi da yake shiga cikin ?ashin jikinta ya na nu?ur?usanta.

Abin takaici gashi suna da test don ana gabda yi masu jarrabawa.

Ganin ba zata iya zuwa ba gashi matar gidan ba ta nan kuma yau A.m zai dawo daga tafiyar da ya yi,wayarta ta Wauka tare da duba numbar ta kiran numbar Hauwa Tukur amma wayar ba ta shiga ba sai ta yi tsaki ta jefar da wayar ta kwanta.

Ta na kwance jikinta na ?ara zafi sosai kamar wuta misalin tara sai ga kiran Hauwa Tukur ya shigo,da ?yar ta janyo wayar da ke kusa da ita ta kanga a kunninta ta na nishi a wahalce.
"Hello Juwairiya ba za ki zo makaranta ba ne lafiya kin san muna da test ga shi Malam D.d ba shi da mutunci."Hauwa Tukur ta faWa a ranta ta na tunanin mai ya hanata zuwa,kasancewar ba ta wasa da karatu.

" Wallahi ba na jin daWi ne kin san sai da lafiya ake komai.Don Allah ki yi min test Win in zai yi wu."Ta ba ta amsa ta na kyarmar jiki.

Bayan ta yi mata sallama tare da mata al?awarin in dai ya yadda za ta yi mata ta kashe wayar ta koma ta kwanta.

Sai misalin shidda na yamma A.m ya shigo babu abin da ta yi masa na abinci.
Ganin halin da take ciki ya ruWe sosai kamar zai yi hauka a tunanin sa ciki ta samu,don haka jiki na rawa ya Waga waya ya kira likita ya zo ya duba ta.

Juwairiya ta ji hankalinta ya yi ?ololuwar tashi jin ya kira likita ita yadda take jin ciwon gani take kamar ciki ne.

Kawai sai ta ji hawaye ya fara sauka a ?uncinta don ta san lokacin rabuwar su ya yi daga ranar za su fara irga kwanaki.

Bayan likita ya zo ya yi mata gwaje-gwaje ya sa ta yi fitsari ta kawo masa.

A.m da ya yi zugum duk ya ?osa ya ji abin da likitar zai faWa,ya na ta addu'ar Allah ya sa likita ya yi mishi kyakykywan albishir.
"Ga wannan maganin za ka siyo maleria ce ke damunta in sha Allahu tasha magani za ta warke."

Hankalin sa ne ya tashi matu?a kawai sai ya ji hawaye na son ya zubo a ?uncin sa yayin da zuciyar sa ta karye da tunanin zai samu Wa.

Jikin sa a sanyaye ya karSi takaddar ya fice tare da likitan don ya siyo magani ko kallon ta da take zaune bai yi ba.

Wani wawan ajiyar zuciya ta saki wani irin sanyi ya ziyarce ta jin ba ciki ta samu ba.

A ?alla sai da ta yi kwana uku sannan ta warke sarai ta shirya ta tafi makaranta.

Suna zaune da Hauwa Tukur ba yan sun fito daga lakca Hauwa Tukur da hankalinta yake kan danna wayarta ta kalle ta da ta zuba uban tagumi ta yi nisa gurin karanta wasi?ar jaki.

"Yawan tunani ba shi da amfani ga lafiya kuma ban ga dalilin da zai saka ki zo makaranta ki zuba uban tagumi,ba yan kin baro gwarzon ki a gida nifa da kika ce baki da lafiya na Wauka ciki ne da ke."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta zare idanunta ta na kallonta.
"Subuhanallahi ciki kuma ni fa ba matar aure ba ce."

Ta faWa tare da gwalalo idanu jin abin da ta faWa yayin da take mamakin mai ya saka ta faWi haka.

Sakin dariya mai sauti ta yi ta Wauki lemun robar da Juwairiya ke sha ta zu?a tare da kwashewa da dariya.

"To don Allah meye na tsorata haka sai ka ce na ce kin yi kisa."

Ta faWa ta na mamakin yadda ta razana haka saboda ta ha?i?ance ma kanta ita matar aure ce,sai dai in ba ta son ta ga ya mata amma ko wa ya kalle ta ya san ta na da aure.

"Haba Juwairiya ko wane mutum ya kalle ki ya san kina da aure kin san a kwai matan da dole a gane matan aure,duba ga yanayin jikinta ki kalle kanki kema kin san bakya son ki gaya mini ne,to ki mai da wu?ar ni ban ce zan gan shi ba bare ki yi tunanin ko zan bashi ?anwata ne."

Ta ce da tsigar wasa saboda ta na son ta kwantar da hankalinta ganin yadda ta birkice lokaci guda.

Jin abin da ta faWa sai hankalinta ya tashi sosai duk da gargaWin da zuciyarta take mata na kar ta faWa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login