Showing 15001 words to 18000 words out of 86898 words

Chapter 6 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

komai suka fito tare da Baba Rabi.

Abin

mamaki a zaune a tsakiyar parlour in da ta aje ta da fari tana wasa, agurin yanzu ta tarar da ita, zaune tana wasa, jikin ta tsaf babu d'in komai.

kallon saman dinning tayi shima a kimtse komai na zaune a gurin zamansa.

Baba Rabi tayi wa Aunty sai da safe

tayi waje bayan ta gama yi wa Feeryal d'in wasa,

har Aunty ta juya zata wuce bedroom sai kuma ta juyo ta dawo inda take ta mika hannun zata d'auke ta ba shiri ta cire hannunta a cikin ta tayi wani irin mikewa ta ja da baya da sauri jiki na rawa.........!

Mommyn Twins ce

🌺🌺

*FEERYAL*

🌺🌺

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*____________________________________*

*

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S

✍

🏼

*

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition i

s to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*

πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________

___*

*Bismillahirrahmanurrahim*

πŸ…Ώ

️

5

Wani zabgegen maciji tagani sakankanin kafafuwanta, a kanannad'e acure guri guda ya fasa kai.

takuma yin baya a muguwar razane,

da karfi ta furta "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!."

cikin tsananin kad'uwa.

t

ana furta kalmar innalillahi da sauri macijin ya shiga ware jikinsa yana bi ta kan kafafun Feeryal da ke zaune tana wasa da shi, yanufi kofa yana isa dai-dai bakin kofa ta nime shi ko sama ko kasa ya b'ace mata bat bata kuma ganinsa ba,

bata kuma san ta i

n da ya bi ba dan kofar a rufe take.

Rasashi ke da wuya tasoma jin wani kara mai cike da amon sauti na dukar can cikin kunnuwanta.

da karfi ta rumtse ido tare da kai hannu cikin kunnenta da take ji kamar dodon kunnuwan nata zasu zazzago su fito waje.

ji t

ayi ana fad'in

"Ke kad'ai bazaki iya bata kariya ba dole sai da taimakon muuuu!."

kuma toshe kunnuwanta tayi da karfi tana juyi had'e da tangad'i har sai da ta zube kasa.

a dai-dai lokacin da taji kamar an fisge mata dodon kunne, nan da nan wani uban zufa

ya shiga keto mata.

a hankali kuma taji yanayin ya d'auke cak cikin second 1 tadawo dai-dai.

Da sauri ta mike zaune tashi ja da baya tana bin Feeryal da kallon tsaro.

ita ko yarinyar baki ta b'are tana mika mata hanu alamun ta d'auke ta.

Cikin rawar mu

rya Aunty tashiga fad'in

"Ban tab'a cutar da ke ba, ban d'auko ki dan na cutar da ke ba,

sai dan na taimake ki, ki dubi girman Allah kada ki cutar da ni,

zan mai da ke in da na d'auko ki,

nayi zaton ke d'in jinsin mu ne shiyasa na d'auko ki, ban d'auko ki

dan na cutar da ke ba!."

Gaba d'aya Aunty ta birkice ta ko ta ina a jikinta b'ari yake, tsoro mai tsanani ya baibaye ta.

ta kasa iya mikewa kan jafafunta sai ja da baya take a zaune.

Jin karar bud'e kofa ta waigo da sauri a bala'in razane, dan tagam

a zaton macijin ne ya dawo.

ganin Daddy ne ya shigo da sauri ta mike a guje tayi gurin shi,

ta fad'a jikin shi ta kankameshi da karfi tana fad'in

"Daddy maciji na ganshi da ido na! dan Allah ka d'auke ta ka mai da ita in da muka d'auko ta,

wlh nahakura z

anci cigaba da zama a haka gara na tabbata a matsayin juya, na hakura bana son d'a zanyi rayuwa ta ni kad'ai a haka!."

Da sauri yadad'a rukota sosai ganin yadda gaba d'aya ta fita hayyacin ta.

ya janyo ta suka karaso cikin parlour, ya zauna kan kujera tar

e da zaunar da ita a gefen sa.

"Fad'imatu."

ya kira sunan ta yana kallon fuskarta.

ido ta zuba masa sai kuma ta girgiza kanta kamar wacce ke son dawowa hayyacin ta.

ta yunkura zata mike da sauri ya ruko ta yakuma duban ta da kyau ya ce

"Ki dawo hayyacin k

i."

wani nannauyan numfashi ta sauke da sauri ta waiga gefe da gefen ta sai kuma ta maida duban ta gareshi.

"Fad'imatu." yakuma kiran sunan ta

murya a raunace.

kai ta girgiza ta ce

"Daddy."

"Numfashi ya fesar sannan yakuma rukota da kyau ya ce

"A ina kik

a ga macijin Fad'imatu? akaf fad'in gidan nan da kewayen sa, ba macijiba ko kwaro in har mai cutar wa ne bai isa ya matso yankin gidan nan ba, ta ko wane kusurwa;

tazarar taku dubu ne ta ko wata kusurwa sakanin mu da duk wani nau'in kwaro mai cutar wa,

ko

ta sama ko ta kasa,

sam maciji bazai iya shigowa gidan nan ba, a zagaye gidan nan yake da maganin su,

idan kuwa sukayi gigin shiga to kuwa zasu mutu tun kan su karaso,

koda ta cikin karkashin k'asa ne kuwa."

"Daddy na ganshi da ido na fa babba ne sosai

agaban Feeryal tana wasa da shi, kuma naji ana magana da karfi kamar za'a fasa min kunne,

ni dai a maida ita kawai wlh na hakura."

shiru ya yi yana kallonta a kasan ransa yake fad'in

"Anya ba aljanu ne ke son shafarta ba?."

kwana biyu gaba d'aya yaga yanay

in ta ya sauya, abin da bazai faruba tarika cewa ya faru.

kai ya jinjina sannan ya ce

"Gizo ne kawai."

da sauri ta ce "A'a Daddy wannan kam ba gizo bane nagani da ido na da gaske ne."

"D'azu bakya hayyacin ki Fad'imatu akwai abin da ke shirin faruwa da ke

, yakamata a dakile faruwar hakan,

ina zuwa."

Yafad'a yana mikewa ya nufi bedroom yafito d'auke da Alkur'ani mai girma ya dawo in da take, ya bud'e ya mika mata.

ya ce "Kirika karantawa ina zuwa, bari naje na dawo, dan shi yafi komai kariya."

Ya isa ya d

'auki Feeryal data fara kuka ya ajeta a gefenta.

yana cewa

"Ta gaji da zamane ko tana jin yunwa."

ido ta bita da shi harga Allah tsoro take bata yanzu.

Cikin hanzari yafita, Daddy yakai awa d'aya zuwa d'aya da rabi kafin ya dawo.

a bedroom ya same su dan

ta sami kwarin gwuiwa da taimakon karanta Alkur'anin da tayi, har ta ji karfin zuciya ta d'auke ta ta je tamata wanka, tana gama shiryata kuwa tayi bacci.

Daddy ya mika mata kullin laidar daya shigo da shi.

ta karb'i laidar tana d'an jujjuyashi a hannunta

sai kuma ta kunce laidar.

da mamaki take kallon kulli-kullin magunguna.

da fuskar tambaya ta dube shi,

sai kuma taga ya d'au abin saka kuraren wuta ya jona shi gijin wuta,

yana fad'in

"Hayaki ne da wanka na karb'o miki, zo maza kiyi hayakin anjima in zak

i kwanta kiyi wankan maganin sai ki kara yin hayakin."

"Hayaki da wanka kuma? asabo da me ni fa lafiya ta kalau."

kai ya girgiza ganin ba tasowar zatayi ba ya janyo hanunta.

"Aljanu na son shafarki kice lafiyan ki lau, ina kuwa batun lafiya anan."

"Daddy k

ada ka rika yarda da wad'annan masu magungunan karyar fa."

"Zauna dan Allah."

ya yi maganar yana zaunar da ita.

da kansa ya bud'e yahakin ya saka yakuma rufeta da hijabinta kamar yadda aka ce masa.

sai da ya tabbatar hayakin ya ratsata sosai tana ta sauke

tari da atishawa kafin ya bud'e ta.

yana fad'in

"Sai dai su kare a haka amma bazasu tab'a samin damar shigar jikin ki ba."

ita dai ido ta bisa da shi.

Da daddare kafin ta kwanta sai da ya tabbatar da tayi wankan maganin da hayaki.

duk da bataso ba.

Wash

egari da safe Aunty ta fito zata nufi kichin, tana bud'e kofar bedroom taga wani katon zomo fari soll,

idanunsa manya masu matukar razanarwa. yana zaune a dai-dai tsakiyar bakin kofa,

ya d'aga kunnuwansa sama yana juya idanun nasa da sam basuyi kama da ida

nun zomo ba.

wani irin juyi ta yi da farfe ta maida kofar ta rufe.

Tana waigowa kirjin ta ne yawani irin tsinkewa hango sa da tayi kan gadon Feeryal, wacce ke bacci yanzu kafin ta fita sai da ta gyara mata kwanci,

sai ga shi ta ganta zaune suna wasa da zo

mon da ta gani a bakin kofa,

yanzu-yanzu da ko second 1 baiyi ba

wani uban kara ta sake sakanakon had'a ido da shi da idanunsa masu matukar ban tsoro.

ta yanke jiki ta zube kasa.

Da sauri had'e da gudu Daddy dake cikin bathroom yafito, ya yi kanta cikin

hanzari yana jijjigata da kiran sunan ta.

gani bata ko motsi da sauri yaje ya d'au gorar ruwa yazo ya yayyafa mata.

numfashi mai karfi ta sauke ta zabura zata mike, da sauri ya ruko ta.

"Fad'imatu mene ne ki natsu."

hannu ta shiga nunawa in da Feeryal ta k

e

"Yana can yana can akwai wani abakin kofa."

ya waiga in da take nuna masa baiga komai ba, sai Feeryal da ke zaune.

ya ce

"Babu komai fa ni ban ga komai ba, bakiyi hayakin nan ba yau, muje maza kiyi."

ya d'agota suka karasa cikin d'akin.

Ranar haka Aunt

y ta wuni sukuku lamarin nason fin karfinta

β˜…β˜…

Tekun Matip acan cikin fadar sarkin aljanu Matip,

dake karkashin teku cikin wani katon kasurgumin kogo mai matukar girma.

duniya ce guda a gurin.

matakan tsaro ne jiga-jigai masu matukar had'ari.

kifaffen m

asarautar da aka kifeshi tun tsawon shekaru d'ari biyu da hamsin da suka shud'e.

shine yakuma dawowa daram.

shugaba sarkin aljanu Matip yake cigaba da mulkarsa.

bayan tsawon shekarun da ya yi a tsare a kuma garkame sakamakon faruwar wani lamari.

Manya-ma

nyan jiga-jigan dodanni aljanu majiya karfi masu tsuffar ban tsoro ne ke tsaron kofar masarautar, tasama da kasa.

Acikin fada sarki aljani Matip ne zaune a kan karagarsa na alfarma da aka yi sa da gundarin zinari.

ya yin da fadawa ke zagaye da shi.

Sarki

aljani Matip ya dubi wazirinsa Kutub sannan ya yi gyaran murya, ya ce

"Akirawo Tarmuzu yanzun nan."

waziri Kutub ya dukar da kai ya ce

"Angama ya shugaba na."

wani kambu dake rike da shi ya murza cikin second 1 wani aljani ya bayyana a gaban sarki Mati

p. yazube gaban sa yana fad'in

"Na amsa kira ya shugaba na."

Sarki Matip ya dubesa sannan ya ce

"Tarmuzu Kudakata haka ku dai na bayyana ta ko wata tsuffa kuna razanin uwar gijiyarta,

zata rasa samin kula yadda ya kamata idan hakan ta faru kuma bazan yafe

muku ba!."

"Tuba muke ya shugaba na a gafarce mu."

aljani Matip ya girgiza kai sannan ya d'aga masa hanu, nan take yab'ace..

Kimanin sati biyu kenan Aunty bata cikin walwalar ta, sai baya-baya take da Feeryal burin ta dai surabu lafiya.

kullum dai Daddy

na karfafata da bata kwarin gwuiwa, yana ta so yaga ta cire kokonto kan Feeryal d'in, duk da shima yanzu lamarin yafara jefashi cikin nazari.

sun shefe tsawon sati gudannan bata kuma ganin wani abin tare da Feeryal ba.

sai dai wani lokacin idan ta barta i

ta kad'ai takanzo ta same ta tana ta wasa kamar tana yi da wani, haka nan zata d'auke ta, dan tayi alkawarin cigaba da kulawa da ita, amma cikin takasantsan burin ta dai surabu lafiya..

β˜…β˜…

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Feeryal nata dad'a kara wayo, ya yi

n da suffarta dake saka kokonto cikin zukatan duk wanda ya ganta ke dad'a karuwa.

zuwa yanzu Aunty ta saki zuciyar ta da Feeryal.

har ta yarda abaya wancan lokacin da take gane-ganen Feeryal tana wasu abubuwan da gaske gizo ne, da kuma sharrin shed'anun al

janu da suke son shafarta kamar yadda Daddy ya fad'a mata.

sosai ta dawo kula da d'iyarta.

tuni Feeryal ta kai na yaye aka yaye ta..

Kamar wasa rayuwa mai tafiya da sauri shekarun Feeryal hud'u ke nan, amma a zahiri idan ka ganta zaka iya kira mata sheka

ru biyar har da d'ori.

Aunty bata barinta fita ko nan da can,

iyakacin ta cikin side d'in da farfajiyar sa zuwa garden d'in cikin side d'in.

bata zuwa side d'in kowa a gidan, kamar yadda kowa ma baya zuwa nasu side d'in.

in banda Hajiya Safiyyah da kuma 'y

arta Meimei sa'ar Feeryal ce,

sai dai ta d'an girme mata ita shekarunta shida ke nan,

amma kusan tsawon su d'aya,

sosai Feeryal ta saba da Meimei, Hajiya Safiyyah tana kawota suyi wasa da ita.

Ganin bakinta ya bud'e sosai da magana,

Daddy yace za'a sata

a makarantar su Ameerah.

Ranar wata juma'a Daddy na zaune a parlour'n sa yana waya.

Mommy ta shigo parlour'n ta taras da shi na waya, ta zauna gefe tana saurarar abin da yake fad'a

"Ashirya mata duk abin da ya dace zuwa ranar Monday nake so ta fara zuwa m

akarantar, a kawo mata uniform da sauran abubuwan bukata gida ranar Lahadi,

Monday kuma ta fara zuwa."

yana sauke wayar Mommy ta bishi da kallon tambaya

"Alhaji wa kuma za'a canzawa makaranta, kar dai ace Ameerah sarkin rigima ce ta kuma tada buren sai an

sauya mata wani makarantar?."

ta karashe maganar tana washe baki da jin dad'in fitinar d'iyar tata.

Daddy ya ce

"Ai naga alama Ameerah yanzu tana son makarantar nan, tun da najita shiru bata kuma tada borin a canza mata wani ba,

Feeryal ce za a kaita maka

rantar tasu."

Da mamaki ta ce "Feeryal kuma wacce Feeryal d'in?."

dan ita tagama mancewa da wata Feeryal a gidan ma, dan tun lokutan baya da suka tab'a tafiya saceta sukaga abin da yafi karfin su.

tun da suka gudu basu sake gigin kuma zuwa ba, a sannu kum

a suka mance da batuntu, tun da ba ganin ta suke ba, bugu da kari kuma gargad'in da Daddy ya yi musu, kan duk wanda ya fad'awa hajiya abakin auren ta.

Daddy ya ce "Feeryal y'ar wajen Fad'imatu mana."

wani uban ashar Mommy ta mulmulo tare da buga kirji ta g

walalo ido waje

"Kutumar ubancan Alhaji dama aljanar nan tana gidan nan!? muna shakar iskar numfashi d'aya da ita?

wato Fatima b'oye aljanar nan taye,

ta b'oye bakar gamasheka tayi ta raino harta hab'aka tazamo muguwar dafi,

to wlh bata isa ba

dolen ta

tabar gidan nan, dan wlh bazamu rayu da aljana ba,

wai kuma har kake batun sakata a makarantar su Ameera, wlh bazai sab'u ba, bazai yuwu a had'a mana ya'ya da aljana ba, taje can ta karaci tsiyarta."

"Ke Halima ina ruwan ki, idan an sakata a makarantar su

Ameerar ke zaki biya kud'in ko me? ki cire bakin ki a lamarin yarinyar nan tun ranki bai b'aci ba, idan aljanar ce sai me ni na shirya taimakon ta."

zumbur ta mike tsaye har tana kumfar baki

"Wlh ba a isa a sakata makaranta d'aya da ya'yan mu ba,

Alhaji ka

fa fitar da mayyar aljanar nan a gidan na, idan kuma ba haka ba to mu zamu kwashe ya'yan mu mubar mata gidan,

dan bazamu zauna da mayyar aljana ba,

Fatima ta gama asirce ka takawo mayya gida ka runguma wane d'iyar cikin ka,

sabo da haka ka hana Hajiya dawo

wa kasar ma baki d'aya, to wlh asirinsu sai ya tonu,

babu abun da zai hana ni sanarwa hajiya komai,

dan wlh ina ji ina gani kam bazan zauna da mayyar aljanar ruwa ba!."

Daddy ya gyara zaman sa tare da d'aukar gilashin sa ya saka, ya mai da dubansa kan TV

sannan ya ce

"Sai dai kubar gidan nan badai Feeryal ba kam, je ki sanar wa Hajiya daga nan kinsan sauran."

Fuuu tayi waje tana cigaba da zazzage buhun masifa

ba'a isa a had'a musu ya'yan su da aljana a makaranta d'aya ba.

Har ta isa side d'in ta bata fasa

masifar ba,

ta kirawo Umma Karima ta sanar mata da abin da ke faruwa.

a bujajan Umma Karima ta taho side d'in Mommy

tun daga bakin kofar parlour ta ke fad'in

"Kar ki gayamin wannan zance Hajiya Halima, ya akayi mukayi bacci ne bamu farka da wuri ba,

Eh la

llai Fatima tasan me tayi, wato sai da tabi kowa ta toshe masa baki, tasaka kowa baccin ido biyu ta yadda babu wan da zai kuma batu kan aljanar nan,

hahahaa wlh karya kike Fatima bokanki ya yi kad'an."

tawani saki makirin dariya takaraso cikin parlour'n t

a hakimce kan kujera.

Da sauri Mommy ta ce

"Meye mafita Hajiya Karima, idan fa bamuyi da gaske ba, Hajiya Fatima zataga bayanmu."

"Akwai mafita amma bazamu sami ganin Mali ba sai nan da karshen wata sabo da sun shiga mitin natsawon wata guda,

sai dai mu

yi hakuri zuwa lokacin."

kai Mommy ta girgiza tana ciza yatsa.

Farida da Sumayya dake zaune can gefe suna karatu a littafan makarantar su,

Farida ta rike had'a tana wani yamutsa muska cike da iyayi da manyance kamar uwar mata ta ce

"Yanzu dama har yanzu y

arinyar nan tana gurin Aunty? sai da Hajiya ta ce wa Daddy su mai da ita

cikin ruwan da suka d'auko ta shine suka ki, ai Hajiyar zata dawo."

ta karasa maganar cike da zallar manyance da rashin kwab'a irin na iyaya.

idan manya suna magana

sai yaro ya tso

ma baki, ba a hanashi ahaka duk

suka gina ya'yan su.

babu kwab'a ko kad'an.

"Ai rannan da naje side d'in Aunty na ganta tagirma kamar Ameerah, har ta ce zata bini Aunty

ta ce ta zauna, kun ga in da tayi kamar Miesho

nacikin Film d'in Tigezam, har idon s

u iri d'aya

da gashinsu."

cewar Sumayya tana waro ido.

Harara Mommy ta banka mata ta ce

"Ai ke kam albasa batayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login