Showing 54001 words to 57000 words out of 143803 words

Chapter 19 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4715

tsawa ya fargar da ita halin da take cikin da sauri ta ruga da gudu,ta shige Wakinta har ta na bugewa da bango ?um!Amma ba ta kula ba don tsoron Zainab take yi sosai a ranta.

Ta na shiga cikin Wakinta ta fasa kuka sai kuma ta toshe bakinta tuna ko a ina take daga ?arshe toleit ta shige, ta kulle ta ?ara sakin kuka ta na buga kanta a bango amma ba ta kula ba ko kaWan.

" Na shiga uku a haka zan rayu a gidan nan? Na tabbata zuciyata ta kusan kamuwa da hawan jini!Allah na ro?e ka ka yafe min laifin da na yi maka ka haWa ni da A.m wanda da ma burin sa ya kawo ni gidan sa kishin sa ya yi ajalina!"

TO FA JUWAIRIYA AN YA DAI? GARA DAI KI TSAYA A MATSAYIN KI KISAN KE FA AUREN GWANGILA CE AKAN KI AMMA BA MATAR SO BA.INA JIRAN COMMENT TSAKANIN FANS ?IN ZAINAB DA JUWAIRIYA.







TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO


?UBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ?IN KU YA NA SAKA NI NISHA?I.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi noma sha shidda.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.






*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 18*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM





Tun daga wannan ranar Juwairiya ba ta ?ara saka shi a idonta ba wanda hakan ya tabbatar mata da tafiya ya yi tafiya, ita ma kan ta mai gidan ba zama take ba tun safe in ta fita sai dare za ta dawo,ta kwashi abincin da Juwairiya ta dafa,wanda tun daga ranar farko ta yi amanna da abincinta mai shigen daWin tsiya,don ko A.m da ya ci ya yaba sosai ji ya yi abincinta ya yi kama da wanda yake ci a gidan iyayen sa.

Rashin zaman mutanen gidan haka ya ba Juwairiya damar sakewa a gidan kamar na ta ba ta da wani matsalar takura.

Juwairiya a Wan zaman da suka yi da Zainab ta gane ko ita wace ce mace mai son hutu da gata,ga shi ta tsani zaman gida ko da ace mijinta na nan ga ta da shegen son ?walama kullum ta na yawon siyo kayan daWi da ciye-ciye.


Juwairiya ta Wauki tsawon wata Waya a gidan a cikin wata Waya ta ?ara kyau da kuma irin mai da cimar da take yi,ita kanta in ta kalli kanta a madubi sai ta ?ara juyawa ta kalli kanta cikin jin daWin yadda ta sauya,wanda har take zolayar kanta da in ta je gida Mama ba za ta gane ta ba.

Juwairiya ba ta da son jiki ku san duk wani aikin gidan ta Wauke shi shi ya sa kullum gidan ya ke cikin tsananin tsafta da ?amshi, ita kan ta Zainab kullum yabawa take sai dai tsabar girman kanta ba ta taSa nunawa ba.

Aiki Waya da yake Sata ranta shi ne gyaran Wakin A.m wanda kullum ta shiga sai ta yi kuka sosai,musamman da Zainab komai ba ta Waukewa sai ita take gyarawa cikin kuka da zafin kishi.

Ganin yadda Juwairiya take da hankali da natsuwa ga shi mijinta ya yaba kuma har ya yi tafiya bai ce komai ba,sai Zainab ta Wan saki jiki da Juwairiya kaWan duk da ta san rabuwa za su yi saboda ta isa aure,don haka ta yanke shawarar za ta Wauko yarinya ta haWa ta da Juwairiya ta din ga koya mata girki da yadda take gyaran gidan,saboda ko ba?i ta yi sai sun ya ba gidanta.

Ta na tsaye a kicin ta na tunanin abin da za ta dafa sai ta ji Zainab ta ?wala mata kira,da sauri ta ruga kamar yadda ta bu?ata duk lokacin da ta yi kiran ta.

Ba tare da ta kalle ta ba ta na ri?e da jaka ta ci uwar gayu ta ce " Fi ta zan yi yau zauji ya na hanya don haka ina son ki shirya abinci masu daWi."Fita ta yi ba tare da ta ji mai ta ce ba.

Kwan biyu da dawowar shi da rana ta na shirya abinci a falon cikin sauri take son ta yi ta kammala kafin ya fito,wanda ta yanke shawarar haka ya dace ta din ga kauce mishi ?ila zuciyarta ta huta da raWaWin son da take mishi.

Ta na cikin shirya abinci kan dinning ta ji ?arar kiran waya ya shigo sai ta shiga dube-dube a tunanin ta wayar Zainab ce ta manta fa ita,don sam ba ta kula da A.m da yake bacci ta bayan ta akan doguwar kujera.

Sai dai jin ?arar wayar ya sa ta gane ba ta Zainab ba ce, wanda kuma haka ya ba ta damar fahimtar a kwai mutum a cikin falon.
Kiran wayar ya sa shi juyawa da nufin ya kashe wayar saboda a gajiye yake matu?a! Kwanan nan sam bai samu ya huta ba,ya laluba wayar sa da nufin ya janyo wayar ya kashe bai jita in da yake tsammani ba,tunawa ya yi da jifa da ita da ya yi lokacin da ya shigo cikin falon.

Sai ya buWe idanun sa a wahalce ya na waigen in da yake jin ?arar ta amma tsabar gajiya ya saka shi kasa motsa jikin sa ya Wauko wayar.

Ganin haka sai ta nufi in da wayar take ta na neman agaji ta Wauko masa tare da mi?a masa,yayin da idanunta suke cikin na sa kuma ta kasa Wauke ?wayar idanunta ga barin kallon sa.
Idanu suka zuba ma junan su na tsawon lokaci wanda hakan ya sa Juwairiya ta rasa natsuwarta,shi ya fara Wauke idanun sa ya lumshe su.

A hankali Juwairiya ta tako ta mi?a masa wayar da ta ?ara rurin neman agaji.

Idanun shi ya ?ara maida wa kanta ya na mata kallo ?asa-?asa ya na son ya gano halittarta,don shi zai iya rantsewa bai taSa yi mata kallon cikakke ya san ya take ba,shi dai ya san ya yaba da ita har ya ji zai iya aurenta matsayin matar da zai iya aure na kwangila ta haifa mishi yaro.

Wayar da ta mi?o masa ya kai hannun sa zai ?arSa ya haWa har da hannunta ya na ?are mata kallo tun daga sama har ?asa,da sauri Juwairiya ta janye hannun tare da fara tafiya a hankali da nufin tabar gurin don jin wani irin tsau da ta ji jikinta ya yi,yayin da take jin wani ?arin sa?o daga zuciyarsa ya na aika mata cikin zuciyarta.

" Juwairaah."

Ya kira sunanta ba tare da ya mi?e ba cak tsayawa ta yi ba tare da ta jiyo ba,haka shi ma ya na kwance ya na kallonta kusan tsawon minti biyu,sai ta jiyo gabanta ne ya buga ras!
Da sauri ta ruga zuwa Wakinta tare da faWawa kan gado ta saki gwauron numfashi idanunta ta rufe cikin wata irin murya ta ce."Allah na ro?e ka kasa na zama jaruma na gama kwangilata na bar gidan nan kamar yadda na saka ma raina."
Ta nisa tare da ?ara juyawa ta kuma ce wa." Haka kawai ka shigo cikin rayuwata ka hana zuciyata sukuni."

Idanunta ta buWe suka tsar?e a na A.m da yake tsaye a gefenta ya na jin abin da take faWi,ya kai hannu ya fi sau uku da nufin ya ri?e ta amma sai ya kai ma iska nushi don ya na ganin in ya taSa wata ?a mace bai yi wa Zainab halacci ba.

Ganin ta buWe ido sai ya ja baya ya haWe rai hakan sai ya Wan tsorata har sai da ta ja da baya ta na kallon shi don ba ta san ya shigo cikin Wakin ba.

" Ji nan Juwairaah! Ko kaWan kar ki saka a ranki zan iya rayuwa dake kin ga matata kuma iya Wan zaman ki a cikin gidan nan,kin ga irin tsananin son da nake mata don bai kamata sai na gaya miki zaki fahimta ba,don na faranta mata na aure ki don haka ki kiyaye duk wani abin da zai sa ki yaudari kan ki,don kin san haka ba mai yuwu wa ba ne sanin kan ki ne ruwa ba tsaran kwando ba ne?"

A hankali ta Waga mishi kai ganin ya tsare ta da ido ya na son ya ji amsar tambayar sa.
" Sannan kar ki Wauka ko na manta dalilin da ya saka na aure ki ne.".
Ya juyo ya na kallonta ya ce da ita." Wallahi na rasa yadda za' yi na fara Waukar ki a matsayin matata don ba mu dace ba,ni sai yanzu nake dana sanin da idona da ya rufe na yadda na aure ki,amma duk da hakan zan daure na aiwatar da shirina da zarar kin sami ciki na kai ki wani gurin ki haihu na karSi yarona mu shafe babin rayuwarmu."

Ya na kai nan ya fice ba tare da ya lura da kukan da take yi ba na ba?in cikin tsanar ta da ya yi,sai dai kuma daga ba ya ta dai na jin haushin kalaman da ya faWi saboda duk abin da ya faWa gaskiya ne,ita ma ta karSi auren sa ne saboda ta ta ceci ran mahaifiyarta da Wan'uwanta.

Washegari da safe Juwairiya na kwance hayaniyar masu gidan ya tashe su wanda ta kasa gane ko menene,amma ta tabbata ba lafiya ba jin yadda suke magana sama-sama musamman muryar Zainab wacce har kukanta ta ji.
Matu?ar tsoro ya kamata ji ta yi ta ?ara mugun tsoron A.m don ba ta san haka yake da tsiya ba.

Ta na zaune a Wakinta ta yi tsumu so take ta haWa abin karyawa amma ba zata iya fita ba jin yadda suke ta Waga murya kamar za su dambace.

Mamaki ya kama ta sosai wai masoya ne suke irin wannan faWar,ganin sun ?i yin shiru da sauri ta shige kicin ba tare da sun gan ta ba,ta fara Wora abinci jikinta na rawa gani take kamar a kanta faWan zai ?are.

Ta na shirya a binci a dinning ta ga A.m da ?atuwar troley Win sa ya na ja, ransa kamar an aiko masa da mala'kan mutuwa, ba tare da ya kalle ta ba ya fice daga gidan.

Ba'a jima ba sai ga Zainab da na ta jakar ta na waya bayan ta gama wayar ta kalli Juwairiya ta ce " Ke wai me sunan ki baki gaya min ba?Ko ki na jiran na tambayeki ?ila uwar ki zan ci da sunan."

A hankali Juwairiya ta furta." Juwairiya sunana."Yayin da hawaye suka fara turereniya a fuskarta.

Tsaki ta saki." ko ma mene ne ni tafiya zan yi kuma ?asar zan bari, ban ce kije ko ina ba kar a kwashi kayana akai gidan matsiyata,ki kula min da gidana duk abin da kike so ga waya ki kira ni in da matsala."

Jefa mata wayar ta yi a jikinta ta fice ba tare da ta yi tunanin za ta iya fashewa ba.

Tsananin mamaki ya kama Juwairiya yanzu ne ta gane musabbabin faWar su.Da sauri ta le?a ta windo don idanunta su fita da shakkun kayan da ta saka za ta ?etare wata ?asa a matsayin ta na matar aure.

Haka ta wuni sukuku daga kallo sai kwanciya tunna ba masu gidan da za ta yi musu girki.Da daddare sai ta kasa bacci saboda ita kaWai ne sai masu gadi,Baba in ta gama ayyukanta gida take tafiya saboda ba ta da nisa sosai da gidan.

Kasa bacci ta yi ta na ta juye-juye girman gidan yake matu?ar tsorata ta, sai take ganin kamar wani zai shigo ga ihun karnikan gidan da suka hana kunninta sa?at!

Da ga ?arshe ma tashi ta yi ta Wauro alwala ta yi sallah sannan ta Wauki alkur'ani ta na karatun suratul Ali imran don ta samu ta yi bacci.

A ?alla mutane gidan sai da suka yi sati biyu ba su dawo ba.A.m ya fara dawowa ranar talata da rana dama tun da safe Zainab ta kira Juwairiya ta gaya mata zai dawo ,don haka ta shirya abinci wanda Zainab ta saka direba ya siyo duk kayan bu?ata na girki.

Misalin biyu da rabi ya shigo da jakar shi rataye a kafaWar sa,sai dai kamar mahaukaci ya shigo saboda zargin sa da yake na Zainab ta yi tafiya zuwa Dubai saro kaya duk da ya hana ta.
Duk da cewa ta ji shigowar shi sai ba ta fita ba ta yi zaman ta a Waki ta na jan carbi,domin ta sama ma kanta natsuwa.

" Ina Zainab?"

Muryar sa ta ji lokacin da ya banko ?ofa ya shigo da sauri ta matsa ganin kamar zai kai mata duka lokacin da yake tambayarta.

Ba ta ba shi amsa ba amma yanayin da take kallon sa ya tabbatar masa da Zainab ta tafi duk da gargaWin ta da ya yi,cikin Sacin rai ya lailayo ashar zai yi ko me ya tuna sai ya fasa ya fita cikin Wakin da sauri.

Juwairiya da sauri ta bi bayan sa saboda tashin hankalin da ta ga ya shiga,abincin da ta girka masa ya yi jifa da kwanonin da suke jere a dinning Win,ya zaro wayar sa ya kira ta sai dai har ta gama ringing ba ta Wauka ba.

Jifa ya yi da wayar ta faWi a kan tayas ta fashe ya dun?ule hannun sa guri Waya ya furta." Zainab ki na son sa min hawan jini sai dai wannan karan ba zan Wauki wannan iskancin ba,ina mijin ki ki tsallake ki tafi wata ?asa hakan ba zai yiwu ba.

Idanun Juwairiya suka kawo ruwa sai hawaye ganin ita kuma haka Allah ya ?addara rayuwar ta su dun ga sauke fushin su akan ta.

" Ke!"

Ya daka mata tsawar da ya firgita ta sannan ya ci gaba da magana da ce wa." Wallahi yanzu jikin ki zai gaya miki dukan ki na yi zaki saka min kuka bayan na gaya miki na tsani kuka a rayuwata,maza fice ki ba ni guri sannan ki ?ara min wani abincin.

Hakan ya ?ara saka ta sakin wani kukan tuna yadda ta sha wahalar girkin ya zubar kuma yake bu?atar ta ?ara yi masa.
Da sauri ta wuce kicin ta bar shi a falon ya kai gwauro ya kai mari da ga ?arshe wayar sa ya Wauka da nufin ya kira A.k,sai dai kuma ya ga aika-aikar da ya yi tsaki ya yi da nufi Waki don ya Wauko wata.

Bai jima ba ya fito bayan ya yi wanka ya canza kaya ko kallon abincin da ta girka bai yi ba ya fice daga gidan.

A haka suke ta zama na rashin daWi duk da A.m na bu?atar ya kawo ?arshen zamanta a gidan amma ya kasa,haka dai yau ya daure da nufin zai ya?i zuciyar sa don ta bar mishi gidan sa saboda ba ya son ganin ta a ciki.

Da misalin biyar da rabi ya dawo gida Juwairiya na falo ta na kallo da ?aton hijabin ta,ya na hango ta ya tsaki wawan tsa?i saboda shi haushin hijaban da take sawa yake yi bayan ta san ko shi wanene a gurin ta.

" Wawiya ?azamiya a haka yadda kike Soye jikin ki ko uban me take Soyewa shi bai ga abin sha'awa a jikin ta ba."

Ganin sa ya sa ta mi?e da sauri za ta shige cikin Wakin ta.


"Ke."
Tsayawa ta yi ba tare da ta kalle shi ba don ta san wani wula?ancin zai yi mata.
Hararar ta ya yi ya zauna akan kujera tare da Waukar remote ya canza tasha,sannan ya kalle ta ya ce " Gidan uban wa za ki saboda dodo ya dawo ko?Wai haka kika ga matan aure suna rayuwa a gidan mazajen su kullum cikin hijabi ke sam baki da wayewa ne?"

Juwairiya ta yi sororo ta na kallon shi jin wani sabon salon da ya fito da shi,amma ba ta ce masa komai ba sai kallon shi da take tamkar ba?o a gare ta.

" Maza ki je ki kawo min abinci."

Ya ce ganin ta kafe shi da ido ba ta san shi ma ransa a Sace yake maganar ba saboda tsanar ta da yake ji kuma wai ta na matsayin matar sa.

Juwairiya ta so ta bi umurni n shi ta cire hijabin sai dai ina sam ba za ta iya ba,don tsananin kunyar shi take da ke,don haka ta ?i cire hijabin ta Wauko abincin ta na ije mishi ta ruga zuwa Waki.
Bayan ya ci abinci ya na zaune a falon har aka kira magariba ya yi sallah bai dawo ba sai da aka kira isha'i,sannan ya dawo gida ya rufe gidan duk da ran sa a Sace yake akan Zainab kuma ya rantse in ta dawo sai ta ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login