Showing 3001 words to 6000 words out of 86898 words
abinci,
bari nashiga kichin yanzu na samar maka abincin da
zakaci."
Hannunta ya rike ganin tana kokarin mikewa ya ce
"Dakata mufara samar mata da nata abincin kafin,
muje asibiti musami shawarwari gurin likitocin yara, ta in da zamu inganta mata lafiyarta da kuma abincin da zata rika ci."
kai Hajiya Fatima ta gi
rgiza kana ta ce
"Kuma yunwa takeji da gani, tun d'azu take ta kananun kuka."
mayafinta ta d'auka yana gaba rike da FEERYAL tana biye da shi suka fita,
direba yakaisu asibiti.
Kasancewar likitan sananne ne agurinsu,
Alhj Abubakar ya yi masa bayanin komai
kan tsintarta sukayi.
bayan likitan ya bincika lafiyar ta da nazari kan abincin da zai karb'i jikinta.
ya shaida musu madara bazai d'auki jikinta ba, idan har akace za'a masa kan sai tasha madara,
karshe ta iya rasa ranta dole nono ne kad'ai zai iya d'auk
ar ta.
Alhaji Abubakar ya ce
Za'a nimi mai shatar da ita, Hajiya Fatima ta ce ina ita zara shayar da ita.
Da amincewar maigidan nata atake agun aka sakamata sinadaran da zasu kawo mata ruwan nono bayan wasu y'an awanni suka juyo gida.
Kan kace me ruwan n
ono ya kawo tamkar mai sabon haihuwa kuma na fari, haka ruwan nono yaciko.
nan da nan kuwa yarinya ta karb'i nono takama sha.
Washegari da safe.
Hajiya Fatima ta shirya jaririyarta cikin wasu kaya masu kyan gaske, suna zaune a parlour,
Alhaji Abubakar naz
aune a gefen ta yana kallon yanda take yashar da jaririyar, gwanin ban sha'awa.
murmushi ya yi tare da shafo gefen fuskarta.
"Yamiki kyau sosai shayarwa, Allah ya baki iko da lafiyar cigaba da shayar da ita."
da ido ta amsashi tana aika masa murmushi.
Kno
cking akayi tare da turo kofar parlour'n.
burki taja daga bakin kofar tarike hab'a tana kallon Hajiya Fatima da jaririyar da take shayarwa, cike da matukar mamaki.
murmushi Hajiya Fatima ta yi ta ce "Ki karaso mana Farida, ya kika tsaya daga bakin kofa."
Fuska ta yamutsa gulma na cinta har kafarta na rawa tana alla-alla ta yuya ta ce
"Daddy wai kazo inji Hajiya."
tana gama fad'i ta juya da sauri.
gudu ta saka bata tsaya ko ina ba sai side d'in Hajiya Halima mahaifiyarta kuma uwargida ga Alhaji Abubakar Fi
ya.
a parlour ta tadda uwar tata, da kuma Hajiya Karima mata ta biyu ga Alhaji Abubakar, da y'ay'an su duka.
kamar zata zube kasa cikin haki take fad'in
"Mommy Aunty ta haihu."
cikin rashin fahimta Hajiya Halima wato Mommy ta ce "Ke wata Aunty? kin shigo a
razane duk kin razana mutane."
murya na rawa cike da tsugudidi ta ce
"Aunty Fatima wlh yanzu nan naganta tana baiwa jariri nono, Daddy na zaune a gurin."
Ido Hajiya Karima ta gwalalo tare dare da fad'in
"Zancen banza kai yaushe akayi cikin da za'a yi hai
huwar har kowa ya kasa sani, ai wannan sai dai taga haihuwa a tsuliyar wani badai a nata ba."
"Wlh Umma Karima naganta da idona tana bawa yaro nono."
kirji Hajiya Karima ta buga har suna had'a baki da Mommy wajen fad'in
"Yaushe tayi ciki har ta haihu bamu
sani ba."
"Wlh ni dai na ganta dama Hajiya ce ta aike ni kiran Daddy tun jiya take ta kiransa a waya baya d'auka,
shine tace naje na kirawo mata shi dan tasan yana can makale wajen kinibabbiyar matar nan tasa, bari ma naje na sanar mata sabon labari."
ta
fice da gudu tanufi sashin Hajiya wato kakar su.
Tun daga bakin kofa take fad'in "Hajiya Hajiya Hajiya."
wata dattijuwar mata dake zaune a wani kayataccen parlour tana sanye da gilashi a idanunta, hutu da kwanciyar hankali sun bayyana a kijinta, wanda ya
b'oye tsufarta, zaka iya mata kallon daya gaza shekarunta sabar hutu.
"Ke wani irin shashancin kira ne wannan, sai naci mutuncinki Farida, ina tun d'azu na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa ko."
cikin rad'a da iya gulma ta ce
"Hajiya wlh Aunty ta haih
u Daddy yana can."
baki Hajiya ta karkace ta ce
"Ke Farida Fatima ce ta haihu cewa akayi miki haihuwar wasa ce, shekara nawa tana zaune sai dai taci taje ta juye a shadda, ko b'atan wata bata tab'a yi ba,
wannan da ita yafara aura nasan bazata tab'a barins
a ya kara aure ba, da ni da ganin jikokina ta gefen sa kuwa har abada, sai dai in cikin abinci tayi ta haifa a shadda, bari naje na ganewa idona."
"Wlh Hajiya kije kigani da gaske ne."
Hajiya ta mike tanufi kofa tana fad'in
"Yanzu ma kuwa, dan rashin dara
ja Fatima tafi masa ni, tun jiya baizo ya gaishe ni ba yana makale a gurin ta."
A b'angaren su Mommy kuwa bakaramin girgiza sukayi da jin lamarin ba, dukkanin su suka nufi sashin Aunty dan gane wa idon su abin da ke faruwa.
a kusan tare suka iso da Hajiya
dan ita direban ta tasa ya kaita side d'in Aunty'n dan tafiyar tafi yi mata sauki.
suna shiga parlour'n kowa yatsaya cike da d'in bin mamakin ganin jaririya a hannun Aunty tana shayar da ita.
hankali tashe Mommy da Umma Karima suke kallon-kallo, kowa da i
rin abun da yake sakawa a ransa.
hajiya ta rafka wani uban salati tare da tafa hanu tana fad'in
"Ikon Allah Abubakar ina cikin gidan ayi haihuwa ban sani ba, kamar yadda bansan da cikin ba, Eh lallai ta wanke ta baka kasha, ka mance da uwar da ta haife ka.
"
Da sauri Daddy ya mike yana fad'in
"Sannu da zuwa Hajiya yanzu nake shirin zuwa gaishe ki, bismilla ga guri zauna."
hannu ta d'aga masa tana fad'in
"Ba zama ne ya kawo ni ba, na ce yaushe ta haihu ban sani ba!."
kai ya sunkuyar kana ya d'ago ya dubi mah
aifiyar tasa kana ya ce..........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺
*FEERYAL*
🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biy
a ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S
✍
🏼
*
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawr
itersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*
👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
🅿
️
2
"Da ma Hajiya zanzo muyi magana, amma t
un da har kinzo ki zauna kiji yadda akayi zata haihu ne baki sani ba."
"Ba gashi kuwa sai zuwa nayi naga d'a a hannu ba, ai baka d'auke ni da mahimmanci ba, narasa me ke damunka Abubakar akan Fatima duk ka susuce kazama wani iri, tun jiya nake kiran ka a w
aya sabo da kuna nakudar munafurci kaki d'aga wayar ma, bare har kazo in da nake,
Allah yasa kafin ta haihu dubunta sun haihu,
ko wani munafurcin ne na b'oye cikin da haihuwar oho."
wani irin mummunar fad'uwar gaba Umma Karima ta ji.
yanzu bawai haihuwar
ce ke firgitata ba, duk da tabbacin da take da shi kan cewa bazata tab'a haihuwa ba har abada, ga kuma akasin hakan ta gani.
fatan ta d'aya kada a ce namiji ta haifa.
a b'angaren Mommy ma haka abun yake.
mita ta shiga yi tana dad'a ingiza Hajiya
"Yanzu h
ar rashin muhimmancin mu yakai ta haihu a cikin gidan nan bamu saniba, idan an b'oye ciki sai a b'o haihuwa, haba Alhaji me ka mai da mu haka."
Hajiya ta cab'i zancen da fad'in
"Marasa mutunci mana haka ya mai da kowa, to ka zauna da matarka kucigaba da mu
nafurcin ku, kada ka sake kazo in da nake."
Ta juya tana kokarin fita da sauri ya tare ta
"Hajiya kiyi hakuri ki saurare ni,
bafa haihuwa Fatima tayi ba, sai kuma tayi ciki har ta haihu ki gaza sani, abun da ake fatan samu idan aka samu ai kowa sai ya san
i,
bana gida ba har da na waje, kowa za'a sanar masa yataya mu farinci,
jiya a hanyarmu ta dawowa muka tsinci jaririyar a cikin ruwa, da alama had'ari iyayen ta sukayi tana bukatar taimako,
shine muka d'auke ta, likita ya shaida mana bazata iya rayuwa ba
sai da nonon uwa shiyasa aka samarwa Fad'imatu ruwan nono domin ta ceto rayuwar ta."
Wani irin zabura dukkanin su sukayi.
Hajiya ta bigi kirji ta tuma tsalle ta zube kasa ta saka hannu a ka tana fad'in
"Wayyo Allah Abubakar da Fatima zasu kashe ni, tsin
tar ta kukayi kuma a cikin ruwa, anya Abubakar
kanka d'aya kuwa ko aljanu sun shafe ka ne,
ku tsinci 'yar kuma acikin ruwa ma har ka lamunci matarka ta shayar da ita,
sabo da karasa 'ya'ya ne ko me?
idan ita juya ce bata haihuwa ai kai da 'ya'yan ka ta
ganka tafe da kafafun su,
duk basu ishekaba har sai kanimi kari da 'ya'yan aljanu."
Tamaso ta leka fuskar Feeryal dake rungume a hannun Aunty, data rungume ta tsam kamar za'a kwatar mata ita.
Hajiya takuma zabura tare da mustsuke idonta tana fad'in
"La
haula maganin baki wasayyahuuuuu ya tsaya a kanki Fatima!
Abubakar d'iyar aljanu kuka d'auko kuka kawo mana gida,
wlh ko shakka babu wannan d'iyar aljanu ce, tun da nake ban tab'a ganin mutum irin wannan ba,
ko a fina-finan masu jajayen kunnuwan da nake
gani ana haskosu a TV,
dubi kalarta dubi kalar kwayar idanun ta, sam basuyi kalar na mutane ba,
kwayar ido kamar na magen mayu wlh ba mutum bace;
maza-maza kuyi gaggawar d'aukar 'yar su ku mayar musu in da kuka d'auko musu ita,
tun kafin bala'i ya sauka a
gidan nan,
dan bazamu iya da fad'an aljanu ba,
dan babu kaura cikin dangin mu,
wani bala'in kuke son d'auko mana, zaku d'auko aljanar ruwa ku kawo mana ita gida."
Mommy da Umma Karima har suna rige-rigen zuwa leka fuskar yarinyar, bakaramin firgici suka
shiga da ganin halittar 'yar ba,
'ya'yansu ma kowa sai da yaje yagano fuskar ta.
Mommy tashiga zabga salati da tafa hannu tana fad'in
"Wlh aljana ce Hajiya dakur'ani bazamu zauna da aljanar ruwa a gidan nan ba, ko a fita da ita ko mu mufita da 'ya'yan mu
, dan ambaliyar ruwa bazataci da mu ba ehe."
Umma Karima ta karkata baki cike da rashin mutunci tana aikawa Aunty kallon banza ta ce
"An dai yi asara rashin haihuwa nason bud'a miki kai shine har zaki d'auko aljana ki kawo mana ita cikin gida,
to wlh ba
a gidan nan ba, idan haihuwar abin banza ne ki haifa mana,
sai kinje kin d'auko aljanar ruwa kin kawo mana damuwa."
Rumtse ido Aunty tayi tana jin yanda maganganun su ke mata yawo cikin kwakwalwa.
da sauri Daddy yataro Hajiya ganin yadda take shiga bata n
an take fita ba.
ya ce
"Hajiya kiyi hakuri amma ba aljana ba ce mutum ce, ina kyautata zaton watakila badaga yankin kasarmu take ba,
shi yasa kamanninta ya bambanta amma mutum ce ita irin mu."
"Inji uban wa tun da kake katab'a gani mutum kyakkyawa irin wa
nnan?
kana kallon aljana kiri-kiri kace mutum,
dama ance aljanun ruwa kyawawa ne gashinan kiri-kiri ina gani kace ba haka ba,
kai Ajimi kirawo min Sulaiman da Tukur yau zan bar gidan nan dan bazan zauna da aljana ba."
Ajeemal ya juya yana jan kwafa, sa
m baya son fitinar kakar nan tasu.
Hajiya ta cigaba da fad'a har tana kumfar baki, su Mommy na tayata.
batare da b'ata lokaci ba Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suka amsa kiran mahaifiyar tasu.
Hajiya na ganin su takawo kuka ta saka tana sharb'e hanci d
a fad'in
"Zamata yakare a gidan nan Abubakar ya zab'a ko ni ko aljanar ruwa da matarsa."
da sauri suka karaso in da take sukashiga bata hakuri, Alhaji Sulaiman ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri zo muje sashin ki muyi magana."
da kyar suka janye ta zuwa s
ashin nata.
Numfashi Daddy ya sauke ganin fitarsu kana ya maida dubansa kan Mommy da Umma Karima ya ce
"Duk wacce bazata iya zamaba ta kama gabanta."
yana kaiwa nan yajuya yabi bayan su Hajiya.
Mugun kallo suka wasawa Aunty Umma Karima ta ce
"Bokanki yaf
ad'a miki karya sai dai ke kibar gidan nan ba dai mu masu 'ya'ya ba."
Mommy kuwa kwafa tayi tare da kuma wasa mata harara tajuya takad'a keyar 'ya'yan ta tana fad'in
"Maza kubar nan kada aljana tashiga jikinku."
Murmushin takaici Aunty tayi tare da bin ba
yansu da kallo, tana mai dad'a rungume Feeryal ajikinta.
A can sashin Hajiya kuwa sosai ta tubure ita ala dole sai dai Daddy ya zab'i ko ita ko aljanar ruwa,
dan bazata zauna da aljana a gida d'aya ba, bare ta shafe ta ta shafi jikokinta.
da kyar suka sh
awo kanta da alkawarin za'a mai da yarinyar inda aka d'auko ta.
Ko da suka fito daga sashin nata Alhaji Sulaiman wato Abbieh da Alhaji Tukur Dad suka dubi d'an uwan nasu.
Dad ya ce
"Yaya ina ganin a d'auki yarinyar nan a mayar da ita in da aka sameta ina
ganin shine kad'ai samin masalaha,
Hajiya tayi fushi sosai."
Kai Daddy ya girgiza sannan ya ce
"Adai canza mata wani gurin dai-dai ta huce, ta ya za'a ce a maida ta cikin ruwa kisan kai ke nan zamuyi,
yarinyar nan ba aljana ba ce mutum ce, imma aljanar
ce iyayen ta suzo su d'auke ta anan ba sai an kaiga cutar da rayuwarta ba,
sannan idan aka rabata da Fad'imatu itama an cutar da rayuwarta,
dan yanzu tamkar mai sabuwar jego take."
"Yaya to kayi wani abu dan Allah dan gujewa fushin hajiya."
cewar Abbieh,
kai Daddy ya girgiza kana ya ce
"Insha'allah."
Aunty na zaune tayi jigum Daddy ya shigo, ya zauna gefen ta.
da sauri ta dube shi jiki a sanyaye ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?
dan Allah Daddy kar a rabani da Feeryal wlh ina son ta."
takarashe maganar
da damke hannunsa murya a marairaice tamkar zata zubda kwalla.
Hannunta yakuma rikewa cikin nashi kana ya ce
"Insha'allahu baza'a rabaku ba nayi miki alkawari."
wasu hawaye ta share ta ce
"Nagode Daddy." murmushi mai sauti ya yi tare da jan hancinta
"Amm
ie'n Feeryal a kwantar da hankali haka a daina damuwa da yawa."
kai ta girgiza tana mai da masa murmushin.
A sashin Hajiya bayan fitar su Daddy da d'an jimawa, Hajiya ta cewa Farida taje ta duba mata aljanar tana nan har yanzu ko an tafi da ita.
ko da Fa
rida taje sashin Aunty'n a kulle yake tadawo ta shaidawa Hajiya.
Hajiya tayi kwafa dan a zaton ta sun tafi mai da jaririyar in da suka d'auko ta ne.
ta gyara zama ta soma cin abincin da kulu mai aikin ta takawo mata yanzu,
tana fad'in
"Iya shegen banza da
raina da lafiya ta ina gidan wai sai abin da Fatima ke so za'a yi,
rashin haihuwa hauka ce, da zata fara bin teku tana d'iban 'ya'yan aljanu tana kawo mana cikin gida;
wan nan badun daga gidan arziki tafito ba sai na ce wani muguntar take son kitsawa,
t
akawo aljanu su kwashe mana dukiya su kai mata gidan iyayenta."
"Hajiya wai ashe aljana Hajiya Fatima ta kawo wlh kar kiga yadda na razana aljana kuma a cikin gidan nan, to ita meye gamin ta da aljanu kuma."
cewar Kulu tana zama kan kujera d'an nesa da Ha
jiya.
Hajiya takai loman katon nama baki tana fad'in
"Niman jaraba mana da niman ganin bayan mutum, to ni nafi karfinta da jikokina,
sai dai taje can ta karata da aljanun, ba dai a gidan nan ba kam, je ki kawo min lemon gorar nan mai d'an sanyi."
Kulu ta
tafi tana rike hab'a da mamakin lamarin.
Kwanan Feeryal uku a gidan batare da kowa yasan tana nan ba, dan kowa ya yi zaton da hajiya ta tada bori an mai da ta in da aka d'auko ta.
itama Hajiyar sam batasan tana nan ba.
Umma Karima ce cikin Bedroom in Da
ddy, shigowarta kenan bayan komawar ta part inta da asuba, data kwana a sashin nasa,
anje anyi wanka an cab'a kwalliya, an shafo wasu turaruka masu tsayawa a kuwa.
ganin baya side d'in gaba d'aya, ta koma side d'in ta,
ta tura babbar 'yarta Saddiqa taje
ta duba mata Daddyn su yana part d'in Aunty'n su.
A bakin get in shiga side in Aunty suka had'u da Ajeemal zai wuce side d'in Hajiya.
yana ganin ta ya sai da ta.
"Ina zakije?."
ta ce "Umma ce ta ce naje na duba Daddy a side in Aunty."
ya ce "Wuce ki kom
a kice baya nan."
baki ta zumb'uro, tana ganin wucewar sa da gudu tayi cikin side d'in.
tana shiga parlour'n Aunty kai tsaye ta wuce cikin bedroom inta babu ko knocking bare sallama.
Aunty na zaune bakin gado tana shirya Feeryal data yi mata wanka,
jin an
turo kofa yasata d'agowa tana duban mai shigowar.
ganin Saddiqa ce, ta girgiza kai tana fad'in
"Saddiqa bana ce in zaku shigo kurika yin knocking da sallama ba, ba kyau shigowa d'aki kai tsaye batare da yin sallama ko niman izini ba,
to ya akayi?."
Aunty
tayi tambayar tana mai da hankalinta kan shirin da take yiwa Feeryal.
Saddiqa ta juya ta fita bare da ta ce komai ba, kai takuma girgiza wa ta cigaba da abin da ta ke.
Da sauri ta koma side d'in su, tun kan takaraso in da Umma Karima ta ke tashiga fad'in
"Umma Umma Umma wlh Aunty tadawo da