Showing 48001 words to 51000 words out of 86898 words

Chapter 17 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

bata kuma kwana."

"Ato gara dai dan wannan babbar annoba ce, idan tafi haka a gidan nan ba'a san iya barnar da zatayi ba,

Hajiya

ga wannan hayaki ne na ruko miki,

in zaki kwanta sai kiyi, nima jiya ne nasa aka kawo min, na mance bany

i ba na kwanta ai kuwa nasha wuya cikin bacci,

bana kuma kwanci batare da nayi duk da yaran ba."

Hajiya ta amsa tana cewa

"Ai ko nagode zan ajiye maganin wata rana zaiyi amfani,

amma yau kam bata kuma kwanan gidan nan,

bare ma tazo min cikin bacci."

Sai

da Umma Karima ta tabbatar da munafurcin ta ya ginu kafin ta tattara ta koma sashin ta.

Hajiya tayi ta zuba ido ganin dawowar Daddy amma shiru har dare.

ta d'agawa Hajiya Bishira hankali sai ta kira mata shi, aka kuwa yi rashin sa'a wayarshi a kashe.

zo

kaga masifa gurin hajiya.

tana fa d'in

"Wlh yau sai ta bar gidan nan a daren nan."

Hajiyq Bishira ta ce

"Hajiya bakya jin tsiro idan kuma aljanar ce da gaske ranta ya b'aci tayi miki wani abin fa."

"Ashsha ke kike tsoron aljani, ai idan kika nuna kina ji

n tsoron su shine ma suke samin garab'asar yi miki tsiya, ai ba'a nuna a na jin tsoron su,

tun kana yara kake gwagwarmaya da su, ni da natab'a kawance ma da aljana tun muna yara,

ai dana gano ta

nayi mata dukan tsiya sai da ta b'ace."

Hajiya Bishira ta gir

giza kai.

Hajiya kota d'auki kafa tayi sashin Aunty dan taci alwashin yau fa Feeryal bazata kwana gidan nan ba.

tarika bubbuga jikin get d'in sashin Aunty,

mai ganin get d'in ya bud'e.

jiyo muryar Hajiya ce.

ta shige ciki da sauri ta isa jikin kofar parlo

ur tarika bubbugawa.

Aunty ta taso ta bud'e, ga nin Hajiya ce tashiga yi mata sannu.

ko amsata batayi ba ta bangaje ta tayi cikin parlour'n

"Ina kike tsintacciyar mage fito nan tun da ba gidan ubanki bane, zo ki koma in da kika fito."

Aunty ta durkusa gab

an Hajiya ta had'a hannaye biyu tashiga magiya da rokon ta

"Dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri, idan ta fita a daren nan ina zata je,

bata san kowa ba sai mu, kiyi hakuri dan Allah Hajiya gari ya waye."

"Bafa zan bari takara ko da kwana d'aya ne a gidan

nan ba, bari ma ki gani naje na taso direba yazo ya d'au keta ya fita da ita, can takataci tsiyar ta a can."

ta juya ta yi waje fuuu.

tana fita Aunty ta d'aga waya ta danna lambar Daddy wan da ita kad'ai take da shi a gidan,

idan duk ya kashe sauran wayoy

in sa baya tab'a kashe waya mai d'auke da wannan layin, da yanzu take kira.

Feeryal da har tafara bacci tajiyo hayani, ta mike ta fito.

tsayuwa tayi tana kallon Aunty dake tsaye cikin parlour tana hawaye.

da gudu ta karaso inda take ta rungume ta itama

ta saki kuka

tana fad'in

"Ammie bakuwa mai duka ne tazo ai naji maganar ta, Ammie tare zamu tafi ni dai bazan tafi na barki ba."

Bubbuga bayanta ta shiga yi tana fad'in

"Yi hakuri yi shiru Feeryal, babu in da zaki je,

kafata kafar ki duk in da zaki shiga

ina gun, sai dai mu bar gidan tare tun da ba gidan aljanna ba ce."

"Kada b'acin rai yasa ki fad'in haka,

shin kin mance anan gidan zaki nimi aljannar taki iye Fad'imatu."

maganar Daddy daga cikin wayar dake rike a hannunta wacce ta ma mance da ta kirasa h

ar yama d'aga yana sauraron su,

yayin da yake jin zafi mai gauraye da d'aci a duk fitar sautin kukan su.

Daddy yaci gaba da fad'in

"Hajiya ce ko? kuyi hakuri uwace a gare mu babu yadda muka iya da ita, yazama wajibi muyi mata biyayya amatsayin ta na uwa,

Fad'imatu lallai yau nasan an kure ki har bango, tun da naji fitar kalmar nan daga bakin ki,

kiyi hakuri har na dawo zan yi wa tufkar hanci."

Yana kaiwa nan ya katse kiran.

Ya kunna d'aya daga cikin wayoyinsa.

Lambar Hajiya Bishira ya kira, ya ce ta baw

a Hajiya wayar, yakira wayarta bata d'aga ba.

Hajiya Bishira ta shaida masa Hajiya ta fita, taje side d'in Aunty, ya ce

tayi sauri ta kai mata wayar.

Hajiya Bishira na fita can ta hango Hajiya kofar d'akin direbobin gidan, tana bokarin buga musu kofa.

Mu

rya ta d'aga ta dakatar da ita daga bugun kofar nasu.

da sauri ta karaso ta mika mata wayar tana fad'in

"Gashi Yaya na magana."

ta karb'i wayar ta kai kunne tana ce wa

"Ka gama abin da kaje yi tsaf abin ka, bama sai ka dawo ba, yanzu nazo d'aga direba ne y

a fita da ita."

"Hajiya kiyi hakuri na dawo tukun ni da kai na zan fita da ita nayi miki alkawari."

Da kyar Daddy ya shawo kan Hajiya akan idan ya dawo zai d'auki Feeryal d'in ya mai da ita in da suka d'auko ta.

Washegari kuwa da zasu tafi makaranta, Haj

iya ta fito ta tsare ta ce Feeryal bata isa ta shiga moto d'aya da jikonkin ta ba.

Feeryal ta d'an kalleta a tsorace dan ba karamin tsoron matar take ji ba,

tun da aka ce mata tana duka, Feeryal kuwa ba karamin tsoron duka ta ke ba.

Hajiya ta buga mata wa

ni uban tsawa

"Daina kallo na da wad'annan idanun naki masu kama da na mayu, da jan fuska kamar nunannen gwanda,

anya wannan yarinyar, ta ya za'ayi a ce mutum ce ma, habawa wannan irin kyau haka hankali bazai d'auka ba, wasayyahuuu ya tsaya a kanki li'eeel

afi aniya bi aniya, nafi karfin ki da jikoki na."

Feeryal tayi kasa da kai tana kyafkyafta ido zatayi kuka.

ta zuba mata rankwashi a kai

"Munafuka wuce ki bar nan kar ki shafa mana annoba."

ba zato taji saukar rankwashi a ka.

a birkice ta saka hannu tana

yamutsa kan, nan da nan idanun ta suka shiga tsiyayar da kwalla.

Hajiya ta kad'a keyar jikokin ta suka shiga mota direba ya ja su suka tafi.

ta juya tana bin Feeryal da harara

"Ai ke da shiga motar nan sai dai ki ganshi da ido mayya mai zubin aljanu, sai

ki taka a kafa kije makarantar."

ta wuce ta barta nan tsaye.

tazo daf zata shige side d'in ta kafarta ya hard'e.

ki kake shirimm ta zube kasa kan gwuiwowinta.

Kururuwa mai had'e da salati Hajiya ta sake, tana fad'in

"Wayyo jama'a kuzo kafata, shike nan ka

far ta b'alle

yafita, jama'a kuzo jama'a kuzo!."

Feeryal tayi saurin kai hannu ta toshe bakinta da dariya ke son kwace mata, ga kuma tsiraren hawaye a kan kyakkyawar fuskanta.

tana kallon inda Hajiya ke zube, sai kuma ta girgiza kanta.

da alama dai magana

take da kai.

A guje security suka taho, Ajeemal Shamsuddin Zaraddin Faisal da suka fito zasu tafi school, suka karaso a guje.

kowa na tambayar yaya me ya faru lafiya?.

Hajiya takuma wage baki tana fad'in

"Ku kirawo mai d'auri na karye wayyo Allah na shi

ke nan nazama gurguwa."

Ciccib'arta sukayi suka shige da ita parlour'n ta.

dan sunga alamun da gaske ko tsayuwa bazata iya ba bare ma tafi.

Dad da Abbieh ne suka shigo hankali tashe.

nan da nan suka kirawo mai d'auri.

Sai a lokacin su Ajeemal suka fito d

an in suka dad'a b'ata lokaci zasu makara.

Har lokacin Feeryal tana tsaye a gurin har suka karaso inda take,

tun kan su iso Zaraddin yakafe ta da ido, sai da ya iso daf da ita kafin yawani lumshe ido yaja numfashi kana ya fesar tare da kuma bud'e su a kan

ta.

murmushi Shamsuddin ya mata yana cewa

"Badai latti kika yi ba Feeryal?."

kai ta girgiza.

Faisal kuwa cewa ya yi

"Shine Miemie bataje ta kira ki ba suka tafi, suka bar ki."

nan ma shiru tayi tana wasa da 'yan yatsunta.

Ajeemal kuwa da ke da tabbacin Ha

jiya ce zata iya hanata tafiya kamar jiya ya ce

"Zo muje mu sauke ki sai mu wuce."

Suka karasa parking lot, Zaraddin ya yi saurin bud'e gidan baya ya shiga yana fad'in

"Shigo nan ki zauna."

"A'a dawo gaba ku ku zauna a baya."

Ajeemal ya fad'a yana bud'e m

ata gaban motar, fuska a d'aure, dan tun d'azu ya lura da yanayin sa tun da ya ganta.

tana zama ya rufe ya zaga ya shiga mazaunin direba suma suka shiga yaja motar suka bar gidan.

Sai da suka sauke ta a school d'in su sannan suma suka wuce nasu school d'i

n.

A gida kuwa maid'auri yazo ya duba kafar Hajiya,

ya ga gwuiwar ta ce ta goce, da kyar aka mayar aka shafa mata magani, Hajiya tayi shame-shame tana sallallami.

mutan gida sai shigowa suke ana gaidata.

dangi na kusa ma tuni sunzazzo.

Satin Hajiya guda

ke nan tana zaune tana jinyar kafa,

har kuma yanzu Daddy bai dawo ba yana can kasar China,yana gudanar da wasu harkokin sa.

sai dai kullum suna video call yana ganin yanayin jikin nata.

duk da cuwon dake jikin Hajiya baisa ta saduda ba,

tana daga zaune ta

na bada umurni da oda.

haka ta kekashe kasa ta hana a rika d'aukar Feeryal a motar kaisu school, takuma sa dole Daddy ya canza musu wata mota yana can kasar bai dawo ba,

a cewar ta wai akwai abu a ciki tun da Feeryal ta shiga.

Ajeemal ne ke kai ta school

a motar sa, wani lokacin ya jirata har su tashi idan bashi da abin da zaiyi, wani lokacin kuma ya ajeta yaje ya dawo ya d'auke ta.

baya tab'a bari Zaraddin ya kaita ko ya d'aukota, ko baya da lokaci, yakan iya kashe damuwar sa wajen kaita da d'auko ta,

sau

d'aya yatab'a sa Shamsuddin da Faisal suka tab'a d'aukota, ranar d'in ma yana class ne bai fito ba, dan su yana da d'an tabbacin nutsuwa tare da su.

Aunty na kichin tana aiki Feeryal da ta dawo daga school ta shigo.

ta fad'a jikin ta,

Aunty tayi murmushi

ta rungume ta tana fad'in

"Oyoyo 'yanmatan Ammie, an dawo ya school?."

d'an karamin bakin ta ta cuno cikin tsiririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce

"Ammie wai ba ke kika haife ni ba?."

hannu takai ta toshe bakin ta,

sannan ta waro ido ta ce

"Inji wa? ni na haife ki Feeryal duk wanda ya fad'a miki yafad'a ne kawai, kar ki yadda ki sawa ranki hakan,

to idan ba ni na gaife ki ba to waya haife ki, ko akwai wata mamarki ce a gidan nan?."

kai ta girzaza tana kallon fuskar Aunty.

kumatun ta taja ta

ce

"Ko in kaiki gurin wata ce tazamo mamarki tun da kin gaji da ni."

da sauri ta fad'a jikin ta tana cewa

"O'o Ammie ni dai bazanje ba."

dariya Aunty taji ta dad'a rungume ta tana jin kaunarta cikin zuciyar ta.

baki ta kuma cunowa ta ce

"Basu Ameerah bace

suke fad'a, wai ke ba ce mamata ba ce kuma Daddy ma ba babana bane, wai ni mayyar aljana ce."

da sauri Aunty ta ce

"Karya suke ni ce nan mamarki Daddy kuma baban ki, kar ki sake biye musu,

oya je ki cire uniform kiyi wanka kizo, ko nazo nayi miki."

kafad'

a ta make

"A'a ni zanyi Ammie Miemie tana min dari ta ce wai har yanzu ana min wanka."

"To in banda Miemie ai itace gaba da ke, in ita ta iya ke da sauran ki."

"Ni dai Ammie na iya nima."

"To je jiyi yanzu anjima da daddare da kaina zan miki."

ta juya da s

assarfa tayi ta fice a kichin d'in..

Hajiya ce kwance a kan makeken gadon ta tana sharara bacci sai gwarti take saukewa.

daga cikin bacci taji ana kiran sunan ta, ana jajjan kafafunta.

A firgice ta mike tana fad'in

"Wayyooo ni Hanne nayi mugun ji, waye

waye anan, Bishira wane ne?."

ta lalub'o makunni wuta dake d'aure a kan bedside ta kunna.

d'akin ya bada haske ba mai yawa ba.

can kuma hasken ya soma karuwa da kansa, yayi wani irin bau ya haske d'akin gaba d'aya lokaci guda.

a take kuma d'akin yasoma am

sakuwar magana had'e da tafi tamkar ana gad'a cikin d'akin.

ga wasu irin maganganu barkatai wannan nayi wancan nayi fad'i a ke

"Hajiyaaaa taso muyi gad'a, taso ke ce da shiga fili yanzuuu."

Hajiya da fitsari ke kokarin kwace mata sabar azabebben tsoro tas

higa fad'in

"To to laaaha'ilaaaha'illallahu, wasayyahu wasayyahu wasayyahuuu, li'eelafiiiikuraishin,

dan girman Allah kuyihakuri wlh lalurar ido gare ni, ga kwab'ewar gwuiwa, ta ina zan fara,

kuyi min rai."

"Bafa zamu kyale ki ba ke ce da shiga fili taso

ki fad'o mu cab'e."

Hajiya ta kwalala uban ihu

"Wayyo Allah jama'a ku kawo min d'auki yaukam nayi gamo,

dan Allah dan ma'aiki Rasulullahi nagama ku da Allah kui hakuri ku kyale ni,

ta ina zan fad'o bana ganin ku, tun zamanin yaranta rabon da nayi gad'a,

wl

h babu kafar yin gad'a kuyi hakuri kuje gurin masu kafa."

"Dole ki taso Hajiyaaa ko mu d'aga ki, kuyi sama da ke."

Ba sai ga Hajiya ta mike da kafafunta ba, dama tun sati biyu aka ce ta gwada takawa ta ki ta ce wai da saura tukun guiwar bata gama had'ewa

ba.

"Ku taro ta zata gudu."

tuni Hajiya ta saki fitsari, jiki na kakkarwa ta nufi kofa fitsari na zuba,

kafin ta isa kofar ta bud'e tazo daf zata fice kofar yakuma kullewa garamm.

Hajiya tayi dakuwan 'yan bori a kasa, daram da d'uwawu.

ta rufe idanunta ga

m tana fad'in.

"Yasin kafa dubu, li'eelafi kafa bakwai, lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya,

yasin me manjagara yakwasheku ya zubdaku can kuyi nesa ku tsaya a can, wasayyahuuu wasayyahuuu ku tsaya a can laaaa'ilaaaha'illahu,

aniya bi aniya aniya bi aniya,

fatiha da salatin annabi."

Ji kake kuuu cikin Hajiya na bada sauti, tsoro iya tsoro firgici iya firgici a tare da Hajiya.

sai ihu da kwalala take kamar makogoron ta zai fita.

A tare Hajiya Bishira da Kulu suka fito daga d'akunan su, suna rige-rigen shi g

a d'akin Hajiya.

a bakin kofa suka ganta tayi zaman dirshem tana kwarara ihu.

duk sukayi kanta suna had'a baki wajen fad'in

"Lafiya Hajiya me yafaru, ciwon kafar ce ta motsa? subhanalillahi!."

Jin moryoyin Hajiya Bishira da kulu yasa Hajiya bud'e idanunta

.

ta kankame kafafunsu kad'an yarage ta zubar da su kasa.

Hajiya Bishira ta kara hasken d'akin ta hanyar kunna makunnin koyayen wutan da sukayi wa tsakiyar p.o.p d'akin kawanya,

tamkar kwalliya ta sama.

d'akin yabada haske sosai tamkar tsakiyar rana.

Ha

jiya tashiga binsu da kallo da alama dai yanzu ne ta dawo cikin hayyacin ta.

Hajiya ki sake mu kar ki yardamu a kanki."

cewar Bishira tana janye kafafun ta daga rukon da tayi musu.

cikin sauke numfashi'n tsoro irin wanda mutum ya kub'uta daga azaba Hajiya

ta ce

"Nayi gamo gamo nayi da bakaken aljanu, ku kaini bayan gida ciki na ya rud'e."

"Hajiya wa ya kawo ki nan to ke da ba tafiya kike ba?."

cewar Kulu tana rike hab'a.

"Ban san ya akayi nazo nan ba ina ga su suka kawo ni, ke da'alla kamani ku kaini masai

ko sai nayi anan nabar muku aiki."

Suka tallafe ta ta mike Hajiya ta d'aga kafa tana d'ingisawa.

"Hajiya kin warke ashe."

Kulu ta fad'a tana bin kafarta da kallo sai kuma ta waro ido

"Me zan gani Hajiya fitsari kamar kikayi a zaune."

"Har uwar fitsari ma

zanyi a nan in ya kama,

da'alla ku kaini bayi na matsu."

Hajiya Bishira ta bi gurin da kallo tambas fitsari ne tun daga bakin gado har zuwa inda suka same ta zaune.

Suna kaita bayi ta sunkuya gudawa daya murd'e ta, zasu fita su bata guri, ta ce babu wan

da ya isa ya fita su jirata sai ta gama.

Suna fito da ita takuma cewa su koma tana jin wani.

sai da ta shiga bayi sau biyar a kai a kai.

Tana zaune a bakin gado tana sauke numfashi, su Hajiya Bishira da suka gama tsaftace cikin d'akin da sarkake shi,

su

ka dawo inda take suna yi mata sannu.

Kulu ta dube ta tana fad'in

"Sannu Hajiya dare d'aya har kin zabge, wai ya akayi mu bamuga bakaken aljanun ba sai ke, ta ina suka shigo ne, ko dai mafarki kika yi,

anya ba mayu ke bibiyar ki ba kuwa?."

"Uhum ke dai b

ari Kulu ko ta sama ko ta kasa sai Allah, ina bacci narika jin ana kira na, da na amsa kiran da sun tafi da ni, kin san ba'a amsa kiran dare kana amsawa to ka tafi ke nan,

yazama dole a sawa gidan nan kafi, tun ba yau ba nake fad'awa Abubakar ya sa kafi a

gidan nan sabo da miyagu yaki ji, to ba ga irin ta ba da babu wani mugun da zai iya shigowa gidan nan, kota sama ko ta kasa ko a b'oye ko a bayyane,

badun nayi ta addu'a ina ja musu yasin ina sauke wa ba da sun tafi da ni."

D'ip Hajiya tayi jin motsi kark

ashin gado ta kankame su Kulu ta na fad'in

"Yasin kafa dubu li'eelafi kafa bakwai lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya fatiha da salatin annabi wasayyahuuuu."

Hajiyq Bishira ta ce

"Hajiya bafa komai kinga ni kyanwarki ce gata can fa, magen ki ce a kasan gado

taga haske ta fito."

"Kin tabbata mage ce."

Hajiya ta fad'a tana zazzare ido.

"Itace ba gata nan ba ta fito, watakila ma ita ce ta razane ki d'azu."

"Um-um ba ita ba ce magana naji bilhakki, kyanwa tana maga ne."

"Hajiya in zaki kwanta kirika addu'a, babu

abin da zai same ki insha'allahu."

"Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login