Showing 42001 words to 45000 words out of 86898 words
aka shinfid'a musu suka zauna.
D'aya daga cikin mutanen da suke tare da su Daddy a waje, ya kwad'a sallama cikin zauren gidan.
Malam Buba Mani ya amsa tare da nufar zaure ya f
ita.
Aunty na zama Feeryal ta dawo jikinta ta zauna, tana ta zuba mata shagwab'ar ta data saba.
Aunty dai bata iya ko kyakkyawar motsi ba dan tsoro yagama cinye kanta,
sai satar kallon goshin ta take inda d'azu ke fidda jini yanzu kuma yadawo tamkar inda
da yake.
Jim kad'an Mamal Buba Mani ya dawo gidan, ya karasa 'yar rumfarsa ya zauna.
da hannu ya kira Aunty ya ce
"Kuzo ku da d'iyar ta ki."
jiki a sanyaye Aunty ta mike rike da Feeryal suka karasa cikin rumfar ya nuna musu gurin zama suka zauna.
Datti
jon ya dube Aunty da kyau kana ya soma magana cikin nutsuwa,
"Duk wani wanda Allah ya hukunta zamanta a gurin sa dole yaji fargaba da tsoron abubuwan da zai rika gani da ji a gare ta,
shin ke ce mahaifiyarta?."
Aunty ta girgiza ta ce "A'a."
"To wace ce k
e a gareta?."
Aunty ta gyara zama tare da duban Feeryal sannan ta ce
"Tsintar ta mukayi, ni da megida na acikin ruwa, ruwa yana shirin gudu da ita,
shine muka riketa har izuwa wannan lokacin."
kai ya jinjina kana ya ce
"Angaishe ku da kokari, sannunku da c
eton farar aniya."
ya shafa kan Feeryal da ke ta wasa da igiyar tabarma,
ya ce
"Karni bayan karni shekaru masu tsawo fidda rai ga samin 'yanci bayyanar ki ya dawo da komai sabo,
an jinjina miki 'yar baiwa,
shekaru arba'in rabon da na shiga wancan d'akin am
ma yau ganin ki ya bani tabbacin zan iya shigarsa batare da wata tsaiko ba,
zan kuma cigaba da taimakawa mutane da baiwar da Allah ya yi min,
wan da nakasa kuma taimakawa wani tun bayan shekaru arba'in."
ya gyara zaman sa kana yaci gaba da fad'in.
"Nasan
abinda ya kawo ku nan bai wuce kokon to a kan ta ba,
ita mutum ce kamar ki kamar ni kamar kowani mutum, sai dai ita ta bambanta, tana da wasu irin tarin baiwa da ba kowa yake da irin sa ba,
ita kanta a wannan shekarun nata sam bazata fahimci komai cikin r
ayuwar ta ba,
har izuwa wasu shekaru masu dama,
kada ku damu da yana yin ta ko wani d'abi'arta,
idanunta da kanta a bud'e suke tana iya ganin abin da ku bazaku iya ganinsa ba,
baiwa ce daga Allah, kada hakan yabaki tsoro,
zata iya yin mu'amala da su kamar
yadda zatayi da ku, kada ganin hakan yatada muku hankali babu komai da yardar Allah,
naji dad'i da Allah ya nufeku da tunanin zuwa nan, bakuyi tunanin zuwa gurin wani ba,
bamu sani ba wanin ko shi wane ne, wala'alla ko shi na d'aya daga ciki 'yan kwangilan
da aka baza domin niman ta,
a wannan lokacin da sukasan da bayyanar ta, suke fafutukar niman inda take,
shi yasa nayi gaggawar goge shaidar da zai sa suyi saurin gane ta, a duk inda zasu had'u bazasu tab'a gane abin farautarsu ba,
haka zasuyi ta nima su
rasa, na goge tabon da ke goshinta da zai bayyana ta a gurin su cikin ruwan sanyi."
Kai Aunty ta jinjina cikin ranta cike yake fal da tambayoyi.
kamar yadda nasan kuma kan ku masu karatu kuke d'auke da shi cikin zuciyar ku.
"Wace ce ita meye had'inta da
aljanu bayan ita mutum ce ba aljanar ba,
me yasa wasu ke niman ta, to ko shi yasa aka jefata cikin ruwa ya tabbata ba had'arin jirgin ruwa sukayi da iyayen ta ba?."
ya akayi ya santa bayan bai tab'a ganin ta ba."
ire-iren wa
Ι
annan tambayoyin ke yawo cikin
zuciyar Aunty.
Malam Buba Mani ya yi murmushi ya na fad'in
"Nasan akwai tarin tambayayo cikin ranki amma lokacin sanin hakan yana zuwa, naji dad'in jin a hannunku ta ke, nasan zata sami tsaro da kulawar daya da ce,
kutashi ku koma gida d'iyarku mutum ce m
ai daraja ma kuwa."
Kai Aunty ta jinjina tana fad'in
"Mungode Malam Allah ya saka da alheri."
"Amin amin Allah ya tsare muku hanya nasan bazasu bari ku d'au hanya ku kad'ai ba, zaku sami 'yan rakiya, dan ita d'in mai girma ce agare su, tana tare da tsaron
su a ko yaushe, gudun faruwar wani abu."
kai Aunty ta jinjina ta mike tana cigaba da masa godiya ta ruko hannun Feeryal, sukayi masa sallama har bakin zaure Inna Delu ta rako su.
Malam Buba Mani kuwa har jikin mota sai da yaga tashin su kafin ya koma gu
rin zaman su da mutanen sa.
Cikin garin Bauchi suka dawo a government House suka kwana washegari suka bi jirgi suka koma Lagos.
zuciyar Aunty wasai da jin Feeryal d'in ta mutum ce, sai dai wani b'arin zuciyar ta na kunshe da tambayoyi da son sanin dalilin
daya sa wasu ke niman ta.
A b'angaren Daddy ma sai da suka dawo gida kafin yasa mi sukunin tambayar ta me Malam Buba Mani ya fad'a a kanta.
Aunty ta shaida masa komai, ya jinjina lamarin ba kad'an ba ya ce
"Ita d'in ikon Allah ce, Allah ya taya mu rukont
a ya kauda idon makiya a kanta,
zamu bada iya karfin mu wajen bata kariya idan har idanunmu zai iya ganin abin cutarwa a gare ta."
Aunty ta amsa da amin amin.
Daddy ya mike yanufi kofa domin zuwa side d'insa, dan dama Umma Karima ce da shi, tafiyar daya t
aso ne ya tsallaka ya tafi.
har ya d'aura hanu kan handle ya jiyo muryar Feeryal
"Daddy kar ka kwanta a kan gadon ka akwai jiji."
cak yaja ya tsaya tare da juyo wa.
Aunty ta yi saurin cewa
"Ke Feeryal a ina kika ga jijin?."
"Na gani yana cikin pillow Daddy
."
Daddy ya tako in da take yarage tsawon sa dai-dai nata ya ruko fad'unta sannan ya ce
"Zai min wani abu ko?."
ido ta wawwaro ta ce
"Eh jiji ne fa Daddy, yana cikin pillow'n ka."
kai ya jinjina ya ja kumatun ta yana murmushi.
Ya juya har ya kai kofa Aunt
y ta ce
"Jira ni Daddy, Feeryal je gurin Baba Rabi tayi miki wanka."
da gudu tayi kichin gun Baba Rabi ita kuma tabi bayan Daddy.
Tare suka tafi side d'in sa.
suna shiga bedroom d'in sa suka soma binciken cikin pilullukan da suke jere a kan makeken bed d'
in sa na alfarma.
kaf suka cire rigunan filon basuga komai ba, suna cikin mai da pillowcases d'in ne idon Aunty ya sauka kan na hannunta da alamun kamar anyi d'inki ta tsakiyar sa, wan da duk pillows d'in na kamfani ne babu alamun d'in ki a jikin sa.
hannu
ta saka tana shafa gurin,
ganin hankalin ta ya koma kan sa Daddy shima ya maida hankalin sa kan gurin.
ya mika hannu ya janyo durowar gifen gado ya d'au almakashi ya tsaga gurin, ya zazzage audugar pillow'n a sakiyar gadon sai ga wani d'aurin laya ya fad'
o.
Aunty tayi saurin d'auka da mamaki suke kallon sa.
Daddy ya karb'a yana kokarin warware shi Aunty takuma amshewa tana fad'in
"Babu amfanin bud'e wa aga me ya kunsa a kona kawai."
kai ya jinjina.
Tayi saurin tattara audugar ta mai da shi cikin pillon k
ana ta maida komai in da yake, taje ta d'auko wani sabon pillow ta saka masa pillow cases d'in da ta citewa wancan, ta d'au wanda aka saka layar ciki ta tafi da shi side d'in ta.
a tabaya ta can gefen garden taje ta kona duka da layar da pillow'n.
Aunty
da Daddy kad'ai suka san da wannan labarin na Feeryal ko Baba Rabi da kusan komai ya faru a kan idon ta bata fahimci komai ba, sai dai itama da tarin tambayoyin cikin zuciyar ta,
bata kuma da mai bata amsa dan bata da ikon tinkarar uwar gijiyar tata, hak
a tabar abin a ranta.
Yau Monday Aunty ta gama wa Feeryal shirin makaranta tsaf, suna zaune kan carpet tana breakfast, Aunty ta dube ta cikin hikima ta ce
"Yammatan Ammie, kina ji na ko, kada ki fad'awa wani kina ganin wasu, ko Miemie ce kada ki fad'a mat
a,
in ba hakaba zasuce ke mayya ce, ko kina so su Ameerah su rika ce miki mayya suna dukanki?."
kai ta girgiza tana yin rau-rau da ido hawaye nason taruwa.
"To ko kin ga kawayen ki kiyi shiru kada ki fad'awa kowa, idan ke da sune babu kowa a gurin sai kuyi
wasan ku, kinji ko."
ta ce "Tom."
"Yauwa good girl, to yi sauri ki cinye ku tafi karkuyi latti."
Kamar kullum da ko yaushe har cikin mota ta kaita kafin ta dawo......!
Mommyn Twins ce
πΊπΊ
*FEERYAL*
πΊπΊ
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTO
R*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'S
β
πΌ
*
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
ππ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writer
s-association
*____________________________________*
π
Ώ
οΈ
12
(Bayan shekaru uku)
Wanda hakan yayi dai-dai da shekarun Feeryal 7 ke nan ta kara girma da wayo sosai.
ya yin da kyara da tsangwamar dake sakanin ta da su Ameerah Sahla Nabila, da kuma
iyayen su mata ke dad'a ninkuwa.
kawancen ta da shakuwar ta da Miemie kuwa ke kara karfi.
Egypt
Hajiya ce zaune a wani kayattaccen parlour a can ka'sar Egypt.
Kulu na zaune a kasa a gefen ta, tana mammasa mata kafafu.
tun safiyar yau Hajiy
a ta tashi da masifa, ita fa bata kuma kwanar kasar nan k'asar ta zata koma ita dai gida zata koma taga jikokin ta.
waya ta mika wa Kulu ta na fad'in
"Kulu kirawo min Abubakar, yau bani kuma kwanan k'asar nan, aikin banza kawai yakawo ni ya aje cikin masu
jajayen kunnuwa ina rayuwa ni kad'ai kamar mayya,
duk sanyi yabi ya addabe ni, jekoki na suna can ni ina wani gurin,
to yau bazan kuma kwana garin nan ba maza yasa jirgi ya d'auke ni ya mai da ni in da nafi wayo."
Kulu ta mika mata wayar tana cewa
"Gash
i Hajiya ya d'aga."
"Yauwa bani ni shi nan."
daga cikin wayar Daddy ya yi sallama yana kokari gaisheta ta katsashi da fad'in
"Kai Abubakar ka kawo ni ka aje nan ni kad'ai kamar mayya, shekaru uku ina zaune kamar wata mara galihu,
kullum nace kasa a maido
ni gida sai ka ce to zaka sa, sai kuma kayi buris abib ka,
wancan zuwan naka na ce mu tafi tare kace nabari nadad'a jin sauki tukun,
awani dadilin zaka rabani da kasata; ce maka akai banji sauki ba,
jikoki na suna can ni ina wata duniyar daban, to yau-yau
d'in nan ka sa a maidani gida dan ni na warke,
ko kai yanzu baka kaini lafiyar ido ba,
an d'aga ni an rabani da jikoki na an kawo ni wata duniyar da ban san kowa ba, shekara uku ina zaune kamar mara galihu,
to nagaji da zama tun marmaza kasa a mai da ni g
ida, yau-yau d'in nan."
Daddy ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya bari nasa ayi muku bukin d'in jirgi zuwa ranar Litinin sai ku dawo."
"Da dai yafi dan ni nagaji da zaman shiru, in ba haka ba naje tasha nashiga mota."
"Hajiya daga can zaki shigo mota zuwa Nigeria ai
bazai yuwu ba, jirgi ma zaki biyo kiyi hakuri dai."
"Ni dai na fad'a maka idan ranar Litinin tayi baka sa an d'auko mu ba tambaya zanyi a kai ni tashi."
ta katse wayar tana cigaba da bombomi.
Hajiya Bishira dake gefe tayi murmushi rigimar uwar tasu kullum
karuwa yake.
Ta ce
"Hajiya wa ya ce miki akwai tashar mota na zuwa Nigeria anan, ai sai dai airport d'in jirji,
dan Allah ki barmu mu zauna anan yafi mana babu hayaniya ba komai, sai dai kaci ka kwanta hankali kwance,
acan fa hayaniyar yara ma kad'ai ya
isheka, da wad'an nan masifaffun matan Yaya Abubakar d'in."
"Allah ya sawake min ni da zaman shiru ai sai dai in nashiga kabari, da raina ina numfashi kam baza a hanani walwala ba,
ai dama ku zaman bariki baya damun ku, in da Abubakar zaibi ta nawa ma da
gida muka koma can Yelwan Shandam, muje muyi zaman mu hankali kwance, amma kullum kana kulle a gida baka d'an zagawa ina zan iya ciwon kafa ya kamani, ai in baka yawatawa kai da ciwon kafa kun kulla,
ina zan iya wani zama anan, ku da kuka ga zaku iya zama
ga guri nan amma ni kam kafata tana takalmi gara na koma in da nafi wayo."
"Wlh kuwa hajjaju da kin bari mudad'a hutawa jiya kuwa Hajiya Bishira take cewa yau direba zai kuma fita da mu mu yawata."
cewar Kulu tana washe baki.
"Amma dai anyi asara Kulu, in
a zaki yawatan da kai duk furfura,
an girma ana cin kasa,
sai kuyi ta zama ni kam dai jikoki na nake son gani,
tafiya gida ba fashi, ina zan iya da zaman shiru,
in ban da ma abokin turawa, ya kawo min ziyara wancan satin ai da tun a satin na koma Nigeria
abina,
ina zan iya shege da hauka,
tun da kunga gurin zama sai kuyi ta zama."
Kulu ta b'ata rai ita a duniya bata so ace mata tsohuwa, ta buga cinya tana mara baki.
"To Allah ya baki hakuri Hajiya."
Hajiya ta mike tana fad'in
"Bari ma kiga, ni kam naje
na fara shiri."
ta shige bedroom..
Ranar Litinin tun da Hajiya tayi sallar asuba bata zauna ba ta rika jidar kayan ta dana tsarabar datayi,
ta tarasu a parlour.
tsabar mitar da take yasa su Hajiya Bishira fito da nasu kayan badun sun shirya ba.
"Ke bi
shira sake kira min Abubakar idan jirgin ta cika yanzu direba ya kai mu tasha mushiga mota."
"Hajiya ki kara hakuri mana tun da shi jiya ya ce, an shirya mana komawa ai dai zamu koma yau, kuma ma ai har yanzu ba'ayi sallar asuba a Nigeria ba, yanzu haka y
ana bacci a barshi idan ya tashi sai a kira shi,
karfe 8 ya ce direba ya kaimu airport, jirgi zai tashi karfe 9,
kuma yanzu karfe 6 da rabi ne,
idan muka tafi yanzu zama kawai zamu sha duk mu d'ibi sanyi."
"Yoo bagara a kaimu muna kusa da jirgin har loka
cin tafiyar tayi ba, me zamu zauna yi a nan d'in, maza kirawo direba ya kaimu yanzu,
maje mu jira a can,
ke Kulu taso ki je ki kirawo direba,
ko da shike bajin yaren nasu kema kike ba,
ke Bishira da kika iya turancin je ki ce masa yazo ya kwashi kayan mu.
"
Babu yadda suka iya da Hajiya haka taje ta kirawo direba, ya kwashe su da kayan su suka tafi airport.
sun sha zama ga sanyi sai karfe 9 da 'yan mintina kafin jirgin su ta tashi.
Karfe 2 agogon Nigeria jirginsu ya sauka a babban airport d'in da ke cik
in birnin Lagos.
tun saura mintuna 30 kafin saukowar su, mota ta isa airport ana zaman jiran saukowar su.
Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci Aunty lokacin da ta sami labarin dawowar Hajiya Nigeria a bakin Baba Rabi.
dan kuwa Daddy yaki sanar mata dan
yasan dole ne hankalin ta ya tashi.
shi kansa bai so dawowan ta yanzu ba amma tun da ta kafe sai ta dawo babu yadda ya iya dole sai ya dawo da ita.
Jiki a sanyaye Aunty ta ja hannun Feeryal da yanzu dawowar ta daga school suka shige d'aki.
Abakin gado t
a zauna, ta ja hannunta tana fad'in
"Zauna Feeryal."
zama sosai tayi tana fuskantar Aunty nan da nan yarinyar da wayo sosai ya bayyana gare ta ta fahimci da akwai abin da ke damin Ammie'n tana, gashi nan tana hango damuwa shinfid'e a kan fuskarta.
Cikin
yana yin ta maikama da shagwab'a ta karyar da kai gefe kana ta yin rau-rau da ido,
"Ammie mene ne baki da lafiya ne?."
kai Aunty ta girgiza
"Lafiya ta lau Feeryal, yau zamuyi wata bakuwa ce ko ince maman maigidan zata dawo, kibi a hankali kiyi taka tsant
san wajen mu'amala da ita, babu ruwan ki da zuwa side d'in ta ko da kin ga Miemie zata je, ki zauna a in da Allah ya aje ki kiyi hakuri."
ta waro manyan gold eyes d'in ta.
ta bud'e baki cikin yanayin shiga mamaki, wan da yin hakan yaba da gudumawa wajen b
ayyanar kyakkyawan dimples d'in dake like jikin kyakkyawar kumatunta, wan da suka karawa kyawawan kumatunta kyau da k'awa.
"Ammie bakuwar tana dukan mutane ne?."
tayi maganar tana dafe kumatun ta da hannayen ta biyu.
kai Aunty ta gyad'a ta ce
"Sosai ma, k
i kiyaye babu ruwan ki da zuwa gurin ta, duk lokacin da taso kije gurin ta sai kije."
d'an karamin bakin ta cuno ta ce
"Bazan je bama kar ta duke ni."
"Oya to taso muje kiyi wanka."
"Ammie ni zanyi da kaina na iya fa, Miemie ma da kanta take yi."
"To dai m
uje nayi miki yau gobe sai kiyi."
Motar su Hajiya ce ya faka a parking lot d'in side d'inta.
in da tuni mutanen gidan suka hallaro suna oyoyo.
jikokin ta suka rufu