Showing 9001 words to 12000 words out of 86898 words

Chapter 4 - FEERYAL BOOK1 COMPLETE

gida d'aya, daga nan duk ta shige jikin ya'yan mu."

"Karima ya ishe ki haka fita kitafi sashin ki nace!

."

Umma Karima ta juya tana cigaba da mita tafice.

tsaki Daddy yaja tare da cigaba da abun da yake cikin computer sa.

Washegari da misalin karfe 6, su Hajiya ne zaune a parlour anata fita da kayan su zuwa mota.

Mommy Umma Karima Hajiya Safiyya matar Alha

ji Sulaiman wato Abbieh da kuma Hajiya Nafisat matar Alhaji Tukur Dad ke nan.

da ya'yan su duk suna parlour'n.

Hajiya Bishira tun a daren jiya ta iso kamar yadda Daddy ya fad'a.

Mommy ta nisa ganin saura kad'an a gama fita da kayan su ta ce "To Hajiya i

n an tafi kuma sai yaushe?

yauwa Hajiya dan Allah ki kumakiyiwa Alhaji magana kafin ki tafi,

har yanzu fa baya cin abincin mu sai na wancan matar Fatima, ma'aikata masu tsafta muke da su amma ya ce wai bazaici abincin mu ba,

sai dai yarika shiga hakkinm

u ran girkin mu ma ita ke masa girki."

Hajiya ta d'au gilashin ta ta saka tana fad'in

"Kai sai dai fa kuyi hakuri dan abinshin gado ne dan asali ya samo,

da ubansa ma baya cin abincin mai aiki, idan ina so yaci kuwa dole sai na girka masa da kaina, shima

kuma Abubakar d'in a haka ya taso in har me aikice ta dafa to bazaici ba sai in ni na girka da kaina kafin yaci,

bai iya cin abincin masu aiki bane tuntuni,

in kun zab'i hutu kawai ku huta ku barta ta cigaba da bauta."

Kai Hajiya Safiyya ta girgiza tana

mai mamakin hali irin na Mommy da Umma Karima,

Hajiya Nafisat kuwa cewa tayi

"To me akayi ke nan kana da halin hutu baka hutan ba."

Shigowar su Daddy ne yasa Umma Karima da ta budi baki zatai magana yin gum da bakinta.

Daddy ya ce "Hajiya taso maza saura

awa guda jirgin ku ya tashi."

duk suka mike sukayi waje gurin mota.

Hajiya na kokari shiga mota Aunty ta karaso gurin,

tad'an rusuna tare da fad'in

"Ina kwana Hajiya, Allah ya tsare hanya ga wannan ki samu na d'an tab'awa a jirgi."

Hajiya ta karb'i laida

r da take mika mata ta bud'e, wani roba ne mai d'an girma cikin laidar, ta bud'e robar lafiyayyen dambun naman kaza ce dayaji kayan had'i yana fidda wani irin sihirtaccen kamshi.

Hajiya tahad'iye miyau mukutt, ba yabo ba fallasa ta wage baki tana fad'in

"L

afiya lau amin amin to angode."

"Cusa kai ba kwari niman gindin zama."

Aunty tajiyo muryar Mommy dake tsaye a bayanta, bata kula ta ba, yi tayi kamar ma bata jita ba.

tamasa in da Hajiya Safiyya take suka shiga gaisawa, Hajiya Nafisat kam 'yar fatin su Mo

mmy ce ko kallo bata isheta ba.

Motar su Hajiya na tashi ta juya ta wuce sashin ta...

Yau ya kama kwanan Daddy hud'u a side in sa, yau ne zai koma gurin Aunty.

lafiyayyun girki kala-kala ta shirya masa, bakajin komai sai tashin daddad'an kamshin turare n

a musamman ke tashi a side in.

Aunty tagama shirya tarb'ar mijinta.

Al'adar ta ne a duk san da zai dawo gurin ta, da daddre kafin yatafi side d'in ta sai tazo ta gyara masa sashinsa, dan basa gyarashi haka kowa zata gama zamanta ta tafi, tun da ya ce baya

son me'aiki ta gyara masa sashinsa, suka gwammace su barshi haka, dan suma nasu sashin masu aiki ne suke gyara musu.

duk da sashinta yake zuwa ya tare idan kwanan ta ya zago,

amma sai ta taho ta gyara masa side d'in sa idan yana d'akinta.

Tana saka da g

yaran part d'in nasa da ya yi datti tamkar ba mata bane sukayi rayuwa a ciki, tsawon kwanaki hud'u.

Feeryal na kwance a kan kujerar parlour'n Daddy Aunty na goge-gogen parlour'n.

Mommy da Umma Karima suka shigo, kallon banza sukabi ta da shi.

ko in da suk

e ma bata kalla ba in da sabo ta saba.

idon Mommy ne ya sauka kan Feeryal da ke kwance kan kujera.

ido ta gwalalo ta buga kirji tare da fad'in

"Me zan gani haka anan aljana a parlou'n Alhaji!."

Umma Karima ta shiga tafa hannu tana fad'in

"Dama ashe baki ma

yar da ita ba sai da kikaga Hajiya ta tafi kika fito da ita,

ai kuwa babu abinda zai hana Hajiya bataji labarin nan."

"Duk matar da tayi gigin kiran Hajiya a kan maganar nan to a bakin aurenta!."

Suka jiyo muryar Daddy dake fitowa daga bedroom d'in sa.

"

Kasan me kake fad'a kuwa Alhaji? akan wata banza aljana tsintacciyar cikin ruwa kake mana barazana da auren mu."

Mommy tayi maganar tana nuna Feeryal.

Umma Karima ta karb'i zancen da fad'in

"Eh ba laifin ka bane shi dama aljani da makiri babu ta inda baya

b'ullowa da salonsa, muje Hajiya Halima amma dole za'a yi zama dan bazamu yarda ba wlh."

taja hannu Mommy suka fice sunata surfa bala'i

Da sauri Aunty ta dubi Daddy ta ce "Daddy ya zaka ce haka."

"Dukkanin su na san halin su idan ba haka nayi musu ba to k

o shakka babu sai sun kira Hajiya da zancen, tanan ne kad'ai zai sa su hakura da kiran nata."

kai Aunty ta jinjina.

Daddy ya isa ya d'auki Feeryal dake ta baccin ta ya sakata a kafad'a, kana ya dubi Aunty ya ce "Muje ko."

nan suka fita suka nufi part in Au

nty'n.

Waiwaye adon tafiya shin wane ne Alhaji Abubakar Fiya? kubiyo ni dan jin wane ne shi.

Alhaji Shitu Fiya, mahaifi ga Alhaji Abubakar Fiya haifaffen d'an jahar plateau state ne awani gari da ake kira da Yelwan Shandam,

Alhaji Shitu Fiya shahar

arren manomi ne wanda yake noma gonaki sama da hamsin a ciki da wajen Yelwan Shandam.

yana da mata d'aya da ya'ya biyu Abubakar da kuma Sulaiman.

yana da manya-manyan gonaki da girman su yakai girma, a kalla sama da guda hamsin, yana noma nau'ikan abubuwan

da akafi amfani da su sosai a kasarmu.

Auduga, Shinkafa, Masara, Gero, Dawa, Maiwa, Rid'i, Agushi Gyad'a, farar Wake, Waken soya, Doya, Dankali, na hausa da kuma na surawa Rogo. da dai sauran nau'o'in kayan masarufi nayau da kullum.

ba a iya noman damina

ya tsaya ba har da noman rani.

idan amfaninsa tayi bayan ya cire zakka.

zai aje wanda gida zai ci na tsawon shekara, kana ya cire wanda zai raba kyauta wa danginsa da y'an garinsa, san nan a kai sauran kasuwa.

Cikin kankanin lokaci yazamo shahararren mai

kud'in da babu kamarsa a yankin.

a lokacin yakara iyali matansa suka zamo biyu, in da aka kuma samin karuwa bayan d'an wani lokaci amarya ta haifo d'anta na miji yaci suna Tukur.

Dukiyar Alhaji Shitu Fiya sai dad'a hab'aka take tamkar kullum dare ninka ma

sa ake.

ya yi shaharar da kaf fad'in kasar nan ansan da zamansa a wannan gari na Yelwan Shandam.

dan yanzu manya-manyan y'an kasuwa ne suke shigowa cikin garin Yelwa suke sayan kayansa suna fita dashi zuwa jahohin kasar nan.

Amaryar Alhaji Shitu wato Lub

a batayi tsawon rayuwa ba, ta koma ga mahaliccin ta ,

tare da tsohon ciki na biyu a jikin ta, lokacin d'anta Tukur yana da shekaru uku.

nan fa mutane masu fama da cutar gulma suka shiga kai kawo suna yad'a jita-jita, aka d'aura alhakin mutuwar ta kan kishi

yarta, wai ita ta kasheta dan ta zauna cikin daula ita kad'ai, dama da kyar ta bari akayi auren.

nan fa dangin Luba suka rungume zancen a kirjinsu suka yarda kan cewa ita ta kashe musu 'yar'uwar su, dan yanzu taga dukiyarsa ya ninka na da.

suka d'auki kara

r tsana suka sakawa uwargidan Alhaji Shiru, suka masa sai dai a basu Tukar kar shima ta kashe shi.

Alhaji Shitu Fiya bai yarda ya basu shi ba, ya ce yana da ransa da rufin asirin da Allah ya yi masa d'ansa bazai je agolanci wani gida ba.

Dayaki basu shi s

ai suka shiga zuwa suna d'aukarsa yana wuni a gurin su.

lokacin da yakara wayo kuma yashiga zuwa da kansa,

duk san da ya je, haka zasu zaunar da shi suna tambayarsa, me matar ubansa take masa, duk abinda ta bashi idan bai yarda da shi ba kada ya ci dan ita

ta kashe masa mahaifiyarsa.

da ire-iren wad'annan abubuwan suka rika cusa masa ra'ayi suna dad'a masa hud'uba kan cewa,

ita abokiyar gabansa ce dan ita ta kashe mamarsa kada ya yarda da ita, da kuma ya'yan ta.

a lokacin Hanne wato uwargidan Alhaji Shitu t

akuma haihuwan 'ya mace taci suna Bishira.

ai kuwa gari yakuma d'aukawa dama ta kasheta ne dan ta tara ya'ya tasami gado.

Hannatu ta toshe kunnuwanta da jifan da magauta suke mata, baisa tayi wasi da rukon d'an mijinta ba, bata tab'a nuna masa bambanci sa

kanin sa da ya'yan da ta haifa ba.

Ya'yan Alhaji Shitu Abubakar Sulaiman Tukur da kuma autarsu Bishira.

sun fara datawa, in da babban d'ansa Abubakar yafi mai da hankalin kan sana'ar mahaifin nasu, a duk in da Alhaji Shitu ya ke to zakaga Abubakar.

Wani

aminin Alhaji Shitu ya janyo ra'ayin sa kan sana'ar man fetur da shi ya ke yi, nan yakuma fad'awa tsundum cikin harkar man fetur, bai kuma sake harkar noman sa ba,

sai ma abin da ya karu.

dan yanzu yasabunta sana'ar ta hanyar amfani da hanyoyin zamani.

ya

nzu shi da kansa yake sarrafa duk abinda ya noma, akasin da da sai masaya sun shigo sun sayi kayansa, su su fita dashi suje su sarrafashi ta hanyoyi daban-daban.

Alhaji Shitu Fiya ya kafa manyan kamfanoni a manyan jahohin mu, wan da yasashi dole barin gari

nsa yakoma Lagos da zama, in da babban kamfanin sa na sarrafa auduga ke gurin.

gonakin da yake noman auduga shi ake kaisu kamfanin ake sarrafasu baya sayan auduga daga ko ina shi yake noma kayansa, yaku sarrafa shi ta hanyoyi daban-daban.

har wasu ma suzo

su siya.

duk kayan amfanin da yake nomawa ko wanne sai da ya bud'e masa kamfani na musamman a ko wata jahar dake cikin fad'in kasar nan.

Tuni Abubakar ya yi koyi ga mahaifinsa domin kuwa shima harkar noman yarike, baji ba gani, ba karamar karb'arsa noma

tayi ba, har mutane suna cewa makoyi zaifi gwani.

sosai ya maida hankali kan karatu kan fannin noma daya zab'a.

akasin 'yan'uwansa da kowa ke karantar wasu abubuwan daban.

lokacin da yakai munzalin aure takanas Alhaji Shitu yaje Yelwan Shandam yanimawa Abu

bakar auren 'yar d'an'uwan sa, wan da dama maganar had'in take aje dun da jimawa.

A Yelwa aka gudanar da duk shagulgulan bikin kana aka d'auko amarya Halima aka kawo ta Lagos.

Bayan wani lokaci kwasam Alhaji Shitu yakwanta jinya,

daya fahimci rayuwar sa

tazo karshe sai ya tarkaso kan takardun kadarorin sa, kana ya tara ya'yan sa da matarsa, ya ce Alhaji Abubakar ya sayi kamfanonin sa da gonakin sa, dan bazai siyarwa wani bare ba.

da arziki a garin wani gara a garin ka.

ya yi hakan ne badun komai ba sai du

n yadad'a karfafawa Alhaji Abubakar gwuiwa kan harkokin noma daya gaje sa.

Alhaji Shitu Fiya ya sa hannu cikin takardun mallakawa babban d'ansa Alhaji Abubakar Fiya gonaki da kuma kamfanoni, shikuma ya damka masa kud'ad'ensa.

Bayan rasuwar Alhaji Shitu ak

a rabawa magada makudan kud'i da sauran kadarorin da ya bari, irinsu gidaje da filaye da kuma gidajen man fetur, ban da gonaki da kuma kamfanoni da yanzu suke a matsayin mallakin Alhaji Abubakar Fiya.

Sosai Alhaji Abubakar yake gudanar da harkokin noman s

a, Allah kuma ya sanya masa albarka, arziki yacigaba da hab'aka.

Alhaji Abubakar ya kammala gina wani katafen gida unguwa guda, wan da girmamsa yakai girman wani karamin gari guda a cikin garin Lagos.

manya-manyan part-part ne da akalla zasu kai guda go

ma shabiyar ne a gidan, kuma ko wani side yana d'auke da get da parking lot mai d'aukar motoci uku, had'e da garden na musamman.

Katafaren katanga mai matukar girmar tsawo ke zagaye da gidan gaba d'aya, wan da saman ginin aka sanya wayoyin shokin domin

tsaro aka zagaye garun gaba d'aya da shi.

(A.A FIYA STREET)

sunan da unguwar take amsa wa ke nan.

Lokacin da zasu tare a gidan Alhaji Abubakar yakara aure ya auro Hajiya Karima, iyayen Umma Karima asalin 'yan Kano ne mazaunan Lagos.

lokacin yana da 'ya'

yan sa biyu maza da suka haifa da Hajiya Halima, Abdurrahim da Ajeemal.

Sai a lokacin Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suma sukayi aure, bai bar su sun tare a gidajen da sukaci gadon sa ba, ya ce duk suzo su zauna a gidan da ya gina, suka d'auko mahaifiyar

su suka koma da ita sabon gida,

in da ko wannensu ke zaune da matarsa a side guda guda.

Shekara biyar da dawowan su sabon gida Alhaji Abubakar yahad'u da Fatima a gurin taron bud'e kamfanin mahaifinta a birnin tarayya Abuja. mahaifin Fatima abokin kasuwan

cin Alhaji Abubakar ne, yana siyan kayan kamfanin sa yakai nasa kamfanin.

ya gayyaci Alhaji Abubakar ne shagalin bud'e sabon kamfanin sa, a nan yahad'u da y'arsa Fatima ya yaba da nutsuwa da kamalanta, ya nimi yardar mahaifinta atake kuwa ya aminta yakuma

yi masa alkawarin aura masa ita.

ba'a d'au lokaci ba akayi bikin.

Fatima ta fuskanci kalubale da dama a tun ranar da ta sanya kafarta cikin wannan gida.

do min kuwa Hajiya Halima da Hajiya Karima sun had'e kansu a tun ranar da suka sami labarin auren da mi

jin nasu zai kara.

wan da a da sam basa zaman dad'i sakaninsu, tun da sukaji zaiyi aure suka had'e kansu.

Cikin kankanin lokaci family'n ta soma hab'aka suka fara tara iyali.

Hajiya Halima uwargidan Alhaji Abubakar ya'yan ta biyar bayan maza biyun data h

aifa kafin sudawo sabon gida, takuma haihuwar mata uku, Farida Sumayya Amira.

Hajiya Karima ya'yan ta hud'u dukansu mata.

Bilkisu Saddika Rahama Nabila.

Hajiya Fatima kuwa har yanzu Allah baibata haihuwa ba, wan da hakan yazame mata abin gore a gurin abo

kan zamanta..

Alhaji Sulaiman shima 'ya'yan sa biyu da matarsa Hajiya Safiyya, Faisal da Miemie

Sai kuma Alhaji Tutur y'ay'an sa uku da matarsa Hajiya Nafisat, Shamsuddin Zaraddin Sahla

Family ya had'u cas da su

πŸ€—

.

Wannan shine takaitaccen labarin Fam

ily'n Alhaji Abubakar Fiya.

Mutane na kudai ku biyo ni yanzu wasan yasoma

πŸ€ΈπŸ€—

Mommyn Twins ce

🌺🌺

*FEERYAL*

🌺🌺



*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*____________________________________*

*

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S

✍

🏼

*

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*

πŸ‘‡πŸ»

https://bakandam

iya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*Bismillahirrahmanurrahim*

πŸ…Ώ

️

4

A b'angaren su Mommy tun da suka fita daga side in Daddy suka koma part in Mommy.

suke kitsa ta yadda zasuji da lamarin,

Umma Ka

rima ta gyara zama ta ce

"Hajiya Halima ga wani shawara, muje mu d'auki yarinyar nan mu nimi ruwa nan kusa ko na kwalbati ne mujefa ta ciki, ta koma gurin danginta,

kowa ma ya huta,

idan fa muka zuba ido muka barta daga karshe mu zata zame mana karfen kafa

, tazo ta shafe mana ya'ya ko jinya kad'ai tabarmu da shi ai ta cutar da mu, Fatima bata da asara tun da ba d'a take da shi a gidan nan ba,

sai dai tayi farin ciki da hakan, ina tunanin ma wani makircin take son kitsa mana, idan muka zuba ido kuwa mu zata

kaimu ta baro mu,

kinga ta dad'a mallake Alhaji gaba d'aya ta in da dolen mu mubar gidan nan, bakiji yafara fad'a da bakinsa tun yau ba."

Mommy ta jijina kai tare da fad'in

"Kwarai kuwa akwai abin da Fatima take son kitsawa wata kila bokanta ne yabata wa

ni sa'ar, dole aljanar nan ta bar gidan nan,

to amma yanzu ta ya zamuyi mu d'auke ta daga gidan nan, kinsan fa wannan Fatima mai taurin kan ba bari zatayi ba."

"Ai dama ko ta karfin tsiya sai ta bar gidan nan, yanzu dai shammatar ta zamuyi,

mu d'ake ta mu

fita da ita,

idan bamuyi sa'a ba sai mu nimi masu d'auko mana ita."

Mommy ta girgiza kai cike da gamtsuwa da maganar Umma Karima.

Kusan raba dare sukayi suna kitsa yadda zasuji da lamarin, Umma Karima ta koma side d'in ta, da shirin gobe zasu je su d'auk

e ta sufita da ita a gidan.

Washegari da sassafe Mommy da Umma Karima suka fito da shirinsu na d'auko Feeryal, dan sun san yau talata iwar haka Daddy yana masallaci yana sauraran wa'azi.

koda suka iso side d'in Aunty, ganin babu kowa cikin parlour kai tsa

ye bedroom d'in ta suka wuce.

batare da ko d'ard'ar ba dan sun lashi takwabin sai tabar gidan ko ta alin kaka, ko kwana bazata kuma yi a gidan nan ba.

Feeryal ce ita kad'ai a d'akin kwance a kan gado Aunty na cikin bathroom.

da sauri suka isa bakin gadon c

ikin kasa da murya Mommy ta ce

"Yi sauri mu d'auke ta kafin ta fito."

Umma Karima ta mika hanu zata d'auketa, wani irin dirrr taji tamkar jan wutar lantarki, da karfi ta janye hannunta jiki na rawa.

a d'an tsorace Mommy ta ce

"Mene ne kuma?."

batakai ga

rufe baki ba sukaga ta wani irin waro ido tana jujjuya shi, ya yin da kwayar idanunta suka fara sauya kaloli daban-daban.

kwan wutan cikin d'akin yashiga kawowa yana d'aukewa.

tare da sauya kaloli daban-daban kamar yadda kwayar idanunta suke sauyawa, izuwa

fari baki ja kore, da sauran kaloli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login