Showing 78001 words to 81000 words out of 86898 words
a gurinki tazo ta zauna damu nad'an wani lokaci kafin komai ya lafa, hukuma sugama bincike su kama sauran 'yan ta'addan sai ta kom
a Abuja,
Hajiya ta ware ido tare da buga kirji
"Nashiga uku! Abubakar kasan me kake fad'a kuwa,
'yarda ta kai fitina can kake so ka kuma dawo mana da ita ta kawo mana fitanar nan,
Abubakar annobar da muka kakkab'eta agidan kake so ka kuma yayub'o mana ita
ka dawo mana da ita,
kanka d'aya kuwa Abubakar,
to ka dawo hankalinka ko da wasa kada ka soma ban yarda ba Allah ma bai yadda ba,
kada ka sake ka kuma jajjab'o mana fitina a gida,
barsu su karata a can."
"Hajiya ki fahimce ni ba fa zata dawo gidan nan di
n-din-din bane zuwa na d'an wani lokaci ne zata koma, daga zaran an gama bincike,
zata zo ne a matsayin bakuwar da zata koma,
ba wani jimawa zatayi ba, daga zaran an kama sauran b'arayin zata koma."
"Oho kace kawai zaka kawo ta sabo da b'arayin su biyo ta
nan, sai su had'a da jikokina su kwashe suyi gaba,
Abubakar ina rabaka da kiwon shanu kana ce kyalla ta b'ata, to ban amince ba kada ka soma, na gaya maka ke nan."
Shiru Daddy ya yi bai kuma ce komai ba, kana ya mike ya ce
"To shike nan, duk yadda kika ce
hakan za'ayi Hajiya Allah ya huci zuciyar ki, a wuni lafiya."
ya d'aga kafa yana kokarin tafiya da sauri ya kai
hanu ya d'an dafe kirjinsa.
ya shiga d'an kananun tari yana dafe da kirjin nasa.
Hajiya ta mike da sauri tana bubbuga kafad'ar sa
"Kai Abubaka
r zauna zauna tukun, kana ma shan maganin ka kuwa, ko na kira abokin turawa ne ya rubuto wani maganin da zaka sha yanzu."
kai ya girgiza ya ce
"Kafin na fito ma sai da nasha magani, ba komai zai lafa."
Hajiya ta rud'e gaba d'aya tana jera masa sannu.
Dadd
y ya ce
"Bari naje na d'an kwanta nasan zai lafa zuwa anjima,
amma hajiya da an duba batun nan wanda ya taimaki wani Allah zai taimake sa, shifa d'a na kowa ne,
idan kaso ya yi kyau ka taimaki al'umma gaba d'aya ne."
Hajiya ta kwantar da murya, duk abinta
sam bata so taga 'ya'yan ta cikin halin ciwo
"In ban da kai Abubakar ciwonka na kokarin tashi amma kana magana kan aljanar can,
ina mu ina taimakon aljana ai sai dai danginta aljanu,
duk in da zata zauna sai ta haifar da fitina,
sabo da ba jinsin mu ba
ce,
kaje ka nutsu kada ciwo ya kayar da kai,
amma tun da ka matsa sai ta zo ai amma tayi harkarta karta shiga harkar jikokina,
ta zauna can kada ta rab'e su,
ana gama bincike kuma takoma can in da akayi gayyarta."
Daddy ya ce
"Nagode Hajiya."
"Jeka maza k
aje ka kwanta ka natsu kirjin zai lafa."
ya ce to.
ya fita ya koma sashin Aunty.
Aunty na ganin sa ta tare sa da sauri tana tambayar sa ya dai dan taga alamar kamar da akwai abin da ke damun sa.
ya ce
Ba ko mai tun shekaran jiya yake jin kirjinsa yana mas
a zafi, sai da abunnan ya faru ya gane fargabar hakan ne ke bibiyarsa.
nan yake shaida mata Hajiya fa ta amince FEERYAL ta zauna kafin komai ya lafa.
Aunty tayi farinciki matuka sai dai kuma ganin kamar ciwonsa nason tashi sai duk ta shiga damuwa.
bata gus
heba sai da ta tabbatar da yasami bacci.
Su Aunty na parlour bayan sunyi breakfast, FEERYAL na kwance jikinta tana ta zuba shagwab'a,
Aunty na taje mata gashi wai dan ta ce zata kira mai kitso tayi mata kitso, take ta birgima a jikinta wai ita bata so ya
na mata zafi.
Aunty tarike hab'a tana fad'in
"To kawai a aske gashin tunda bakya son kitso,
kinfi so kiye ta nad'e gashi, ai ko tace gashin ma kad'ai ya ishe ki,
in kikayi kitso fa ai zaki huta na kwana biyu,
kafin aje a sake wankewa."
da sauri ta ce
"All
ah a aske Ammie damina yake."
dungurin kanta tayi ta.
zatayi magana kiran Ammah ya shigo wayarta
ta d'aga da sallama bayan sun gaisa Ammah ta ce
"Hajiya Fatima ban samu na shigo da safen nan ba,
ya dai kika sami labarin jikin FEERYAL."
Aunty ta yi murmushi
ta ce
"Ai gani ga FEERYAL jiya Daddy ya d'auko ta."
"Dan Allah da gaske ikon Allah FEERYAL anzo amma dai jikin nata da sauki ko, bari na gama na shigo."
Miemie dake zaune can gefe tana dane-dannen waya jin Ammah ta ce FEERYAL tazo.
ta jifar da wayar tana
fad'in
"Ammah FEERYAL tazo?."
kai Ammah ta gyad'a, aiko da sauri Miemie ta mike da gudu tayi waje........!
Mommyn Twinc ce
🌺
*FEERYAL*
🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne
500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S
✍
🏼
*
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entert
ain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿
️
21
Da gudu Miemie ta shigo parlour'n Aunty tun daga bakin kofa ta ke fad'in
"Aunty ina FEERYAL wai da gaske tazo, FEERYAL FEERYAL kina ina?."
FEERYAL dake kwance kan kafar Aunty ta mike tsaye da sauri.
Miemie ta karaso ta tsaya suna kallon-kallo.
y
ayin da dukkanin su kamannin yarantar su yake zuwar musu cikin kwakwalwa,
duk da kamannin su dukansu ya canza a yanzu bai hana amintakarsu tasiri wajen gane junan su lokaci guda ba.
a tare suka nuna junan su da hannu tare da kiran sunan junan su a tare.
"F
EERYAL!."
Miemie ta fad'a.
FEERYAL ma ta ce
"Miemie!."
wani irin rungume junan su sukayi cikin mashahuriyar murna da farinciki, suna dariya.
Miemie ta janye jikinta tana duban ta da mamaki take fad'in
"Wai FEERYAL ke ce haka?."
FEERYAL tayi murmushi ta ce
"Miemie kema ke ce haka? ga yadda kika zamo wata katuwa da yawa."
"Kee da ma na girme ki, ko ba haka ba Aunty, amma dubi yadda kika zama har kin fini fa."
cewar Miemie tana zagayata da duba gaba da bayan ta.
Aunty dai dariya take ta binsu da shi, kaunarsu
tun na yarinta abin yana ta burgeta.
Miemie ta b'ata rai tare da hararar FEERYAL ta ce
"Ko tuna ni ma bakyayi ni ce kad'ai mai damuwar tunaki, nifa da tunanin ki ma na girma,
ki tambayi Aunty kullum sai na zo part d'innan,
sanda na mallaki hankalin kaina
kuwa nakarb'i lambarki wajen Aunty amma ko na kira ki bakya d'agawa,
kusan kullum sai na kiraki bazaki d'aga ba, sai na hakura kawai na daina kiran naki amma ban iya cireki cikin raina ba."
"Miemie nimafa ban cireki a raina ba, kina raina,
bakuwar lamba c
e bana d'agawa da kinzo kin kirani da lambar Ammie'na."
"Ai nazo ranar nasa Aunty ta kira min ke aka ce bakya gida kin tafi school,
da yamma kuma nayi ta kiran lambar ki yana shiga baki d'aga ba."
Ganin diramar nasu Aunty tayi dariya ta ce
"Ai wayar FEERY
AL kam na buga game ne, na mance ne ma da lamban Hajja Umma ko na Maryam na baki, shine zaki same ta."
Miemie ta ce
"To sannu biloniya wato bakuwar lamba ce bakya d'agawa, gudun kada ace ki kawo kud'ad'e ko."
dariya FEERYAL tayi
cikin tsiririyar muryarta
mai fita da yanayin shagwab'a ta ce.
"Ke ba haka bane ina d'agawa sai ace FEERYAL mun had'u a waje kaza dama wata ce ko wani ne ya bani lambar ki,
to ya yanzu in zo ne,
niko sai in kashe wayar daga nan na daina d'aga bakuwar lamba."
dariya duk suka fashe
da shi harda Aunty.
Miemie ta ja hannunta tare da d'aukar d'an karamin gyalen ta dake kan kafar Aunty ta mika mata ta ce
"Zo muje Ammah ta ganki."
Suna tafe Miemie tana ta zuba mata surutu,
FEERYAL ba gwana ce a iya surutu ba, sai dai tayi ta binta da mu
rmushi had'e da dariya.
wani bin kuma ta amsa mata ba mai tsawo ba.
Miemie taja ta tsaya ta d'an waro ido da damuwa ta ce
"FEERYAL karkiga yadda hankalina ya tashi da akace
an sace ki, ranar ko abinci banciba nayi ta kuka."
kafin FEERYAL tace wani abu
suka hango su Ameerah sun fito daga side d'in Hajiya.
Miemie ta ce
"Yauwa tsaya gasu Ameerah can bari naga ko zasu gane ki taho muje."
ta janyo hanun ta suka karaso gurin su.
Tun daga can suka kafe FEERYAL da kallo suna son sanin wace bakuwa sukayi a gida
n.
suna isowa inda suke Sumayya ta ce
"Wow see beautiful Miemie wannan fa? a ina kika zamo balarabiya haka."
"Dan Allah Sumayya baki gane ta ba?."
cewar Miemie tana dariya.
Ameerah ko hanci sama ta d'aga tana yamutsa fuska ita a rayuwar ta ta tsani taga wa
cce ta fita.
ta ce
"Sai wani rawar kafa kike ta ya za'ayi ta santa bata tab'a ganin ta ba, kasarsu ba d'aya ba."
"Laa Ameerah ke ma baki gane ta ba, Sahla Nabila kuma duk baku gane ta ba, to ku bani goron albishir na fad'a muku ko wace ce ita."
Miemie ta m
iko musu hanu tana dariya.
Sumayya ta zuba mata tafi a hannun tana fad'in
"To an baki."
su Nabila da Sahla dai murmushi sukayi.
Ameerah ko fuska ta yamutsa, ita haushin ganin yadda Miemie'n ke ta rawar kafa.
Miemie ta ce
"So surprised! FEERYAL ce."
Sumayy
a ta ce
"What!.
"Yes of course ita ce dai."
kai Sumayya ta girgaza tana kare mata kallo sai kuma ta ce
"Ba laifi."
Ameerah Sahla Nabila a tare suka bud'e ido da baki suna kallonta.
Ameerah ta ce
"Tabd'i jam! annoba ta kuma dawowa gidan mu,
wai ke baki da g
idan uba ne kam sai dai ki rika yawo gidan mutane kina addabar rayuwar su,
idan da kin zauna lokacin muna yara yanzu kam baki isa ki zauna da mu ba, mayyar aljana,
mttsss dalla kuzo mu tafi,
akan wannan aljanar kika tsayar da mu har dawa ni wai Surprised a
ikin banza."
Nabila da Sahla suka ce
"Ai kuwa bara da bana ba d'aya ba ki karanta hakan da kanki."
Ameerah
ta janyo hannun Nabila da Sahla, da suke aikawa FEERYAL harara, Sumayya ta biyo bayansu sukayi gaba.
Jikin FEERYAL ya yi sanyi matuka.
Miemie ta bi
bayan su da harara tana fad'in
"Ai ke kam Ameerah kin shiga uku sai ki hanata zama ai tun da ke kika gina gidan,
ku kuma kun bita kamar wata uwar ku, dalla rabu da su zo mu tafi FEERYAL suyi abinda zasuyi."
ta jata suka nufi sashin Ammah tana ce mata
"Ka
rki wani damu da su."
cikin sanyin murya FEERYAL ta ce
"Hum Ameerah ke nan har yanzu dai bata sauya ba."
"Ai bazata sauya ba haka zata mutu da halinta,
kinga Sumayya tana da sanyin hali ita dai kawai zugi ke mata tasiri,
mance da su dalla."
ta d'auko mata
wata hirar har suka wuce sashin Ammah.
Ammah na ganin ta ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo FEERYAL ke ce haka,
Allah sarki ya jiki ya abinda ya faru?."
FEERYAL tayi mirmushi tana gaisheta.
Miemie ta jata sukayi cikin d'akin ta bayan su. gaisa da Ammah.
hir
a sosai Miemie ke janta da shi ita dai murmushi sai dariya take binta da shi dan bata iya dogon hira irin haka ba.
sun jima sosai har wajen azahar sai da FEERYAL tace zata koma tayi wanka.
Miemie ta ce
"Kiyi wankan a toilet d'in na sai kije ki sa kaya."
id
o FEERYAL ta waro ta ce
"To kaya fa bazan iya maida na jikina ba."
"Sai kisa nawa ba ga nawa ba, ko an ce miki kin fini kiba ne."
"Miemie muje dai ki rakani zan canza pad wajen awa uku yana jikina."
"To ai ina da shi shiga kiyi wanka bari na d'auko miki."
dole Miemie tasa ta shiga bathroom d'in ta tayi wanka ta bata pad da sabon pant ta saka,
ta fito ta samu ta ciro mata doguwar rigar abaya,
zata tafi da nata kayan Miemie ta ce ta barshi anan.
sannan suka fito ta rako ta.
Suna fita can suka hango su Ajeema
l Faisal Zaraddin Shamsuddin, zasu shige side d'in su.
Miemie ta d'aga murya tana fad'in
"Kai-kai ku tsaya ku tsaya."
ta janyo hannun FEERYAL da sauri suka karo gurin su.
Faisal ya harare ta yana cewa
"Ke mu sa'annin ki ne da kike mana irin wannan kiran?."
Shamsuddin ya kai mata bugu a baki ta yi saurin kaucewa.
tana cewa "Wayyo Allah baki na, to ku tsaya kuji mana."
ya ce "Waye sa'anki."
Ajeemal ya ce "Ku kyale ta, mene ne Miemie?."
baki ta turo ta ce
"To ai bana so na kira sunan ku ne taji game d'in ya
rushe,
yauwa kutsaya-kutsaya kuji in kun canka waye wannan?."
ta nuna FEERYAL sannan ta ce
"Ke ma in kinci su waye wad'annan fad'o min sunan su."
tayi maganar tana dariya da tafa hannu.
duk suka bi FEERYAL da kallo Zaraddin da shi dama ya kasa magana tun d
'azu idanunsa yana kan ta gaba d'aya yawun bakin sa ya gama tsinkewa.
Ajeemal da ke ta juya kamannin nata cikin kwakwalwarsa, ya yi saurin janye idanunsa daga kallonta, jin yadda gaba d'aya kasala ke kokarin shigarsa.
Faisal kuwa cewa ya yi
"Nasanta mana
balarabiya ce ai mun sani duka."
dariya ta kwashe da shi ta nuna Zaraddin da Shamsuddin da Ajeemal ta ce
"Kuma baku gane ko wace ce ba, to ke suwaye ne su."
tayi maganar tana kallon FEERYAL.
murmushi ta sake wanda ya sami nasar bayyan hushiryar da ke tsaki
yar kyakwawan jerarrun hakorar ta,
yayin da kumatun ta ya lotsa dimples d'in ta ya bayyan.
ta kai yatsarta baki tana bin ko wannen su da kallo.
wani irin had'iye yawu Zaraddin ya yi yawani lumshe ido tare da jan numfashi a fili.
Dariya Miemie tayi ta ce
"
Wai dukan ku baku gane ta ba, kema baki gane su ba? yee naci wina."
tayi maganar tana tsalle a tsakiyar su.
Ajeemal ya ce
"Ke Miemie wani irin shiririta ne wannan."
"Ya Ajeemal ku bani gari kawai FEERYAL ce fa,
FEERYAL baki gane Ya Ajeemal Ya Shamsuddin Ya
Zaraddin Ya Faisal ba."
ido ta waro tana murmushi da bin ko wannen su da kallo, sai da ta fad'a sannan kamannin nasu na tun da yake zuwar mata ido.
suma d'in mamaki duk suka cika da shi,
wai FEERYAL ce ta zamo haka.
Zaraddin da yakuma hadiye miyau ya fur
ta
"Wow! she is cute completely."
Shamsuddi da Faisal suka had'a baki wajen fad'in
"Haka kika girma FEERYAL."
nan ma murmushi ta bisu da shi batayi magana ba.
Ajeemal ne ya ce
"FEERYAL ya abin da ya faru ina tayaki jaje, ya karatu kuma,
au na mance wani r
ana Aunty take sanar min graduation naki, kinyi kokari fa kinfi su Miemie."
"Haba Ya Ajeemal sai kasa tayi tunanin bamuyi ba muma, tun yaushe mukayiwa secondary bye-bye, mun barwa yara."
hararar ta Faisal ya yi ya ce
"Wuce ki bar nan ke d'in mece ce."
hann
un FEERYAL ta ja suka bar gurin da sauri tana dariya dan tasan zuwa anjima zata sami tsarabar mari.
Zaraddin yabi bayanta da kallo yana wani matse ido da latsar lips d'in sa.
Ajeemal ya d'an harare shi dan ya lura da yanayin da ya shiga tun d'azu, ya yi t
saki yana girgiza kai ya yi gaba abin sa suka biyo bayan sa.
Kan ka ce me gidan ya d'auki labarin FEERYAL ta dawo,
a bujajan Umma Karima ta d'auko kafa tayi sashin Mommy.
tun kafin ta zauna take cewa
"Hajiya Halima wai da gaske ne batunnan ko maganar yara
nnan ne kawai?."
"Ni ma yanzun nan su Ameerah suke sanar min kin san bazasuyi karya ba."
Umma Karima ta zauna tana fad'in
"Tabd'i jam wata sabuwa inji d'an caca!
aljana mayya annobar ta kuma dawo mana gidan."
ta saki dariya
"Hahaha lallai Hajiya Fatiya ba
karamar 'yar wasa bace, sai da ta bari muka sakankance sannan ta shammace mu,
ta dawo da ita bayan ta hab'aka dafinta yagama kwari ta inda duk wanda ta kaimai sara zaiyi masa mummunar illa,
Fatima Fatima Fatima muzuba mugani waye zai cinye wasan!."
Mommy
ta ce
"Ham tun da suka kawo min batun nan narasa a bin yi, yanzu ya kike ganin za'ayi Hajiya Karima."
"Yanzu ne za'a yi mai gaba d'aya ai ta farkar da mu daga nannauyar baccin da muke."
cewar Umma Karima tana girgiza kai.
Ameerah dake zaune sai cika tak
e tana batsewa,
tun dataga FEERYAL, bakinciki kamar ya kasheta,
bata kaunar ganin wacce ta fita bare kuma a yabeta a gabanta.
ta ce
"Mommy amma dai zata bar gidan nan ko, dan wlh bazamu zauna da ita ba,
ta ya za'ayi ne ma kawayen mu suzo su ganta,
ina baza
i yuwuba,
nifa duk yadda za'ayi Mommy tabar gidan nan."
"Ai barin gida ma yazama dole kwantar da hankalin ki d'iyar masu gida,
har wacce ta kawo tan ma wannan karon tare zasu bar gidan."
cewar Umma Karima tana gyara zaman ta.
Sumayya ta ce
"Wlh bakuga yadd
a ta girma ta zamo wata tsaleliyar budurwa ba,
ko gane ta bamuyi ba, ni na d'auka ma bakuwar balarabiya mukayi,
sai da Miemie ta ce mana wai ita ce,
wlh tafi da kyau