Showing 12001 words to 15000 words out of 86898 words
daban-daban.
tuni jikinsu yakama b'ari zufa yashiga keto musu,
kowa ya shiga neman ceton rayuwar sa.
da gudu sukayi bakin kofa tun kan su karaso kofa ta rufe.
sai ga Mommy da Umma Karima suna kwalla kururuwan niman taim
ako.
Aunty da ke gyaran cikim bathroom tafito da sauri, nan take wutan nan ya tsaya yadawo dai-dai.
da mamaki ta tsaya kallon su Mommy dake cikin bedroom d'in ta sunata kururuwa.
kallon kan gado tayi in da Feeryal ke kwance, da sauri taga idon Feeryal ya
rufe sai kuma kofar d'akin ya bud'e.
aiko da gudu su Mommy suka fice har suna ture juna.
shiru Aunty tayi idanunta akan Feeryal sai dai har lokacin bata kuma motsi ba.
kirjin ta ne yad'an buga tayi saurin fad'in
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."
acik
in zuciyar ta, nan take taji zuciyarta ya yi wasai.
numfashi ta sauke a fili ta furta
"Lallai Hajiya Halima Hajiya Karima kun d'ebo da zafi amma muzuba mu gani."
gaban gadon ta isa tana mai dad'a karfafa zuciyar ta, kan cewa Feeryal mutum ce ba abin da zuc
iyar ta ke bijiro mata da shi bane ayan da taga yarinyar yanzu.
ta gyarawa Feeryal rufuwa kana ta juya ta koma ta cigaba da aikinta.
A guje suka karaso parlour'n Mommy suna haki, ganin yadda suka shigo a hargitsi 'ya'yansu duk suka mike suna tambayar su
me ke faruwa.
"Kada wani a cikinku ya sake yaje side d'in Fatima!."
cewar Mommy tana zama kan kujera gaba d'aya a firgice ta ke jikinta sai rawa yake..
Ajeemal ne yakaraso in da take yana fad'in
"Mommy wai mene ne kam naga duk kun firgice?."
"Ajeemal aljan
a wlh aljana ce ba mutum ba, mun shiga uku ankawo mana annoba cikin gida, wlh yarinyar can ba mutum ba ce aljana ce, Fatima takawo mana aljana gida, Hajiya Karima kinga abin da nagani kuwa?."
"Ni kuwa naga sihiri aljananci maitanci ido da ido, ko shakka b
abu 'yannan ba mutum ba ce."
Umma Karima da tsoro yakusa kasheta taja 'ya'yanta, suka koma side d'in ta, suka rufo kofa a kansu.
A b'angaren Mommy kuwa har ta d'aga waya zata sanarwa Hajiya abin da ke faruwa, ta tuna da gargad'in Daddy ta aje wayar jiki a
sanyaye
tana ciza yatsa.
A b'angaren Umma Karima ma taso kiran Hajiyar sai dai tana gudun abin da zaije ya dawo, dan bata kaunar abin da zai gutsire mata igiyar aurenta, takan bi ko wace hanya wajen dakile faruwar hakan.
Bayan wata 5
Tun daga wancan r
anar su Mommy basu kuma wani yunkuri a kan Feeryal ba,
Aunty kuwa ta dage wajen kula da rainon d'iyarta yadda ya kamata.
yarinya tana ta murjewa fatarta na dad'a kyau babu alamar maraicin uwa tare da ita, ta sami ruwan nono mai kyau da inganci.
tayi wayo s
osai tayi mul-mul da ita.
har ta fara iya zama.
sosai Aunty ke kula da ita Daddy na bata gudumawa yadda ya kamata.
bata fita da ita ko ina ko side d'in Daddy zataje ba sosai take zuwa da itaba, takan barta wa Baba Rabi.
kaf fad'in gidan kuwa dama babu inda
take shiga side d'in Hajiya Safiyyah ce kad'ai take d'an lekawa.
kowa na harkar gaban sa a gidan.
Yanzu duk wanda yazo gurin ta bata bari yaga Feeryal,
b'oyeta take a d'aki har sai ba'in sun tafi kafin tafito da ita.
sabo da gujewa maganganun da ake akan
ta, dan duk wanda ya ganta sai ya ce wuuu a'ina ta samo wannan mai kalar aljanu sam batayi kama da mutane ba.
kyawun ta ya yi yawa.
Aunty ce tsaye cikin kichin bayan ta gama shiryawa Daddy abincin sa dan yau zai dawo gurin ta.
baba Rabi tana ta goge-g
ogen in da suka b'ata.
Aunty ta dubi Baba Rabi tana fad'in
"Bari naje nayi wanka kafin rikicacciyata ta tashi, idan kazarnan ta kara zafi a ciro ta kada ta kone."
"To Hajiya." Baba Rabi ta amsa tana maida komai wajen zaman sa.
Aunty ta fito daga kichin t
a nufi bedroom d'inta, a hankali ta tura kofa cikin kasa da murya take fad'in
"Allah yasa bata tashi ba har sai na gama komai."
ta maida kofar a hankali ta rufe.
idanunta a kan inda bed d'in Feeryal yake,
tana fata Allah dai yasa bata tashin ba.
da d'an m
amaki take kallon cikin d'akin, ganin babu gadon nata gaba d'aya a cikin bedroom d'in.
"Ta ina tayi ko ta tashi garin rarrafe ta fad'o a gado ne, to ina ma ganon yake?."
ta had'a tambayoyi wa kanta tana rarraba ido.
da sauri ta d'aga kafa tana kokarin kar
asawa cikin d'akin.
wani irin tsinkewa gaban kirjinta ya yi tayi baya da sauri, jikinta na wani irin cirawa tsoro da firgici suka dirar mata lokaci guda. gaba d'aya jikinta ya d'auki b'ari.
Hango gadon Feeryal ya tashi sama tamkar ana lilata gadon yana ju
yawa shi kad'ai sai kyakyata dariya take.
kamar yadda take mata wasa take b'allewa da dariya haka nan take yi, har tana mika hanu alamun a d'auke ta.
Cikin kad'uwa da firgici Aunty takuma yin baya da karfi ta furta
"Innalillahi'wa inna'ilaiihirraji'un!."
ai ko kamar jira ake tayi magana.
a hankali godon yashiga saukowa har ya diro kasa tamkar an dai-dai ta zamansa a gurin zaman sa.
Karaf Feeryal ya saukakan Aunty,
ganin Aunty tafara mika hanu ta d'auke ta, Aunty kuwa cikin hanzari ta bud'e kofa jiki na
b'ari tayi waje cike da d'inbin tsoro.
Tana jiyo kukanta bata ko waiga ba,
a parlour ta tsaya tana maida numfashi, tare da dafe kirjinta dake dukan tara-tara!.
addu'a tafarayi wanda duk yazo bakinta yi take tana saukewa.
a matukar tsorace tashiga kwad'a
wa Baba Rabi kira.
"Baba Rabi Baba Rabi!."
da sauri Baba rabi ta fito tana amsa kiran, ganin yadda gaba d'aya ta rasa nutsuwarta Baba Rabi tashiga tambayar ta ba'asi.
bata iya magana ba sai nuna kofar bedroom d'inta take da hannu.
da sauri Baba Rabi ta nuf
i kofar bedroom d'in jiyo kukan Feeryal daga ciki.
dan tagama tsinkewa wani abun ne ya sameta, ganin yadda gaba d'aya Aunty ta firgice.
Tana shiga d'akin ta hangoto zaune a kan gadon ta tana kela kuka da mika hanu tana niman mai d'aukarta.
da sauri ta kar
aso gareta ta sa hanu ta d'auke tana fad'in
"Me ya same ki Feeryal Ammie'n ki ta shiga firgici? kuma dai gaki lafiya lau nagan ki, to ko wani abun tagani cikin bayi?."
Tayi waje da ita tana jijjigata.
ta taho in da Aunty take tsaye zuwa yanzu nutsuwa yafa
ra shigarta da taimakon addu'o'in da take ta yi.
ta mika mata ita tana fad'in
"Hajiya wani abin kika gani ne cikin band'aki akirawo security suzo su cire?
dama da an fara zafi wad'an nan muggan igiyoyin kasan zasu fara niman gurin sanyi su rika fitowa daga
mab'uyarsu suna shigewa ramuka ta baya suna shigowa mutane ta cikin toilet."
Ido Aunty ta kurwa Feeryal da tsoron ta ya kamata
batare da ta karb'e ta ba, itako sai zillo take tana mika hanu tana so ta taje gurinta.
"Rike ta naje na kirawo su suzo su kash
e kada ya shige wani gurin a rasa shi."
Baba Rabi ta kuma fad'i tana dad'a mika mata ita.
Ja da baya tayi idon ta a kan ta tana kallon cikin kwayar idanunta farare soll masu sananin farin haske, kwayar idanunta madadin fari da d'igon ash, shi fari ne tas
da d'igon green da d'igo-d'igon gold and ash a had'e.
yanzu kuwa yadda'a sauyawa har wani kore'kore yake ga duk wan da yaga yanayin sai ya bashi tsoro.
Ido Aunty ta rumtse tana kuma bud'e su a kanta, sai taga kalar ya ragu ya koma irin kalar idanunta.
"
Baba Rabi bakiga komai cikin d'akin ba?."
"Babu komai cikin d'akin nan hajiya, sai dai naje na kirasun suzo su bincika kin san igiyar kasa basa tsoron mata."
kai Aunty ta girgiza ta ce
"Kar ki kirasu babu komai kawai na tsorata ne."
Baba Rabi zata kuma ma
gana Daddy ya shigo.
Da sauri ta d'an rusna tana miko gaisuwa.
ai ko Feeryal na ganin sa tafara miko masa hanu tana wage baki.
ya karb'e ta yana amsa gaisuwar.
da sauri Baba Rabi ta wuce kichin domin kammala aikin ta.
Daddy ya zauna kan d'aya daga cikin
kujerun parlour'n yana yi wa Feeryal wasa sai b'arkewa da dariya ta ke.
har lokacin Aunty na tsaye jikinta a sanyaye.
"Ya dai Ammie'n Feeryal wani abin ne?."
cewar Daddy yana duban ta.
kai ta girgiza jiki a sanyaye ta ce
"A'a." ya jinjina kai yaci gaba da
yiwa yarinyar wasa.
A hankali Aunty ta ja kafafunta d'aya daga cikin bedrooms d'in parlour'n ta shiga, ba bedroom d'in kwanan ta ba, a nan tayi wanka.
ta fito tana shirin yin sallar magriba da aka soma kira.
Daddy ya shigo da Feeryal a kafad'ar sa tana b
acci.
"Yau an sauya mana gurin kwana ne dama an jima ba'a sauya ba."
murmushi ta yi "Ba yau ba wanka kawai nayi a nan d'in zan koma can."
"Feeryal tayi bacci tayi ta mita da alama yunwa take ji ko za'a tasheta tasha mama ta koma."
"A'a abarta tayi bacci sa
i ta tashi, Daddy ka shinfid'a ta a can zanje nayi salla a bedroom ina."
ta nuna kan bed d'in d'akin.
Da sauri tayi waje yana kwantar da ita yabi bayan ta.
"Fad'imatu."
yakira sunan ta tana daf da shigewa d'aki.
taja ta tsaya tare da waigowa gare shi.
yak
araso in da take, idon sa a kanta ya ce
"Wai me ke faruwa ne me ke da min ki? akwai abin da ke damun ki nafi kowa sanin ki."
ido ta d'an lumshe ta bud'e su a kansa sannan ta ce
"Daddy nafara shiga kokonto akan Feeryal, acikin kwanakin nan ina ganin wasu sa
uye-sauye tare da ita, idan na aje ta naje nayi aiki na sha zuwa nasame ta tana wasa ita d'aya tayi ta dariya kamar wanda take kallon wani da ni bana ganin sa;
da fari ban d'auki hakan akomai ba nasan yaro yakan yi haka, amma yau Feeryal ta bani tsoro!."
da sauri ta waiga jin kamar an wulga ta bayanta.
ido Daddy ya kura mata ganin yadda taja numfashin tsoro.
hannunsa ta rike gam sannan ta ce
"Bakaji kamar an wuce ba?."
kai ya girgiza ya ce
"Banji ba."
sai kuma ya janyo hannunta suka shige cikin bedroom.
a
bakin gado ya zaunar da ita yana tsaye a kanta ya dafa kafad'arta, ya dube ta da kyau sannan ya ce
"Fad'imatu, kar dai ace maganar mutane yafara tasiri a kanki? kada ki bari kururuwan jama'a yayi galaba a kanki, ya akayi kika mance da addu'o'in ki, kefa kk
tunasar da ni wani lokacin,
duk in da bawa yake shed'an yana nan a gurin, haka aljanu duk in da muka sa kafarmu suma suna gurin, imma shed'anunsu imma na kirkinsu, sai dai mu bama ganin su, akwai hanyoyin da ake bi dan nisanta kai daga sharrin shaid'an i
bilis da kuma shaid'anun aljanu, ina sammanin sai dai ki fad'awa wani dan kinsan hanyoyin,
babu abun da shaid'an bazai iya ba ko kin mance wa'azin malam Aminu Daurawa ya ce
shaid'an yakan zuba kasa akan gado, mata tayi shinfid'a tayi komai dan ya had'ata f
ad'a da mijinta?."
ya karashe maganar da murmushi.
kai ta jinjina ta ce
"Amma Daddy kasan ya na shigo na tadda Feeryal kuwa, gadon ta yana lilo a sama fa tana ta dariya, ina tsaye ina gani kuma gadon ya sauko."
d'an shiru ya yi alamun nazari sai kuma y
a d'an dara ya ce
"Da alama dai yau bakiyi Azkhar d'in yammaci ba, idan kikayi salla kiyi, kisa a ranki babu komai gizo ne kawai, sa rai akan abu yakansa kaga abun kamar ya faru, yau she kika fara yarda da maganganun mutane iye Fad'imatu?
kada ki bari maga
nganun su ya yi tasiri a zuciyar ki,
har yayi nasarar hanaki taimakon rai da kika d'au himma."
"Ban tab'a yarda da maganar mutane ba, ban tab'a jin Feeryal amatsayin aljana ba,
kawai abin da nagani ne yasani shiga shakku."
Nurmushi Daddy ya yi da
n son share mata shakkunta yakuma karfafa mata guiwa ya ce
"Gizo ne kawai kinsan wani lokacin haka d'an adam yake musamman wad'an da damuwa tayi musu yawa a kwakwalwa,
yau dai da alama kin shiga sahun su, bari na tafi masallaci kada na rasa salla babu kom
ai Ammie'n Feeryal kiyi addu'a kinji."
Kai ta girgiza tare da sauke numfashi, yafita zuwa masallaci ita kuma tamike domin gabatar da sallah.
Tajima tana addu'o'i har sallar ishe yasame ta kan sallaya.
bayan ta gabatar ta mike ta shirya ta fito, tana jin
zuciyarta wasai nutsuwa na shigarta.
D'akin da Feeryal ke bacci ta shiga, ta isketa tana ta baccinta. ta d'auko ta, ta mai da ita bedroom d'in ta.
Washegari da safe bayan Aunty tagama kimsa side d'inta da taimakon Baba Rabi,
kamar yadda suka saba idan Da
ddy yana gurin ta,
tun kan Daddy ya fito parlour Baba Rabi take shigowa side d'in.
ta gyara parlour zuwa kichin, ta tanadar mata da duk abin da tasan zatayi amfani da shi na breakfast a kusa, sannan ta koma b'angaren su na ma'aikatan gidan.
dan a iya nan a
ikin ta ya tsaya dan ko gyaran bedrooms d'in cikin side d'in Aunty ke yi da kanta, idan kaga Babaa Rabi tayi girki; to Daddy baya side d'in.
bayan Aunty ta fito ta wuce kichin ta tadda Baba Rabi ta tanadar mata da duk abin da zata bukata kusa, nan ta soma
had'a breakfast d'in da tasan Daddy ya fi so.
Bayan ta gama ta kwaso hadaddun breakfast data shirya wajen kala uku ta kawo su kan dinning.
ko da ta koma bedroom ta tadda Daddy ya farka,
ta wuce bathroom ta had'a masa ruwan wanka.
bayan yafito ya shirya ya
fito parlour.
a tare suka yi breakfast cikin plt d'aya kamar yadda suka saba.
Bayan sun kammala Daddy ya dawo parlour yana kallon labarai.
Aunty ko na kichin tana wanke kwanukan da suka b'ata.
kukan Feeryal da tajiyo ne yasa ta fita da sauri tana fad'in
"
An tashi ke nan."
Daddy da ya mike zuwa d'auko ta ganin fitowar Aunty yasashi komawa ya zauna.
Da sauri ta kara cikin d'akin ta d'auke ta tana jijjigata.
"Ya isa ayi shiru antashi ne yunwa ake ji ne?."
tana fad'i tana bubbuga bayanta.
ta zauna bakin gado
sai da ta rarrasheta tayi shiru,
sannan ta mike ta aje ta a kasa tana fad'in
"Nasan hali zauna a kasa bazan aje ki a kan gado ki fad'o ba, ba'a iya rarrafe ba sai rawar kai, zauna muzo muyi wanka, yau muyi anan ba sai munje bayi ba."
ta shige bayi ta had'
o ruwan wankan a bawo mai d'an girma ta fito.
Feeryal na zaune a gefe tana ta wasa da abin wasan da ta saka mata shi a gabanta.
d'an gajeren tsaki Aunty taja, tuno da bata d'auko sabulu ba ta mike ta koma bayin.
Ta fito d'auke da sabulu turus taja ta tsa
ya bakin kofar bayin tana kallon Feeryal da ta ganta cikin bawon wanka, ga kuma kayanta a gefe an cire mata, tana zaune cikin ruwa sai wasa take tana dariya.
tana mika hanu kuma alamun a d'auketa tana kuma kallon gabanta tana cigaba da dariyar da kuma mika
hanun ma wanda ita bata ganinsa.
Bin cikin d'akin tayi da kallo tana tunanin ko wani ne ya shigo ya tub'e mata kayan ya sata cikin bawun d'in.
babu kowa cikin d'akin babu wani alamar da ya nuna wani ya shigo daga d'an shigarta bayi d'aukar sabulu zuwa fi
towarta, da bai wuce second 40 zuwa minti 1 ba.
ta kuma san ba Daddy bane dan shi bazai barta a cikin ruwa mai yawa haka yafita ba.
Numfashi taja sai kuma ta d'an saki murmushi ya yin da take karanto wasu addu'o'i cikin ranta,
tana fata idan abin da take
tunani hakan ne to surabu da ita lafiya dan ita bada niyyar cutarwa ta d'au ko ta ba.
ta karaso in da take tana fad'in
"Nab'ata lokaci wajen d'auko sabulu ko? bari nayi miki wankan ki ko Baby'n Ammie'n ta."
kamar wacce ta fahimci abin da take fad'a tashiga
bubbuga hanunta cikin ruwan tana yin irin yadda yara suke idan suna cikin ruwan wanka suna wasa da shi.
da karfin addu'ar da take taga ma yi mata wanka, kana ta shirya ta cikin kaya masu kyau da tsada.
sannan ta d'auko ta suka fito parlour bayan ta gyara
in da suka b'ata.
Daddy na ganin su ya mika hanu itama ta wage baki ya karb'eta yana cillata sama, tana kyakyata dariya.
Aunty ta bisu da murmushi.
har Daddy ya fita batayi masa hirar abin da tagani ba, dan tasan yanzun ma ce mata zai yi gizo ne...
Da ya
mma Aunty na kichin tana aiki, Feeryal kuma na parlour tana wasa a zaune da kayan wasanta.
lokaci zuwa lokaci take fitowa duba ta.
ta kwaso kulolin abinci kan babban tray tanufi dinning da shi.
tun kan ta karaso dinning d'in take kallon ikon Allah.
Feeryal
ce zaune a tsakiyar dinning hannunta biyu cikin bama tana sha tana kwab'awa, ta kwab'a bakinta da fuskanta gaba d'aya,
sai ta kwamulo shi ta mika hanu alamun tana mikawa wani sai a karb'a sai dai bata ganin mai karb'ar sai dai taga babu komai a hannunta.
A hankali Aunty ta juya ta dawo parlour ta dire tray'n kan table d'in parlour,
sannan ta koma kichin da sauri bata bari ta ganta ba.
suka cigaba da gyara kichin d'in tare da Baba Rabi.
bata fitoba sai da suka gama