Showing 69001 words to 72000 words out of 86898 words

Chapter 24 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

aiki a asibitin gidajen su yana kusa da asibitin, har da shi kansa me asibitin ma gidan sa na kusa a gurin,

sai dai ba lallai ne

mu same shi ba dan bana da tabbacin yana kasar, amma ko sauran muka samu ina da yakinin zasu fito dan suna da kokari sosai kan majinyata."

"Muje can d'in please Nasir yi sauri dan Allah bata numfashi."

ya bud'e mota ya shinfid'a ta a gidan baya.

dukan su

suka bada umurni wa tawagar su, su kwashe b'arayin su tafi da su.

Major Sadam yaja motar da kansa batare da ya bukaci wani jami'in sa ba, inspector Nasir na gefen sa suka nufi hospital d'in.

Suna isa kofar katon asibitin ya yi hon, mai gadi ya leko, ganin

soja da police a gaban mota,

da sauri ya wangale musu get.

suka shige harabar asibitin, ya gyara parking suka fito.

da sauri Sadam ya bud'e inda take ya ciccib'ota, sukayi cikin asibitin.

Cikin hanzari ma'aikatan asibitin suka nufo inda suke da welcher.

Sadam ya ce "Not ina za'a shiga da ita?."

da sauri wani nurse ya yi gaba ya tura kofar ICU yana fad'in

"A shigo da ita nan."

Sadam ya shinfid'a ta kan bed yana cewa

"Ina likitocin ku suke?."

nurse d'in ya ce

"Tun 6 suka tashi, yanzu nan kuwa bada jimawa b

a Dr A.A FIYA ya bar nan ya yi wa wata me ciki C'S ko 30min baiyi da barin nan ba,

amma gaskiya da kyar ya dawo sabo da yau ya shigo kasar, ya shigo asibitin ne kawai ya taras da ita cikin wani hali shiyasa ma ya tsaya har ya mata C'S d'in."

Da sauri Majo

r Sadam ya ce

"Kirashi dan Allah ita ma wannan baka ganta cikin wali hali ba, yazo ya ceci rayuwar ta pls!."

Shiru nurse d'in ya yi yana tunanin ta in da zai fara tuntub'ar Likitan nasu,

ta ina zai fara gashi a gaban soja yakuma umurceshi, wanda aka umurt

a da ya kira shi d'in ma

a gefe guda shima sojan kansa ne.

bayan keyar sa ya d'an sosa ya ce

"Zaizo kuwa? adai kira wani Dr dai."

tsawa Sadam ya buga masa ya ce

"Kana kallonta a sume ka tsaya kana wani kame-kame,

shi wanda bai jima da barin nan ba shi yaka

mata ya dawo ya duba ta, sauran da duk yanzu sun jima da yin bacci ta ina zasu iya kulawa da ita yadda ya kamata, ka kirashi yanzun nan!."

Hannu na rawa yashiga lalub'o lambar Dr A.A FIYA. har kiran ya yanke bai d'aga ba.

Sadam yana tsaye yana ji dan way

ar a handsfree ya saka, ya ce yakuma kiransa.

sau uku yana kira ba'a d'agawa sai ana hud'u tukun ya d'aga bai yi magana ba.

ganin ya d'aga ya yi shiru da sauri shi nurse d'in ya fara magana.

dan yasan halinsa idan zasu kwana a haka shi ba zai fara yin mag

ana ba,

sai dai ya aje wayar idan ya gaji, kai da ka kirashi kai kasan sauran da kud'in ka,

ko ya kashe watar.

"I'm sorry Sir an kawo patient emergency."

tsaki ya ja tare da kashe wayar ya jefata gefe ya gyara kwanciyar sa, ya mai da kansa pillow.

Major

Sadam ya ce "Ka sake kiran sa maza yasan wa yake wa tsaki anan kuwa!."

jiki na b'ari ya mai da kiran shikam yau tashi ta same shi wuta biyu ta gefe da gefe suke kokarin amsawa da shi.

nan ma wayar ta yanke bai d'aga ba, yakuma mai da kiran a karo na biyu h

ar ya kusa yankewa ya d'aga.

da sauri Sadam ya karb'i wayar ganin ya d'aga ya ce

"Kana magana da Major Sadam Wakili, patient tana bukatar taimako kazo ka duba ta."

"I'm Doctor Abdurrahim A.A FIYA, yanzu lokacin bacci na ne."

d'inp ya kashe wayar gaba d'aya

ya jefata gafe yakuma gyara kwanciyar sa.

A fusace Sadam yashiga kokarin kuma mai da kiran sai jin sa ya yi a kashe.

"Amma d'an ji da kan nan bai san da wa ma yake magana ba, zan nuna mashi ko wane ne ni!."

Inspector Nasir ya yi murmushi tare da bubbuga

kafad'ar sa ya ce

"Yanzu ba wannan ne a gaban mu ba, damuwar mu ta farfad'o ta sami lafiya ne."

ya dubi nurse d'in ya ce

"Gidan sa nan kusa ne ba? taho muje ka raka ni."

Sadam ya ce

"Wai gurin sa zakaje shi zai zo da kafarsa har barrack ya same ni, zan p

unishment nashi,

mu d'au keta mu tafi wani asibitin."

kai Nasir ya girgiza yana murmushi ya ce

"D'an'sandan ke nan abokin kowa, zanje na d'auko shi, kasan kowa sarki ne a fannin aikin sa,

yanzu idan aka barmu da ita bamusan ya zamuyi da ita ba, saboda ba a

ikin mu bane,

a wannan fannin dole mu zamu bisa aikin sa ne,

yanzu idan mukace zamu d'agata a nan kafin mu isa wani asibitin ai zamu b'a lokaci, kuma tana bukatan taimakon gaggawa."

da sauri Inspector Nasir ya fita nurse d'in yabi bayan sa.

Babu nisa sak

anin gidan nasa da asibiti, titi ne ta rabasu, gidan na kallon asibitin.

suka sallaka suka isa bakin get d'in gidan.

Nasir ya kwankwasa, mai gadi da ke gyangyad'i kan kujera ya zabura da sauri ya mike, ya leko ta mahangarsa dake jikin get d'in.

ya hango po

lice da ma'aikacin asibitin mai gidan sa.

ya bud'e karamar kofa yana rarraba ido da son jin ba'asin abin da ya kawo su tsohon daren nan.

Inspector Nasir ya ce

"Sannun ka da aiki, mun zo gurin mai gidan ne."

ido mai gadi ya gwalalo ya ce

"Yallab'oi Allah da

i yasa lafiya, wlh shi kam ma yau ya shigo kasarnan yana can kasan turawa,

yana rayuwar shi babu ruwan shi da kowa."

"Bamu hanya dai yanzu mu wuce."

da sauri mai gadi ya matsa gefe.

suka shigo ciki Nasir ya dubi mai gadin yana fad'in

"Kayi mana sallama da

shi yanzu dan Allah."

mai gadi ya isa da sauri jikin garun d'akin sa, in da wayar tafi da gidan ka take sakale a gurin.

ya daddanna ya kara a kunnen sa.

Aci kuwa nan take wayar ta soma kara ta karad'e cikin parlour.

yana kwance idanunsa a lumshe da sauri

ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa,

"Ya salam."

ya furta yana mikewa zaune.

kai ya dafe da hannunsa biyu, jin yadda kiran yake kuma shigowa babu kakkautawa.

ya mike a fusace ya fito parlour.

ya fincike wayar ya kai sa kunne cikin tsawa ya ce

"Kai wani irin

hauka ne wannan zaka cika min kunne da kira!."

mai gadi ya durkusa kaman yana gaban sa ya ce

"Allah baka hakuri oga hankali na ne a tashe ganin police a tsohon daren nan wai yazo niman ka."

tsaki yaja ya saki wayar Allah ya kare bata isa kasa ba da sai d

ai wata ba dai ita ba,tana ririto ajikin igiyar ta.

Kugu ya rike tare da furzar da huci mai zafi daga bakin sa.

ya yi da na sanin zuwa kasar shi da ya gudo domin ya huta ashe wata musifar aikin zai kuma gamuwa da shi a nan.

a hankali ya ke takawa yana ma

mmatse idanunsa da bacci yake cike tam a cikin su,

Allah ya sani ba karamin bacci yake ji ba.

ya isa in da takalman takawan cikin parlour'n suke ya zura d'aya a kafarsa ya fito da gajeren wandon jikin sa da singileti.

yana aikin jan tsaki fuskarsa a had'e

kamar tun da yake bai tab'a dariya ba.

tun kan ya karaso in da suke Nasir yashiga takowa gare sa shima suka had'e a tsakiya.

I'd d'in sa ya ciro a aljuhu ya nuna masa yana fad'in

"Inspector Nasir B Suleja, barka da dare Dr Abdurrahim A.A FIYA."

Nasir ya m

ika masa hannu, da kyar ya miko masa nasa hannun suka gaisa.

Nasir ya gyara tsayuwar sa ya ce

"Nasan baka sanni ba, nima dai bana ce nasan ka a ido ba, amma ina jin sunan ka,

akwai kuma kyakkyawar alaka sakanin Alhajin ka da hukumar mu."

fuska ya dad'a h

ad'ewa dan ya kosa da jin bayanan sa, katse Nasir ya yi da fad'in

"I'm okay me ya kawo nan?."

Nasir ya yi murmushi ya ce

"Dole zan sanar maka abin da ya kawo mu ai bayan gabatarwa,

kayi hakuri mun katse maka baccin ka,

dole ne yasa hakan, muma bamu samu mu

n rumtse ba cikin daren nan,

aikin mu da naka yana kamancece niya so dole bacci zai zamo mana short saboda taimakon al'ummar mu,

muna tafe da patient tana asibitin ka, amatsayin mu na jami'an tsaro mun sami nasarar kwato ta daga hannun 'yan tadaddan da su

ka saceta suke kokarin guduwa da ita,

mu munyi aikin mu saura naka,

kai kuma a matsayin ka na likita yanzu sauran aikin naka ne, tana bukatar taimako dan Allah kaje ka duba ta."

Fuska ya dad'a had'e wa, ina gashi nan kalar aikin da yakin aka matsa masa sa

i ya yi, shi kullum bashida lokacin kansa sai na mutane.

d'an baccin ma baza'a barshi ya yi ba.

juyawa ya yi yana kokarin barin gurin tare da fad'in

"Ku barta a gurin gobe Doctor's zasu shigo su duba ta."

da sauri Nasir ya sha gaban sa ya ce

"Haba kai kuwa

yarinyar da take cikin halin mutuwa ko rayuwa, idan ka taimake ta kaima Allah zai dad'a taimakon ka, bata cikin hayyacin ta gaba d'aya please ka taimaketa dan Allah, daure dai muje ka duba ta,

ai duk irin aikin namu ke nan muna son baccin nan muke hakura

da shi."

Gajeren tsaki yaja, kana ya zura hannayen sa cikin aljuhun gajeren wandon jikin sa, ya juya suka nufi kofa.

Nasir yana ta bashi baki har suka fice a gidan suka ketare titi suka shiga asibitin.

Ma'aikatan da suke kwana asibitin suna ganin sa kowa

ya mike tsaye da kafafunsa, suna mika masa gaisuwa, ba wanda ya amsa gaisuwar sa ya wuce ICU Nasir na biye dashi.

Har lokacin Major Sadam yana tsaye da kafafunsa yana ta kai kawo cikin room d'in.

yana shiga room d'in ya zare hannayen sa daga aljihu ya na

d'e su a kirji yaja ya tsaya.

inspector Nasir ya dube sa, ya yi murmushin gefen baki, a ransa yake fad'in

"Wannan fa d'an zafin kai ne, dube shi kamar wani boss yawani b'ata rai, ya juye tamkar shine sojan."

a fili kuwa cewa ya yi

"Yauwa Dr bari mu baka gu

ri ka gudanar da aikin ka, Major muje ta waje ko."

Sadam ya watsa masa mugun kallo cikin kakkausar murya ya ce

"A kiraka kana wani ji da kai who are you! idan kayi wasa sai Kayi sallen kwad'o a nan,

yarinya tana cikin wani hali kazo ka duba ta,

kana gayaw

a mutane magana,

mu da muke hana idanun mu bacci domin baku tsaro bamu ce mun gaji ba sai kai ne zaka wani ce wai lokacin baccin ka ne,

kai dole ma na baka wani punishment idan ka gama dubata ka biyo ni office!."

wani kallo ya bisa da shi sannan ya ce

"Go

ehead for the punishment in zaka iya,

ku d'auke ta ku fita da ita a nan bazan duba ta ba!."

a fusace Sadam ya bud'i baki zaiyi magana

Nasir ya yi saurin ruko hannunsa.

"Please Major barshi ya yi aikin sa dan Allah babu tima.

ya janyo Sadam dayake nuna Dr

A.A Fiya da hannu yana fad'in

"Who are you be careful."

ya jashi suka fito dan yaga Dr nan ba sauki damasan sa sai wani bud'ewa suke babu tsoro ko d'igo a gare shi.

za'a iya yin ba dai-dai ba,

karshe ya nimo masu taya shi rabon fad'a dan bazai iya shi ka

d'ai da wannan murd'ad'd'en Dr ba.

duk da kuwa kasancewar sa hukuma shi da yake likita yafisu zubin kakkarfan zaratan jaruman maza.

Dogon tsaki yaja a fili ya furta

"See this guy mttss."

yakuma jan tsaki akan wata patient sun d'aga masa hankili sun hanash

i bacci, daya sani ma da baizo kasar ba, shi da ya gudo yazo dan ya huta amma daga zuwan sa an wani takurawa rayuwarsa, shifa wannan aikin in da yasan yadda zaiyi ya yakace shi a gareshi daya kakkab'e shi,

domin babu komai cikin aikin sai takura a hana mut

um sakewa da hutawa kullum mutum bashi da lokacin kansa sai na mutane,

da Daddy zai duba masa da ya barshi ya jingina aikin nan gefe baya son damuwa.

kwafa ya yi a fili.

tare da sauke idanunsa kan bed in da take kwance flat kamar babu rai a jikin ta, tana

sanye da riga da wandon bacci.

a hankali yashiga d'aga kafarsa yana takowa inda take.........!

Mommyn Twins ce

🌺

*FEERYAL*

🌺

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

~Free page~

( _Bismillahirrahmanurrahim_)

*_L

ittafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*

🌈🇰

AINUWA

🇼

RITER'S

✍

🏼

*

*

🇦

SSOCIATION

🤝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our

ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*

👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*______________________

______________*

🅿

️

19

Dipp! karar sautin bugun zuciyarsa dai-dai san da idanunsa ya sauka a kanta.

babu zato yaji bugun zuciyar da baisan musabbabin abin da ya haifar da shi ba.

da karfi ya rumtse idanunsa yana sauraran sautin bugun zuciyarsa.

"Why

!."

ya furta a file sai kuma ya yi gajeren tsaki.

ya na bud'e idanun nasa,ya janye shi daga gareta ya matsa gefe, yasoma had'a abubuwan da zai yi mata amfani da su wajen bata taimakon gaggawa.

ya taho dasu bakin gadon.

tsayuwar sa ya gyara, a hanlali ya ka

mo tsinsiyar hannunta, da yatsunsa biyu kamar baya son tab'awa, idanunsa yana kan na'urar da yake ta kokarin saita shi.

2 seconds yana rike da hannun nata, tsaki ya ja sai kuma ya saki hannun,

ya dad'a matsowa yakai hannunsa ta saman wuyan rigar baccin

jikinta yad'an jashi kasa,

ya saka yatsarsa a jikin jijiyar gefen wuyanta,

2 seconds nan ma yatsarsa yana gurin, kana ya janye.

ya d'an juyo ya dubi nurse d'in da ke tsaye a gefen sa ya ce

"Je ka kirasu suzo su d'auke ta ta mutu."

da sauri ya juya ya fita

yaje ya sanar musu.

a razane duk suka mike suka had'a baki wajen fad'in

"What!."

Major Sadam da ya ji kansa na juyawa ya nufi kofar ICU Nasir na biye da shi.

ya tura kofar da karfi yana fad'in

"No bazai yuwu ace ta mutu ba! ya za'ayi kace ta mutu no bazai

yuwu ba!."

gefe Dr A.A Fiya ya matsa yana zura hannayen sa cikin aljuhu, tare da mara baki ganin yadda Major Sadam yawani birkice ya yi kanta yana fad'in

"FEERYAL please ki tashi no bazai yuwu ace kin mutu ba!."

ya jijjiga hannunta yana kiran sunanta.

sai

kuma yayi wani irin juyowa yana duban Dr A.A Fiya da jajayen ido

ya ce

"Kar ka sake kabari ta mutu, wlh idan ta mutu da kai da b'arayin can, tare zakuyi freezing sannan na harbe ku da kaina, kayi mata abin da zaisa ta tashi!."

Sadam ya fad'a da karfi yana

jijjiga kafad'ar Dr A.A Fiya.

ture hannunsa ya yi daga kafad'arsa ya ce

"Kai ka dawo da ita mana kayi mata abinda zaisa tatashin,

ka d'auke ta ku fita min a asibiti ni na gama nawa sai kaje kayi yadda zata tashin a can waje."

Inspector Nasir ya matso da

sauri yana fad'in

"Please let me know Dr da gaske ta mutu!?."

kafad'a ya d'aga kana ya ce

"Ina tunanin hakan."

da sauri Nasir ya rike hannunsa ya ce

"No! tunani kake, bai tabbata ba, ka taimaka ka sake gwadawa insha'allah zata tashi, aikin ka ne mu bamusa

n yadda zamuyi da ita ba, dan Allah Dr dan Allah ka taimaka dan Allah dan Allah please help."

ya jijjiga hannunsa yana magiya da rokon sa.

hannu ya d'aga musu yana jifan Major Sadam da mugun kallo kana ya ce

"Ku jira a waje."

Nasir yaja Sadam da sauri suka

yi waje.

Gajeren tsaki yaja ya matsa bakin gadon,

ya rike kugu yana dad'a jan tsaki.

sannan a hankali ya kai hannunsa kan cikinta ya janye rigar baccin jikinta da yatsu biyu,

ta d'an sama har zuwa saman cibiyarta, yadda yake yi kamar mai tab'a wani abin k

yama da baya son hannunsa ya tab'a.

ya d'au defibrillator yana had'asu, kana ya dad'a matsowa ya manna shi kan cikin ta.

da karfi ta zabura ta kuma komawa tana kokarin kuma shiga dogon suman.

yakuma manna mata sau biyu a jere tawani irin zabura da karfi ta

re da jan numfashi,

mai had'e da ihu a firgice ta yunkura ta fad'a jikinsa ta tsakalo wuyansa ta kankamesa da karfi tare da fasa kuka,

tana b'oye fuskarta cikin kirjinsa.

cikin fizgar munfashi mai nuni da zallar tsoro wanda a yanzu kwakwalwar ta ke tsaye c

ak baya nanata komai sai kasantuwarta da b'arayin nan.

cikin had'a kalomomi take fad'in

"Dan Allah.. ka..kayi hakuri kar..kar ka tafi da ni, ni bana sonka bazan aure ka ba."

A fusace ya fisgota da karfi ya cirota a kirjinsa ya turata kan bed d'in, ya yi s

aurin binta da allura ya dannan mata, ta saki wani uban kara jikinta na rawa.

zuwa can kuma a hankali tashiga sauke numfashi, a hankali a hankali nan da nan bacci ya tafi da ita.

Tsayuwarsa ya gyara tare da gyara zaman singilet d'in jikin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login