Showing 39001 words to 42000 words out of 86898 words

Chapter 14 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

ya tada miki hankali kin san dai Abba'n ku bazai jure jin ki cikin matsala ba,

idan ni na jure shi bazai jure ba."

Numfashi Aunty ta sauke ta ce

"Umma ni damuwar mutanen gidan mu baya gabana yanzu, dan nagama gane cewa j

ahilci ke damun su, ina da ilimi na bazan zauna biyewa jahilai wad'an da basu san abin da suke yi ba,

Hajja umma matsala ta yanzu d'aya Feeryal,

natab'a fad'a miki tun tana jaririya abubuwan da narika gani a tare da ita,

sai gashi a 'yan kwanakin nan ina k

uma ganin wasu sauye-sauye a gurin ta,

Hajja Umma ita kad'ai zakiji tana magana kuma bil'hakki da wani take, yanzun nan kamma tayi wani abinda ya shanye min ruwan kai,

wlh Hajja Umma ta dad'a jefani cikin kokonto daban-daban,

anya yarinyar nan ba miyagu

suke son kulla alaka da ita ba,

d'ayan biyu ko hakan ko kuma da gaske ita d'in ba mutum bace........!

Mommyn Twins ce

🌺🌺

*FEERYAL*

🌺🌺

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*_Littafin na kud'i ne 500 accoun

t no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S

✍

🏼

*

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & mot

ivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*

πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

πŸ…Ώ

️

11

Shiru Hajja Umma tayi tana sauraran bayanan da Aunty take kora mata,

na duk abinda ya faru a baya da kuma abin da ya faru da Mommy yanzu ba da jimawa ba.

Aunty tad'aura da fad'in

"Nakanji tsoro wani lokacin na tsinci kaina cikin fargaba, wlh Hajja Umma in

a son Feeryal bana son rabuwa da ita,

ni ko aljana ce ma ita ina son ta zan rayu da ita a haka,

abin da nake tsoro d'aya kada ta cutar da ni ko wad'an da nake tare da su, bana so na rabu da Feeryal, wlh ina son ta a haka."

Aunty ta karasa maganar cikin san

yin murya.

Hajja Umma ta jinjina kai sannan ta ce

"Yanzu ina Feeryal d'in?."

"Tana parlour tana ta kan wasa wai da kawayen ta, da ni bana ganin su, ni tsoro na ma d'aya kar ta faje da wasu tarika cutar da mutane."

d'an shiru Hajja Umma ta yi kana ta soma

magana.

"Akwai wani malami a can jahar Bauchi awani gari da ake kira Duguri,

Allah ya basa baiwar fahimtar irin wad'an nan matsalolin,

ki kaita can koma mene ne zakiji, in har ba mutum bace bama kafin ku isa zaki nime ta ki rasa, dan bazan mance ba, lokac

in jinyar Yayan ku da muka gama karad'e kasashe da dama bamu dace ba, a can gurun sa muka dace,

lokacin da mukaje wata mata tazo da kwatankwacin irin wannan matsalar sai dai ita haifar d'iyar tayi aka canza mata,

ya ce taje ta zo da yarinyar, 'yar tana goy

e a bayan ta a hanya ta b'ace, bata sani bama har sai da tazo zata kunceta ta shafa taji wayam babu komai a bayan ta,

ganin yadda hankalin ta ya tashi malamin yace ai dama ba 'yarta bace nasu ne ta koma gurin iyayenta,

shi da kansa yaje ya karb'o mata asa

lin d'iyarta a gurin su,

idan zaku tafi ki sanar mata da in da zakuje, in har Feeryal ba mutum bace baza ta soma dumfarar gabansa ba zata gudu, tun kafin ku isa,

zan bincika ko yana nan har yanzu dan shekarun da dama tun Yayan ku na d'an shekara uku."

Au

nty ta ce "Amma Hajja Umma ba dai irin mushrikai d'in nan ba ko? yanzu sai susa ka kauce hanya."

"Haba Fatima ni da kaina bazan kaiki in da zaki halaka ki rasa imanin ki ba,

kin san ba irin wannan tarbiyyar na baku ba, haka nima ba irin wacce iyayena suka

bani shi ba ke nan,

idan da yana shirka da tun zuwata ta farko bazan kara zuwa ba,

bare kuma har na tuna da shi a yanzu har nayi miki sha'awar zuwa gurin sa,

malami ne mai aiki da ilimin addini, ba irin masu fad'e-fad'e da karyace-karyacen nan ba,

zan bin

cika ayau d'in nan idan yana nan sai kubi jirgi kuje."

Aunty ta ce to. nan sukayi sallam.

A b'angaren Mommy kuwa, tana fita ta had'u da Ajeemal dasu Sahla suka kira sa.

da sauri ya tare ta yana fad'in

"Mommy lafiya? su Nabila sun ce min wai kin fad'i ki

na ihu."

"Biyo ni kawai Ajeemal kar ka tsaya anan da alama kaf yankin side d'in ta ta zagaye shi da kafin asiri."

kai ya girgiza shi sam baya son irin wad'an nan abubuwan da Mommy da Umma Karima suke yi,

baisan me ya kaita sashin Aunty'n ba da take maganar

wani asiri.

su komai sai sun dangantashi da asiri.

sam baya jin dad'in yadda iyayen nasa suke zama da abokiyar zamar tasu.

yabi bayanta.

Suna shiga parlour'n ta Mommy ta zube a kan carpet tana dudduba kafafunta, da d'azu take jin sa tamkar za'a finceke

su sufice daga ganganr jikinta.

"Kai Fatimah bakar munafuka ce, wannan zata iya kashe mutum da bakin asiri take aiki."

Fuska Ajeemal ya b'ata ya ce

"Mommy to me ya kaiki side d'in Aunty Mommy ku dai na yin haka fa."

wani uban harara ta buga masa.

"Rufa m

in baki dan ubanka me kasani a rayuwar duniyar, abin da yafi asiri ma in akwai Fatima zata iya, an tab'o uwar ka ai dole ka nuna b'acin rai, ai nasan ba banza ta barku ba,

dole ma na tashi tsaye,

kafin a fini karfi a kan 'ya'yana."

Bai kuma yin magana ba

yaja bakin sa ya yi shiru yana girgiza kai kawai.

a sawace ta ce

"Wuce kabani guri ai najima da sanin 'ya'yana mata ne kad'ai masu tausayi na, dama ciwon 'ya mace na d'iya mace ce, da kazo ka same ni cikin halin da nake ciki ma d'azu da asirinta ya rike n

i, da babu abin da zaka iya yi min ma acan sashin nata, sai dai in zanmutu ad'au gawata."

"Allah ya baki hakuri Mommy."

yafad'a yana nufar kofa ya fice abinsa.

Kamar yadda Hajja Umma ta fad'a, a ranar tasa a binciko mata labarin malamin da yake garin Dug

uri dake jahar Bauchi.

ta turowa Aunty cikakken adireshin sa har da lambar waya.

kana ta biyo bayan sakon da kira.

Aunty tana rike da waya tana saurarar karin bayanin da Hajja Umma take mata.

Hajja Umma ta d'aura da fad'in

"Idan kun d'au hanya ki ambata ma

ta inda zakuje da sunan wanda zakuje gurin sa,

sunan sa malam Buba Mani,

na sami labarin tun a wancan lokacin bayan jinyar da mukayi a gurin sa bada jimawa ba,

ya daina jinya da shigan irin wad'annan kasadar daya shafi junnu,

ko an je masa baya saurara, a

mma kuje ku gwada Allah zai wuce gaba"

"Har jikina ya yi sanyi kuma Hajja Umma, anya zai saurare mu?."

"Insha'allah mu dai gwada mu gani, ni ma nafi kyautata zaton 'yar nan mutum ce, sai dai su jinnu basu da kama,

sukan iya sajewa a cikin mu tamkar mu d'in

, surika yin komai irin namu, ku dai je muji,

in kuma ta koma gurin danginta a hanya to ai shike nan sauki ma ke nan."

jiki a sanyaye Aunty ta ce to.

Ko da Aunty ta sanarwa Daddy, da fari kamar bazai amince ba, amma dayaji ta ce Hajja Umma tabada yakinin

mutumin baya shirka sai ya aminta.

ya ce zaiyi musu bukin zuwa jibi sai subi jirgi su tafi, har da shi za'a tafi.

da kuma Baba Rabi ko bukatar wani hidima zai taso a can suna da mai yi musu.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan kuwa suka biyo jirgi daga Lag

os zuwa Bauchi.

bayan Daddy ya sanar wa aminin sa gwamnan jihar Bauchi, zai shigo garin sa.

suna sauka a airport, suka taras da motar zuwa d'aukarsu a cikin airport d'in.

motar da gwamnan jihar Bauchi aminin Daddy ya turo a d'auke su a kaisu masauki.

direc

t government house aka wuce da su.

a kyakkyawar masauki na alfarma aka sauke su,

bayan sun gaisa da mai girma gwannan jihar Bauchi, sukaci suka sha.

gwamna yaso su kwana kafin su wuce Duguri, Daddy ya ce kawai zasu wuce yau baya so su b'ata lokaci.

nan d

a nan aka shirya musu jagora zuwa garin Duguri, da motoci uku, biyu nasu d'aya na jami'an tsaro.

tun a mota a kan hanyarsu na zuwa Duguri Aunty tarika sanarwa Feeryal inda zasuje.

suna zaune a bayan mota su biyu Baba Rabi tana gaba a gefen mai zaman banza.

sai direba a mazaunin sa.

Daddy na d'ayan motar shi da deputy governor.

sai direbar dake jan su.

Aunty da tun d'azu hankalin ta ke kan Feeryal d'in tana ta son gano wani sauyi tattare da ita,

ta ce

"Feeryal kinsan ina zamuje?."

Feeryal dake tsaye kan sit

tana leka titi ta jikin window mota tana kallon wuraren da suke giftawa ta girgiza kai alamar a'a.

D'an numfashi Aunty ta sauke cikin yin kasa da murya ta in da direba ko Baba Rabi baza sujiba ta ce

"Zamuje gurin Malam Buba Mani ne, malami kuma mai maga

ni."

Feeryal ta b'ata fuska ta dawo jikin Aunty ta kwanta tana fad'in

"Ammie kice kar ya min allura, yabani magani kawai, zan sha bazanyi kuka ba, kar ya min allura."

tawani cuno baki tana dad'a shigewa jikin Aunty tana niman yin kuka.

Aunty dai shiru tay

i tana binta da kallo ya yin da kaunarta ke dad'a shigarta bata fata ace ta tafi ta barta,

ita dai fatan ta arabata da gane-ganen da take, taji ta gani zata iya zama da ita ko ba mutum d'in bace.

Jin mota ta tsaya yasa Aunty d'agowa sai gani tayi ashe dai

har sun iso, gasu a kofar wani d'an madai-daicin gida ginin laka.

Duk suka firfito daga cikin motocin,

inda Daddy da dipiti gwamna suka fito daga tasu motar.

cikin azama jami'an tsaron dake tare da su suka zagaye su sukayi wa gurin kawanya.

dattijan dake

zaune a gindin bishiyar kofar gidan.

duk suka mike cike da girmamawa suka shiga mika musu gaisuwa,

duk da basu san ko su d'in su waye bane, amma sun fahimci su d'in ba kananun mutane bane.

Daddy ya mimmika musu hannu duk suka gaisa,

suna mai mamakin gani

n sanyin hali irin nasa.

da gani ba sai an fad'a musu ba sun san cewa shi d'in bana wasa bane.

Dipiti gwamna da tun saukar su waya yake sai sannan ya sauke wayar, yad'aga musu hannu alamun gaisuwa yana fad'in

"Sannunku dai barkanku da war haka."

da sauri

d

uk suka amsa da "Barka dai ranka shidad'e, sannunku da zuwa."

shi kam sun gane shi mataimakin gwamnan jahar su, suna ganin sa a jikin posta.

"Yauwa godiya muke, am nan ne gidan malam Bubu Mani ko?."

cewar dipiti Gwamna yana nuna kofar gidan da suke.

suka

ce "Kwarai kuwa nan ne gidan ai yanzun nan ma yashiga ciki duk muna tare da shi a nan."

D'aya daga cikin mutanen cike da girmamawa ya ce da su Aunty

"Hajiya bismilla ku karasa ciki mutan gidan suna ciki."

kana yayi saurin d'auko d'aya daga cikin taburman

da suke zaune a kai mai hasken ciki ya shinfid'a wa su Daddy yana fad'in

"Bismilla ranku shidad'e ga gurin zama bari a kirawo sa."

Aunty na rike da hannun Feeryal Baba Rabi kuwa na rike mata da handbag d'in ta suka shiga gidan da sallama.

Inna Delu matar

malam Buba Mani, dake aiki a sakar gida ta amsa musu sallamar tana fad'in

"Lale barkanku da zuwa."

tayi saurin mikewa ta isa ta d'auko tabarmar kaba ta shinfid'a musu tana cigaba da fad'in

"Ku iso ga gurin zama maraban ku dai."

Wani irin mikewa malam Bub

a Mani dake zaune cikin wata 'yar rumfar kara ya yi.

"Ta bayyana ke nan!."

ya yi maganar a zabure.

kafin su Aunty su karasa gurin zaman da aka musu shi ya rigasu fito wa, daga cikin rumfar karar da yake ciki.

da sauri tamkar mai tafiya kan iska tsohon da

ttijon ya iso gaban su kamar kiftawar ido.

Beyi wata-wata ba ya kai askar dake rike a hannunsa kan goshin Feeryal, ji kake kyasss ya tsaga shi dai-dai tsawon gab'ar yatsa d'aya.

nan da nan wani bakin jini yashiga tsartuwa.

Jikin Aunty ya d'auki b'ari ba

ita kad'ai ba har da Baba Rabi da ita kanta mai d'akinsa Inna Delu.

abin mamaki Feeryal na tsaye babu wani alamar da ya danuna jin zafin yankan da aka mata bare d'igon hawaye a idon ta.

Malam Buba Mani.

ya kamo hannun Feeryal ya janyo ta cikin 'yar rumfa

r karar nan, da sauri ya zaunar da ita kan wata kututturen itaciya.

ya mike da sauri ya shiga wani d'aki dake cikin rumfar,

da sallama mai karfi d'auke a bakin sa.

da gani dad'ad'd'en d'aki ne,

yana duk ya baiyaye ko ina.

ya saka hannu ya yaye yanar da ke

gabansa kana ya mika hannu ya d'au wani d'an karamin tukunyar kasa,

ya yaye yanar da ya rufe jikin tukunyar kana ya juya yafito da sauri.

A gaban ta ya aje tukunya yasaka hannu da sauri cikin sa, ya d'auko wani magani ya mannashi a goshin ta dai-dai gurin

da ya tsaga.

da sauri ya danne gurin da yatsarsa ta tsakiya.

yashiga goga maganin a gurin yana zagaye da shi kamar zagayen mantega.

sai da ya d'anyi fad'i da shi kana ya d'aga hannunsa ya d'au wani, maganin yakuma shafe gurin da shi.

nan take gurin ya s

hafe tamkar ba gurin bane a ka yankata kafin yanzu, ya dawo normal kamar inda ainihin fatarta yake.

Aunty suna tsaye suna kallon ikon Allah.

Numfashi Malam Buba Mani ya sauke, ya mike tsaye yana dafe jikin karar rumfar sa, yana kuma sauke numfashi, kamar

wanda ya yi aikin gayya.

kan kace me suka fara jin kukan tsuntsaye da wasu nau'ikan dabbobi.

kamar kiftawar ido tsuntsaye suka cika gidan ta sama suna ta shawagi da kuka iri daban-daban.

Dajin Malie.

A can cikin kasurgumin dajin boka Malie a

karkashin kogon tsafin sa.

A firgice boka Malie ya mike yana zazzare jajayen manyan idanuwansa, masu matukar tsoratarwa had'i da firgidar ga duk wanda ya yi arba da shi.

ya damke tsandar tsafin sa, cikin hargitsatsen murya mai fidda amon sauti maraddad'i

mai cike da razanarwa ya furta

"Ma somar faruwar wata husuma!."

Ya buga sandar tsafin sa a kasa, yana gwalalo manyan munanan idanunsa, yana son ganin me ke faruwa.

sai dai daya buga kasa madadin ya sami amsar tambayar sa,

sai dai yaga bakin hayaki mai duh

u ya kasa ganin komai.

Nan da nan ya tura aike izuwa fadar sarkin bokaye.

Sarkin bokaye Lazzi shima a gurinsa yaji alamun faruwar wata husuma, sai dai duk iya binciken sa ya kasa gane mene ne, ya wanzu yanzu-yanzu.

Dole shima sai da ya dangana ga sarkin

bakaken aljanu.

Sako ne ya dawo wa sarkin bokaye Lazzi daga gurin sarkin bak'aken Aljanu,

wacce suke nima ce ta bayyana sai dai babu haske a gareta basa iya ganin komai sai duhu.

Nan da nan sarkin bokaye Lazzi ya sanarwa boka Malie abin da ke faruwa.

ts

abar firgita sai da ya fad'i ya suma.

Duguri

Malam Buba Mani yafito daga rumfar karar sa, in da Feeryal ke zaune ko a jikin ta tasa yatsar ta cikin baki tana wasa da shi.

har lokacin su Aunty suna tsastsaye da kafafun su, sai dai yanzu duk kawunan su

a sama yake suna kallon tsuntsayen da suke ta shawagi saman gidan. kasa-kasa kamar zasu sauko kansu.

ya yin da tsoron su ya karu ganin wasu irin halittun tsuntsaye daban-daban, wasu masu yanayin ban tsoro.

lokaci kankani suka cike saman gidan sai kuka iri

daban-daban suke.

sunayi kamar zasu sauko kasa.

Malam Buba Mani ya d'aga hannu sama yana fad'in

"Maza kuyi tafiyar ku babu abin da ke faruwa anan, tana cikin koshin lafiya."

ai ko nan take tsuntsayen nan suka soma watsewa, har suka watse duka.

sai guda b

iyu suka rage akan rufin d'aki.

Baki Feeryal ta washe daga in da take zaune tana hango tsuntsaye guda biyun nan, wan da a zahiri ita ba tsuntsu take gani ba mutane ne.

da saure ta mike tafito daga cikin rumfar tana nuna su da yatsa

"Laa Chuchu Chulu yaus

he kuka zo kuma a jirgi kuka zo, ya ban ganku ba,

shine kuka hau sama kuma?

ai naga mutane da yawa a sama, nima ku hau da ni."

ta d'aga hannu sama tana tsalle, wai itama zata haura sama.

Aunty ta zubawa tsuntsaye biyun nan ido da Feeryal ta kira su da

sunan da take kiran kawayen ta da su, abin ya matukar d'aure mata kai.

Maganar Malam Buba Mani yasa Aunty dawowa daga tunanin da ta tafi jin yana cewa

"Ku gusa a gareta kar ku shagaltar da ita."

yana rufa baki suka fire.

Fuska ta bata tana cuno baki

"Ba

kun tafi ba, ko kunzo gidan mu bazan baku baby na kuyi wasa da ita ba, ai Ammie na ta siya min babban baby kuma."

Malam Buba Mani ya dubi Aunty da ke tsaye tsoro ya bayyana gare ta.

ya ce

"Bismillah Hajiya ku isa ku zauna."

da kyar ta iya jan kafarta, Ba

ba Rabi ma da tsoro ya gama da ita ta biyo bayan ta suka karasa kan tabarmar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login