Showing 6001 words to 9000 words out of 86898 words

Chapter 3 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

aljanar nan, naganta tana sa mata kaya."

huf Umma Karima ta mike ta ce "Ke wai da gaske kinga yarinyar nan a sashinta, eh lallai Fatima anyi bakar munafuka wato boye 'yar tayi,

ko komawa tayi takuma d'auko ta, to wlh s

ai ta bar gidan nan."

tayi waje fuuu sai sashin Hajiya.

Kirji Hajiya ta buga da jin abun da Umma Karima tazo dashi.

Hajiya ta mikawa Umma Karima waya tana fad'in

"Lalub'o min lambar Abubakar yanzu-yanzun nan, wai ni Abubakar zai maida mutumiyar banza, ya

zab'i tsintacciyar aljana a kai na."

Daddy na d'aga wayar Hajiya tafashe da kuka tana fad'in

"Ni zakayiwa haka Abubakar wlh yau babu abin da zai zaunar da ni a gidan ka, yanzu-yanzun nan zan bar maka gidan ka,

kacigaba da zama da matarka da bakason b'aci

n ranta da aljanar da ta tsinto."

Hajiya ta kashe wayar tana sharb'ar hanci, tamike ta nufi bedroom d'in ta tana fad'in

"Ina zan iya zama da annoba a gida d'aya, gara natattara inawa-inawa na koma Yalwa yafi min kwanciyar hankali."

Umma Karima ta saki mur

mushi akasan ranta tana fad'in

"Fatima ke karamar makira ce."

tamike tafice takoma part d'inta.

Cikin hanzari Daddy yashigo side d'in Hajiya, yana shiga parlour'n ta,

Hajiya nafitowa janye da akwati.

da sauri ya isa inda take yana fad'in

"Dan Allah Haji

ya kiyi hakuri kada ki tafi."

"Bani guri da alla! in zauna inmaka me?, ni da bani da mutunci agurin ka,

gara nabaka guri kacigaba da zama da wad'an da kake ganin su da kima,

ina dalili ina mafari zama da aljana guri guda, ina bil adam, kai da kazabi haka

sai kayi ta zama da ita,

amma kasani idan jikokina suka sami wata matsala bazan yafe maka ba!."

Da sauri Daddy yarike akwatin ganin tana kokarin tafiyar da gaske ya ce

"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki gafatarce ni, kada ki tafi, za'a maida ita inda aka d

'auko ta dan Allah kiyi zamanki."

"Ni Abubakar ai ka gwada min iyakata aljanar ruwa tafiye maka ni,

ni uwar da na haife ka naci kashinka, ni Abubakar ni."

Hajiya tasaki kuka tana sharb'e hanci da bakim mayafinta.

akwatin ya karb'a a hannunta yana

"Yi hak

uri dai Hajiya yanzu za'a fita da ita."

yaja akwatin ya maida shi ciki bedroom, yafito ya isketa zaune a parlour.

hakuri yacigaba da bata sai da yaga ta d'an sauko kafin yafita.

A b'angare Aunty lokacin da Hajiya ta kira Daddy shigowar sa side d'in ta ke

nan, ko zama baiyi ba yafita zuwa kiran Hajiya.

Kuma jin motsi yasa Aunty fitowa, ganin Daddy ne ta karaso in da yake jiki ba kwari.

murmushi ya yi mata domin karfafa ta, fuska ta dan marairaice ta ce

"Hajiya bata hakura ba ko?."

zama ya yi a bakin gado y

ana fad'in

"Zanji da ita zaki rayu da Feeryal insha'allah, nayi miki alkawari."

zama tayi gefen sa kana ta ruko hannunsa tana jaddada godiyar ta a gare sa.

tana mai alfaharin kasantuwar sa a matsayin abokin rayuwarta,

dan bai tab'a rageta da wani abu ba,

duk abin da ta nima a gurin sa tana samu; hakan kuma baya rasa nasaba da so da kauna da kuma yardar da yake yimata.

Wanda itako take saka masa ta hanyar nuna masa tsantsar kulawa mai had'e da zallar soyayya da nuna damuwa kan abin da ka damu da shi.

Hak

an yasa abokan zaman ta suke ganin tagama mallakesa ta hanyar asiri, wan da sam abun ba haka yake ba, Hajiya Fatima babu abin da ta tsana take kyamatar sa sama da bin bokaye da malamam tsubbu.

Hajiya Fatima mata ce mai hakuri da juriya gami da kawaici, ta

na da matukar hakuri ga ladabi da biyayya; tsafta iya girki iya kwalliya, iya tafiyar da miji yadda ya kamata, uwa uba ruko da addini.

shiyasa tazamo lamba d'aya a gurin maigidan nata wato Alhaji Abubakar Fiya.

Da yamma Daddy yashigo sashin Hajiya, H

ajiya na ganin sa ta b'ata fuska, ya isa ya zauna yana yi mata barka da warhaka.

ta katse shi da fad'in

"Har kun dawo daga mai da aljanar in da kuka d'auko ta, ko yaya?

wlh Abubakar ka kiyaye ni in ban da rashin hankali ina kai ina taimakon aljanu,

kai da

bakada da wata sari a jikin ka, ko wannan maganin tsari idan nabaka kayi amfani da shi saboda makiya bakayi, bare kayi wa kanka kyakkyawan shiri;

kana nan bakasan da wasu irin mutane kayi huld'a ba, makiya ta ko ta ina sukan iya rab'ar ka, kai har matan

da kake aure ba abun yarda bane a wannan zamanin,

amma ka tattara yarda kaf ka d'aurawa Fatima, gashi har ta fara kaika ga halaka,

ai ko matan da suka haifa maka ya'ya Halima da Karima ba zaka tattara yarda duk ka daura a kansu ba,

bare Fatima da bata a

je ko d'an hanji agidan nan ba,

shine zaka biye mata ku d'auko aljana har ka lamunce ta shayar da ita,

kaga daga nan sai duk tashige jikin mutanen gidan nan, ayi ta jinya har kud'i ya kare dama abin da takeso kenan,

shi mutum a rayuwarsa baya son ganin wa

ni yaci gaba."

Kai Daddy ya girgiza ya ce

"Kiyi hakuri Hajiya ai shi kariya yana daga Allah, idan kayi ruko da addu'o'in da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam,

ya koyar babu mutum ko aljanin da zaiyi galaba a kanka,

ko kin mance daga gidan manya Fa

d'imatu ta fito, wani dukiya ne zai tsole mata ido."

"Eh ai kai a kan Fatima da uban kowa ma zaka ja, tun da ka iya ja da ni,

su sauran da suka fito a tsatson talauci sun fita sau dubu, tun da suka iya haifo min jikoki, tana nan shekara goma da d'ori, ko

b'atan wata bata tab'a yi ba."

Kai ya girgiza sannan ya ce

"Kiyi hakuri Hajiya shifa haihuwa na Allah ne kada muja da ikon Allah."

"To jamin aya tun kan a haifeka nasan wannan."

kai ya kuma girgizawa kana ya ce

"Dama Hajiya nazo ne na sanar miki zaki tafi

umura ke da Bishira, daga nan zaku kuwuce Egypt kuga likitan idon ki, gobe da karfe 7 na safe jirkin ku zai tashi,

nasanarwa Bishira zata taho da daddare gobe sai ku wuce."

Hajiya Bishira kanwarsu Daddy ce autar Hajiya ke nan, tana zaune a gidan gadon

'ya'yan ta, mijin ta Allah yamasa rasuwa shekara d'aya daya wuce ya barta da yara biyu,

mace da na miji.

Baki Hajiya ta washe "Kai dama idon nan ya dame ni da kaikayi yanzo ko har ruwa yake idan ya fara kaikayin nan,

ko d'azu sai da nayi ta sosashi kafi

n naji dad'i."

"Hajiya shifa ido baya son hanu bakiji abin da likita ya fad'a miki ba, idan fa kika matsa da sosashi za'a sami matsala, ana sammanin ya iya rufewa ma."

da sauri ta ce

"A'ah a'ah ai kad'an na sosa ba da yawa ba,

kuma ina sa magani kullum,

id

o na bazai makanta ba in Allah yaso, ni dama can ganin likitan muka fara zuwa kafin muje saudin, ai likitocin tacan sunfi kwarewa zasu bani maganin da zai warke da wuri, kai wannan ciwo Allah yaraba bawa da shi."

Gaba d'aya Hajiya ta rud'e, ba karamin raz

ana take a duk sanda taji anyi mata zancen idonta zai iya rufewa ta makanta ta daina gani ba.

tana matukar taoron jin idonta zai iya rufewa bata kaunar makanta a rayuwar ta.

cike da fargaba ta dubi Daddy ta ce

"Amma dai zan warke bazan makanta ba ko!?."

ka

i Daddy ya gyad'a ya ce

"Insha'allahu zaki warke Hajiya babu abin da zai sami idanunki, amma dai kirika kiyaye wa ki rage sosa idon."

"To-to ai insha'allahu ma na daina da zarar naji kaikayin zan saka masa magani."

Kira ta kwalawa Kulu mai aikin ta

"Ke

Kulu d'auko min maganin idon nan nasaka."

"Hajiya a ka'idance ake saka maganin ciwon ido ba ko da wani lokaci ba."

"Ai dai Abubakar yau ma ban saka ba ko sau d'aya, barni kawai nasaka yanzu."

kai ya girgiza ita da ta ce, d'azu ta saka da idon ya dame ta da

kaikayi yanzu kuma ta ce bata sakaba, Hajiya ke nan ba'a kaunar abin da zai tab'a lafiyar jiki.

Ya mike yana fad'in

"To Allah ya sauwaka sai ayi miki shiri da wuri, zaku tafi da Kulu dan ku sami mai yi muku d'an wasu aikace-aikacen."

Hajiya kam gaba d'ay

a hankalin ta ya koma kan maganin da take ta afkawa idon ta, har Daddy ya fita.

Aunty na zaune tana shayar da Feeryal bayan tayi mata wankan yamma, kiran Daddy yashigo wayarta.

da sallama ta d'aga kiran; daga cijin wayar Daddy ya ce

"Ammien Feeryal ba'a

bani abincin rana ba har dare ya soma yi."

kai ta dafe tare da fad'in

"Ya subhanallah ayi min afuwa gani nan zuwa insha'allah."

ta sauke wayar ta mike da sauri tare da gyara rukon Feeryal a kafad'ar ta, ta nufi kichin cikin hanzari.

Baba Rabi ta tarar tan

a ta goge-gogen kichin, Baba Rabi na ganin ta tayi saurin d'an risinawa tana far'in

"Barka da warhaka Hajiya."

"Yauwa barka dai Baba Rabi sannu da aiki, wai me kika dafa ne? gaba d'aya na mance da abincin Alhaji."

"D'aya daga cikin abun da kike so aka dafa

Hajiya."

kyakkyawar tukunyar dake kan gas Baba Rabi ta bud'e, wani daddad'an kamshi ya bigi hancinsu.

lafiyayyen jalof d'in shinkafa da macaroni yaji kifi da nama yasha kayan lambu irinsu karas da fis.

Kai Aunty ta girgiza ba laifi girkin ya had'u, Baba

Rabi kwararriya ce a fannin girki, tana daga cikin ma'aikatan da suke aikin girki a gidansu. shiyasa da tayi aure ta bukaci mahaifiyarta da ta bata ita su taho tare dan ta yarda da iya girkinta.

amma duk da kwarewar ta a fannin girki, bata lamunce ta girka

mata abincin da mijinta zaici ba, ita da kanta take shiga kichin tayi masa girki a duk sanda yake gurinta.

Kai Aunty ta d'an dafe tana tunanin idan fa tace zatayi masa wani girki yanzu lokaci zai kure.

kuma tana da tabbacin baici komai ba tun bayan abinc

in safe.

da fuskar tausayi Baba Rabi take duban Aunty sanin dalilin da yasata mancewa da lamarin girkin maigidan nata.

sakamakon Hajiya data d'agawa kowa Hankali kan sai an maida Feeryal inda a ka d'auko ta.

cikin muryar tausasawa ta ce

"Kikara hakuri Ha

jiya."

murmushi Aunty tayi kana ta ce

"D'an rike min ita haka."

ta mika mata Feeryal, ta isa ta d'auki wani kayataccen kula mai matukar kyau da burgewa da ka ganshi kasan ba kirar nan bace, ta zaro wani farin karamin towel da suke a jere a ma'ajin su na mu

samman.

ta goge kulan ciki da waje, ba wai ko dan ya yi datti ba al'adar ta ce hakan.

sannan ta zuba abincin ta rufe kular.

kana ta d'au plt da cokali da sauran abubuwan da ake bukata wajen cin abinci, tasaka su cikin

Kyakkyawan basket na musamman.

Ta du

bi Baba Rabi tana fad'in

"Yauwa bari naje na kai masa, ki kula da ita kafin na dawo."

"To Hajiya." Baba Rabi ta fad'a tana mamakin yau abincin data girka zata kaiwa Alhaji, sai dai taga sauri tattare da ita, wan da shi yahanata tsayuwa girka masa wani abin

cin.

Sai da Aunty ta koma bedroom ta d'au mayafi kafin ta fita ta nufi sashin Daddy.......!

Mommyn Twins ce

🌺🌺

*FEERYAL*

🌺🌺

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*_Littafin na kud'i ne 500 account no 31

70524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S

✍

🏼

*

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate t

he mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*

πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Bismillahirrahmanur

rahim

πŸ…Ώ

️

3

Direct bedroom d'in sa ta wuce, a zaune ta taddashi kan wani lafiyayyen dogon kujerar da ke sakiyar katafaren d'akin nasa, mai matukar kyau da tsaruwa.

yana zaune yana duba wasu takardu ya yin da gefe guda yake lasa laptop d'in sa.

gefe d

a shi ta zauna tana yi masa barka da warhaka, kana ta d'aura da fad'in

"Ayi min afuwa a gafarce ni."

murmushi ya yi sannan ya ce

"Ina Feeryal data kwace min ke?."

itama murmushin ta yi kana ta ce

"Tana gurin Baba Rabi."

kai ya jinjina. ta zubo abincin ta j

anyo karamin table ta d'aura kai, sannan ta mike ta isa in da fridge ya ke ta bud'e ta ta ciro lemon da yafi so; had'e da kunun ayan da take masa na musamman take aje~ masa cikin fridge in sa, ta dawo ta zuzzuba masa cikin cups.

ta zauna a gefen sa yana ci

tana had'a masa kan takardun daya wargaza su.

"Insha'allah ko mai yazo karshe na shiryawa Hajiya tafiya umura gobe, daga nan zasu wuce Egypt taga likitan ido, zasu zauna a gida na dake can nad'an wani lokaci kafin su dawo, insha'allah daga nan komai zai

dai-dai ta."

duban sa Aunty ta yi tare da sauke numfashi ta ce

"Allah ya sa."

"Amin amin." Daddy ya fad'a yana kurb'an kunun ayanta mai sashi santi.

yana ci tana d'an janshi da hira cikin sigar jan hankali ta in da zai ci abincin sosai.

Yana kammalawa ta

had'a kan kayakin cikin basket.

ya ce taje ta tuba Feeryal kada ta yi kuka, sukayi sallama ta fito, dan yau ce ranar da zai bar d'akinta.

shiyasa ma ya dawo side d'insa.

dan idan itace da kwana sashinta yake tarkasawa ya koma, har sai ya yi mata kwana biyu

n kafin yadawo side d'in sa da yamma.

sauran matan kuwa nan suke zuwa su same sa, sunyi fad'a har sun gaji kan suma sai dai yarika biyo su,

ya ce dasu duk wacce bazata iya zuwa ba ta zauna abinta baiyiwa ko wa dole ba.

A kofar parlour'n sa suka had'u da U

mma Karima tana kokarin shigowa.

kallon banza tabi Aunty da shi tare da yamusa fuska cikin gatse ta ce

"Uhum iyayen jaraba har ya gudo ya dawo ma ba'a kyalesa ba, me yakawo ki nan a wannan lokacin, bakida hurumin zuwa nan yanzu, sai ayi gaggawar fita a bam

u guri, in ba satar kwanan za ayi ba da ma an saba,

kada kuma ki sake ki ce zaki rika shigo mana da aljanar nan nan, ya'yan da ya haifa sune kad'ai ke da hurumin shigowa side d'insa, ba agolar aljanar ruwa mayya ba."

Murmushi Aunty tayi kana ta ce

"Ni da

mijina har sai an iyakanta min san da zan zo inda yake?

a duk san da na bukaci zuwa in da yake zanzo; ko da kuwa a d'akin barcin ki yake, har a yanzu yana cikin lokaci na daga nan har zuwa fad'uwar rana,

ba ke ba ko wacce zai koma gurin ta yau bata da iko

n dakatar da ni, zuwa in da mijina yake."

Aunty na kaiwa nan ta rab'a gefenta tayi gaba abinta, bata kuma bi ta kanta ba.

dan bata fiye biye musu ba idan suna haukansu, manna musu hauka take tabarsu suyita haushin su.

Umma Karima tabi bayan ta da harara

da basket d'in da ke hannunta, tasan abinci takawo masa yaci.

hakan ma bakaramin kona su yake ba, dan ba kasafai yake cin abincin su ba.

a kufele ta karasa ciki, tun kan ta karasa cikin bedroom d'in sa tasoma mita

"Alhaji abinda kake mana fa baka kyauta ma

na, mu masu ya'ya mu ne abun wulakantawar ka, mu mukasan zafinka mu yakamata ka daraja mu."

hannu yad'aga mata kana ya ce

"Yanzu ni kin daraja ni da kika fad'a min d'aki kai tsaye babu ko sallama bare gaisu,

babu tausasa lafazi, me nayi muku na rashin kya

utatawa?."

fuska ta yamusa tana cika tana basewa ta tsaya a tsaye a kansa tana fad'in

"Shekara nawa baka cin abincin mu tun da ka auro waccan matar ka ya ye cin abincin mu, a nan duk ran kwanan ta side d'inta kake tarewa, kana gurin mu ma tana biyo ka da a

binci."

Dakatar da ita yakuma yi ta hanyar kuma d'aga mata hanu ya ce

"Ya isa, ai na fad'a muku duk sanda kuka shirya yin girki da hannunku zan ci."

"Haba Alhaji me zai sa mu yin girki bayan ga masu aiki har rai nawa, babu kalar girkin da basu iya ba,

Al

lah ya bamu hutu sai kuma mu kasa hutawar,

a ce duk wannan daular da muke ciki mukasa hutar da rayuwar mu sai mun bautatu,

haba Alhaji ai kai yakamata ma ka ce mu huta, ma'aikata sucigaba da hidimta mana."

Kai Daddy ya girgiza kana ya ce

"Fad'imatu duk da

kaancewar ta d'iyar masu kud'i; bata d'auki girman kai ta sawa ranta ba, da kanta take girki dan naci abinci cikin kwanciyar hankali, da sauran aikace-aikacen da ya kamata, dan haka bakuda bakin da zaku dakatar dani daga cin abincin ta,

fad'i abin da yak

e tafe da ke, in kuma wannan ce ta kawo ki to ki koma sashin ki bana son damuwa."

"Eh ai basai kayi mana gori ba, mu y'ay'an talakawan ita 'yar masu kud'i, a haka kuma muka fita ba,

idan kud'i na iya yi maka komai taje ta sayi haihuwa tasakawa cikinta ta

yi nakuda da kanta ta haifa mana,

bata soma bin 'ya'yan aljanu tana d'ibowa tana kawo mana su gida ba,

kai kuma ka amince mata mu rayu da aljana cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login