Showing 81001 words to 84000 words out of 86898 words
gaskiya tana da kyau sosai kamar ita tayi kanta."
Mommy da ke ta aika mata harara tun da t
a fara maganar ta ce
"Dalla rufa mana baki, kusheta kike ko yabon ta, ni fa watarana tantama nake akan ki dan naga kamar halinki na kamancece niya dana Ajeemal duk zan ci ubanku ai marasa ziciya,
wad'annan badun lokacin da na haifeku a take aka d'ago aka n
una min kuba da sai nace canza min ku a kayi."
Ameerah tabi Sumayya da harara tana jan tsaki ta mike tayi bedroom d'insu.
gaban mirror ta tsaya tana karewa kanta kallo.
sai kuma ta juya ta koma bakin gado ta zauna tana fad'in
"Aikin banza banga abin da ta
fini da shi bama."
Yau kwanan FEERYAL uku a gidan.
kullum suna tare da Miemie ko a sashin Aunty ko a sashin su Miemie'n.
ko yanzu ma sun fito ne daga side d'in su Miemie zata rakata side d'insu.
Ammah ce ta kwallawa Miemie kira ta koma ciki,
kula mai d'
auke da dambu ta mika mata ta ce
"Mikawa Hajiya wannan sai ku wuce."
ta amsa tana fad'in
"Hajiya mayyar dambu sai ya shake makogwaron masifar nan mu huta,
wata rana da kaina zan mata mara kayan had'e na kai mata taci ta shake."
"A bakin ki akaji ba a baki
na ba, ke da Abbieh'n ku idan ya jiki."
Ammah ta fad'a tana juyawa ciki.
Miemie tayi waje tana cewa
"Allah sai na yi mata sai dai Abbieh yayi min masifa ko ya bige ni, mata kullum masifarta karuwa yake takusa mutuwa madadin ta rusuna amma sai gaba abin ta
yake."
ta karaso in da FEERYAL ta ke ta ce
"Taho muje ki rakani na mikawa Hajiya dambun nan sai mu wuce."
FEERYAL tad'an waro ido ta ce
"Muje dai na jira ki a bakin get d'in ta."
"Dalla matsoraciya zo muje me zata yi miki, ai yanzu ta saduda, tun da ta a
msawa Daddy ki zauna."
FEERYAL dai shiru tayi har suka karasa sashin Hajiya.
dan Hajiya tana daga cikin abubuwan da suka ki gogewa cikin kwakwalwarta na tun yaranta.
A parkour suka tadda Hajiya FEERYAL ta karaso a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a cik
i.
Miemie nayiwa Hajiyar magana ita hankalin ta na kan FEERYAL da ta d'an rusina tana fad'in
"Ina yini Hajiya."
Hajiya ta ce
"Ke Miemie wannan ba aljanar yarin yar nan bace?."
Miemie ta b'ata rai sannan ta ce
"FEERYAL sunan ta."
"Da gani ai ba sai an fad'a
ba, dan ina ido biyu da ita naji tsikar jikina ya tashi,
haba kyan har ya kazanta hankali bazai d'auka ba,
ke tashi min a kai fita waje! kar na sake ganin ki cikin sashin nan,
ki zauna can sashin Fatima kafin a gama binciken ki koma can in da akayi gayyar
ki ba gidan d'ana ba, mayya aljana mai zubin aljanun ruwa."
Da sauri FEERYAL ta juya har tana had'awa da sassarfa tayi waje.
sai da tafi wajen get d'in sashin kafin ta tsaya.
Miemie ta dad'a b'ata rai ta ce
"Haba Hajiya ya zaki ce mata mayya kuma aljana,
yanzu idan wani ya tsangwame mu haka kema fa bazakiji dad'i ba."
"To uwar ta ki karb'a mata, kefa Miemie tun da na datsa ayar tambaya a kanki, dan naga alama yarinyar nan bata barki banza ba,
kar na sake ganin ki da ita, kuma zanje na amso magani a soma m
iki dan da gani turen aljanu ta miki."
Miemie ta tura baki tana kunkune ta nufi kofar fita tana cewa
"Ni ba wanda ya isa ya rabani da FEERYAL, ba kuma maganin da zanyi in kin karb'o maganin sai kiyi amfani da kayanki."
tayi waje abin ta ta bar Hajiya tana
ta masifa.
Bilkisu Saddiqa Rahama da Siyama kanwar Umma Karima da yanzu ta dawo gurin Umma Karima da zama,
suka fito daga sashin Umma karima.
Nabila da tayi fitowar karshe idanunta ya sauka kan FEERYAL da ke tsaye a bakin get d'in Hajiya.
da hannu ta nuna
musu ita tana fad'in
"Yauwa kun ganta can ga FEERYAL d'in can."
duk suka maida dubansu gareta.
Saddiqa ta bud'e murya tare da yafaro ta da hannu ta ce
"Ke FEERYAL zo nan."
A hankali ta ke d'aga kafarta cikin yanayin ta na sanyi har ta iso inda suke.
dukk
anin su suka bita da kallon tsaf,
Siyama ta yamutsa fuska tana fad'in
"FEERYAL d'in ke nan?."
Bilkisu ta ce
"Wai ita ce, bamu sani ba dai ko Aunty ta kuma d'auko wata ce tace ita ce ta da d'in data tsinto cikin ruwa,
dan lokacin da aka koreta a gidan nan
tana ficiciya."
Rahama ta ce
"Ke kifa daina mana yawo a gida idan kuma kika ki dukan tsiya zaki ci, dan sau uku ke nan nake hango ki kina kai kawo cikin gidan nan."
Nabila tace
"Ah to gaya mata dai dan nan gidan ubanmu ne agola bata isa tayi abin da ta so
ba,
ke daga yau ma duk abin da zakiyi sai kin nimi izin mu, har idan kina so ayi miki alfarmar zama na d'an wani lokaci."
Siyama ta bita da kallon banza tana wani yamutsa baki ta ce
"To dai kinji abin da masu gida suka fad'a, sai kibi a hankali domin ki ci
gaba da zaman alfarma, in ba haka ba kuma a koma in da aka fito."
Rahama ta ce
"Ai kuwa dama zaman alfarma take dan Hajiya ta fad'awa Umma Daddy ne ya nima mata alfarman zama dai-dai, kunsan 'yan kidnapping d'in nan wannan mai tawagar d'aukar amaryar nan s
un d'auke ta da kyar aka kwato ta,
bayan ya gama bidirin sa da ita."
dariya suka kwashe da shi Siyama ta ce
"Kice ashe dai fanko ce tsaye a nan, kyalkyali daga waje ciki fanko."
FEERYAL na tsaye bata ce da su kala ba,
gaba d'aya tsoro ya rufe ta bata saba
ganin haka ba,
tun bayan da ta sami 'yancin barinta gidan rabon da ayi mata irin haka.
Miemie da ta fito daga sashin Hajiya ta hango ta can tsaye dasu Bilkisu,
kugu ta rike tana kallon su sai magana suke suna nuna FEERYAL da yatsa.
itako tayi kasa da kai
kamar mai d'aukar wa'azi,
a kufule ta nufo gurin su fuska d'aure ta ce
"Ke kuma FEERYAL me kike a nan? na fito ina ta duba ki a she kina tsaye anan, to muje."
Bilkisu ta ce
"Mu muka kirata muna mata kashedi ne, kar ta sake ta rika mana yawo a gida."
Miemi
e ta dube ta shekeke ta ce
"Kuma dai Aunty Bilkisu meye wani abin kashedi dan anyi ya wo a cikin gida,
waje ke nan kuke so muje murika yawo."
Rahama ta ce
"Bawai ke ba da ita muke."
"Har da ni mana Aunty Rahama tun da tare kuke ganin mu, idan bamuyi yawo a
cikin gida ba waje kuke so mufita."
Siyama ta ce
"Ke Miemie ana gaya miki ba ke ba da ita ake."
"Dakata Siyama ba da ke nake ba da su nake, ban kira sunan ki ba,
Aunty Bilkisu Aunty Rahama Saddiqa Nabila,
ina ga acikin mu da ni da ku duk babu mai hurumin
ikon hana wani yawo cikin gida, tun da babu wacce ta gina gidan a cikin mu,
Daddy ke da ikon yanke hukunci ba mu ba."
"Ke karkice zaki min rashin kunya dan tuntuni nake ganin take-taken ki."
Siyama ta fad'a tana nuna Miemie da yatsa.
Miemie ta wani dalla m
ata harara taja tsaki tare da jan hannun FEERYAL tana cewa
"Dalla zo mu tafi, sai naga wanda ya isa ya hanaki yawo,
ai agololin suna da yawa a gidan idan sauran suka daina ke ma zaki daina."
Sai da sukayi nisa da su Miemie ta harare FEERYAL tana fad'in
"K
in wani tsaya suna gaggaya miki magana baki maida musu amsa ba, in fad'a miki a gidan nan idan bakada baki anrika cin tuwo a kanka ke nan,
garama ki koya kiyi baki,
duk ba mutunci suke da shi ba, shi yasa nima bana ganin su da mutunci, Bilkisu da Rahamar m
a albarkacin Ammah suka ci nake had'a su nan su da Aunty, amma ba dun haka ba duk da sunan su zan kira su, tun da basu rike girman su ba,
duk sun turewa shekara 27 ko uwar me suke d'auka a gidan suka kasa aure oho,
ita kuma wannan shegiyar Siyamar ba karam
in haushi take bani ba,
an kasa auruwa a Kano an dawo Lagos ko za'a sami mashinshini,
wai a haka budurwace da kike ganin ta nan kamar bazawara,
da gani wannan ta kai shekaru arba'in
kanwar Umma Karima ce da bushasshen jiki ko ina a bushe ba soka."
FEERYA
L dai murmushi tayi bata ce ko mai ba,
Miemie ko bata fasa mitar ba har suka shige sashin Aunty.........!
Mommyn Twins ce
🌺
*FEERYAL*
🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 5
00 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S
✍
🏼
*
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to enterta
in & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿
️
22
Suna shiga parkour suka tadda Aunty zaune,
Feeryal ta karaso ta kwanta kan kujerar da Aunty ke zaune tayi pillow da cinyar.
Aunty ta zame d'ankwalin kanta tana fad'in
"Me kitso anjima tana zuwa."
fuska ta kwab'e ta ce
"Ammie gyaran gashi fa zamuje d
a Miemie jibi."
"Wai haka Miemie? ko duk gudun kitson ne haka."
cewar Aunty tana duban ta.
Miemie ta gyad'a kai tana dariya.
Feeryal ta dubi Aunty ta marairaice fuska da fad'in
"Ammie ba kince za'a aske gashin ba."
Aunty ta dunguri kanta tana fad'in
"Baki
da kaine, ama bar gyaran gashin a gyare yake,
maza akitsa kyan yau,
in anyi tsifa sai aje a gyara gashin."
birmima ta shiga yi a jikinta tana bubbuga kafa kan kujera Miemie sai dariya take mata.
Mai kitso ta zo da yamma, tana ganin gashin nata ta ce wlh b
azata iya kitsa shi ba dan ya yi yawa.
Aunty ta ce ta gwada dai da kyar aka tuttuka akayi biyu,
karshe tsefe biyun akayi ta tafi,
Feeryal ko sai murna take dama bata son kitson har da hawaye da aka kama kan ana kitsawa...
Umma Karima ce ta fito tana gy
ara mayafin kan ta,
da alama dai shirin fita tayi dan ga jaka rike a hannunta.
a parlour ta tadda 'ya'yan nata duka kowa na sha'anin gabansa.
Siyama ta mike tana fad'in
"Aunty Karima fita zakiyi ne?."
"Eh fitan gaggawa ce ta taso min bazan jima ba zan daw
o, wai ina Nabila ce?."
bata rufa baki ba Nabila ta shigo tana kananun magana.
"Ke kuma da wa kike?."
uwar tata ta fad'a tana duban ta.
ta ce
"Ni da wancan direban naki Sule mana Umma, d'an rainin wayo wai kullum ya ganni sai jira yake ni na fara gaishe sh
i har na wuce bazai haishe ni ba,
shine yanzu nazo zan wuce har da ce min wai ban gaishe shi ba,
kajimin fa d'an rainin wayo,
ni da gidan ubana yazo cin arziki yace ni zan rika gaishe shi ba shi zai gaishe ni ba,
kaf ma'aikatan gidan nan su ke gaishe mu ba
mu muke gaishe su ba,
hatta Baba Ilu mai baiwa fulawa ruwa shi yake gaishe mu ba mu muke gaishe shi ba,
na gaya masa na rantse watarana sai na d'auke shi da mari,
kuma zan gayawa Daddy sai ya bar gidan nan,
ni ban san me yasa kiko son tukin wannan kazamin
buzun ba ma Umma, to wlh
ya yi a bakin aikin sa dan wlh sai na sa Daddy ya kore shi."
Umma karima ta ce
"Ke dalla tafi can, ko da wasa naji batun nan a bakin Daddy'n ku sai na sab'a miki,
kaf direbobin gidan nan banga diriban da ya kai Sule iya tuki ba,
tukunna ma ina direba na ne ba naku ba,
ko da wasa na sake jin kin masa rashin kunya sai na sab'a miki,
kiyi wa kowa rashin mutunci banda Sule dan shi mutumin kirki ne,
babu ruwanki da shi na gaya miki ke nan,
ni bari na tafi, ke Siyama bana ji kince anji
ma zaku fita da saurayin ki ba."
"Eh Aunty Karima yanzu ma mukayi waya ya ce min yana zuwa."
Umma Karima ta ce
"Wai har haka kika bashi dama ne Siyama karfa ya b'ullo da batun aure ya b'ata mana shiri."
"Ah haba ina ai shi wannan d'an hirar rage zafi ne ka
wai,
yaushe zan bashi dama ga dahir a kasa."
"Yauwa to yanzu naji batu zanje na dad'a jin nasarar da take tinkaro mu,
wai ke Bilkisu har yanzu Bilal bai kiraki ba?."
Bilkisu ta mara baki tana gyara zaman ta idanunta a kan wayar da take chatting ta ce
"Tun
da ya tafi Japan sau biyu mukayi magana, yanzu ko na kira sa ma wayarsa baya tafi,
ni bazan ma kara niman sa ba in ya gadama ya neme ni,
ni na sami wani ma yana ma zuwa anjima."
"Dalla tafi can yaushe zaki jira har sai ya neme ki, kiyi ta nimansa har wayar
sa ta shiga,
zan sami Daddy'n ku muyi magana a d'aura auren kawai a kaiki can Japan d'in a wuce gurin,
karki sake ki kunyata ni gaban kawaye na,
ni dana gama fad'a nima 'yata zatayi aure a kasar waje,
yanzu ki kawo min wani batu zanje har gida na sami mama
n Bilal d'in bari na je na dawo."
Ta fice waje tana sambatu.
burin ta ace itama d'iyarta tayi aure a kasar waje kamar yadda d'iyar Mommy Farida itama ta yi.
ta nufi parking lot d'in ta,
a jikin motarta ta dadda Sule direba yana gogewa yana magana.
yana ga
nin ta ya wani washe baki yana fad'in
"A'a hajiya barka da fito wa."
"Barka dai Sule yi sauri muje bar goge motar nan,
da wa kake surutu haka?."
fuska ya d'an had'e ya ce
"Da waccan yarinyar mana Nabila yanzunnan ta gama gwazamin rashin mutunci."
"Rabu da
ita da'alla sai hakuri kasan har yanzu Nabila yarinya ce, kuruciya ke damun ta."
ya ce
"To ai shike nan adai rika gwada mata babba babbane,
yauwa ba dai gurin wancan Mali'n zamu ba, tun kan muje ki zazzage masa bakin jaka duka ina bukatar kud'i fa."
"Kai k
a fiye korafi Sule, yaushe-yaushe ne na baka naira dubu d'ari biyar, kayi yaya da su wai kana nufin har ka kashe su,
a karshen watan da ya karen nan fa Alhaji ya baku albashin ku,
da abin da kowa zaici a gidan sa na tsawon wata guda,
yabaku baiyi da sati b
a na baka kud'i dubu d'ari biyar d'in nan da karin kayan abinci,
matan ka d'aya da 'ya'yan ka uku me kakeyi da kud'i haka."
"Haba Hajiya kya tambaye ni abin da nake yi da kud'i,
kud'in haya na biya na siyi abinci na turawa tsoffi can Nijar, kin ga ko ai ku
d'i sun kare."
"Ni Sule kana bani mamaki, banga ammafin sai da gidan da Alhaji ya raba muku da kayi ba,
ko wani ma'aikaci yana zaune a gidan da aka bashi cikin rufin asirin shi, babu ruwanshi da batun wani kud'in haya,
amma kai ka tashi ka d'au gida ka siy
ar babu kud'i babu gida,
gashi kana kan damuwar kud'in haya."
"To ya ya za'ayi kinsan dai lalurar jinyan iyaye ce ta sani sai da gidan nan,
a ni ma min alfarma Alhaji ya kuma bani wani,
amma kafin nan dai ki bani wani abu a gurin ki kada muje ki juye masa
kud'in duka."
Umma Karima ta shige mota ta zauna gaba shima ya shige mazaunin direba,
yana cigaba da fad'in
"Hajiya matsuwa ce adai bani wani abin."
ta zuge jaka ta ciro d'aurin 'yan dubu d'ai-d'ai guda biyu ta damka masa tana fad'in
"Ga wannan 200k ne sa
i ka lallab'a, bari mu dawo zan kara maka,
sannan zanyi wa Alhaji magana za'a kuma baka wani gidan,
yanzu dai muyi sauri ina da babban matsala so nake na ga Mali cikin gaggawa."
ya ja motar suka fice daga side d'in ta suka nufi babban get suna fita gaba d
'aya a gidan ya juyo yana fad'in
"Ace wai ina gidan nan a karkashin Hajiya Karima,
sakani na da jirgi wai sai dai gani da ido idan na kai masu shiga cikin sa airport,
haba Hajiya wai ina batun tafiya ta makka ce ta kwana."
"Wannan shekarar zan biya maka h
ajji shike nan."
ya washe baki
"Shike nan fa Hajiya kin gama min ko mai wayaga Sule a hajji."
ya sheke da dariya.
Tafiya mai nisa sosai sukayi da ya kai awanni hud'u kafin suka shige dajin boka Mali.
sai da sukayi tafiya kusan na awa guda daga bakin dajin
zuwa cikin dajin kafin suka faka a ginfin wata katuwar itaciya.
Umma Karima ta fito a cikin motar in da Sule direba ke zaune yana zaman jiran ta a cikin mota.
wani katon kogo dake gaba da itaciyar ta nufa.
a bakin kogon ta cire takalmarta da mayafin ta,
ta kunce d'ankwalin kanta duk ta had'a ta ajesu a gurin.
ta shige cikin doguwar kogon nan mai zurfi ba d'ankwali ba mayafi ba takalmi.
fad'i ta ke
"Gafara dai boka sannunka dai mai magance matsala ko wacce iri ce."
wani irin kazamin dariya aka kece da shi
gaba d'aya cikin kogon yake amsa sautin dariya mara dad'in ji.
ya yin da