Showing 51001 words to 54000 words out of 143803 words

Chapter 18 - SAKACINA KO HALIN MAZA COMPLETE

14 Jul 2025

4744

ta sannan ta dawo sallah ta yi suka kama hanya.

Wani irin faWuwar gaba take yi har sai da ta dafe ?irjinta.Kasancewar a kwai tazara sosai da gidan Atine sai da suka hau nafe.

A lokacin da suka iso ?ofar gidan da Juwairiya ta saka a ranta na A.m ne hankalinta ya yi matu?ar tashi matu?a gaya.Kawai sai ta ji ?asa ba za ta iya Waukar ta ba ta sani A.m suna da kuWi amma ko kaWan ba ta taSa tunanin haka gidan sa yake ba.

" Dole ka ce baka sona kuma ba zaka taSa sona ba saboda ba mu dace ba ni kai na sheda ne."

Ta furta cikin karayar zuci don ta san ya fi ?arfinta na har abada.Gaskiya fasalta gidan sa abu ne da zai Wau lokaci saboda gida ne mai matu?ar girma, da tsari ga shukoki masu kyau waWanda suka ?ara ?awata gidan,don haka mai karatu na bar maka aikin tsara fasalta iya tsaruwan gidan,A.m a hannun ka don in na ce zan yi zan Wauki lokaci ni dai na yi wa gidan suna da aljarnar duniya.

Lokacin da suka shiga cikin falon Juwairiya ku san neman numfashinta ta yi ta rasa, don barazanar shiWewa yake yi saboda tsaruwar falon da ke Wauke da ku san set huWu na kujeru mabambanta.

Duk lokacin da ta ?ara taku a cikin falon zuciyarta karaya take da son A.m da ya shige zuciyarta saboda ta ha?i?ance ma kanta da yaudarar kanta take yi A.m babu abin da zai yi da ita.

A ?asar kafet Win dake zagaye a tayas Win da ya sha guga ya na ta ?yalli da Waukar ido ta zauna tare da rintse idanunta,hakan ta ji ba ta son idanuwarta su yi tozali da matar A.m don ta san zuciyarta za ta buga.

Atine ta zaro wayar ta ta yi kiranta sai dai cikin takaici ta ije wayar ta kalli Juwairiya ta ce." Ba ta dawo aiki ba amma ta ce mi jira ta za ta duba patient ta dawo."

Sai Juwairiya ta sauke idanunta daga kallon Atine saboda kiran sunan ta da ta yi,ta ci gaba da kallon ?asa yayin da zuciyarta yake bugawa tamkar za ta fito.

Kusan waya biyu suka shafe suna zaune a falon sai kowa shiru jefi-jefi Atine take sakin tsaki,amma Juwairiya iya tsawon lokacin ko tari ba ta yi ba sai sautin bugun zuciyarta da yake ta ?ara tsanantuwa.

?was!?was!!?was!!! Suka ji sautin takalmi wanda Juwairiya ta sada?ar da matar gidan ce ta dawo,bayan iya tsawon lokacin da ta Wauka ta shanya su zaman jiran ta kamar wasu dussa.

Bugun takalmin Zainab ya na tafiya tare da bugun zuciyar Juwairiya da take jin tamkar za ta fito,ta rintse idanunta ta na burin a ce ba Zainab Win ba ne take ?o?arin shigowa,domin tsoro ya bayyana a fuskarta sai take ganin kamar za ta gane dalilin shigowar ta gidan.

Koda ta shigo waya take yi zama ta yi ba tare da ta ce musu komai ba ta ci gaba da wayar ta.

Juwairiya ta kasa Wago idanunta ta ga matar mijinta na wucin gadi wanda take cikin zuciyar sa yake fifita ta fiye da komai har ya zaSi ya cutar da rayuwarta duk akan ya farnta mata.

Amma idanuwanta sun kasa haWa ido da ita hasalima ko Wagowa ba ta yi ba, duk da ta fahimci ta gama wayar da take yi bayan ta Wauki rabin awa.

" Am Atine na Sata miki lokaci ko?"

Tambayar da ta yi mata kenan ta na kallon matar da ta kusa jika da ita a yatsine.
" Ba komai Hajiya dama me aikin ne da muka yi magana da megidan ki na kawo miki."Ta ce mata ta na kallonta.
" Ok."

Abin da tace kenan ta janyo wayarta ta kunna data yayin da tsa?wanni suke ta shigowa ta na duba wayar har na tsawon lokaci,daga bisani ta kashe ta kalle su duka daidai lokacin da Juwairiya ta yi sa'ar ya?ar idanunta, na tsoron haWa ido da ita da suke ta kalle ta, don ta ga wannan mace mai ji da kanta da wula?an ta mutane.

Karab ida???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nun su duka suka haWu da juna Juwairiya da ?yar ta yi nasarar da?ile gangar jikinta da yake shirin tashi da zura da gudu ganin kalar matar da A.m yake aure.
" An ya ?ar Nigeriya ce?"

Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki domin yanayin ta da kyanta surar ta gabaki Waya ya tsorata ta,saboda hasken ta har wani kashe ido yake yi sosai da ta yi duba ga kalar fatar jikinta sai ta ga ta yi ba?a wuluk kamar gawayi,duk da ya ba kyan fatarta da ?awayenta suke yi.

Zainab kuwa wani irin tsanar ta ya shiga ranta haka kawai sai ta ji ba ta kwanta mata ba,ba wai kuma kyan da ta gani ba ne ya tsorata ta a'a ita sheda ne akan A.m ko ?an mata larabawa za ta kawo mishi ba zai yi dubi garesu ba, duba ga yadda ta sha wahala kafin ya amince da ita sannan tun da su kai aure ba ta taSa jin ya yi maganar wata ko wata ta kira shi ba.

Amma sam Juwairiya ba ta yi mata ba saboda daga ganin ta za ta yi munafunci ganin yadda take du?ar da kanta ?asa-?asa.
" Atine an ya wannan ?arinyar kina ganin ta yi?Kin san A.m a kwai shi da ?yan?yani ji yanayin shigar ta da wani zumbulelen hijabi kin san ya na da tsafta, kar ta zo ta na ma na girki ya na shiga sannan wallahi zubin ta bai yi min ba don ni na daina Waukar ?an aiki gidahumai ?auyawa,bai gaya miki Wakin sa da komai na shi ita za ta din ga gyarawa ba?A can zo wata kawai."

Juwairiya ta yi ?asa da kanta jin abin da ta faWa duk da ranta ya Sace,amma ta yi tunanin fiye da hakan a gurin ta saboda ta karance ta tsaf mace ce mai Wagawa da nuna ta isa,musamman ga talakawa ?as?antu irin ta.

Sai kuma ta ji daWin abin da ta ce ranta ya yi fari ko banza ba za ta zauna agidan wannan mai kama da canis ba sai ya zo ya san yadda zai yi da ita,ai dama abin da ya shirya a yi mata kenan shi ya sa ya aure ta ya kawo ta kuma ita ta sai ma kanta don in da ?waWayi a kwai wula?anci!

Atine ta ji jikinta ya yi sanyi sosai har ta fara tunanin in da za ta samu kuWin A.m ta mayar masa don ya na ba ta ta kai ma mai kujeru akan bikin ?arta marainiya wanda mijinta ya mutu ya bar mata.

Sai ta ji kamar ta ce ai mijin ta ne ma ya bu?aci ta kawo ta,amma da ta yi tunanin ba ta san dalilin da ya sa ka shi ya bu?aci hakan ba sai ta kama bakinta ta guntse ta ce." Ai Hajiya Juwairiya a kwai aiki da tsafta sosai ta yi aiki da dama shi ya sa na kawo ta,kuma za ki ya ba sosai sai kin gode min,amma ki gwada ta in ba ta yi miki ba sai a kawo wata.Kin sai an gwada akan san na ?warai.

" In ko haka ne ta na bu?atar gyara don sai na canza mata tufafi ba za din ga mana girki da shi ba,ni ban san da?i?anci da rashin wayewa."

Ta ce ta na kallon Atine da ta yi hamdala a ranta jin ta amince da ita,sai kuma ta kalli Juwairiya ta na mata kallon tsaf irin na ciki da waje har mutum ya gano munin ka.

" Ina yini"

Juwairiya ta ce mata ganin ta na mata kallon ke ba kya gaisuwa ne.

?auke idanunta ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk da ta tabbata ta ji gaisuwar da ta yi mata.
Sai ta mi?e ta kalli Atine ta ce."Wash na gaji ba ri na shiga ciki."Har ta fara tafiya sai ta tsaya.
" Ina fatan Atine ta yi miki bayanin aikin da za ki din ga yi a gidan nan? Ina da da tsohuwa da take share-share da ?an abin da ba'a rasa ba.So ke aikin ki kula da Wakina da na mijina da wankin underwears Win mu da girki.Kasancewar ba zama nake ba don yanzu waje zan fara fita na baki amanar gidana, da mijina duk sanda ba na nan ki rin?a kula da abincin sa ruwan wankan shi kayan sawan shi da wanda ko ina nan ke zaki kula da wannan."

Ta Wan numfasa ta Wora da ce wa " Game da kayan sawar shi irin wanda yake so ina fatan ke ba da?i?iya ba ce kuma ba' a yi asaran tara ba na yi mishi time table a Wakin sa na kayan da yake saka wa sai ki din ga dubawa ki na cire masa."

Wani iri Juwairiya ta kanta ya yi mata take wani irin zafin kishin mijinta A.m ya taso ya mamaye zuciyarta,har ya hana ta jin abin da Zainab take ce wa sai kuma tausayin sa ya kamata matu?a jin irin ballagar mace da yake aure.

Ta ?ara rintse idanunta ta na jin kishin iya adadin masu aikin da Zainab ta yi waWan da suka gama kallon mata miji,kuma a haka yake i?irarin ya na sonta lallai ta yadda so halitta ce kuma makaho ne.

" Ki na ji na ina magana kin yi banza da ni!"

Zainab ta daka mata tsawa ganin ta tafi duniyar tunani.

" Yi ha?uri ina sauraren ki ne."

To ba na son shashanci in ina magana du?ar da kunnin ki saitina za ki yi kuma duk na yi magana ki Waga kanki."
Ta ce sannna ta ci gaba da tafiya ta na faWin." Atine ba ri na Wauko miki abu."

" Kut! Na shiga uku A.m ya san halin matar sa ya kawo ni cikin gidan nan."

Ta faWi ta na jinjina kanta tare da tunanin irin zaman da za su yi da ita .A jiyar zuciya ta saki mai ?arfi jin sakacin da Zainab ta yi da mijinta.

KuWi masu yawa ta mi?a ma Atine wacce ta sandare da jiranta,saboda har wanka ta yi ta saka kaya shara-shara wanda al'dar ta ce zama da irin wannan kayan a gida.

A lokacin Juwairiya ta gaji har ta fara gyangyaWi ga yunwa dake ta ?wa?wular cikinta.

" Kin ga na jima ban dawo ba ruwa na watsa ga shi ki yi ha?uri."

Ta ce da Atine sannan ta kalli Juwairiya ." Ke ki tashi ki fara aiki kuma na manta ban gaya miki ba! Ba na son raini da ?azanta."

Sai kuma ta ?wala ma Baba mai aikinta kira da gudu sai ga shi ta ?araso mari ta zabga mata.Banza da?i?iya ba na ce miki za'a yi sabuwar mai aiki ba? Da kika gan su sai ki fara nuna mata aikin gidan ko sun yi miki kama da irin ba?in da zan yi ne?"Ta tambayeta ta cikin zafin rai.

"Ki yi ha?uri Hajiya ai ba ki bani umurnin haka ba kuma..."

" Rufe min baki banza maza ki je ki nuna mata."

" Allah ya huci zuciyar ki."

Ta ce tare da kallon Juwairiya sannan ta ce ." Mu je na nuna miki aikin."

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye ta dafe ?uncinta don gani take kamar ita ta mara.Zainab ciki ta koma tare da Waukar wayarta ta yi kiran rabin ranta.
Tsananin tashin hankali Juwairiya ta shige shi ji ta yi tamkar ba za ta iya rayuwa a cikin gidan ba,a tare suka share hawaye da Baba suka kuma kalli juna.

" Ki yi ha?uri Baba haka matar gidan take miki?Gaskiya ba ta da mutunci a matsayin ki na wanda kika haife ta.Wai mai masu da shi suka Wauki talaka shi ba mutum ba ne don kawai ya na nema a ?ar?ashin wani sai wula?anci."

Baba ta share hawayenta ta kama hannun Juwairiya ta ce " Humh ba zaki gane ba ne!Hajiya Zainab ta wuce tunanin ki ina tausaya miki wallahi Allah ya sa kin iya girki."

Ta Wan ?ara matsowa kamar ta na tunanin Zainab za ta yi musu laSe ta ce." Ina gaya miki wacce ta kora ta kawo ki da ta yi abinci juye mata ta yi a jikinta,ta rufe ta da duka wai mijinta ya ce ba ta iya girki ba.Ni fa ban taSa ganin mutum irin maigidan nan ba,ya tsane mu sai dai shi baya duka."

Duk da Juwairiya ta san matsayinta a gidan amma sai da gaban ta ya faWi ras!Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Da Juwairiya suka shiga kicin kusan ruWewa ta yi kamar za tai hauka,irin dukiyar da aka narka da kayan na'ura,duk da ta yi aikatau gidan masu kuWi ta san yadda ake sarrafa na'ura amma a ranar yar ?auye ta dawo.


Abinci mai rai da lafiya Juwairiya ta shirya sannan ta shiga Wakin da aka ba ta wanda Zainab ta yi mata umurnin duk ta yi girki ta yi wanka.

Juwairiya ta da fari kasa amfani da kayan bayin ta yi sai daga baya a hankali ta fara gane yadda ake amfani da shi bayam ta Sata lokaci ta na ?auyanci.


Juwairiya ta yi mamakin irin kayan da ta jibga mata da sunan ta dun ga amfani da shi,haka dai ta shirya ta na ta tunani barkatai a ranta yayin da kewar su Mama ya kamata, matu?a har ta ji hawaye na zuba a ?uncinta.

Juwairiya na zaune a Wakin da ya zama mallakinta bayan ta idar da salla sai kuma ta mi?e da sauri jin kamar Zainab na kiran ta.

Ta na ba?in ?ofar fita daga Wakin suka yi kicibis da ita za ta shigo." Ke kurma ne ina kira kin yi banza dani."

Ta faWa cikin Waga murya." Ki yi ha?uri ban ji ki ba ne."
Ta ce ta na kallonta amma kuma a tsorace take saboda kar ta kai mata mari.Tsaki ta yi." Maza ki je ki shirya dinning za mu ci abinci mijina yanzu zai shigo.Kuma ki cire wannan ?azamin hijabin na ki don na san ina ya gani ba zai iya cin abincin ba."

Juwairiya ta ji jikinta ya yi sanyi jin umurnin da ta ba ta domin ba za ta iya fita a haka ba,amma sai ba ta ce komai ba ta saSule hijabin ta koma ciki.

Hankalinta ya kwanta da ta tuna a kayanta a kwai hijabi wanda bai kai wancan tsawo ba,da sauri ta Wauko ta saka a jikinta bayan ta saka turare kamar yadda ta murceta.

Juwairiya na gyara dinning ta ji dirin mota alamun an shigo da mota,gaban ta ne ya faWi ras! Don jikinta ya ba ta masoyin ta ne ya dawo haka kawai sai ta ji gaban ta na faWi.


Da sauri take shirya dinnnig Win saboda ta gama ta kauce ma ganin sa,amma sai kafin ta gama ya riga ya shigo ya na takun sa da sarsarfa irin na ingarmar namiji mai jini a jika.

Shigowar sa ya yi daidai da fitowar Zainab daga cikin Wakinta cikin wata irin shiga ta alfarma,amma fa a gurin sa wanda kuma Juwairiya ta ga bai kamata ta fito da irin wannan shigar ba,sanin a kwai ta a cikin gidan don har tafi shigar Wazu rashin kyan tsari.

Da gudu ta faWa jikin sa ta na dariya cikin farin ciki.
Shigowar sa ya sa Juwairiya ta gane ashe tafiya ya yi saboda direban sa da yake janye da troley Win sa guda biyu kuma masu girma.

Duka suke dariya sannan suka faWa kan kujera suna bayyana iya kewar da sukai ma junan su.

A hankali A.m ya zura ma Juwairiya ido shi har ya manta sun yi da Atine yau za ta kawo ta.Ya Wauke idanun sa da sauri ganin Zainab ta bi in da yake kallo.

" Hubbina sabuwar mai aikin da Atine ta kawo mana ne,Allah ya sa ta yi maka sai dai na ganta kamar gidahuma ce ko ina yawo da hijabi,amma haka zamu yi ha?uri da ita don gaskiya na gaji da Waukar masu aiki."

A hankali Juwairiya ta Wago idanunta ta Wara su akan A.m duk da ba ta son hakan,amma ta na son ta ji mai zai ce mata.

Ga mamakinta sai ta ga ya taSe bakin sa ya kalle ta kamar ya ga kashi ya ce." Uhm na gan ta sai dai ki yi mata magana ta kiyaye sosai in kuma ta?i dole ki canza wata don kin san halina."Ya ce a ta?aice sai kuma ya canza maganar ya na kallon Zainab ya ce." Na yi missing Win ki babyna sati Waya da na yi kamar na yi shekara,yanzu haka ma ban gama abin da na ke yi ba na baro A.k a can na dawo na ga kyakykyawar fuskar ki."

Ya faWa kamar zai yi mata kuka yayin da idanunsa suka bayyana hakan ga Zainab da take kallon sa da wani irin murmushi ta na kashe masa ido.

" Allah ko zauji ka san ni da kai kamar hanta da jini ne Wazu ina ma wani operation, ka san Allah saura kaWan na yanka sa ba in da ya kamata ba kuma fa kai na ke tunani."

Dariya suka yi duka ya ri?e hannunta ya ce." Na san za ki yi fiye da hakan akai na amma ki kula rai ya wuce wasa."


" Ke banza wawiya!Ba ki da tarbiya ko?Ko baki ko ya a gida ba in ma'aurata suna magana ki ba su wuri maza wuce daga nan stupid kawai!"

Juwairiya da ta yi mutuwar tsaye tun lokacin da A.m ya shige ta nemi hankalinta ta rasa ji take kamar ta ruga da gudu ta faWa jikinsa.
Gabaki Waya ta manta a wace duniyar take wasu irin zafafan hawaye ta ji ya wanke mata fuska, saboda tsananin son da take masa wani irin kishin sa ya tokare mata ma?ogaronta, har ta ji ta na son ta yi aman sa don ta na jin Wacin sa ya na hawowa bakinta.

Muryar Zainab da ta daka mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login